Showing 6001 words to 9000 words out of 59226 words
Chapter 3 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
kwance �
kasa, duk jikinsa yai kaca-kaca da raunika, jini na zuba yana
numfashi da kyar kamar ransa zai fita. A Sannan ne nadama
tazo masa, ya tabbatar da cewa abune mawuyaci ya sami
nasarar daukar takobin daraja a cikin wannan kogo,
musamman da ya dubi ragowar rijiyoyin da bai bude ba guda
?ari tara da casa 'in da tara.
Babban abin tsoroa gareshi shi ne, rashin sanin rijiyar da
takobin Saiful Lujara ke ciki, ko shakka babu kowacce rijiya ba
Za a rasa mugun abu ba a ciki. ldan ya bude wadda ya gamu da
abin da zai hallakashi a ciki shi ke nan burinsa ya yanke, kuma
dak wahalar da ya sha a baya ta zAma a banza.
Hantaru ya tuno da batun mahaifiyarsa Salimat wadda ba ita ce
ta haifeshi ba amma kuma yana kaunarta fiye da kowaa
rayuwarsa sai kuma gimbiya Larziya wadda a halin yanzu ya
kamu da tsananin begenta har ya amince ya sallama rayuwarsa
domin ya mallaketa. Hantaru ya tuno da batun cin amanar da
mahaifiyarsa ta jini ta yiwa sarki Kusaidu ita da boka Ardusa.
Lallai yana son ya koma birnin Kisra domin ya yiwa Farzira da
boka Ardusa hukunci bisa wannan cin amana, kuma ya sadu da
sarki Kusaidu wanda ke matukar kaunarsa a matsayin dan
cikinsa.
To amma ai Salimat ta gargadeshi akan kada ya taba lafiyar
Zarifa. Abu na biyu da ya fadowa Hantaru a rai shi ne, batun
alkawarin da ya ?aukarwa gimbiya Lazirina cewar duk wuya duk
rintsi ba za su rabu ba, kuma duk bukatar da tazo masa da ita
zai biya ma ta ita. Koda Hantaru yazo nan a tunaninsa sai
zuciyarsa ta karaya, ya fara tunanin hanyar da zai bi ya yi jinyar
jikinshi sannan ya ci gaba da bude ragowar rijiyoyin guda dari
tara da casa'in da tara har ya sami wadda takobin Saifal Lujara
ke ciki.
Hantaru ya tambayi kansa a cikin ziciyarsa ya ce, "Yanzu ta ya
ya zan reyu a cikin wannan kogon dutse babu ruwa babu
abinci?" Koda aiyana hakan, sai idanunsa suka kai kan sassan
jikin Macijiyar da ya kashe da kuma jinin jikinta da ya malala ya
cika kasan kogon wanda za a iya yin wanka a cikinsa.
Hantaru ta daga kansa sama ya yi arba da wasu tsirarun ciyayi
da kananan bishiyoyi da tsirai da suka tofo a cikin dutsen, sai
farin cilki ya kama shi, don ya fahimci cewa zai iya rayuwa a
cikin kogon izuwa tsawon kwanaki kadan.
Hantaru ta daga kansa sama ya yi arba da wasu tsirarun ciyayi
da kananan bishiyoyi da tsirai da suka tofo a cikin dutsen, sai
farin cilki ya kamna shi, don ya fahimci cewa zai iya rayuwa a
cikin kogon izuwa tsawon kwanaki kadan.
Hantaru ya fara da tunanin abinda ya kamata ya fara yi a yanzu
tun da gashi har jiri ya fara dibarsa sakamakon jinin da ke zuba
daga raunikan jikinsa Lallai ya zama dole ya yi tunanin abin da
zai ya tsaida jinin. Cikin matukar karfin hali ya mike tsaye yana
tangadi ya kama hawa kan duwatsun dake cikin kogon yana
dogarawa ya isa inda ya hango wata bishiya mai faffadan
ganye.
Sai da ya rage saura baifi taku uku be ya isa inda bishiyar take
sai ya zame ya fado kasa Haka dai ya daure ya sake tashi ya
hau kan ?utse. A karo na biyu ma bai nasara ba sai ya fado. A
karo na uku ne ya samu dama da kyar ya tsinko ganyen ya fado
kasa a matukar galabaice.
Da jen ciki yaje inda wata busasshiyar karamar bishiya take ya
karyo kirare a jikinta, ya sake dawowa da baya ya dauki
duwatsun wuta biyu ya dinga gogasu akan wadannan kirare har
wuta ta kama A haka ne ya dinga narka ganyan wannan bishiya
da ya karyo yana mannashi a jikin raunikan jikinsa.
Duk sa'adda ya manna ganyen sai yaji kamar ya kurrma ihu
saboda tsananin zafi da zogin da ke shigarsa. Har wani irin
gumi da haweyen azaba ne ke zubo masa.
Bayan ya gama sa maganin a jikin dukkanin raunikan jikinsa ne
ya kwanta ya huta tsawon rabin saa a sannan ne jini ya daina
zuba daga jikinsa ya dawo cikin haiyacinsa sosai. Nan take
Hantaru ya mike zaune ya tsinto sassan jikin Macijiyar nan ya
soka a jikin itace ya gasa, wato yai tsire. Haka ya ci gaba da
gasa naman Macijiyar har ya gasa mai yawa ya zamana Cewa
naman ya gasu sosai yadda zai kwana biyu bai lalace ba. Daga
wannan rana Hantaru ya ci gaba da rayuwaa cikin wannan kogo
yana mai ci gaba da jinyar jikinsa domin ba zai iya ci gaba da
bude Sauran rijiyoyin ba, ya zamana cewa bashi da abinci sai
wannan gasasshen naman Macijiyar, kuma bashi da ruwan sha
sai jininta da ya malala a kasa.
Har sai da jinin Macijiyar ya daskare ya ZAmana cewa sai ya
sareshi da takobi yake sha. Wannan gasashen naman kuwa sai
ya lalace ya rube har ma ya fara tsutsa, amma a hakan yake
cinsa domin ya rayu kada yunwa ta kashe shi. Hantaru dai bai
samu cikakkiyar lafiya ba sai bayan kwana goma sha uku.
ranar kwana na goma sha ukun ne Hantaru ya je gaban rijiya ta
biyu ya tsaya yana shawara da zuciyarsa akan ya budeta ko
kada ya bude. Da zarar ya kai hannu da nufin zai sare mukullin
rijiyar sai hannunsa ya kama karkarwa ya kasa saboda tsoron
kada ya budo abin da yafi na rijiyar farko balai wanda ka iya
zama sanadin ajalinsa gaba daya.
Sai da Hantaru ya jarraba hakan sai ya kasa sare mukulin, Nan
take Hantaru ya tuno da irin gwagwarmayar da ya sha a baya da
lamarin da ke gabansa na auren gimbiya Larziya da batun
komawa birnin Sin, sei kawai yi kanin tsoro ya kau dagA
zaciyaraa Nan take ya daga takobinsa sama yana kurma ihu ya
sare makullin.
Nen take murfin rijiyar ya fadi cen gefe daya. Bisa mamaki sei
baiga komai ba Hantaru ya sake rike takobinasa da kyau ya
gyara tsayuwa ya jiran yaga abinda da zai fito daga cikin rijiyar.
koda ya ji shiru sai ya matsa gaba da nufin ya wuce kan rijiya ta
uku itama ya budeta. Yana gifta wennan rijiya ta kwatsam sai ya
jiyo wani irin gurnani irin wanda bai ta6a ji ba da huci na
busowa. Cikin razAni Hantaru ya ja aa beya ya sake gyara
tsayuwa
Wani irin dogon hannun bil'adama ne lafcece ya fara lekowa
daga cikin rijiyar, sannan hannu na biyu ya leko. Daga can kuma
sai ga mutum ya taso sama a hankali gama mikewa gaba daya.
A sannAn ne Hantaru ya gA she maridi ne. Tun da Hantaru yazo
duniya bai taba ganin bil'adama mai tsananin tsawo da kauri ba
tamkar wannan maridi, domin ita dai rijiyar zurfinta ya kai kamu
dubu, amma gashi ta yiwa maridin kadan, tsugunnawa ma yai a
cikinta.
Fadinta ya kai kamu arba'in, amma da kyar maridin ya fito daga
cikinta, sai da ya muskuta kirjinsa sannan ya sami damar
fitowa. Hantaru ya karewa wannan maridi kallo daga sama har
kasa sai zuciyarsa ta karaya ya tabbatar da Cewa rayuwarsa na
tsakanin RAI DA MUTUWA. Kawai sai yaja da baya ya takure a
jikin bangon kogon, amman bai yar da takobinsa ba.
Maridin ya wangame katon bakinsa ya kurma wani ihu, wanda
ya haddasa girgizar kogon gaba ?aya har duwatsu kanana suka
rinka zubowa kasa. Karar ihun tasa Hantaru ya yarda takobinsa
ya rufe kunnuwansa har��ya tsugunna kasSa yana neman maboya,
domin ji ya yi kamar dodon kunnensa zai fado kasa.
Nan take maridin ya shako wuyan Hantaru ta baya da 'yan
yatsun hannunsa biyu ya ?aga sama tamkar ya dauki fara, sai
ga kafafun Hantaru na wutsi-wutsil, gaba daya jikinsa na reto.
Maridin ya tsaya yana tunanin irin kisan da ya kamata ya yiwa
Hantaru. Da farko sai ya dunkule hannu ya kai masa wawan
naushi a fuska. Duk da cewa yana ruke da wuyan Hantaru gam-
sai da Hantaru yi waf ya zunguri idon maridin da f
kafa, domin ya tabbatar da cewa idan maridin ya gabza masa
Wannan naushi, sai ya tatitse fatarsa tamkar an taka ayaba
akan dutse.
Tsokanewar idon da Hantaru ya yiwa maridin ne yasa ya
dimauce ya saki wuyan Hantaru ya fado kasa, amma huk da
haka sai da hannun Maridin ya nutse a cikin bangon kogon
dutsen tamkar ansa diga da guduma an buga a cikin bengo sai
gashi ya haddasa wawakeken rami ajikin bangon, amma bai ji
zafin komai ba a hannunsa tamkar ma takarda ya huda.
A fusece maridin ya juyo ya ?aga kafarsa pa y kawowa Hantaru
mugun taku. Cikin matukar zafin nama Hantaru ya goce ya bar
inda yake.
Sai ga kafar Maridin ta lume a cikin kasa iya kaurin gwiwarsa.
De ya zare kafarsa kuwa sai ga rami zururu wanda za a iya saka
mutum uku a ciki a binnesu. Nan fa aka fara guje guje
tsankanin Hantaru da Maridin a cikin kogon, yana kai masa
wawan naushi da bugu da hannu da kafa shi kuma yana
gOcewa da zallewa. Dak inda maridin ya gabza sai ya haddasa
mugun rami, walau bango ko kan kasa. Al'amarin da ya janyo
gaba dayan kogon ya kama rugujewa.
Sai ga kafar Maridin ta lume a cikin kasa iya kaurin gwiwarsa. De ya zare kafarsa kuwa sai ga rami zururu wanda za a iya saka mutum uku a ciki a binnesu. Nan fa aka fara guje guje tsankanin Hantaru da Maridin a cikin kogon, yana kai masa wawan naushi da bugu da hannu da kafa shi kuma yana gOcewa da zallewa. Dak inda maridin ya gabza sai ya haddasa mugun rami, walau bango ko kan kasa. Al'amarin da ya janyo gaba dayan kogon ya kama rugujewa ke nan, ya zamana cewa shi kansa maridin hankalinsa ya tashi, don haka sai ya koma gefe daya ya tsaya cak Yana hanki suka kara kallon- kallo tsakaninsa da Hantaru.
Babban abin da ya fi tayarwa da Hantaru hankali shi ne, kofar kogon ta rufe ruf, babu ta inda ma zai iya fita bare ya nemi hanyar gudu sakamakon rugujewar da kogon ya yi, manyan duwatsu suka rikito kasa.
Nan fa Hantaru ya aiyana a ransa cewa bashi da wata mafita face ya tunkari wannan maridi ya San dabarar da zai bullo masa ya kashe shi.
Dole ne ayi daya cikin biyu, ko shi maridin ya sami nasara ko shi Hantaru ya samu.
Kamar hadin baki sai maridin da Hantara suka wangame baki a lokaci guda kowannensu y kama kwarara ihu.
Abin da ya ?aurewa maridin kai kenan, domin a wannan karon ihun maridin bai ruda Hantaru ba, bare ya dimauce har ya toshe kunnuwansa.
Tun da wannan maridi ya wanzu a cikin wannan kogo tsawon daruruwan shekaru bai ta6a ihu ba ga duk abin da ya shigo abin ya iya jurewa ba. Kai bama mutum ba hatta aljan idan yana Wannan ihu nasa firgicewa suke, wasu su kama gudawa, Wasu ma sanadiyyar kurmancewarsu ke nAn.
Idan kuwa mutane ne ma take suke haukacewa, amma yanzu sai gashi Hantaru ya jure masifar ihun nasa harma yanA mai da martani da Dasa ihun.
A zahirin gaskiya Hantaru bu karamar juriya ya yi ba a wannan karon, domin gaba dayan jikinsa ya kama tsuma da karkarwa domin ji yake kamar an dura masa kwari masu yawa ba adadi a cikin kunnuwansa, suna tsinttsinka jijiyoyin kunnen, kuma yana jin kamar ana tsotse jinin jikinsa.
Bayan kowannensu ya yi ihu da kururuwa har gabadaya kogon ya gama rugujewa, duwatsun suma suka rikito kasa, al'amarin da ya janyo Hantaru ya sami sababbin raunika ke nan a sassan jikinsa, in banda ma yana gocewa da tuni manyan duwatsu sun danneshi. Shi kansa Hantaru ya san cewa tsananin sa'a ne kawai ya ceceshi a cikin wannan kogo, sa'adda yake rugujewar amma ba zafin namansa ba.
Koda gama rugujewar kogon sai Maridin ya falfalo da gudu yana take duwatsu suna rumurmushewa, ya yiwo kan Hantaru gadan- gadan. Koda Hantaru ya ga mutuwa ta durfafoshi sai shima ya yi ta maza ya ruga izuwa kan maridin Shima yana mai ci gaba da kwarara ihu shima, maridin yana nasa ihun, kowannensu tafe yake cikin mugun nufi, kai da gani ka san cewa idan akayi wannan gamo dole ne mutuwa ta sami rabonta Sai da ya rage bafisaura taku daya ba A tsakaninsu ba sai Hantaru ya yi sufa a kasa tamkar akan kankara mai santsi yake ya shiga karkashin Maridin ya takarkare iya karfinsa ya gabza masa naushi da hannaye biyu a marainansa.
Take maridin ya yi suman tsaye ya kame kamar ya zamo gunki. Cikin zafin nama Hantaru ya mike zumbur ta bayan maridin yasa guiwar hannunsa ya doki tsakiyar hannun maridin na hagu. Take hannun ya karye ya yi kara kas! Maridin ya kurma ihu ya juyo a fusace ya kawowa Hantaru mangari da daya hannun nasa. Cikin sa'a kuwa ya sami Hantaru a kirji. Karfin mangarin ne yasa Hantaru yai sama ya fado kasa kan dutse ya baje a sume.
Maridin ya yunkura da kyar yana tafiyar tatata kamar sabon dan kaciya a lokacin da karyayyen hannunsa ke gilu-gilu kamar zai fadi kasa ya nufi inda Hantaru ke kwance a sume.
Nufinsa kawai yaje ya tallafo kan Hantaru ya yi masa rotse a ka, wato ya dagwargwaza fuskar Hantaru. Har Maridin ya isa kan Hantaru ya tsaya, Hantaru bai farfado ba. Nan take Maridin yasa hannunsa ya tallafo kan Hantaru da nufin ya naushi fuskar da dukkan karfinsa.
A dai-dai wanann lokaci ne Hantaru ya farfado, idanunsa suka bude. Koda ya ga maridin ya daga hannunsa lafiyayyen zai nausheshi. sai ya yunkura cikin mugun zafin nama ya kamo kary?yyen hannun ya fincika. Saboda tsananin zafi da zogin da maridin yaji bai san sa'adda ya saki ftsari ba.
Kafin ya yi wani yunkuri na cutar da Hantaru tuni Hantaru ya sake kamo daya Iafiyayyen hannun shima ya gabza mAsa naushi da guiwar hannunsa. Take hannun ya karye ya yi kara kamar na farko. Maridin ya fadi kasa da ruf da ciki. Duk da haka Hantaru bai kyaleshi ba sai da ya kama kafafunsa duka biyun da karfin tsiya suma ya kakkaryasu daya bayan daya.
ihun da maridin ya yi a lokacin da Hantaru ke karya masa kafafunsa ya ninka wanda ya yi da furko sau goma, domin gaba daya halittun da ke dajin sai da suka firgice suka kama sauya sheka. Sauran wadunnan rijiyoyi kimanin guda dari da casa in da ya'ya sai da murafensu suka bude, gaba daya a lokaci guda.
Abinda ya fara yin fitar burgu daga cikin rijiyoyin shi ne, takobin Saiful Lujara. Wata irin takobi ce ta musamman wacce aka kerata da lu'u lu'u sai sheki da walwali take tana kashe idanu. Nan take haskenta ya haskake kogon gaba daya. Da wani irin mugun karfin gudu takobin ta taso sama. Koda Hantaru ya yi arba da takobin sai ya yi wuf ya taka bayan maridin ya daka tsalle sama yabi takobin tamkar an harbashi daga cikin kwari. A can saman ya kamo murikin takobin. Koda ya sunkuyo da kansa kas a lokacin da yake durowa sai ya yi arba da mugayen abubuwan da ke fitowa daga cikin rijiyoyin, sai hankalinsa ya dugnzunma ainun, domin ya san cewa irinsa ari ma ba za su iya hallaka abubuwan ba.
Zan ci gaba.
Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp.
MAZAN JIYA
Littafi na biyu 2
Part D
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
Mugayen dabbobin daji ne suka rinka fitar burgu daga cikin rijiyoyin, mASu yawan tsiya ba iyaka. Daga manyan zakuna, irin wanda ido bai taba gani ba, sai manyan Kuraye da Damisoshi, kuma fitowa suke tayi daga cikin rijiyar kamar ba za su kare ba. Rijiyar da takobin Saiful Lujaran ta fito ne kadai wani abin bai sake fitowa daga cikinta ba. Tun a saman Hantaru ya kara rike takobin Saifal Lujara da hannayensa biyu gam-gam. Ai kuwa yana dira a cikin kogon azababben yaki ya kacame tsakaninsa da miyagun dabbobin, suka yanyameshi suna kai masa cizo da yakushi, shi kuwa ya dinga ragargazarsu da takobin Saiful Lujara, sai dai ka ga a lokaci guda ya dara dabbobi uku ko hudu ya tsargesu gida biyu sun zube kasa matattu.
In banda cewar Hantaru mutum ne mai matukar zafin nama yana kaiwa dabbobin sara ta ko ina, wato gabas da yamma, kuda da arewa, sama da kasa, da tuni sun tumurmusheshi. Duk da zafin naman nasa SAi da suka rinka kartar jikinsa suna cizonsa amma saboda karfin sihiri kaifin faratansu dana hakoran nasu baya tasiri a jikinsa, amma kuma sun kumbura masa jiki sun taru masa jim.
Babban abin da ya fi tayar Masa da hankali shi ne, rashin karewar dabbobin, domin yana kashe su ne wasu na kara fitowa daga cikin rijiyoyin tamkara sannan ake haihuwarsu. Kuma abin da ya lura da shi shi ne, babu kokarin da dabbobin ke yi face su kwace takobin Saifal Lujara daga hannunsa.
Hantaru ya yi nazari ya fahimci cewa idan da aka Sami koda rabin sa'a ne a na wannan gumurza lallai zai gaji har wadannan dabbobi su kaishi kas su turmusheshi, idon kuwa suka turmusheshi Lallai za ta kai cewa sun rabashi da takobin Saiful Lujara, Sannan su hallakashi. Koda Hantaru ya fahimci haka sai ya fara tunanin mafita.
Abin da ya fara fado masa a rai shi ne, masu iya magana sun ce "Gudu ba tsoro bane idan masifa ta kai masifa " Koda gama aiyna hakan, sai Hantaru ya shammaci dabbobin nan ya daka wawan tsalle Sama ya yi fitar burgu daga cikin kogon, tun da dai saman kogon ya yaye sakamakon rugujewar da yayi.
Ai kuwa suma dabbobin sai suka daka tsalle sama gaba dayansu suka bishi a sama. Hantaru na dira a wajen kogon bisa turba sai ya fara falfala matsanaicin gudu. Nan fa aka kasa tsere tsakaninsa da dabbobin. Gudun da Hantaru ke yi ya wuce gaban misali, domin gudu ne na sihiri, Sai dai ka ga yana gifta bishiyoyin dajin giftawar tauraruwa mai wutsiya. Abun takaici da ya waigo sai ya ga wadannan dabbobi na daf da shi kamar marabarsu bai wuce kamu daya ba. Inda zai tsaya da taku daya zasu iya tsalle su cimmesa, Abin da Hantaru bai sani ba shine gudun da dabbobin suke yi shima na sihirine.
Sirrin shine duk halittar da ke cikin kogon da takobin Saiful Lujara take an sihirceta, yadda ba zasu taba bari kowa ya mallaki takobin ba sai sun tsare takobin don kar tabar hannunsu.
Inda ace Hantaru ya yar da takobin dabbobin ba zasu biyoshi ba. Haka dai Hantaru ya cigaba da matsanaicin gudu, dabbobin na biye da shi daf da daf suna gurnani da kartar kasa kamar sa ci babu. shi kansa Hantaru duk da cewar yana da dakakiyar zuciya a