Showing 12001 words to 15000 words out of 59226 words
Chapter 5 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
sakamakon hakan Salimat za ta
kashe kanta.
ldan hakan ta faru za ka tsani kanka kuma za ka tsani komai a
duniya ya zamana cewa soyayyarka da gimbiya Larziya ta
rushe, wato dai ba za ku yi ure ba.
Ina mai shawartarka da ka mance da batun Larziya ka zauna
anan tare dani mu yi aure mu more rayuwarmu cakin dadi da
kwanciyar hankali. Ka sani cewa na fi Larziya kyawu, asali da
matsayi a duniya, kuma duk abin da kake nema a rayuwarka
walau dukiya ko daukaka in dai kana tare da ni tamkar ka
samesSu ne.
Sa'adda Hayatul Lumhas tazo nan a zancenta sai Hantaru ya yi
murmushi gami da ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ya ke
ma'abociyar kyawu, matsayi da daukaka, kiyi sani cewa babu
ruwan S0 da kyawu ko matsayi, don haka martabar gimbiya
Larziya a cikin zuciyata ta ninka taki sau dubu.
Larziya ce mace ta farko da ta fara samun gurbia cikin zuciyata
kuma ita ce za ta zamo ta karshe domin ba zan taba son wata
ba face itan.
Duk bayanin da ki ka yi na gamsu da shi, amma ban yi imani da
shi ba domin na yarda da cewa zan iya sauya kowacce irin
kaddara da ta sameni anan gaba muddin tsafi bai daina tasiri a
doron kasa ba.
Ki sani cewa idan suna nake nema a duniya na gama samunsa
tun da gashi na dauko takobin Saiful Lujara a cikin kogon
Mazabatul Dulshal aikin da ya gagari dubunnan sadaukai a
tsawon dubunnan shekaru da suka gabata.
Idan dukiya nake so ko mulki duk zan iya samunsu da karfin
Wannan takobi da na dauko saboda haka ni yanzu baki da wani
abu wanda zai janyo hankalina har yasa har na manta da
masoyiyata abar begena dare da rana wato gimbiya Larziya.
Abin da nake bukata daga gareki kawai shi ne ki fitar dani daga
cikin wannan gida naki ki ?orani akan hanyar da ZAn nufi birnin
Darul Mahabul domin naje na ida sauran burin rayuwata.
"Ya yin da Hantaru yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubowa
gimbiya Hayatul Lumhas tayi shiru bata ce komai ba tana mai
sunkui da kanta kas saboda tsananin bakin ciki da takaici. Daga
can sai ta dago kai ta dubi Hantaru ta ce,
"Ya kai abin kaunata kayi sani cewa ina binka bashin kubutar da
rayuwarka da nayi daga hannun wadannan muggan aljanu na
cikin kogon Mazubatul Dulshul masu tsaron takobin Saiful
Lujara. Baka da wani abu wanda za ka iya biyana wannan bashi
domin kai fakiri ne a kaina koda kuwa nan gaba ka mallaki duk
kasashen duniya sun zamo karkashin mulkinka saboda a cikin
wannan gida nawa akwai tsubin dukiya wacce tafi duk dukiyar
duniya yawa. Ina son ka biyani bashin da abu daya
Hantaru ya ce, "Mene ne abin da kike so na biya ki da shi?".
Maimakon Hayatul Lumihas ta ce wani abu sai taje ta dauko
wani hoto da aka sasssakashi cikin siffar gunki ta mikawa
Hantaru. Da ya karbi gunkin ya dubeshi da kyau sai ya ga ashe
kamannin gimbiya Hayatul Lumhas ne sak tamkar an tsaga
kara. Hantaru ya sake dago kai ya ?ubi Hayatul Lumhas ya ce,
"Me zan yi da wannan gunki mai siffar fuskarki?".
Hayatul Lumhas ta ce, "Ina son komai wuya komai gumu, ka kai
wannan gunki izuwa birnin Hindu ka sada shi ga mahaifiyata
sarauniya Mashlima wacce a halin yanzu ita ce ta gaji karagar
mahaifina.
Ka bata Labarina da irin daular da nake ciki amma ka sanar da
ita cewa burina bai cika ba wanda shi ne burin mijinta, don haka
har abada ba zamu sadu ba kuma nima ajalina yana daf kamar
yadda na mahaifina ya kasance. ldan kayi haka ka biyani bashin
da nake binka, idan kuma baka aikata hakan ba kaci amanata".
Koda gama fadin hakan sai Hayatul Lumhas ta juyawa Hantaru
baya ta ce, "Ka mike ka ci gaba da tafiya izuwa bangaren gabas
za ka riski wata kofa a gabanka da ka shiga cikinta za ka tsinci
kanka a wajen gidan nan inda za ka iske doki da guzuri wanda
na tanadar maka, amma ka sani cewa daga yanzu har izuvwa
sa'adda za ka isa kofar birnin Darul Mahabul kana da damar
sauya ra'ayi na dawowa gareni, kofar gidana a bude take gareka
kuma ina mai marhaban da sake karbarka. ldan kuwa baka
dawo ba shi ke nan har abada ba zamu sake saduwa ba domin
ni da kai duk ajalinmu na kusa."
Koda gama jin wannan batu sai Hantaru ya nufi gabas yai ta
tafiya a cikin harabar gidan ko Waiwayowa bai yi ba, sai da ya
ga ya yi nisa da Inda ya bar Hayatul Lumhas a sannan ne ya
tuno da irin shakuwar da ya yi da ita a cikin kwanaki goma sha
hudun da kuma irin dawainiyar da tayi da shi na jinyarsa har ya
sami lafiya. Hantaru ya tuno da irin tsananin kyawun Hayatul
Lumhas da kuma irin daular da take ciki da matsayinta na 'yar
sarkin birnin Hindu, birnin da a wannan ZAmani duk duniya
babu kamarsa a karfin mulki. Nan take Hantaru yaji nadama
tazo masa, kuma ya kamu da tsananin tausayin gimbiya
Hayatul Lumhas, bai san sa'adda hawaye ya zubo masa ba,
kawai sai ya waigo baya bisa tunanin ko Zai hangoi Hayatul
Lumhas.Yana waigowa sai ya ganta a tsaye daf da shi idanunta
sun yi sharkaf da hawaye.
Nan take Hantaru ya rungume Hayatul Lumhas ya fashe da
matsanaicin kuka ita kuwa sai ta bushe da dariyar farin ciki bisa
ganin cewa zuciyarsa ta karaya ya fasa tafiyar ya barta. Bisa
mamaki sai Hayatul Lumhas taji Hantaru ya yi wuf ya tureta
daga cikin jikinsa kawai sai ya dubeta ya ce, "Ki gafarceni yake
tauraruwar zamani, hakika ke abar tunawace a zuciyata har
abada, kuma lallai sai na biyaki bashin da kike bina ka fin cikar
ajali, amma ki sani cewa har abada ba za ki mallakeni ba nima
ba zan mallakeki ba domin ba a yimu domin juna ba Koda gama
fadin hakan sai Hantaru ya juya ya ci gaba da tafiya abinsa.
Kawai sai yaji Hayatul Lumhas ta fashe da matsanancin kuka
wanda ya kara dugunzuma hankalinsa kuma ya kamu da
tsananin tausayinta har yaji kamar ya hakura da tafiyar ya koma
gareta amma sai ya kanne ya ci gaba da tafiyar, yana tafe yana
zubar da hawaye har ya yi nisa sosai ya daina jiyo sautin kukan
Hayatul Lumhas a sannan ne ya iso bakin kofar gidan. (Ta tabbata dai hayatul lumhas tawace, Ni mai typing Abu Saleh AlQuyraemey).
Da isarsa daf da kofar sai ya ga kofar ta bude kanta, kawai sai ya ga wani ingarman farin doki a tsaye shi kadai yana harbin iska ga jakar guzuri daure a kansa. Cikin murna Hantaru ya ruga izuwa ga dokin yai tsalle ya haye kansa sannan ya sakar masa linzami ya sukwaneshi da gudu izuwa cikin daji.
Daga wannan rana Hantaru ya ci gaba da tafiya a cikin daji ya
kwana nan ya tashi can har tsawon kwanaki masu yawa amma
mamaki ko sau daya bai gamu da wani mugun abu ba kuma bai
sha wahalar komai ba.
Wata rana da yammaci yana cikin tafiya kawai sai ya hango
kofar birnin Darul Mahabul a gabansa nesa kadan. Al'amarin da
ya matukar bashi mamaki ke nan, domin da can tafiyar da yake
yi kansa a juye yake bai ma san inda ya nufa ba kawai inda ya
ga dokinsa ya yi nan yake bi baya sauya masa akala. Koda
Hantaru ya hango kofar birnin Darul Mahabul sai ya cika da
tsananin farin ciki don haka sai ya sakarwa dokinsa kaimi ya
zabureshi da gudu.
Da isarsa bakin kofar birnin sai ya ci gaba da gudu kuma ya rufe
fuskarsa da rawani, sannan ya boye takobin Saiful Lujara a cikin
jakar guzurinsa bai zame ko ina ba sai gidan Shurem.
Da isar Hantaru kofar gidan sai ya iske Shaulat matar Shurem
ita kadai tana baiwa dokin mijinta ruwa. Koda Shaulat ta ga
mutum a gabanta bisa doki kuma fuskarsa a rufe sai ta razana
ta yunkura za ta ruga izuwa cikin gida. Cikin sauri Hantaru ya
kira sunanta yana mai cewa, "Ya ke kakata yau kuma jikanki
kike gudu?"
Koda Shaulat taji muryar Hantaru sai tayi jifa da bokitin
hannunta ta ruga gareshi. Hantaru ya sauko daga kan dokinsa
da sauri suka rungume juna tana dariyar farin ciki, daga can
kuma sai yaji ta fashe da kuka. Al'amarin da ya matukar
firgitashi ke nan ya janye jikinsa daga cikin nata da sauri suka
fuskanci juna a lokacin da ya rike kafadunta ya ce, "Ya ke kakata
ina dalilin wannan kuka naki?" Shaulat tayi ajiyar zuciya ta ce,
"Ya kai Hantaru kayi sani cewe bayan taf?yarku izuwa kogon
Mazubatul Dulshal kai da sadauki Rabbasu don dauko takobin
Saiful Lujara mutane da yawa sun rasa rayukansu sakamakon
mutuwar mahaifin Rabbasu da kuma mahaifin mijina, wato
boka Sulbaini domin mutuwar tasu ta kawo rudani da tashin
hankali a tsakanin kabilarmu da kabilar su Rabbasu har tasa
muka dinga yakin sunkuru muna kashe juna sai da kyar sarki ya
tsaida wannan yaki.
Ka sani cewa mijina ya mutu a wannan yak?, yanzu bani da
kowa face mahaifiyarka Salimat da kuma kai a wannan birni na
Darul Mahabul. Koda jin wannan batu sai Hantaru yaji wani irin
mugun bakin ciki ya rufeshi, bai san sa'adda ya fashe da
matsanaicin kuka ba. A dai-dai wannan lokaci ne ya hango
Salimat ta fito daga cikin gida ta nufo inda suke hawaye na
zuba a idanunta. Cikin hanzari Hantaru ya ruga gareta suka
rungume juna suka kara fashewa da kukan murna bisa sake
saduwa.
Nan dai suka dunguma su ukun suka shiga cikin gidan. Bayan
Hantaru ya huta kuma ya ci abinci sai Salimat da Shaulat suka
rakashi izuwa inda kabarin Shurem yake ya durkusa a gaban
kabarin yana kuka, sannan ya yi masa addu'oi irin nasu na
kafirai da suka saba yi.
Ba wani abu bane yasa Hantaru yake wannan kuka ba face
gashi ya dawo daga kogon Mazutbatul Dulshal cikin nasarar
?auko takobin Saiful Lujara amma Shurem bai gani ba. Ya sani
cewa a rayuwar Shurem wannan ce rana mafi farin ciki a
rayuwarsa, wato ranar da zuri'arsu ta ci gasar da ta kasa kar6o
kambunta a wajen zuri'ar su Rabbasu tsawon shekaru.
Sa'adda Hantaru ya gama 'yan addu'oinsa da koke-kokensa a
kabarin Shurem sai Salimat ta tasheshi tsaye suka koma cikin
daki suka zauna a sannan ne ya bude jakar guzurinsa ya ?anko
takobin Saiful Lujara ya nuna musu sannan ya kwashe labarin
tafiyarsa kaf ya zaiyane musu tun daga lokacin suka fara shan
wahala shi da sadauki Rabbasu da kuma sauran wahalar da ya
sha har kawo izuwa lokacin da Rabbasu ya karaya ya kashe
kanSa ya isa cikin kogon Mazubatul Dulshur da irin
gwagwarmayar da ya yi da masifun ciki har da yadda ya dauko
takobin ya gudu don tsira da rayuwarsa har ya fadi kasa
sumamme ya farfado a gidan gimbiya Hayatul Lumhas da duk
abin da ya faru tsakaninsa da ita har suka rabu ya taho birnin
Darul Mahabul.
Koda gama wannan labari sai Salimat da Shaulat suka cika da
tsananin al'ajabi kuma suka jinjinawa Hantaru domin sun san
cewa ya yi gagrumar bajinta wacce abu ne mawuyaci nan gaba
a sami wanda ma zai iya kwatanta irinta.
Haka dai suka ci gaba da hira har dare ya raba sosai. Hantaru
da Shaulat suka kwanta suka kama barci amma ita Salimat sai
ta kasa kwanciya kuma idanunta suka bushe ya zamana cewa
ko kadan bata jin barci. Ba komai ne ya haddasa ma ta hakan
ba face tsananin fargaba bisa labarin da Hantaru ya baiyana ma
ta dangane da abubuwan da gimbiya Hayatul Lumhas ta
zaiyana masa akan ababuwan da za su same shi anan gaba.
Tun sa'adda Hantaru ya tafi neman takobin Saiful Lujara ya
zamana cewa kullum sai Salimat...
Tun sa'adda Hantaru ya tafi neman takobin Saiful Lujara ya zamana cewa kullum sai Salimat tayi mugun mafarki akansa kuma abin da ake nuna ma ta a cikin mafarki shine,
Hantaru ya rusa ma ta dukkan farin cikin rayuwarta. Koda ta tuna wadannan mafaekai da wannan labari da yazo ma ta da shi sai ta tabbatar da cewa Lallai mafarkin nata zai iya zama gaskiya.
Bisa Wannan dalili ne Salimat ta kasa barci ta dinga sakar zuci bata san sa'adda ta fara kuka ba. Sautin kukan nata ne ya sa Haataru ya farka daga barci. Koda bude idanunsa ya ga Salimat a zaune tana kuka sai ya mike zumbur cikin razana yazo gareta ya rungumeta yana cewa ya ke, "Ummina kiyi sani cewa har abada wannan mafarki naki ba zai tabe Zama gaskiya ba, domin babu wani aba da ya fiki matsayi da muhimmanci a wajena, na rantse da darajar kaunar da ke takanina da ke da mijinki har abada ba zan taba juya mikk baya ba.
Na yi imani cewa babu abin da zai gagari tsafi saboda haka koda mafarkinki zai zama kaddara a garemu to ni zan sauya wannan kaddar da karfin tsafi, bayan mun karbo kambun gasa wajan sarki an daura aurena da gimbiya Larziya saboda haka inason gobe da sassafe ke da Shaulat ku rakani fada domin na gabatar da takobin Saiful Lujara ga sarki a gaban jama'ar gari domin burin zuri'armu ya cika nima nawa burin ya tabbata.
Sa'adda Hantaru ya zo nAn a jawabinsa sai Salimat taji hankalinta ya dan kwanta, don haka sai ta share hawayen idanunta ta dora kanta bisa kirjin Hantaru shi kuwa ya ci gaba da rera waka, A cikin sanyin murya yana karanto baitoci masu kwantar da zuciya da sanyayata.
A haka barci ya sace Salimat bata sani ba, Har gari ya waye Salimat na barci akan kirjin Hantaru bai yarda ya motsa jikinsa ba don kada ta farka daga barcin kuma bai daina rera wannan wake ba saboda tsananin biyayya da son ganin kwanciyar hankalinta. Hudowar hasken rana ne yasa Salimat ta farka daga barci, koda ta ga kanta bisa kirjin Hantaru kuma ta ga idanunsa wasai babu alamar ya yi barci sai ta cika da tsananin damuwa ta ce, "Ya kai ?ana ya ya aka yi nayi barci akan kirjinka amma baka tasheni ba, domin kaima ka kwanta kayi barcin kuma mene ne ya hanaka kaima kayi barcin?".
TYPING BY : SHURAIH 99%
Sa'adda Hantaru yaji wadannan tambayoyi sai ya yi mumushi ya ce, "Ai kwanciyar hankalinki shi ne nawa, inda baki samu Wannan barci ba da sai na kwana ina kuka da bakin ciki."
Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ga jama'ar zuri'arsu na ta shigowa cikin gidan da murna suna yiwa Hantaru barka da sauka tamkar an yanke musu dukkan bakin cikin rayuwa. Al'amarin da ya ?aurewa Hantaru da Salimat kai ke nan suka cika da mamaki bisa yadda jama'a suka san cewa ya dawo harma suke zuwa yi masa barka da sauka.
Abin da basu sani ba shi ne, tun a yammacin Jiyan wata kuyangar gidan ta watsa labari. Nan da nan gidan Shurem ya cika ya batse da jama'arsu tamkar ana wani gagarumin shagalin biki a garin.
Bayan jama'a sun gama taruwa sai aka cabawa Hantaru ado sannan aka rakashi izuwa fada ana tafe ana kade-kade da raye-raye gami da bushe bushe.
Nan da nan birnin gaba ?aya ya dauka cewar ga Hantaru can ya dawo gida. Nan fa jama'a suka yi tururuwa izuwa fada domin su ganewa idanunsu shin Hantaru ya samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara ne ko kuwa bai samu ba, sannan suna son su ji labarin Sadauki Rabbasu yana raye ne ko kuwa ya hallaka a cikin wannan tafiya.
Lokacin da su Hantaru da sauran jama'ar gari suka isa fada sai suka iske fadar a cike makil babu masakar tsinke. Sarki na zaune bisa karagar mulki ya ci ado na kasaita sai murmushi yake ya kasa rufe baki dalili kuwa shi ne tuni bokaye sun bashi labarin cewa Hantaru ya dauko takobin Saiful Lujara. A hannun daman sarki gimbiya Larziya ce a Zaune ta caba ado na ban al'ajabi sai sheki da walwali take tamkar wata dan daren goma sha biyu, kuma itama tana ta yin murmushi irin wanda ka iya zauta duk wani baligi da ya kuskura ya kura ma ta idanu.
Da shigowar Hantaru cikin fadar tare da jama'arsu sai Dakaru suka tsaida kowa daga baya, Hantaru kadai aka bari ya nufi inda karagar sarki take. Tun daga nesa ya hada idanu da masoyiyarsa gimbiya Larziya ya ga tana yi masa murmushi tamkar ta mike ta rugo gareshi amma sai ta kanne. Shima Hantaru haka ya rinka ji a cikin ransa amma sai ya jure ya rinka maida mata da martanin murmushin. Sa'adda Hantaru ya iso kusa da karagar sarki sai ya zube kasa ya kwashi gaisuwa, fadawa suka karbi gaisuwarsu sannan sarki ya dubeshi ya ce,
"Ya kai NAMIJIN DUNIYA, ina labarin abokin tafiyarka Rabbasu, kuma me ka zo mana da shi?" Sa'adda Hantaru yaji wannan tambaya sai jikinsa yai sanyi, nan take idanunsa suka ciko da kwalla. Ba tare da 6oye komai ba Hantaru ya kwashe labarin tafiyarsu tun daga farko har karshe ya zaiyane musu.
Yana gama bada labarin sai ya ga ashe gaba dayan jama'ar da ke fadar kuka suke yi saboda tausayi a lokacin da shima kansa yana ta zubda hawaye. Nan take Hantaru ta fiddo takobin Saiful Lujara daga cikin rigarsa ya zareta daga cikin kufenta. Koda zare takobin sai haskenta ya cika fadar gaba ?aya, ta rinka kashewa kowa idanu.
Gaba dayan bokayen garin da ke tsaye kusa da sarki sai sukayi sujjada ga takobin suka hada baki suka ce, "Daukaka da jinjina sun tabbata ga jarumin jarumai, gwarzon shekara, sadauki Hantaru mijin gimbiya Larziya". Koda jin wannan batu sai fadar gaba daya ta rude da shewa, kida da wake-wake. Sai da sarki ya daga sandar mulkinsa sannan aka yi tsit! Nan take sarki ya mife tsaye da kansa ya kirawo Halifan baban Rabbasu ya karfi kambun gasa daga hannunsa sannan ya taka yaje gaban Hantaru ya nuna nasa kanbun ya ce, "Gobe wannan kambu zai dawo jannunku ku zuri'ar Shurem," Koda jin haka sai fadar ta sake ru?ewa da shewa.
Sarki ya sake daga kwagirinsa a karo na biyu aka yi tsit, tamkar mutuwa ta gifta, sannan y ce,"Hakika sadauki Hantaru ya bar abin tarihi kuma abin tunkaho a wannan birni namu, wanda zamu ci gaba da tutiya gami da alfhari da shi a dukkan sauran kasashen duniya saboda shi ne jarumin da zai auri 'yata gobe da yamma anan fadata.
Tabbas Hantaru ye kawo karshen gardama da gaba a tsakanin zuri'ar makera da ta mafarauta da a wannan an gari nawA mai albarka saboda haka A yau na rushe wannan tsohuwar al'ada ta gasar tseren gudun barewa".
Koda gama wannan jawabi sai Sarki yaje ya kama hannun 'yarsa gimbiya Larziya ya ja ta suka shige izuwa cikin gidan sarauta t?na waigen Hantaru tamkar ta kufce ta rugo gareshi, shima Hantaru sai yaji kamar ya ruga ya rukota amma da ya tuna da cewa gobe ne za a daura aurenta da shi sai hankalinsa ya kwanta ya bita