Showing 42001 words to 45000 words out of 59226 words
Chapter 15 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
ajiye a bisa tebur bisa faratin yayan itatuwa ta soka wa kanta a ciki, nan take ta sulale kasa matacciya.
Nan fa ango ya dimauce har bai san sa'adda ya fice waje da gudu ba.
Lokacin da labari ya iski sarki cewa ai Gimbiya Rashmin ta kasshe kanta sai ya kmau da tsananin bakin ciki, nan take ya hadiyi zuciya shima ya mutu.
Shiko aljani Maraful Dauwas sai da ya shekara dari biyu a cikin wannan kurkukun a tsare, ba a kuma sake shi ba sai bayan da mahaifiyar Gimbiya Rashmin ta mutu, aka nada sabon sarki a garin.
Koda aka saki Aljani Maraful Dauwas daga kurkuku aai yaji gabadaya ya tsani kansa kuma ya tsani duniyar, dama tun yana kurkukun labari ya riske shi cewa Gimbiya Rashmin ta kashe kanta, dan haka shim aai ya fara kokarin kashe kan nasa, ammab sai dakarun dake tsaronsa suka sa ido soaai a kansa dare da rana bisa dole ya hakura da batun kashe kansa.
Lokacin da Aljani Maraful Dauwas ya fice daga kurkukun kuma yajinya tsani duniya da duk abinda ke cikinta sai ya yanke shawarar ya kai kansa inda b zai sake ganin mutane ko aljanu ba, domin ya karasa sauran rayuwarsa ta duniya, bisa wannan dalili ne ya tafi can karshen birnin sin ya shiga cikin kogon darul ikisina ya rufe kansa a ciki har zuwa tsawon shekaru dubu biyu da dari biyu bai fito ba balle yaga koda hasken rana, dama can shi kogon darul ikisina kogo ne da yayi kaurin suna a duniya kuma babu mai iya shigarsa face wand ya san wasu dalasuman sihiri wadanda na musamman ne guda bakwai, sai mutum ya karanta wadannan dalasuman n tsafi a fili sannan kofar kogon zata bude, idan kuwa yayi kuskure a wajen karanta dalasiman sau daya to shikenan har abada kofar ba zata bude ba, koda kuwa zai sake karantawa sau dubu.
Shi kansa Aljani Maraful Dauwas ya gaji wannan dalasuman ne a wajen kakansa na dari da ashirin da biyu, kuma ba a rubuce suke ba a cikin kundi ko littafi, akan cinyarsa ta hagu aka rubuta su da wata wuka ta sihiri yadda har abada babu wani abu da zai iya goge su koda kuwa wuta ce.
Lokacin da boka Muzafar Ibn Mauzar ya zo nan a labarinsa sai sarki Lafaru ya vika da tsananin mamaki kuma hankalinsa ya dugunzuma sadoda tunanin gagarumin aikin dake gabansa da daharinsa gamj da wahalar dake cikinsa yafi dukkanin dadin da zai biyo baya. Bayan sarki Lafaru yayi dan nazari sai ya dubi boka Muzafar cikin nutsuwa ya ce Ya kai wannan babban bako, ina da tambayoyi kwarara a gareka; tambaya ta farko ita ce shin kaima kana da wadannan dalasumai na tsafi ne guda bakwai wadanda za'a karantasu kofar kogon darul ikisina ta bude ne, tambaya ta biyu ta yaya kake ganin cewa aljanu Maraful Dauwas zai amince ya fito daga cikin kogon darul ikisina har yaje fadar sarki Nashmir ya sato mana gimbiya Ramlatus siyam alhalin ya tsani duniya da duk abinda ke cikinta, tambaya ta uku ita ce me yasa aljani Maraful Dauwas baiyi tawaye ba a lokacin da mahaifin gimbiya Rashmin yasa aka yi masa dukan kawo wuka har aka kaishi kurkuku, bayan aljanin ya kasance gawurtaccen jarumi mai tarwatsa maza a filin daga.
Sa'adda boka Muzafar ya ji wadannan tambayoyi guda uku sai ya bushw da dariya sannan ya ce Ya kai wannan sarki k yi sani cewa makaho baya cewa ayi wasan jifa face ya tabbatar da cewa ya taka hoge, kamar yadda aljani Maraful Dauwas ya gaji wadannan dalasiman tsafin haka nima na gajesu a wajen kakana na uku, kuma duk duniya mutum hudu ne masu wannan dalasuman tsafin sai kuma aljanu uku, a cikin mutane saura mutum biyu jal a raye daga nk sai sarkin birnin Hindu wato mahaifin gimbiya Ramlatus siyam, a cikin aljanu kuwa saura aljani Maraful Dauwas kawai. Dangane da tambaya ta biyu kuwa hakika babu kalaman da zamu fadawa aljani Maraful Dauwas ya amince yayi mana wannan aiki domin dukiya ko mulki basa gabansa, abu daya ne zamu je masa da shi idan muka yi sa'a ya amince, kayi sani cewa a yamma da birnin Misra bayan mutuwar Gimbiya Rashmin da shekaru hamsin an haifi wata kyakkyawar budurwa mai tsananin kama da gimbiya Rashmin tamkar an tsaga kara harma ta fi Rashmin kyawun sura, kai inda za a hada Rashmin da budurwarnan mai suna Rahila da sai mutum yayi tsammanin cewa tagwaye ne, zamu dauki Rahila mu tafi da ita can cikin kogon darul ikisina domin aljani Maraful Dauwas ya ganta da idanunsa, tabbas idan yayi arba da ita zai cika da mamaki wata kila ma yayi tunanin ko fatalwal masoyiyarsa ce Rashmin, nan take sai muyi masa al?awari cewa zamu bashi ita ya aura amman bisa sharadin zai biya mana bukatarmu, ko shakka bana yi nasan aljani Maraful Dauwas zai bari wannan tayi ya wuce shi ba, game da tambayarka ta uku kuwa dalilin da yasa aljani Maraful Dauwas bai yi wa sarki tawaye ba shine akwai alkawari mai karfi da mahaifinsa ya dauka kan cewa har abada shida zuri'arsa baza su taba yi wa sarkk tawaye daga yin bauta ba, face shi da kansa ya daina bukatarsu. Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa yanzu take ba tare da bata wani lokaci ba zan daukeka mu aiwatar da wannan gagarumin aikin da ke gabanmu, amman kafin mu tafi sai na kirkiri mai irin kamanninka sak kuma na kwantar da shi bisa gadonka, ya cigaba da rashin lafiya hadimnaka na ci gabada yi masa hidima har izuwa lokacin da zamu dawo saboda mu bagarar da matarka sharlis, domin idan taga baka nan na san tabbas sai ta yi kyakkyawan shiri, kuma muddin ta gano zata iya tarwatsa shirin namu dan dukkanin wani sihirin tsafi da nake takama da shi itama tana da shi, da abu daya kacal na fita, wannan abu ba komai bane face wayo gami da hangen nesa, kasan ance duk wanda ya rigaka kwana dole ne ya rigaka tashi.
Koda jin wadannan batutuwa sai sarki Lafaru ya dubi bboka Muzafar cikin tsananin farin ciki ya ce ai nima wayo ne ya ceceni yanzu nayi kamar bani da lafiya har nazo na sameka.
Muzafar yayi murmushi yace ai koda baka yi wannan wayo ba, lallai sai na zo gareka a sirrance tunda nayi bincike naga amfaninka a cikar burin rayuwata.
Sarki Lafaru ya yi murmushi sannan ya ce da boka Muzafar na rokeka daka gaggauta dauke ni daga cikin wannan gida domin mu tafi biyan bukatar abinda ke gabanmu, ahalin yanzu ji nake kamar akan kaya nake.
Kafin sarki Lafaru ya gama rufe bakinsa tuni boka Muzafar ya shafi jikinsa da hannunsa na hagu, kawai sai yaga Husaininsa ya fito daga cikin jikinsa, hatta kayan da ke jikin Husaini iri daya ne babu banbanci ko kadan, kawai sai Husaini ya je ya kwanta akan gadon sarki, boka Muzafar ya sake dafa kafadar Sarki Lafaru nan take suka bace gaba dayansu, basu bayyana a ko ina ba sai a birnin Kufa a gaban wani narkeken aljani mai matukar girma gami da ban tsoro, kuma muninsa ya wuce ayi misali idan mutum ya kalli fuskar aljanin zai iya haukacewa nan take, amman da yake sarki Lafaru ya saba gamo da ire-irensu a baya kafin alkadarinsa ya karye sai bai tsorata ba ainun.
Ba tare da bata lokaci ba boka Muzafar ya kama hannun Sarki lafaru ya jashi suka hau kan wannan narkeken aljani sannan Muzafar ya ce Ya kai Marhabul Zaurus maza ka kaimu can yammacin birnin Damaskas a ajiye mu a garin su kyakkyawa Rahila.
Da jin wannan umarni sai Aljani Marhabul Zaurus yayi murmushi mai kama da gurnanin zaki ya ce an gama ya shugabana, nan take nakeken aljanin ya bude fukafukansa ya tashi tre da lulawa cikin gajimare yana mai keta giza-gizai tamkar tauraruwa mai wutsiya
Tafiyar da suka yi bata kai ta rabin sa'a ba suka iso yammacin birnin Damaskas, aljani Marhabul Zaurus ya sakko kasa ya dira bisa turba a bakin kofar wani babban birni wanda suka iske kofar a rufe, dakarun yaki kimanin su dubu suna tsaitsaye a bakin kofar rike da muggan makamai suna gadi.
Ba tare da boka Muzafar ya ce da sarki Lafaru wani abu ba sai kawai ya sauka daga kan aljani Marhabul Zaurus ya nufi wajen masu gadin kofar kai tsaye. Koda ganin haka sai Sarki Lafaru ya sauko da sauri ya bishi a baya cikin sauri-sauri gudu-gudu har ya tarar da hi suka kasara wajen masu gadin kofar a tare. Da zuwansu sai Boka Muzafar ya dubi shugaban dakarun ya daka mashi tsawa sannan ya ce, Ya kai wannan bawan sarki maza ka ruga wajen sarkinku ka fada masa cewa ni boka Muzafar ibn Mauzur gani na dura a kasarsa kuma ina son ya bani aron yarsa Rahila zan dawo da ita bayan kwanaki sittin da biyar.
Koda jin wannan batu sai gabadaya dakarun suka kyalkkyale da dariya, haka suka yita yi kamar ba zasu daina ba, daga can sai shugaban nasu ya dubi boka Muzafar ya ce Kai ko wane irin mahaukaci ne, kuma a ina ka taba ganin uba ya bada aron yarsa budurwa balle kyakkyawa kamar Rahila, wai shin zautuwa k yi ko kuma basirarka ce ta toshe?
Koda jin haka sai zuciyar boka Muzafar ta kama tafarfasa tamkar zata kone daga can kuma sai ya daga hannu ya sharara wa shugaban dakarun mari, sabida zafin marin sai da yayi katantanwa sau uku kuma yaga taurarin wuya. Boka Muzafar ya dubeahi a fusace tare da cewa ubanka ne ya zautu amman ba ni ba, kuma mai tosashiyar ?wa?walwa...
Kafin Muzafar ya gama rufe bakinsa tuni shugaban dakarun da sauran yaransa sun zare makamansu tare da yi masa kawanya, koda ganin haka sai shima boka Muzafar ya zare nasa takobin suka kacame da azababben yaki, shi kuwa sarki Lafaru sai ya buta a bayan wata bishiya yana mai leken abinda ke faruwa.
Kaico! Hakika maza sun fadi, lokacin da Sarki Lafaru aga ana wannan gumurzu tsakanin boka Muzafar da dakarun nan sai yaga boka Muzafar ya zame masu alakakai, amman shi gashi a labe ya kasa kai masa dauki sai hawayen takaici ya zubo masa, saboda tunow da cewa da fa shi Gwarzon Sadauki ne mai tarwatsa gungun maza kuma komai yawansu a filin daga, amman yanzu ko mutum daya ba zai iya gwabza yaki da shi ba, domin yana jin rashin karfi a jikin nasa yadda ko takobi ba zai iya dagawa ba.
Lokacin da boka Muzafar yaga wannan dakarun yakin su dubu ya zame masu alakakai yana ta kashesu tamkar guguwar annoba ce ta sauka a wannan birni, su kuma sun kasa koda lakutar jikinsa, sai ya raina jarumtarsu, dan haka sai ya maida takobinsa cikin kufe ya ci gaba da gumurzu da su babu makami a hannunsa. Duk wanda ya kawo masa sara ko suka sai ya kauce ya gabza masa naushi daya take zai baje a kasa sumamme.
Koda sarki Lafaru ya hango irin wannan tsananin gagarumar jarumtaka da boka Muzafar ke yi, sai ya cika da tsananin mamaki domin ko shi kansa sa'ar da yake da karfin damatsensa bai yi tsammanin ya taba jarumtakar da ta kai irin wannan ba, kuma a cikin tsananin zafin nama kamar haka.
Cikin abinda bai wuce dakika hamshin ba, boka Muzafar ya bazar da dukkanin dakarun su dubu a kasa, daga sumammu sai karyayyu babu wanda zai iya mikewa tsaye a cikinsu.
Koda ganin haka sai boka Muzafar yasa kafarsa ta dama da doki kofar shiga garin wacce aka yita da zallar bakin karfe, mulmulalle mai tsawon kamu dari gami da fadin kamu saba'in. Nan take kofar ta jijjege daga jikin katangar ta fadi kasa rikica! Karar katuwar kofar ce ta cika garin gabadaya, ta dugunzuma hankalin dukkan mutanen garin har suka fara tsammanin cewa rundunar yaki ce ta kawo masu harin sumame.
Nan da nan Sarkin garin da kuma hadimai suka debo makan yki sama da su dubu dari uku suka yi hawa Bisa dawakan tare da sukwanosu zuwa bakin kofar birnin domin su tari Abokan gaba.
Da isowar sarki da dakarunsa sai suka cika da tsananin mamaki da suka ga mutum biyu jal sun tunkaresu.
Sarkinsu ya dubi boka Muzafar da sarki Lafaru ya daka masu tsawa ya ce Ina sauran dakarun naku suka buya, shin kunzo da wani sabon salon yaki ne da kuke ganin zaku iya cutar da mu da shi ne?
Koda jin wannan tambaya sai boka Muzafar ya dubi sarki sannan ya ce mu ba yaki ne ya kawomu ba, ba kuma mu biyu muka zo ba, wadannan masu gadi naku da kuke gani a kasa tamkar tsommokara taurin kai suka yi mana, suka ki isar da sakonmu a gareka, bisa wannan dalili ne na fusata n banke kofar wannan birni naku na shigo. B wani abu ne ya kawo mu ba face mun so ka bamu aron yarka dan tayi mana wani aiki na kwana sittin da biyar kacal, ina mai tabbatar maka da cewa zamu dawo maka da ita cikin aminci da salama kamar yadda muka karbeta daga hannunka.
Lokacin da boka Muzafar ya zo nan a zancensa sai sarki da dukkanin dakurunsa suka bushe da dariya, kamar yadda masu gadin kofar suka yi a karon farko, lokaci daya kuma suka tsuke bakinsu suka yi tsit tamkar mutuwa ta gifta ta tsakaninsu. Sarki ya dubi wasu zakwakurarun dakarunsa mutum hudu ya ce da su maza ku kama wannan baki ku kaisu kurkuku ku kullesu, lallai ba kalau suke ba aljanu ne suka shafesu.
Gama fadin hakan da wuya sai wadannan dakaru hudun suka tasarwa su Lafaru. Da zuwa sai suka kai hannu zasu cafkesu, cikin matukar zafin nama na gaban kwatance boka Muzafar ya cafi hannun nasu su hudun a kuma lokaci guda ya kakkarya su, tamkar ya karya sillen kara. Dakarun suka rusa ihu tare da gaduwa kasa, kaji aikin sadaukai maganin maza.
Koda sarki da sauran dakarunsa suka ga abinda ya faru sai duk suka zare makamansu uka afka wa su boka Muzafar, kawai sai lafaru ya ruga izuwa maboyarsa ya labe, shiko boka Muzafar sai ya tari rundunar shi kadai aka kacame da mummunan yaki. Nan fa boka Muzafar ya gagaresu kuma ya addabesu ya zamana cewa baya saransu da takobinsa sai dai ya kare dukkanin harinsu, sannan ya riga gabza masu naushi da hannu da kafa, komai girman kato idan boka Muzafar ya yi masa naushi daya sai ya kife kasa kuma ba zai sake mikewa ba. Boka Muzafar ya rinka tsale a saman dakarun nan yana shawagi tamkar tsuntsu mai fuka-fukai, yayi tq zubar da su kasa yana masu sarkiya ya hana dawa tsayuwa, kafin rabin sa'a ta cika ya bazar da mutum dari a kasa.
Koda sauran dakarun nan suka ga abinda ke faruwa sai suka zubar da makamansu suka mika wuya, sarkinsu ne kawai ya ki mika wuya, kawai sai ya sakko daga kan dokinsa ya gyara tsayiwarsa kuma ya rike takobinsa da hannu biyu ya tsaya cak a waje daya.
Koda ganin haka sai boka Muzafar ya dubeshi saman yayi murmushi ya ce Ya kai wannan sarki mene ne dalilin da yasa ba zaka mika wuya a gareni ba, alhalin kasan cewa ba zaka iya samun snasara a kaina ba?
Koda jin wannan tambaya sai sarkin yayi ajiyar zuciya cikin alamun takaici ya ce Ya kai wannan Sadauki mai jarumtaka ta ban al'ajabi yi sani cewa har abada sarki sarki ne, bazai taba mika wuya a rabashi da mulkinsa, dukiyarsa ko kuma yayansa ba face bisa dole idan ya ga ya kasa kare kayansa, ya za a yi n dauki yata ta cikin kuma da hannuna na baka ita aro bansan me zaku yi da ita ba, kuma ma bn san ka ba, ai sai dai ku fara kasheni sannan kuje ku dauketa.
Da jin wannan batu sai boka Muzafar ya risina ga sarki ikin girmamawa ya kai gaisuwa tare da cewa Ni din nan ba sarki bane na kasance boka ne, amman ina girmama sarauta, ya kai wannan sarki hakika ka burgeni da ka zama mai kishin jama'arka, mulkinka gami da iyalanka. Nikam.ba zan kasheka hakazalika bazan kashe kowa a cikin garin nan ba domin kawai nazo daukar yarka, amman fa duk wanda yayi gigin hanani daukarta to fa lallai ne zai rasa hanaye gami da kafafu, idan har baka son wannan birni naka ya zama na nakasassu ina mai shawartarka daka bani Gimbiya Rahila salin alin na tafi da ita.
Da jin hka sai sarki ya daka wa boka Muzafar tsawa ya ce da shi Bafa zai yuwuba, idan har kaga ka tafi da ita totabbas sai dai idan bana numfashi.
Lokacin da boka Muzafar ya ji wannan batu sai ya fisata ainun ya zare takobinsa ya ruga izuwa kn sarki, shima sarkin sai ya daga takobinsa sama ya ruga gareshi, saura kiris su hadu sai kawai sukaga gimbiya Rahila ta dako wawan tsalle tare da dura a gabansu, duk su biyu sia suka ja da baya suka yi cirko-cirko kamar zakaru suna masu kallonta cikin mamaki bisa yadda akayi ta bayyana tsulum a gabansu.
Gimbiya Rahila ta kalli mahaifinta a lokacin da idanunta suka ciko taf da kwalla, suka fara zubar da hawaye ta ce Haba ya abbana yanzu akna rayuwata kadai sai ka bari a maishe da jama'arka nakasassu, ka tuna cewa a garin nan akwai iyayenka, kakanninka gami da yan uwanka, kuma su ka fara samu kafin ka sameni, kada ka manta ni ya mace nake, mokai daran daewa dole ne muyi aure mu rabu ko da kuwa wani bai zo ya rabani da kai da karfin tsiya ba, ina mai rokonka da ka hakura ka bayar da ni ga wadannan mutanen domin naje nayi masu irin aikin da nake so, sabida bana son mutum daya ya jara cituwa a wannan birni bisa sanadiyyata, daga kjarshe idan da rabon sake saduwa sainkaga na dawo gida, idan kuma na mutu acan sai ka rungumi kaddara domin ita rayuwa tana da lokacinta, idan babu mutuwa ai akwai tsufa da rashin lfiya.
Lokacin da Gimbiya Rahila ta zo nan a zancenta sai jikin sarki yayi sanyi, kawai sai ya karasa gareta ya rungumeta suka gashe da