Showing 18001 words to 21000 words out of 59226 words
Chapter 7 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
ban isa na yiwa wani aiki ba face su
idankuwa na kuskura na yiwa wani aiki mutuwa zan yi domin an
yi alkawarin ne a cikin sihirin tsafi bisa amincewar mahaifina da
mahaifin sarki Kusaidu.
Yanzu na zo wajenki ba aiki zan yi miki ba kawai zan gaya miki
abubuwan da za ki yi ne a kanki domin bukatarki ta biya, ladana
a wajenki abubiyu ne rak.
Abu na farko,bayan bukatarki ta biya za kibani kanki na sanki 'ya
mace domin a rayuwata nayi alkawarin ba zan ta6a kwanciya
da wata 'yamace ba sai wadda take da tsananin kyawu
nagaban kwatance, kuma wadda ta kasance 'yar attajirin da
babu kamarsa a wannan nahiya gabadaya,gashi kuma na yi dace na sameki.
dace na sameki.
Ladana na biyu shi ne, za ki raba dukiyarki gida biyu ki bani rabi
bayan mutuwar 'yar uwarki Marifa domin a sannan ne za a baki
gaba dayan dukiyar da mahaifinki ya bari.
ldan kin amince da wannan sharadi yanzu
take zan gaya miki abubuwan da za ki yi ki samu cikar burinki.
Sa'adda boka Ardusa ya zo nan a zancensa sai hankalin Zarifa
ya dugunzuma ainun ta rasa abin da ke ma ta dadi a duniya ta
mike tsaye dagakan gadonta ta kama kaikawo da tunani bisa
hukuncin da ya kamata ta yanke akan ta yarda dashi.
Abin da ya fara fado ma ta a rai shi ne ya za ayi ta bayar da
wannan kyakkyawan jiki na ta ga boka Ardusa tsohon da ya kai
sa'an ubanta alhalin tana takama da tsananin kyawun da babu
mai tabata face babban Basarake ko mashahurin attajiri.
Abu na biyu da ya fado ma ta a rai shi ne, yaza a yi ta raba
wannan dukiya ta ta mai tsananin yawa ta baiwa wani rabi,
wacce ta ishi mutum rayuwa a duniya koda zai shekara dubu
Lokacin da boka Ardusa ya ga Zarifa ta shiga halin rudewa da
wasi-wasi sai ya mike tsaye yadubeta ya ce, "Wai shin kin
manta ne da abin da bokaye da dama suka gaya miki cewa
babu mai iya biya miki bukatarki face ni.
Idan zuciyarki bata gamsu da al'amarina ba shi ke nan ni zan yi
tafiyata na barki da wayonki".
Koda jin haka sai Zarifa ta yi sauri ta shagaban boka Ardusa ta
ce, "Ya kai wannan sakin bokaye ka yi sani cewa jikina da
dukiyata ba abakin komai suke ba muddin zan sami biyan
bukata Lallai na amince da dukka wanann sharadi naka don
haka kayi sauri ka sanar da ni abubuwanda zan yi domin bukata
ta biya".
Koda jin haka sai boka Ardusa ya yi murmushi ya ce, "Kafin nayi
miki bayanin abubuwan da za ki yi kuma kika yi su kika sami
nasara sannan daga baya kika yi min butulci, ma'ana kika ki cika
mini alkawari, lallai zaki mutu a cikin kwanaki talatin cicif bayan
yin aurenki.
Haka kuma dole ne ki ci gaba da bani kanki a duk sa'adda na
bukace ki, idan kuwa kikaki asirinki zai tonu kuma ki rasa abin
da kika samu a rayuwa. Yanzu sai ki saurareni da kyau domin
kiji duk abubuwan da zan gaya miki wadanda za kiyi su
bukatarki ta biya.
Abu na farko da za ki yi shi ne, dole ne ki fada mini tambayoyi
guda uku wadanda mahaifinki ya fada miki ki tambayi masu
neman aurenki gami da amsoshinsu domin nasanar da sarki
Kusaidu su ya sami damar aurenki.Kin ga idan kika auri sarki
Kusaidu za ki sami damar da babu wata mace da ta samu a
duniya domin shi ne sarkin da a tarihi sarakan duniya babu
masarautar da ta fi tashi tsohon tarihi da daukaka da karfin
mulki.
Duk sarkin da ya yi zamaninsa har bayan shudewarsa ba a
mancewada shi da matansa domin har a fadar sarkin Aljanun
duniya ana rubuta tarihinsu a ajiye, atakaice dai sai sunanki ya
bazu ko ina a duniya kinga ke nan ko ta nan kin yiwa 'yar uwarki
Marifa fintinkau.
Abu na biyu da za ki yi shi ne, ki samo kasko i yi fitsaria
cikinsa sannan ki diga digon jininki a ciki, sai ki kira sunan 'yar
uwarki sau uku ki tofa a ciki sannan ki wanke idanunki da shi
amma a ranar da za a yi gasar neman aurenku. Dazarar 'yar
uwarki Marifa ta hada idanu da ke awannan rana ba za ta yi
wata goma sha uku ba aduniya za ta mutu, idan kuwa baki hada
idanu daita ba to kece za ki mutu a cikin wata goma sha ukun.
Wannan shi ne iyakar abin da za ki yi. dukkan burinki ya cika..Da
wannan furuci nake miki sallama sai mun hadu a ranar gasa."
Kafin Zarifa ta bude baki ta ce wani abu tuni boka Ardusa ya yi
girgiza ya bace 6at. Al'amarinda ya matukar baiwa Zarifa
mamaki ke anan domin ya tafi ba tare da ta fada masa wannan
tambayoyi uku ba, wadanda zai sanar da sarki Kusaidu gamida
amsoshinsu.
Zarifa ta koma kan gadonta zuciyarta cike da sake-sake da
tunani bisa wannan abu da ya faru tsakaninta da boka Ardusa.
Ba wani abu take tunani da wasi-wasi ba face hadarin da ke
cikin aikin da boka Ardusa ya sa ta.
Koda takwanta akan gadonta domin ta mike kafafunta tayibarci
sai kawai tayi arba da wata takarda akangadon. Al'amarin da ya
matukar ba ta tsoro damamaki ke nan domin a saninta babu
wata takarda& cikin turakar ta ta koda guda daya kuma babu
yadda za a yi a shigo da wani abu ba tare da saninta ba.Hannun
Zarifa na karkarwa ta sa hannayenta biyu ta dauki takardar
wacce ta kasance fara kal babu zanen komai a kanta.Koda ta
dubi takardar sai ga hoton fuskar boka Ardusa ta baiyana akai
yana mai murmushi a gareta sannan ya ce"Maza kifadi
wadannan tambayoyi uku gami da amsoshinsu."
Koda jin haka sai Zarifa ta karanto tambayoyin gami da
amsoshinsu.
Bisa mamaki sai Zarifa ta ga an rubuta duk abin da ta fada akan
wannan takarda ba tare da ta ga mai rubutun ba ko alkalamin
da ke yin rubutun.
Nan take takardar ta6ace 6at tamkar bata taba wanzuwa ba a
wajen.
Koda ganin haka sai Zarifa tayi murmushi sannanta kwanta.
Kwanciyarta ke da wuya sai barci yasace ta,bata sani ba.
Abin da bata sani ba shi ne, kafin boka Ardusa ya bace daga
cikin turakar ya busa mata hodar banju ta shaka, shi ya sa nan
da nan barci yakamata in ba don haka be da ba za ta iya barcin
basaboda tunanin gagarumin aikin da ke gabanta dakuma
sharadin da ke tsakaninta da boka Ardusa.
DA RANAR gasa tazo sai fadar birnin Kisra ta cika ta batse da
mutane duk inda mutum ya duba gabas da yamma, kudu da
arewa sai dai ya ga kawunan bil'adama fululu babu masakar
tsinke.
A tsakiyar fadar ne jaruman gasa suka taru wadanda gaba
dayansu sun kasance sarakai da attajirai da ma manyan bokaye
daga kowanne bangare a kasashen da ke nahiyar.
Sarki Kusaidu da sarkin Darul Mahabul ne suka shigo a
karshe,bokayensu na take musu baya.
Maimakon su sarki Kusaidu su tafi izuwa inda karagar mulki
take sai suma suka shiga tsakiyar fadar inda sauran jaruman
gasar suke.
Saboda shakkar wanman gasa gaba dayan jaruman da suka
tsaya a tsakiyar fadar su goma ne kacal su sarki Kusaidu ne
suka zamo cikon na shabiyun. Ba wani abu bane ya janyo hakan
ba face sauran jama'ar da suke son su shiga gasar wadanda
adadinsu ya fi dubu dari bokayensu sun tabbatarmusu da cewa
6ata lokacinsu za su yi ba za su iyacin nasara ba.
Shi kuwa Sarkin Darul Mahabul ana i gobe za ayi gasar ne ya
sami f
kwarin guiwar fitow awanann gasar bayan boka Sulbaini da
boka Zaharu sun hakura da kiyayyar da ke tsakaninsu sun hada
karfi da karfe sun binciki amsar tambayar da za ayi masa ya iya
amsawa. Kuma a binciken da suka yi sai suka kasa gano
tambayoyin da Zarifa za ta yi sai na Marifa suka gani. Koda
suka ga tambayoyin sai suka kasa fahimtar amsoshinsu har sai
da suka tara gaba dayan hadiman aljanunsu suka bazamasu
?zuwa cikin duniya wajen tsofafin mutane da aljanu masana
ilimin tarihi. Da Kyar da sidin goshi aljanun suka samo amsar
tarabayoyi biyu. Amsar tambaya ta uku kuwa ba a sameta ba
sai a lokacim da suka fito filin gasar sannan wani hadimin boka
Sulbaimi yazo da ita. Ai kuwa cikin gaggawa ya radawa sarki
amsar a kunnensa.Koda jin amsar sai sarki ya cika da farin ciki
kuma ya sami nutsuwar shigar gasar.
Jim kadan de shigar su sarki Kusaidu cikin jaruman gasa sai ga
Zarifa da Marifa suka shigo cikin filin fadar.Kowacce daga
cikinsu ta caba ado na ban mamnaki kuma na kure
adaka,kuyanginta na biye da ita gaba da baya suna watsa
furanni masu kamshi akan hanyar takawarta.
Kamshin turaren da su Zarifa suka sanya a jikinsu ne ya fara
dukan hancin kowa a fadar.Koda jama'a suka ji wannan kamshi
sai suka waigo suka dubi masu shigowar,wohoho! Nan fa maza
suka rude suka dimauce, wasu suka kama
dalalar da yawu, basu sani ba wasu kuwa sai suka kama yanke
jiki suna faduwa kasa sumammu saboda sun ga abin da
kwakwalwarsu ba za ta iya dauka ba.Masu Karfin hali ne suka
rinka kuka suna zubar de hawaye saboda takaici bisa sanin
cewa ba za su taba mallakar wadannan kyawawan 'yan mata
biyu.
Tun kafn su Zarifa su shigo cikin fadar sai Zarifa ta ga Marifa ta
sha lullu6i kuma ta sunku da kanta kas idanunta basa kallon
komai face kasa inda take takawa. Alamarin da ya dugunzuma
hankalin Zarifa ke nan domin ta san cewa idan har basu hada
ido ba ita da Marifa kashinta ya bushe kuma ba za ta taba cika
burinta ba. Nan fa Zarifa ta fara tunanin abin de za ta yi domin
ta tabbatar cewa ta hada idanu da Marifa. Inda matsalar take
shi. ne akwai tazara tsakaninta da Marifa kuma akwai kuyangin
Marifa a tsakaninsu. Koda Zarifa ta ga fuskar Marifa a rufe take
sai itama ta janyo mayafinta tayi lullu6i kuma ta sunkui da kanta
kas amma zuciyarta sai bugawa take da karfi cikin tsananin
tsoro.
Zarifa da Marifa suka ci gaba da tafiya suka nufi inda aka
tanadar musu su zauna amma Zarifa na daga kai tana satar
kallon Marifa ko za ta ga itama ta dago kai domin su hada
idanu, amma bata dago din ba. Zarifa na cikin wannan satar
kallo ne
ta hada ido da boka Ardusa,nan take ya yi ma ta nuni da
idanunsa cewa lallai tayi duk iyakar kokarinta ta hada idanu da
Marifa kafin su isa inda kujerun zamansu suke. Koda ganin
wannan inkiya sai hankalin Zarifa ya kara dugunzuma ta shiga
tunanin abin da za ta yi ya zamana cewa lallai ta hada idanu da
Marifa kafin su kai mazauninsu. Sai da ya rage saura baifi taku
goma ba su isa mazaunin nasu sannan dabara ta fado ma ta.
Kawai sai tayi kamar tayi tuntu6e, cikin shammace ta tafi taga-
taga ta fadi a gaban Marifa.Cikin mamaki da kaduwa Marifa ta
sunkuya ta dubi Zarifa suka hada idanu. Suna hada idon sai
Marifa taji wani abu ya soketa a kirji tamker an tsira ma ta
mashi. Saura kiris tayi ihu kuma ta fadi kasa, amma sai ta daure
ta mike ta ci gaba da tafiya. A sannan ne ta ga Zarifa ta dubeta
tayi ma ta wani irin murmushi na mugunta. Nan take Marifa ta
tsergu da cewa tabbas 'yar uwarta Zarifa tayi ma ta wani
mugun asirin.
Zarifa da Marifa sun dade suna yiwa junansu mugun jifa na
sihiri amma sihirin yaki ya yi tasiri akan kowannensu kuma duk
wajen bokan da suka je yana gaya musu cewa sai dai su yi
hakuri babu wani sihiri da zai iya huda jikinsu a yanzu,domin
mahaifinsu ya yi musu tsari na musamman babu wanda zai iya
karya wannan sihirin face bokan da
ya yishi kuma ba wani bane face boka Ardusa.
Cikin tashin hankali da mamaki Marifa ta karasa zuwa kan
kujerar da aka tanadar ma ta ta zauna,itama Zarifa sai taje ta
zauna akan ta ta kujerar fuskarta cike da murmushi,zuciyarta ta
cika makil da farin ciki. Zamansu ke da wuya sai Alkalan gasar
suka fara zartar da aikinsu aka ware jaruman da ke son Marifa
da wadanda ke son Zarifa.
A zaton sarki Kusaidu Sarkin Darul Mahabul zai shiga cikin
sahun masu son Zarifa amma sai ya ga ya shiga cikin sahun
masu son Marifa. Nan take Sarki Kusaidu ya hau kan layin
masu son Zarife ya tsaya daga Kanhe. Masu son Zarifa mutum
bakwai ne, masu son Marifa kuwa mutun uku ne,sarkin Darul
Mahabul ya zamo na hudunsu. Saboda haka sarki Kusaidu ne
na takwas a cikin sahun masu son Zarifa. Be wani abu bane ya
sa masoyan Zarifa suka hi yawa ba face its Zurifa ta baiyana
fuskarta an gani tun kafin a fara gasar don haka jaruman gasar
sun dauka tafi 'yar uwarta kyau sai da Marifa ta yaye lullubinta
gaba daya aka ga kyawunta de kyawun surar jikinta wanda har
yafi na Zarifa sannan aka dimauce. Shi kuwa sarki Kusaidu ya
zabi Zarifa ne saboda boka Ardusa ya gaya masa cewa na ta
tambayoyin kadai ya sani amma bai san na Marifa ba.Wani abin
mamaki shi
ne duk da cewa Marifa tafi Zarifa kyau sai sarki Kusaidu yaji yafi
son Zarifa kuma nan take ya kamu da tsananin begenta a
Zuciyarsa.
Ba tare da 6ata lokaci ba Alkalan gasa suka umarci Zarifa da ta
mike tsaye ta karanto tambayoyinta guda uku ga jaruman
gasarta mutum takwas bisa sharadin cewa duk wanda ya amsa
tambayar dai-dai shi ne zai zamo mijin da za ta aura.
Cikin mumushi gami da takama Zarifa ta mike tsaye ta fuskanci
miliyoyin jama'ar da ke cikin fadara lokacin da aka yi tsit!
Tamkar mutuwa ta gifta. Zarifa ta bude baki cikin muryarta mai
zaki tamkar sarewa ta ce tambayoyina gareku masoyana su ne
kamar haka.
Tambaya ta farko, a duniya wane abu ne mafi tsananin karfi,
karfin da yafi na radadin mutuwa ciwo kuma yafi karfin
wadatacciyar lafiya dadi a zuciyar bil'adama da aljanu?
Tambaya ta biyu ita ce, "Wacce halittace me rai tana ci kuma
tana sha amma bata kashi da fitsari?.
Tambaya ta uku ita ce"Wane abu ne wanda idan ya baiyana
yana firgita mutane da aljanu a duk inda suke, idan (kuma
kishiyarsa ya baiyana sai su sami nutsuwa da kwanciyar
hankali?"
Sa'adda Zarifa ta gama fadin wadannan. tambayoyi guda uku
sai ta zauna akan kujerarta takasa kunne tana sauraron amsae
da jarumin farkozai bayar.Gaba dayan fadar sai ta sake yin tsit!
Mutane suka shiga zancen zuci suna maimaita tambayoyin uku
a cikin zukatansu suna kokarin amsawa. Nan take jarumin farko
ya mike tsaye yace'Amsar tambaya ta farko ita
ce,soyayya,domin karfin soa cikin zuciya yafi komai tunda
mutum ko aljan zai iya sallama rayuwarsa don yamallaki
masoyinsa haka kuma idan mutum yamallaki masoyinsa yana
jin tsananin farin ciki azuciyarsa fiye da a bashi komai na
rayuwa.
Amsar tambaya ta biyu ita ce babu wata halitta wacce tana ci
kuma tana sha amma bata fitsari da kashi face shuka, domin
taki ne abincinta, kuma ana zuba ma ta ruwa ta tsotse.Har
abada shuka ba ta fitar da takin da ta tsotse daga jikinta kuma
ba ta fitar da ruwan da ta tsotse a matsayin bashi da amfani a
jikinta.
Game da tambaya ta uku kuwa babu abin dake firgita mutane
da aljanu idan ya baiyana face yaki, kishiyarsa kuwa shi ne
zaman lafiya"
Ya yin da wannan jarumi na farko yazo nan ajawabinsa sai
Zarifa tayi murmushi ta ce"Ya kai wannan masoyi nawa hakika
kayi matukar kokari domin ka amsa tambaya ta farko da ta biyu
dai-dai amma tambaya ta uku ba daidai bace don haka sai
ka koma gefe daya ka baiwa wanda ke bayanka wuri ya jarraba
sa'arsa ko zai iya amsa tambaya ta ukun".
Koda jin haka sai wannan jarumi ya kamu da tsananin bakin
ciki, nan take zuciyarsa ta buga ya Sulale Kasa matacce. Cikin
hanzari dakaru suke ruga suka dauke gawarsa aka yi wajen
fadar da shi.
Jarumi na biyu ya matso gaba a lokacin da gaba dayan jikinsa
ya kama karkarwa tamkar an tsamoshi a cikin ruwan Kankara a
lokacin da ake hunturun sanyi. Jarumin ya yi shiru yana tunani
da nazari a cikin Kwakwalwarsa ya tuna irin nisan tafiyar da ya
sha daga garinsu zuwa wannan birni na Kisra da kuma ya tuno
da miliyoyin darhaman da ya kashe kafin ya sami damar shiga
wannan gasa.
Jarumin ya dada tunawa cewa shi fa dan sarkin garinsu ne
kuma shi kadai ne da namiji a wajen ubansa mai gadon
sarauta. Da ya tabbatar da cewa bai san amsar wannan
tambaya ta ukun ba, sai ya koma gefe daya yana mai nuna
alamar cewa ya gaza.
Nan take fadar ta rude da ihu har wasu ma na jifansa suna
cewa ya yi abin kunya.
Sai da Dakaru suka yi tsawa sannan mutane suka daina jifan da
ihun, sannan jaruman gasar suka ci gaba da amsa tambaya ta
uku. Har aka zo kan jarumi na bakwai ba a sami wanda ya amsa
dai-dai ba.
Koda aka zo kan Sarki K��s?idu s?i fadar ta sake rudewa da
shewa da tafi gami da jinjina. Maroka suka kama yiwa sarki
Kusaidu kirari,makada kuwa suka kama buga ganguna da
tambura. Sai da Sarki y�� tsaya a inda zai amsa tumbayar
sannan fadar tayi tsit ya zamana ba a jin komai face numfashin
jama'a. A wannan lokaci Zarifa ta murtuke fuskarta tana kallon
sarki K��s?idu kuma ta kura masa idanu. Dama haka ta rinka yi
duk sa'adda masu gasar ke amsa tambayoyin sai idan ta ga
mutum ya amsa dai-dai sannan tayi murmushi tayi bayanin ko
ya yi dai-dai.
Sarki Kusaidu ya yi gyaran murya sannan ya yi murmushi ya ce,
"Amsar tambayarki ta uku ita ce, "Haske da duhu ba wai ya ki da
zaman lafiya ba. Dalili kuwa shi ne, komai jarumtakar mutum ko
aljan idan ya tsinci kansa a cikin matsanaicin duhu wanda baya
iya ganin komai dole ne hankalinsa ya dugunzuma ya firgice
domin bai san abin da zai faru gareshi ba. Haka kuma idan
haske ya baiyana gareshi ya sami nutsuwa da kwanciyar
hankali tun da zai iya ganin kowacce irin masifa da za ta
tunkaroshi kuma zai yi tunanin hanyar da zai bullowa masifar ya
iya tararta."
Koda sarki Kusaidu yazo nan a zancensa sai fuskar Zarifo ya
fadada da murmaushi ta ce,' Tabbas kai ne mijina domin ka
amsa wannan tamabaya dai-dai, haske da duhu su ne amsar
tamabayata ba yaki da zaman lafiya ba. Dalili kuwa shi ne, yaki
ba kowa ne ke tsoronsa ba don jarumin da ya yarda da kansa
jarumtakarsa da Karfin sihirinsa baya tsoron kowanne irin yaki
komai tsananinsa.Haka kuma akwai mutane da aljanu wadande
suka tsani zaman lafiya kO yaushe ma sun fi so su ga ana cikin
tashin hankali, da kansu ma suke kiran masifu da bala'in".
Zarifa na gama wannan jawabi sai fadar ta rude da shewa da
tafi gami da bushe-bushe da kade-kade. Bayan 'yan dakiku sai
aka ladaftar da jama'a suka yi shiru. Alkalan gasa suka tabbatar
da cewa lallai sarki Kusaidu ne ya sami nasarar wannan gasa
cikin masu son Zarifa da aure yanzu kuma za
Zan ci gaba.
Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp.
tsugunna a kofar dakin ya yi ta rusa kuka kamar ba zai daina ba.
Babu irin rarrashin da Shaulat bata yi masa ba amma sai ya
ki yin shiru bare ta tambaye shi abin da ke faruwa.
Koda ganin haka sai Shaulat tayi tafiyarta izuwa cikin turakarta
suma sauran mutanen gidan sai suka koma cikin dakunansu
suka rufe kofofinsu.
Sai da alfijir ya keto Hantaru bai tashi daga bakin kofar Salimat
ba kuma bai daina kuka da rokon ta bude masa kofar