Showing 48001 words to 51000 words out of 59226 words

Chapter 17 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

gabadayansu sai suka yi cirko-cirko suka rasa abinda za su yi domin kofar gidan a rufe take fam kuma babu masu gadi, shidai wannan gida na jaruma Shadira yana da girma sosai harma ya ninka gidan Sadauki Haiman sau biyu amman wani abun mamaki shine ko kadan ba a kawata gidan ba. Boka muzafar ya karasa ya kwankwasa gidan har sau uku bai ji an amsa ba, kuma ba a bude kofar ba. Kawai sai yayi amfani da sihirinsa domin ya bude kofar, amman sai kofar taki budewa al'amarin da ya baiwa dukkaninsu mamaki kenan. Koda ganin haka sai Boka Muzafar ya ja da baya ya rugo a fusace ya naushi kofar da dukkan karfinsa kamat yadda yayi wa kofar birnin su gimbiya Rahila, kawai sai ya ji kamar dutse ya nausa domin ko motsi kofar bata yi ba. Shima Sadauki Haiman sai ya jaraba tasa Sadaukantakar ya sari kofar da rantsatssiyar takobinsa, take tartsatsin wuta ya tashi amman ko kwarzanewa kofar bata yi ba.
Ba zato a ba tsammani sai kawai suka ga wani yaro wanda bai fi shekara tara ba ya bayyana tsulum a gabansu yana murmushi, kawai sai yaron yasa yatsansa guda ya tura kofar, take kofar ta bude wanwar yaron ya shige cike yana mai yafitosu da hannu cewar su biyo shi a baya.
Saboda tsananin mamakin yadda yaron ya iya bude kofar sai dukkaninsu suka kasa shiga cikin gidan har sai da suka ji muryar jaruma Shadira tna mai kyalkkyala masu dariya sannan suk shiga ikin gidan.
Da shigarsu cikin farfajiyar gidan sai suk yi arba da jaruma Shadira a tsaye ta rataye wata katuwr baka a bayanta, da wani katon kwanson kibiyoyi wanda a cikinsa akwai kibiyoyi dubu biyu.
Koda Lumaira ta yi arba da Shadira sai ta kura mata idanu cikin tsananin mamaki, su sarki Lafaru kuwa basu san sa'adda da suka wangame baki ba suna al'ajabi, ba komai ne ya haddasa hakan ba face yadda Lumaira da Shadira suka yi kunnen doki a tsakanin kyau. Komai na halittar jikinsu ya zo iri daya, abinda ya banbanta su kawai shine kamannin fuskokinsu, amman komai iya kallon kurillar mutum da iya banbance al'amura bai isa ya tantance wacce tafi wata kyau ba. Nan take kishi ya kama Shadira bisa ganin kyakkyawa kamarta.
Shiko sadauki Haiman da yaga irin kyawun shadira kuma yaga cewa tana da idanu bata kasance makauniya kamar matarsa Lumaira ba, sai ta ayyana a ransa cewa inama ace duk matan nan biyu nawa ne, ai da babu sauran damuwa a tare da ni a wannan duniya.
Cikin karfin hali Shadira ta taho wajen boka Muzafar ta ce Lale marhabun da abokin tafiya, ai na dade da gama kimtsawa ina jiranku yanzu kawai tafiya ta rage mana.
Boka Muzafar yayi murmushi ya ce Nasan da haka ya ma'abociyar kibiya, ina fatan kin tanadi dukkanin guzurinki?
Jaruma Shadira ta juya da dubi dn uwanta Masnur cikin tsananin farin ciki sannan ta bude hannayenta ta durkusa bisa gwiywoyinta ta ce ta ho mu tafi ya kai dan uwana lokacin yanke bakin cikinmu yayi.
Koda jin wannan batu sai Masnur ya rugo da gudu zuwa kan Shadira ya fada kan kirjinta suka rungume juna.
Ba tare da bata lokaci ba sum suka debi guzurinsu suka bi wannan tawaga aka wuce zuwa birnin Istin gidan Jarumi Imran Ibn Shuhairu. Da saukar su boka Muzafar a tsakiyar gidan su Imran sai suka iske shi a zaune a gaban mahaifiyarsa wacce ta kasance tsohuwa tukuf yana bata abinci a baka da hannunsa saboda tsufa, da kyar ma take iya hadiye abincin, wani lokacin ma sai ta furzo da abincin waje ya bata wa Imran fuska tamkar ta kasance jaririya amman ko damuwa Imran bayayi sai dai kawai ya goge fuskarsa, itama ya goge mata baki sannan ya ci gaba da bata abincin. Duk da cewa jarumi lmran yaga zuwan su boka Muzafar kuma yayi murna da ganinsu, amman bai sauraresu ba sai da ya tabbatar da cewa mahaifiyarsa ta koshi da wannan abinci, sannan ya dauketa ya goyata a bayansa sannan ya dauki wata kyakkyawar sanda ya jingina a jikin bango, ya dubi boka Muzafar ya ce Lale marhabun ya kai wannan babban boka tare da abokan tafiya, yanzu sai mu wuce gaba ko domin bani da wani sauran shiri na gama, daman ku kawai nake sauraro.
Nan take boka Muzafar ya mika wa jarumi Imran hannu suka gaisa ya cw Gaisheka ma'abocin kyautat wa mahaifiyarsa, hakika kai din abin jinjinawa ne, taho mu kara gaba. Koda gama fadin haka sai boka Muzafar ya juya ya nufi inda aljani Marhabul Zaurus yake tsaye yana jiransu, kowa kuma sai ya bi bayansu ?uww. Jarumi Imran ne a karshe goye da mahaufiyarsa kwance a gadon bayansa wacce take cikin dimbin farin ciki, bisa ganin cewa yau ne zasu tafi neman maganin larurarta, babban abinda ya daure wa Lumaira da Shadira kai shine, tunda suka shigo cikin gidan Jarumi Imran ko kallon daya daga cikinsu bai yi ba balle ma har tsananin kyawunsu ya burgeshi. Kuma a koyaushe hankalinsa na kan mahifiyarsa, ko tari yaji ta yi sai ya tambayeta ko tana da wata bukata? Su kansu su sadauki Haiman suna mamakin jarumi Imran a zukatansu suna masu cewa shiko wannan jarumi wane irin mutum ne haka, wnada bai damu da komai a duniya ba face mahaufiyarsa, wacce ko kuda baya son yaga ya sauka a jikinta, gashi kuma mahaifiyar tasa ta tsufa tukuf, a koyaushe ma lokaci zai iya yin halinsa, abinda basu sani ba shine, jarumu Imran yayi alkawari a zuciyarsa cewa har abada bazai saurari aure ba, kuma bazai nemi muli ko dukiya ba face yaga mahaifiyarsa ta samu lafiya kafafunta sun mike har ta iya takasu, idan kuwa bata samu lafiya ba har salar da ajalinta ya risketa, to shima har nasa ajalin ya zo ba zai nemo komai a duniya ba face abincin da zai ci dan ya rayu. A kullum idan jarumi Imran ya dubi mahaufiyarsa yaga yadda kafafuwanta suke a kanannade sai ya fashe da matsanancin kuka ba zai daina ba har sai ta rarrasheshi da kanta ta kuma kwantar masa da hankali, ba wani abu bane yasa jarumi Imran yake matukar son mahaifiyarsa ba illa cewa ta sha matukar wahala akansa, tun daga lokacin da ta haifeshi kasancewarsa maraya domin ubnsa ya mutu, to sai ta tafi dashi izuwa gidan mijinta ya zama agola.
Sun sha matukar wahala a wannan gidan mijin nata a hannun yayan mijinta kafin daga bisani mijin ya rasu, kuma a lokacin ne yayan mijin suka sake ninka tsanar da suka yi wa jarumi Imran da mahaifiyarsa, har ya zamana cewa basu yarda an raba gadon mahaifinsu da mahaifiyar Imran ba, da kyar ma suka yarda suka zauna a cikin dakin kiwon dokin mai gidan. Da yake a wannan lokacin Imran yana yaro karami ba zai iya yi wa kansa komai ba, balle har yayi wa mahaifiyar tasa, ita take fita da jan ciki taje tayi aikatau a makota sannan ta samo masu abincin da zasu ci ira da danta da kyar, su kuwa wadannan yayan miji nata kullum suna bushasha da abinda mahaifinsu ya mutu ya bar masu gado, ko loma daya ta abinci basa ba Imran da mahaifiyarsa. Sau bakwai yayan mijin suna yi wa Imran dukan tsiya, kuma dukan ma na kawo wuka, wani lokacin ma sai au dauke shi su jefashi cikin rijiya ko kogi domin ya mutu suna yin haka ne dan su cusa wa mahaifiyarsa bakin ciki dan hakan yayi sanadiyyar ajalinta, amman da yake Jarumi Imran na da tsawon rai bai mutu ba, kuma a duk sa'adda uka jefashi a cikin rijiyar ko kogi da yake mahaifiyar tasa ta iya ruwa kuma a lokacin da take budurwa tana da yar jarumtaka, idan sun jefashi mahaifiyar tashi ce take zuwa da jan ciki ta fada cikin rijiyar ko kogin ta lalubo shi ta fito da shi tana kuka ta ci gaba da jinyarsa har ya samu lafiya.
Lokacin da mahaifiyar Imran ta fuskanci cewa idan ta ci gaba da zama gidan wannan Marigayin miji nata tofa lalla? wata rana wadannan yaya nasa zasu samu nasarar hallaka mata da, sai wata rana da daddare ana tsala ruwan sama da walkiya suka saci jiki tare da ficewa daga cikin gida, gashi mahaifiyar Imran bata da kafafu da jan ciki take tafiya, kuma gashi dan yayi yaro ba zai iya daukarta ba, saboda haka lokacin da yaga tana jan ciki tana tafiya da kyar kuma ruwa na dukanta, sai ya kamu da tsananin tausayinta har ya fashe da kuka, a haka dai suka samu da kyar da shidin goshi suka yi nisa a cikin daji suka shiga cikin wani kogon dutse suka fake.
Daga wannan rana suka cigaba da rayuwa a cikin wannan kogon dutse, ya zamana cwa mahaifiyar Imran tana kula da shi matuka, da jan ciki take zuwa farauta ta samo masu abincin da zasu ci, duk da cewa dajin da suke ciki akwai mugayen dabbobin daji da kuma kwari kamar macizai kunamu da sauransu, amman duk da haka duk abinda taga zai cutar da danta tofa sai inda karfinta ya kare, akwai wata rana da wata kura mai fama da jin yunwa ta shigo cikin kogon da suke, a wannan lokaci Imran na kwance yanata sharar bacci abinsa, baima san cewa kurar ta shigo ba. Ita kuwa mahaifiyarsa tana can cikin wani loko a kogon, kai tsaye kurar ta nufi inda Imran yake kwance da nufin cinye shi. Koda mahaifiyar ta hango wannan kura ta nufi inda danta yake, sai ta ji dukkan wani tsoro da fargaba ya kau daga cikin zuciyata, cikin zafin nama ta yi adungure sau uku sai gata a gaban kurar. Ai kuwa sai kurar ta fada kanta suka kacame da fada, kacaniyar da suke yi ne tsakanin wannan kura mai jin yunwa da mahaifiyar Imran ce tasa ya farka daga baccin da yake yi, ko da yaga kura ta turmushe mahaifiyarsa ta yagalgala mata jiki, sai ya rusa ihu ya dauki ice tare da nufar kurar, wannan ihu da Imran yayi ne yasa kurar ta daga mahaifiyarsa da sauri. Koda ta ganshi rike da wannan icce sai ta fara ja da baya-baya har taje bakin kofar kogon ta tsaya.
Haka aka ci gaba da kallon kallo tsakaninta da Imran, abinda ya daure wa kurar kai shine, yadda Imran ya kasa jin tsoronta har ya taso zai yaketa domin ya ceci rayuwar mahaifiyarsa alhalin yana karamin yaro ba zai iya cutar da kurar ba, gashi dai kurar a yunwace take matuka, tana ta dalalar da yawu kuma ga kanshin jini tana ji a jikin mahaifiyar Imran wacce take kwance magashiyan, kuma ba zata iya kare kanta daga komai ba, wank iko na Allah sai kurar nan ta kasa afka wa mahaifiyar Imran. Kawai sai ta juya ta fice daga cikin kogon, a sannan ne Imran ya juya ya ruga wurin mahaifiyar tasa yana mai fashewa da kuka, a lokacin da take numfashi sama-sama tamkar zata mutu sakamakon jinin dake zuba a sassan jikinta.
Imran ya dimauce ya rasa irin agajin da zai baiwa Mahaifiyarsa, da kyar mahaifiyar tasa ta iya bude baki ta fada masa yadda zai ceci rayuwarta, ta fada mashi cewa yaje ya tsunko wani ganye ya daka shi sannan ya shafe mata akan raunin jikinta.
Nan take kuwa ya cika wannan umarni, yana shafa mata jini ya daina zuba a jikinta. Sai da Imran ya kwana arba'in yana jinyar Mahaifiyarsa a cikin wannan kogo, da baki ta rika koya masa yadda zai je ya samo masu abinci, wanann icce wanda ya kori kura da shi, shine ya zama masa makami, ya dinga buge kananan dabbobi suna mutuwa, sai kuma ya jasu da kyar ya kai cikin kogon da suke a matsayin abincin da zasu ci. Daga sannan ne fa zuciyarsa ta bushe kuma ta kekeshe ga barin tsoron komai a dajin, kuma kullum sai ya dauki wannan icce yayita sarrafa shi, kamar yadda ake sarrafa takobi dan koya wa kansa yaki.
Ance sannu bata hana zuwa sai dai a dade ba aje ba, hak dai Imran da mahaifiyarsa suka ci gaba da rayuwa a wannan daji, har ya girma ya zama gagarumin sadauki, kuma jarumi mai ban al'ajabi, ya zamana cewa indai yana rike da sanda komai yawan mugayen dabbobin daji sai ya tarwatsasu ya kashe na kashewq wasu kuma su gudu. Kai sai da takai cewa gabadaya mugayen dabbobin daji suna tsoron Imran, bisa dole sukayi hijira su da yayansu suka bar inda suke. A wannan lokacin ne mafarautan da suke zuwa farauta wannan daji suka ankara da Imran har suka kai labarinsa wajen sarki, musamman sarki ya taka da kafarsa ya ziyarci Imran da mahaifiyarsa. Sarki yayi matukar mamaki yadda har suka rayu a wannan mugun daji mai tsananin hadari, a dalilin haka ne sarki ya shawarci Imran da ya zama daya daga cikin dakarunsa, idan har ya amince da haka to zau basu gida a cikin gari, gami da dukiya mai tarin yawa.
Cikin farin ciki Imran da mahaifiyarsa suka karbi wannan tayi da yayi masu, haka suka bar daji suk koma cikin gari suna masu fuskantar sabuwar rayuwa.
Yakin farko da jarumi imran ya fita ya nuna matukar jarumtaka ta ban al'ajabi, wacce ba a taba yin kamarta ba a tarihin nahiyar gabadaya, domin shi kadai ya yaki dakaru dubu saba'in da sanda, ba da takobi ko mashi ba, ya kashe fiye da rabinsu yayin da sauran suka ga haka sai suka tsere.
Tun daga wannan rana sarki ya daukaka Imran a fadarsa, kuma ta bashi sarautar sarkin yakinsa, ya zamana cewa sun samu daula mai yawa. Wata rana shi da mahaifiyarsa suna zaune sai kawai yaga ta kura masa idanu hawaye na zuba daga cikin idanunta.
Nan take hankalinsa ya tashi ya ce, Ya ke ummina ina dalilin wannan kuka naki?
Koda jin wannan tambaya sai ta yi ajiyar zuciya ta ce Ya kai dana ka yi sani cewa ba komai ne yasa na zubar da hawaye ba illa tsananin takaicin zuwan ranar da zaka yi aure bani da ikon da zan mike da kaffuna na taka rawa dan tayak farin ciki, haka kuma gashi tsufa ya riskeni, abune mawuyaci ma naga ranar aurenka.
Koda jin wannan batu sai imran ya fashe da kuka sannan ya rungume mahaifiyarsa a kirjinsa yana mai cewa yake ummina lallai ba zaki mutu ba sai kinga aurena, kuma duk inda zan tafi neman magani bisa wannan lalura taki sai na nemoshi kin warke.
Da jin wannan batu sai tausayin dan nata ya kamata ta ce kada ka wahalar da kanka ya dana domin mahaifinka ma akan neman maganina ya rasa tasa rayuwar, bokaye sun tabbatar da cewa bazan taba warkewa ba, face na wanke kafafuna da ruwan albarka na cikin kogon darul ikisina, daga nan zuwa kogon darul ikisina tafuya ce ta shekara da shekaru, kuma akwai mugayen dazuzzuka har guda biyar kafin a isa kogon darul ikisina. Fiye da shekaru dubu biyu babu wani mahaluki daya ratsa ta cikin wadannan dazuzzuka ya isa kogon darul ikisina a raye. Saboda tsananin son da mahaifinka yake mani ne yasa ya saci jiki ba tare da na sani ba, ya nemi taimako a wajen bokaye, ya tafi zuwa kogon darul ikisina omin samo mani magani wannan cuta tawa, sai wasikarsa kawai na smu akan gado a cikin dakina, yana mai bar mani bayani akan cewa Shifa ya tafi kogon darul ikisina domin nemo mani magani, ammn bashi d tabbacin zai yi nasara ya dawo a raye har mu sake saduwa, wasiyyarsa a gareni shine na kula da duk abinda zai haifa walau mace ko namiji, kuma na sallama rayuwata domin kare abinda zan haifa, saboda fatan sa anan gaba idan dana ko yata suka girma n basu labarin irin tsananin soyayyar dake tsakaninmu, har yau har gobe tunda mahaifinka ya tafi kogon darul ikisina ban sake jin duriyarsa, a duk sa'adda na bude akwatunsa naga irin suturunsa sai na fashe da matsanancin kuka wannan shine alilin da yasa na sallama rayuwata dan kare taka tun kana yaro karami, domin na cika wasiyyar umarnin mijina.
Lokacin da mahaifiyar Imran ta gama bashi wannan labari, sai ya sake fashewa da kuka ya kankameta a kirjinsa yana mai cewa Ya ke ummina kiyi sani cewa son da nakemaki a yanzu ya ninka wanda mahaifina ke maki sau dubu, sabida haka ina tabbatar maki da cewa omai dadewa sai n ida abinda mahaifina ya kasa, lallai nine zan samo maki maganin cutarki acan kogon darul ikisina, tabbas mutuwa ba zata rabamu ba face naga ranar da kika mike tsaye kika taka da kafafunki kika cashe rawa a ranar bikin aurena. Daga yau nayi al?awarin ba zanyi soyayya ba kuma ba zanyi aure ba har sai na samo maki wannan magani, kuma ba zan nemi mulki ko dukiya ba.
Wannan shine abinda ya faru a shekarun baya tsakanin jarumi Imran da mahaifiyarsa.
Ba tare da bata lokaci ba Imran ya goya mahaifiyarsa a bayansa, sannan ya dauki jakar guzurinsa suka dunguma shi da su boka Muzafar suka je suka haye bayan aljnai Marhabul Zaurus, shi kuma ya tashi da su sama suk ci gaba da tafiya suka durfafi birnin Farisa dan zuwa gidan gimbiya Zarina.
Tunda aka fara wannan tafiya ya zama cewa hankalin jarumi Imran akan mahaifiyarsa yake baya ci ko shan komai face yga ta koshi, haka kuma baya iya yin bacci a duk sa'ad da take bacci sai dai ya sata a gaba ya rinka kallonta yana kuma gadinta har sai ta farka daga baccin sannan shima yayi nas, kai ko tari tayi sai ya tambayeta tana bukatar wani abu ne? Ganin yadda jarumi Imran ya damu ainun da mahaifiyarsa yasa jaruma Shadira taji ya burgeta, aiko bata ankara ba ta ji ta kamu da tsananin kaunarsa, don haka sai ta rinka yawan satar kallonsa. Shiko da ya lura da halin da take ciki sai ya daure fuska a gare ta, al'amarin da ya matukar tayar mata da hankali kenan, ta rasa abinda ke mata dadi a duniya, domin bata taba yin soyayya ba, amman yanzu ga shi ta tsinci knta a cikin kogin soyayya tsundum, kuma ga dukkan alamu wanda take so din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login