Showing 57001 words to 59226 words out of 59226 words
Chapter 20 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
gaba da shawagi akan mata suna son su suresu suyi sama da su. Koda su boka Muzafar suka gane nufin aljanun sai suka saka matan cikin a tsakiya aka ci gaba da bakin artabun a haka, ya zamana cewa su boka Muzafar sun kasa tarwatsa aljanun, haka suma aljanun sun kasa illatasu balle har su samu damar sure matan, ana cikin wannan gumurzun ne wasu daga cikin aljanun masu naci suka samu nasarar yakushin boka Muzafar da gimbiya Zarina a hannu, nan take suka kwala ihu kuma suka zube a kasa a lokacin da jiri ya debesu.
Koda ganin haka sai wasu aljanun suka yunkuro zasu yanyamesu domin su dada sassarasu, koda Gimbiya Rahila ta fahimci abinda aljanun ke nufin yi sai ta daka tsalle sama ta tarwatsa su da karfin sarar takobinta, nan fa ta rinka ragargazarsu cikin tsananin bajinta gami da al'ajabi, domin tun a saman ta dinga katantanwa da shawagi tamkar tsuntsuwa hakan yasa ta addabi aljanun gaba dayansu, kuma ta hana dayansu ya cutar da su boka Muzafar da ke kwance a kasa.
Koda ganin wannan gagarumar bajinta da gimbiya Rahila ke yi sai su sadauki Haiman suka cika da tsananin mamaki, kuma suka samu kwarin gwiywar kara zage damtse, nan fa aka ci gaba da bakin gumurzu mai ban tsoro, ana cikin haka ne Sadauki Shaharan ya dawo cikin hayyacinsa ya lura cewa idan aka ci gaba da wannan yaki a waje daya tabbas su Gimbiya Rahila zasu gaji, in kuwa suka gaji to sai aljanun sun samu nasara akansu, koda gama ayyana haka a cikin ransa sai ya yunkura cikin tsananin zafin nama ya suri yaro Masnur ya goyashi a bayansa ya daure shi tamau, sannan ya falfala da azababben gudunnan nasa, ai kuwa sai wasu daga cikin aljanun suka rufa masa baya aka kasa tsere. Nan fa aljanun suka ga abin al'ajabi iri wanda basu taba gani ba, domin sunga bil'adama wanda yafi aljani gudu, irin gudun da Shaharan yake yi yafi gudun tauraruwa mai wutsiya
.
.
.
Sai kawai suka tarwatse suka fada dajin suna masu neman maboya, kafin kace kabo babu kowa a gaban Gimbiya Rahila face aljanun dake zube kasa nakasassu. Koda ganin haka sai Gimbiya Rahila ta sunkuya ta sabi Shaharan ta dirashi a bisa kafadarta ta wuce da shi izuwa karshen dajin, inda ta kai su jaruma Shadira ta ajiye.
Su boka Muzafar sun kwakkwance suna jinyar raunikan jikinsu sai kawai suka hango gimbiya Rahila ta tunkaro su dauke da sadauki Shaharan akan kafadarta tana mai tafiyar kasaita tamkar ta dauko buhun yayi. Da kyar cikin juriya suka mike tsaye suka kura mata idanu cikin tsananin mamaki har ta iso garesu, tana ajiye Shaharan a kasa sai jaruma Shadira ta yi sauri ta zo kansa ta fara sa mashi magani akan raunin nasa, nan take jinin dake zuba a bayan nasa ya daina zuba. Daman tun kafin Rahila ta zo da Shaharan duk masu raunika an yi masu magani sun dawo cikin hayyacinsu.
Bayan kamar dakika dari da sittin sai Shaharan ya farfado, koda ya bude idanunsa sai ya budi baki ya ce Ina dokina ya ke?"
Cikin fushi Gimbiya Rahila ta dubeshi ta ce da shi yanzu kai baka damu da rayuwarka ba, dokinka ne ma a ranka.
Shaharan ya ce ai dana rasa dokina gwara na rasa rayuwata, tunda saboda shi na siyar da rayuwata na taho wannan daji. Rufe bakin Shaharan keda wuya sai ga aljani Marhabul Zaurus a sama dauke da dokin Shaharan. Cikin tsananin farin ciki Shaharan ya mike tsaye yana kallon dokin nasa, aljani Marhabul Zaurus na sauka kasa sai Shaharan ya ruga gareshi ya rungume dokin nasa yana shafa wuyansa cikin murna.
A sannan ne boka Muzafar ya dubi aljani Marhabul Zaurus ya daka masa tsawa ya ce ina ka tafi ne tunda muka fara gumurzu da wadannan mugayen aljanu ban ganka ba?
Marhabul Zaurus ya risina cikin biyayya ya ce Ya shugabana ka sani cewa idan na fusknaci wadannan mugayen aljanu dukan falan daya zasu yi mani na halaka, bisa Wannan dalili ne na shiga kogon wata bishiya na saje da ita, ina kallon duk abinda ke faruwa tsakaninku da aljanun har saida naga jarumar jarumai, kuma boyayyar basadaukiya ta ragargazasu ta kuma dauki Shaharan ta tafi, sannan na fito daga cikin kogon bishiyar kum na dauko dokin Shaharan na taho nan.
Da jin wannan batu sai boka Muzafar ayi ajiyar zuciya nan take yaji yayi nadama bisa jagorantar wannan tafiya, domin a yanzu zuciyarsa ta karaya, ya fahimci cewar abu ne mayuyaci gabadayansu su iya tsallake hatsarurrukan dake wannan daji, tunda gashi tun kafin su shiga wadannan mugayen dazuzzukan guda biyar sun raina jarumtakarsu, kuma wacce ba a taba zaton zata yi wani abu ba sai gashi ita ce ta fi kowa jarumtaka, kuma inba dan taimakonta dana sadauki Shaharan ba da sai kowa ya halaka.
Boka Muzafar ya kira gimbiya Rahila suna tattauna, inda ya dubeta ya ce yake jarumar jarumai kuma kuma sarauniyar kyawawa yq akayi kika samu irin wannan gagarumar jarumtaka haka ta karfin damtse alhalin a zahiri babu wani alamun sadaukantaka a tare da ke.
Koda jin wannan tambaya sai Gimbiya Rahila tayi murmushi tace inda zamu kwana uku ina baka labarin yadda aka yi na samu sadaukantaka ta lokaci ba zai ishemu ba har na gama baka labarin, amman gaba idan muna raye kuma da dama zan baka labarin, yanzu sai ku tashi mu cigaba da tafiya domin mu riski rukuni na biyu dana uku na wannan mugayen aljanu mu gama da su sannan mu shiga manyan dazuzzukan guda biyar wadanda daga su sai kogon darul ikisina.
Sa'adda Rahila ta zo nan a zancenta sai boka Muzafar ya dubeta ya ce haba yake jarumar jarumai shin bakya ganin gabadayanmu babu mai kwarin jiki a jikinmu face wadanda tsautsayin bai rutsa da su ba, ke kadaice mai cikakken lafiya a cikin wadannan jaruman wannan tafiya, ai dole ne mu zauna anan muyi jinyar jikinmu koda tsawon kwana biyu ne kuwa.
Lokacin da boka Muzafar ya zo nan a jawabinsa, sai sarki Lafaru dake daf da shi ya ji hankalinsa ya tashi, ya ji kamar ya fashe da kuka. Cikin tsananin ya dubi Muzafar ya ce ya kai babban boka shin mantane cewa ka ce dole ne na auri Gimbiya Ramlatus siyam a cikin kwanaki da baza su haura sittin ba, dan kuwa har muna bata lokaci a cikin wannan tafiya haka to gabadaya shirinmu zai wargaje.
Koda jin haka sai boka Muzafar ya daka wa Lafaru tsawa ya ce ya kai wannan sarki kayi sani cewa halin da muke ciki yanzu ba na tunanin yadda burinmu zai cika bane, muna kan tunanin yadda zamu tsira da rayuwarmu ne.
Sarki Lafaru ya dubi boka Muzafar a fusace ya ce wace irin magaana kake haka, ai rai ba a bakin komai yake ba muddin akwai biyan bukata.
Boka Muzafar ya sake fusata ya daka wa Lafaru tsawa a karo na biyu ya ce idan kai baka damu da rayuwarka ba, mu mun damu da tamu. Saboda haka idan zaka iya sai ka kama hanya kayi tafiyarka kai kadai, na fuskanci ka manta da cewa idan buri y cika babu rai sam bashi da wani amfani.
Koda gama fadin haka sai boka Muzafar ya koma gefe daya ya kishingida yana mai duban raunin dake jikinsa, shi kuwa sarki Lafaru sai ya matsa daf da gimbiya Rahila ya dubeta y ce Ya ke jarumar jarumai me zai hana ki zo mu cigaba da wannan tafiyar biyu rak, dan na fuskanci cewar ke kadai ma zaki iya maganin dukkan wasu masifun dake kan hanya.
Da jin wannan batu sai Gimbiya Rahila ta dubi Lafaru cikin tsananin fushi ta ce indai haka kake tunani to ka yaudari kanka, ina tabbatar maka da cewa idan har muka kuskura muka shiga wadannan dazuzzuka guda biyar babu jaruman can to sai mun halaka, domin ko wanne daji akwai jarumin da zai iya ceton rayuwarmu, dukkansu can da kake gani kowa da irin tasa baiwar da kuma sadaukantarsa, gama fadin hakan keda wuya sai Rahila ta je ta zauna nesa kadan da kowa, sannan ta kwanta domin ta huce gajiyar da ke jikinta.
Wannan shine abinda ya faru ga su sarki Lafaru bayan sun tattaro abokan tafiyarsu sun nufi kogon darul ikisina.
Acan birnin Kufa kuwa a ranar da kwanaki arba'in suka cika, tunda duku-dukun safiya aka hango dakarun sarki Nurwas sun durfafo, saboda yawan rundunar idan mutum ya hangosu daga nesa sai yayi zaton cewa sun tokare da sararin samaniya, saboda ba a iya hango karshensu, karar kofaton dawakansu da rakumansu kuwa ya cika kunnunwan mutane har ta kai cewa sun haddasa karamar girgizar kasa, ya zamana cewa gabadaya gidajen birnin Kufa sun kama girgiza kamar zasu ruguje. A lokacin da wannan al'amari ke faruwa sharlis na cikin bangarenta da danta Shaddadu a zaune tana koya masa yadda ake fada da takobi. Koda taji sukuwar dawakan abokan gaba sun durfafo birnin sai ta yi sauri ta shiga daki ta cire tufafin jikinta ta saka fararen sulke sannan ta saka wasu siraran takubba a kugunta na hagu da dama, kuma ta saka hular karfe sannan ta saka wasu dogayen takalma na fata iya gwiywa, hakika shigar da Sharlis ta yi ba karamin kyau ta yi ba, kuma ta yi kwarjini ainun. Da fitowarta daga cikin dakin sai kawai ta dauki danta Shaddadu ta goyashi ta daure tamau a bayanta, kawai sai ta ji Shaddad ya ce da ita Ya ke Ummata ya zaki tafi da ni yaki ban dauki takobina ba.
Koda jin haka sai sharlis ta yi murmushi ta ce kada ka damu ya kai dana lokacin fara naka yakin bai yi ba, yanzu dai in so kaga yadda nake nawa yakin ne dan ka koya. Tana gama fadin hakan sai ta fice da sauri ta nufi bangaren Sarki Lafaru, ga dakaru tsaitsaye a bangaren sarki Lafaru amman babu wanda yaga Sharlis da danta har ta isa can cikin turakar tasa. Da isarta sai kawai ta yi arba da Sarki Lafaru a tsaye yana shirin fita yaki har ya daura damara ya soka takobinsa, al'amarin da yayi matukar baiwa Sharlis mamaki kenan.
Koda Sarki Lafaru yaga sharlis tsulum a gabansa sai ya ja da baya a tsorace ya cw da ita Mene ne kuma ya kawoki wajena tare da danki?
Da jin wannan tambaya sai sharlis ta yi murmushi sannan ta ce Na fito ne domin taya ku yaki, ka sani cewa idan aka rushe daularka an cuceni dan haka bazan samu damar daukar fansa akan ka ba, sabida haka dole ne na bada tawa gudummawar a wannan yaki domin kare wannan birni. Sharlis ta sake duban sarki Lafaru cikin mamaki ta ce Yanzu kai saboda me kake shirin fita yaki, alhalin kasan cewa na cire maka dukkanin karfin damtsenka tun daga ranar da ka sadu da ni?
Sarki Lafaru yayi murmushi ya ce Ai abin kunyq ne a gareni ina sarki amman ace yau gashi an zo yaki kasata na buya ban fito ba, gwara na fito koda kuwa za a yi mani kwab daya ne na mutu.
Sa'adda Sharlis ta ji wannan batu sai ta bushe da dariya sannan ta ce ai indai abin kunya ne ka gamu da shi, sai nan gaba ma idan dana shaddar ya girma ya zama gawurtaccen sadauki da babu kamarsa, sannan ne zaka wulakanta mutuncinka ya zube, kimarka ta watse, duk dukiyarka ta salwanta, sannan a karshe ka rasa mulkinka da rayuwarka bayan dana yayi maka kisan gilla irin wanda kayi wa kakanni na da iyayena, lokacin da Sharlis ta zo nan a zancenta sai kawai taga sarki Lafaru ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya sannan ya ce Ni kuwa zanga yadda dana na cikina zai zamo abokin gabana har ya kasheni.
Da jin haka sai Shaddad da ke goye a bayan sharlis ya leko sannan ya dubi sarki Lafaru ya ce Ya kai abbana tabbatas zakaga yadda zan wualakanta ka a duniya, na tarwatsa kwanciyar hankalinka da dukiytarka, sannan da sannu na zama sanadin ajalinka.
Da jin haka sai Lafaru ya sake bushewa da dariya a karo na biyu, haka yayita wannan mahaukaciyar dariyar kamar ba zai daina ba, al'amari da yayi matukar baiwa Sharlis mamaki kenan ta fara zancen zuci ta ce "Anya kuwa wannan sarki Lafaru ne wanda na sani, a sanina tun daga ranar dana cire wa sarki Lafaru Sadaukantakarsa yake tsorona kuma ya tsorata da lamarina, shin mene ne yasa yanzu ya daina shakkata har ma yake magana cikin gadara, ya zama dole a gareni bayan na gama wannan yaki nayi bincike a cikin hallarar tsafina na gano ko shine Lafaru na gaskiya.
Marubucin yace wane bangare ne zai samu nasara a wannan azababben yaki da za'a fafata tsakanin mutanen sarki Nurwas da mutanen Sarki Lafaru?
Shin idan sharlis ta yi bincike a cikin hallarar tsafinta zata gano cewa Lafaru dake tare da ita ba na gaskiya ba ne, idan ta gano hakan wane irin mataki zata dauka?
Wace irin bakar wahala su boka Muzafar zasu sha a cikin wannan doguwar tafiyar dake gabansu ta zuwa kogon darul ikisina?
Su waye zasu rasa rayukansu a tafiyar?
Shin aljani Maraful Dauwas zai amince da bukatar su sarki Lafaru?
Shin sarki Lafaru zai samu mallakar Gimbiya Ramlatus siyam har ya aureta?
Shin Gimbiya Rahila zata cika burinta na samun daukaka da matsayin da take nema?
Marubucin ya ce mu hadu a Littafin Mazan jiya na Uku dan jin karshen hikayar Jarumi Shaddadu da kuma hikayar Sadauki Hulkas na birnin Romaniya.
Daga mai debe maku kewa a kullum da koda yaushe
Abdulaziz Sani Madakin Gini.