Showing 39001 words to 42000 words out of 59226 words

Chapter 14 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

mace ba, domin aljanu sun shafi al'aurarsa. Babu irin neman maganin da ba'ayi ba amman abu ya gagara. Daga baya ne bokaye suka tabbatar da cewa sai an debo masa tsumin ruwan maganin kogon darul ikisina yayi tsarki da shi sannan zai samu lafiya har ya iyayin aure.
Zarina da sarkin Farisa sun shaku ainun, kuma ko kadan batason taga abinda zai bata masa rai, a duk lokacin da sarkin Farisa a tuno da wannan lalura tasa sai yayi ta kuka da bakin ciki, kuma sai ya kwana uku bai ci abinci ba, ganin wannan hali da yake shiga ne yasa Gimbiya Zarina ta dauki alkawari cewa koda zata rasa rayuwarta sai ta je kogon darul ikisina ta debo wa dan uwanta tsumin wannan maganin.
Zarina ta yi alkawarin zata bani dukiya iya adadin abinda ta gada a wajen iyayensu akan na rakata zuwa kogon darul ikisina, amma sai na fada mata tayi hakuri sai lokacin tafiyar yayi, itama zan nemeta da kaina.
Abokin tafiyarmu na biyar shine Sadauki Shaharan Bn Lawwar na birnin Hairussalas, a duniya kaf babu wani mutum mai karfin gudu bisa turba tamkar Sadauki Shaharan, domin yana iya shafe gudun zira'i saba'in a cikin dakika sittin, a cikin daji na biyar da zamu ratsa mu wuce izuwa kogon darul ikisina akwai wata katuwar kunama guda daya jal, wacce ta kasance mai tsananin karfin gudu, domin udan ta kasa tsere da dawakai tana basu raya ta zira'i arba'in, kuma komai jurewar gudun mutum sai ta kureshi ta harbeshi, da zarar dafinta ya shiga jikin mutum take yake dahuwa ya narke kamar an kada ruwan kwai. Akwai wani ruwan kogi a karshen wannan daji, idan har mutum ya kasa tsere da wannan kunama kuma ya rigata fadawa cikin wannan kogi tana fadawa cikin kogin nan take zata mutu. Babu wanda zai iya kasa tsere da wannan kunama kuma ya rigata fadawa cikin wannan kogi face Shaharan, idan ya samu nasarar hakan ne zamu iya ratsawa ta wannan dajin ba tare da wannan kunama ta halakamu ba.
Sadauki Shaharan yana da wani ingarman doki mai tsananin gudu, tamkar shi kansa, shi dai wannan doki Shaharan yana shiga gasar tsere ta duniya da shi, sau shida ana yin wannan gasa a birnin Hairussalas yana lashewa ya zama zakara. Kuma duk bayan shekaru hudu ake yin wanna gasa, yanzu abokan gasar tasa sunyi wa dokin nasa asiri ya gurgunce gashi saura shekara daya ayi wannan gasa. Babu irin neman maganin da Sadauki Shaharan bai yi ba amman sai abu ya gagara, daga karshe ne shima bokaye suka tabbatar masa d cewa shima sai ya samo tsumin ruwan magani a kogon darul ikisina an shafa a kafafun dokin sannan zai iya mikewa har yayi wannan gasa.
Ssadauki Shaharan ya bugi kirji kan cewa koda zai rasa rayuwarsa ne to tabbas sai yaje kogon darul ikisina ya debo ruwan wannan magani, saboda gasar da za'ayi a shekara mai zuwa ita ce ta karshe, kuma zakaran daya lashe gasar za a bashi auren yar sarkin birnin Hairussalas gami da dukiya mai tsanin yawa da har mutum ya mutu bai isa ya karar da ita ba.
Dama can Sadauki Shaharan ana yana mutuwar son gimbiya Sharilat yar sarkin birnin Hairussalas domin dare da rana a cikin begenta yake, yana raira mata wakoki yana zubar da hawaye, a rayuwar Sadauki Shaharan sau daya ya taba ganin Gimbiya Sharilat, tun daga wannan rana kuwa bai sake yin bacci da daddare ba saboda tsananin begenta, kuma ba zai baccin ba face ya mallaketa ta zama matarsa.
Abokin tafiyarmu na shida ba wani bane face ni kaina, ni kadaine nasan hanyar da za bi a riski wadannan dazuzzuka guda biyar, kuma masifaffu sannan har abi ta cikinsu a isa kogon darul ikisina. Lokacin da boka muzafar ibn Mauzar yazo nan a jawabinsa sau yayi ajiyar numfashi domin makogwaronsa da harshensa su huta bisa doguwar maganar da yayi, shi kansa sarki lafaru sai da jaya dogon numfashi ya ajiye sabida tsananin mamaki, bisa jin wannan dogon bayanin da kuma sanin gagarumin aikin dake gabansu kan wanna tafiya mai tsananin hadari da wuya.
Boka muzafar yayi gayaran murya sannan ya ci gaba da bayanu kamar haka al'amarin aljani Maruful Dauwas kuwa, wanda zamu rik a cikin kogon darul ikisina kuwa mu nemi taimakonsa akan yaje ya sato mata gimbiya Ramlatus siyam, abune mai tsananin hadari a garemu, ya kai wannan sarki kayi sani cewa shi dai aljani maruful Dauwas ya kai shekaru ubu biyu da dari biyu a cikin kogon darul ikisina, kuma tunda ya shiga kogon sai yayi zamansa bai sake fitowa ba balle yaga mutum ko aljan dan uwansa, haka kuma bai sake shakar iska irin ta duniya ba, sannan kuma bai kara ci ko shan wani abu ba, dalili kuwa shine duk halittar data shiga cikin kogon darul ikisina ba zata sake jin yunwa ko kishin ruwa ba, kuma duk irin cutar dake jikinka sai ta warke, ko yaushe kogon a ni'ima yake babu zafi hakazalika babu snyi, bugu da kari idan har halitta ta shiga cikin wannan kogo to fa sai ta ninka adadin shekarunta sau dari a duniya sannan zata mutu walau mutum, aljan, dabba ko kuma kwaro, duk da cewa kawai wadannan ni'imomi a cikin kogon darul ikisina kulum aljani maruful Dauwas kulum cikin kuka da bakin ciki yake, kuma sai yayi kwana arba'in yana raira wakar bege ga masoyiyarsa Gimbiya Rashmin yar sarkin aljanu na birnin Hindu, har takai cewa hawayen nasa sun taru sun zama kamar kogi a cikin kogon darul ikisina, wanann kogi shine ruwan maganin da jaruman biyar suke bukata.
Yau kimanin shera dubu biyu da dari biyar kenan da mutuwar Gimbiya Rashmin wacce ta kashe kanta sakamakon mahaifinta sarkin aljanu na birnin hindu ya ki yarda ya aurar da ita ga bawanta aljani maraful Dauwas. Tun Aljani Maraful Dauwas yana da shekaru bakwai da haihuwa yake bauta a gidan sarkin aljanu, kuma Gimbiya Rashmin sa'arsa ce, wato kai daya suka taso, kuma tun a sannan shine bawanta mai kula da turakarta, abincinta gami da lafiyarta kasancewarsa dan babban likitan sarki.
Sarkin aljanu ya aminta kwarai da aljani Maraful Dauwas, kamar yadda ya aminta da mahaifinsa marigayi, kuma yana kaunarsa matuka, ba wani abu ne yasa Sarki aljanu yake matukar kaunar shi ba face abubuwa uku;
Na farko shidai aljani Maraful dauwas sadaukine, kuma tun yana yaro yake daka wa maza gumba a hannu a duk sa'ar da aka fita yaki.
Abu na biyu yana da matukar karfin gudu a sararin samaniya fiye da tunanin mai tunani, dan haka duk wata bukatar sarki ta gaggawa shine ake aikawa.
Abu na uku shine, shidai aljani Maraful Dauwas yana da amana matuka, domin komai yawan dukiya idan aka bashi ajiyarta bazai taba koda adadin kwayar zarra daga ciki ba, atakaice dai yadda sarki ya aminta da aljani Maraful Dauwas bai aminta da dukkanin iyalansa da matansa gami da sauran fadawansa ba. Kai wani lokacin ma bashi da abokin shawara face aljani Maraful Dauwas, duk da kasancewarsa karamin yaro amman akwai tunani gami da hangen nesa.
A kwana a tashi sai gimbiya Rashmin ta girma ta zama kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance, ya zamana cewa a wannan zamani babu kamarta a dukkanin matan aljanu na duniya, dan haka sai ?a?an Attajirai, bokaye, sarakai masu is da kansu suka rinka zuwa neman aurenta, ita kuwa sai ta ki yarda ta fidda gwani daga cikinsu.
A wannan lokaci dare da rana gimbiya Rashmin na tare da bawanta Aljani Maraful Dauwas, hatta mahaifiyarta bata shaku da ita ba kamar yadda ta shaku da bawan nata, kuma babu abinda ke rabasu face kwanciyar bacci, wani lokacin ma Gimbiya Rashmin ata barin Aljani Maraful Dauwas ya fita daga turakarta koda tana jin bacci, idan yaga haka sai ya shiga raira mata waka mai dadi, a cikin waken kalamai ne na koda kyawunta dan haka bata sanin sa'ar da bacci ke saceta sabida jin dadin waken.
A sannan ne yake samun damar fita daga cikin turakarta ya tafi nasa dakin. Ga bako idan yazo gidan sarautar sai ya dauka cewa Aljani Maraful Dauwas da Gimbiya Rashmin yan uwa ne na jini ba bawa da uwargijiyarsa ba.
Alama daya ce zata tona asirin hakan ganin yadda Aljani Maraful Dauwas ke yin aikin bauta a gidan sarautar da kuma yanayin suturar da yake sawa wacce bta kai darajar ta ?a?an sarakai ba.
Lokacin da sarkin aljanu yaga jama'a sun dameshi akan zuwan neman auren yarsa, sai ya kira Gimbiya Rashmin ya ce da ita "Ya ke yata na baki kwana arba'in kacal da ki fiddar da gwani daga cikin masoyanki, in ba haka ba kuwa zan baki wanda nake ganin ya dace da ke"
Ko da jin wannan batu sai hankalin Gimbiya Rashmin ya dugunzuma ainun, ta ce ya kai abbana ka yi sani cewa ni ban ta?a yin soyayya da wani da namiji ba, koma ban san ma mece ce soyayya ba, ya za a yi kazo ka yi mani titsiye a rana ?aya kace na fitar da gwani a cikin masoyana, alhalin duk samarin dake zuwa wajenka suke zuwa ba wajena ba, kuma babu wanda na tana yin hirar dakika daya da shi.
Koda jin wannan batu sai sarki ya turbune fuska tare da cewa Ya ke yata kiyi sani cewa idan baki yi aure a yanzu ba kimata da mutuncina ne zasu zube a idon duniya, domin dukkan masu sonki da aure sun kasance manyane a cikin al'ummar aljanu na duniya, shawara daya da zan baki itace kije ki samu wanda kike ganin kin yarda da shi, walau a cikin kawayenki ko yan uwanki, ko kuma mahaifiyarki kice da su suyi maki cikakken bayani akan irin namijin da ya kamata ki aura, kuma su fayyace maki mene ne so, domin ki san mahimmanci soyayya dan jada ki auri namijin da bakya kauna a cikin zuciyarki.
Koda sarki ya gama fadin haka sai ya mike tsaye ya fice daga cikin falon da suke zaune, fitarsa keda wuya sai gimbiya Rashmin ta shiga zancen zuci tare da cewa To ni yanzu wa ya kamata naje nayi wa wadannan nan tambayoyi, nikam a duniya babu wanda na yadda da shi sama da bawana aljani Maraful Dauwas, sabida haka lallai da shi zanyi wannan shawara.
Koda gama ayyana haka sai gimbiya Rashmin ta tafi izuwa turakarta, da shigarta cikin turakar sai ta iske Maraful Dauwas ya gama kimtsa komai na dakin yana gyara mata shinfida. Rashmin ta zauna a gefen gadon nata a lokacin da Maraful Dauwas ya kammala aikinsa tare da juyawa zai fice daga dakin, kawai sai yaji ta kira sunansa, kuma ta yafito shi da hannu tana mai yi masa nuni da ya zo ya zauna a gefen gadon kusa da ita.
Koda ganin haka sai zuciyar Maraful Dauwas ta buga da karfi, yaji kamar an doki ransa da guduma, tsoro ya kamashi. Amman sai yayi ta maza ya je ya zauna nesa kadan da ita yana dari-dari domin a iya shekarun daya kwashe yana yi mata bauta yauce ranar farko data tab umartarshi daya zauna kusa da ita.
Koda taga yadda yake dari+dari sai ta bushe da dariya ta cw haba ya kai abokina mene ne kuma haka naga kana rawar jiki, bafa wani abu zanyi maka ba, shawara kawai nake so ka bani, domin babu wani mahaluki dana aminta da shi sama da kai.
Sa'adda da aljani Maraful Dauwas yaji wannan batu sai hankalinsa ya kwanta har ya saki murmushi tare da cewa To ina sauraronki fadi bayaninki naji kuma zanyi iya kokarina wajen baki shawarar da zata fissheki.
Gimbiya Rashmin tayi gyaran murya sannan ta fara da cewa Ya kai abokina kuma amintaccena, kayi sani cewa ayau din nan sarki ya kirani kuma yace na fidda gwani daga cikin masoyana, ni kuwa sai nace da shi ya za a yi na fidda gwani alhalin bantaba yin soyayya ko da dayansu ba, kuma bnsan ma meye soyayyar ba. Koda jin haka sai yace dani naje na nemi wnada na aminta da shi ya bani shawara akan irin mijin daya kamata na aura, kuma yayi mani bayanin mece ce soyayya domin na fahimta sosai.
Lokacin da Gimbiya Rashmin ta zo nan a zancenta sai Aljani Maraful Dauwas yayi murmushi sannan ya ce aiko kinyi tambaya gareni mai sauki kuma mai saukin bayani, da farko dai ina so kisan cewa ita soyayya wata abace wacce ake fara yinta bisa gamon jini, amince da kuma yarda da juna, daga nan sai sabo gami da shakuwa su sa tayi karfi ainun a cikin zuciyar masoya, har takai cewa suna son kasancewa a tare ko yaushe. Idan soyayyar tasu ta kara karfi sai suji cewa duk wuya d tsanani bq zasu iya rabuwa da juna ba, kuma basu da burin daya wuce su zama abokan rayuwa ga junansu, wannan shine abinda ake kira soyayya. Shawarar da zan baki dangane da irin mijin da ya kamata ki aura shine kada ki duba matsayinsa, mulkinaa ko kuma daukakarsa, kiyi duba izuwa halaye na gari, shi din mai gaskiya ne, shin idan aka bashi b zai ci ba, shin zai iya kare mutuncinki gami da lafiyarki, kuma zai iya sallama rayuwarsa domin kare ta ki, shin idan yayi alkawari yana cikawa, tsawon wane lokaci kuke tare sannan ya girman shakuwarku ta ke, yau udan babu mahaifinki zai ci gaba da darajtaki gami da ririta ki, waye zai iya jibantar alamarinki duk sa'ar da wata masifa ta fado maki ba tre da yayi shakkar komai ba. Wadannan sune abubuwan da ya kamata kiyi amfani da su wajen zaba wa kanki mijin da zai dace da ke.
Sa'adda da Maraful Dauwas ya zo nan a zancensa sai kawai yaga hawaye ya zubo daga idanun Gimbiya Rashmin, al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalinsa kenan ya razana kuma ya sakko kasa daga kan gadon, ya tsugunna bisa gwiywoyinsa yana mai cewa ki gafarceni ya shuga ta idan har bayanin da nayi maki ya bata maki rai.
Koda jin haka sai Rashmin ta share hawayebta sannan itama ta mike tsaye ta kama hannayen aljani Maraful Dauwas a karo na farko a rayuwarsu ta tadashi tsaye ta ce Ya kai amintaccena ka yi sani cewa ba komai bane yasa kaga wannan hawaye nawa ba face sai a yaune na san cewa akwai magani a gonar yaro, amman rashin sani ya hanashi amfani da maganin. Lokacin da kake ta yi mani wannan jawabin sai na fahimci cewar babu wani mahaluki da yake da wadannan abubuwa daka lissafo wanda na sanshi a rayuwata face kai, kqine kadai mahalukin da nayi sabo da shi, kuma na shaku da shi ainun, tun daga kuruciyata kawo izuwa girmana, kaine kadai wanda nasan cewa zai iya sallama rayuwarsa domin tawa sabida ka tseratar da rayuwata sau ba adadi, kainne kadai nasan cewa na bashi amanata amman bai ci ba, kaine wanda baka taba karya mani alkawari ba, kuma kaine kadai nasan cewa ko babu ran mahaifina zaka ci gaba da darajta ni, ashe kuma lallai kaine namijin d ya dace na aura dan haka sunanka zan ambata a wajen mahaifina.
Koda gimbiya Rashmin ta zo nan a zancenta sai Maraful Dauwas ya kamu da tsanankn tsoro kuma ya fisge hannunsa daga cikin nasa da sauri, a sannan ne shima hawaye ya zubo daga cikin idonsa kuma ya dan ja baya daga gareta ya ce "Ya shugabata ina kika taba ganin bawa ya auri yar sarkinsa, har abada ruwa ba sa'an kwando bane, ina mai rokonki da ki taimakeni kuna ki janye wannan batu daga zuciyarki gami da bakinki, ki tuna cewa mahaifinki yana da zafi, idan har kika furta masa wannan al'amari zna iya fuskantar fushinsa, kuma allura zata tono garma, wata kila ma sanadin rabuwarmu kenan.
Koda jin haka sai gimbiya Rashmin ta rugo izuwa kan Aljan Maraful Dauwas ta rungumeshi, sannan ta fashevda kuka tana mai cewa aiko idan aka rabani da kai duk wanda zai aureni sai dai ya kwanta da gawata amman ba ni ba.
Kafin Maraful Dauwas yace wani abu sai kawai suka ga an turo kofar dakin da suke ciki an shigo, ba wani bane ya shiga ba face sarki da mahaifiyar Gimbiya Rashmin sunata hira gami da dariya, koda suka yi arba da Gimbiya Rashmin tana rungume da aljani Maraful Dauwas sannan duk su biyu suna hawaye, sai sarki ya kwarara uban ihu cikin tsananin fushi, nan take dakarinsa suka rugu da gudubizuwa inda suka ji ihun sarki, da zuwansu sai sarki ya ce dda su su kama Maraful Dauwas uyita dukansa har sai ya suma sannan su kulleshi.
Ai kuwa nan take wadannan dakarubsuka cika aikin sarki, a lokcin da Gimbiya Rashmin ta rinka ihuwa gami da kururuwa tana kokarin ta kifa kansa dan su daina dukansa, amman sai sarki ya riketa gam da hannunsa biyu, a gaban idonta aka sumar da masoyinta aljani Maraful Dauwas aka kuma tafi da shi.
Nan take itama Gimbiya Rashmin ta sulale kasa sumammmiya.
Cikin firgicewa da dimaucewa sarki da matarsa suka shiga yi mata fifita, da kyar da shidin goshi suka samu ta farfado. Daga wannan rana Gimbiya Rashmin ta kwanta cuta ya zamana cewa kullum tana kwance kuma bakinta baya ambaton komai face bawanta kuma masoyinta aljani Maraful Dauwas. Hakan bata sa sarki yayi umarni akan a saki Aljani Maraful Dauwas daga kurku ba, kawai ma sai ya mayarvda hankalinsa akan nema wa yarsa Rashmin magani, har sai da takai cewa an hada da karfin sihirin tsafi wajen juyar da kwakwalwar gimbiya Rashmin akan ta manta da bawa Maraful Dauwas sannan aka samo kanta ta samu lafiya.
Shiko bawa Maraful Dauwas a kullum sai an gana masa azaba kala dubu a cikin wannan kurkukun, ya zamana cewa ya lallace kuma ya rame sanna ya fita daga cikin hayyacinsa, komai rashin imani da tausayinka idan ka dubi aljani Maraful Dauwas a wannan lokaci ole ne ka zubar masa da hawaye.
A ranar da aka daura auren Gimbiya Rashmin da dan sarkin aljanu na birnin Misra ne, to a ranar ne wannan asiri da aka yi mata na juyar da ?wa?walwarta ya karye, kuma a daidai lokacin da ango ya shigo dakin amaryarsa, koda amarya ta dago da kai taga ba Maraful Dauwas bane sai ta kwala uban ihu, kuma ta dauki wata wuka dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login