Showing 30001 words to 33000 words out of 59226 words
Chapter 11 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
gaba dayan mazajen da ke filin
wannan yaki walau na mutane ko na aljanu babu mahalukin da
bashi da raunuka a jikinsa,hatta manyan baraden kuwa, wato su
sarki Dujalu da su Inmal.
Bayan kOwanne bangare sun ja da baya nesa da juna sai aka
shiga aikin binne gawarwaki, masu kuka nayi, masu bakin ciki
nayi, kuma a sanann ne kOwa ya rinka neman ruwan sha da
abinci, sannan kuma aka rinka sanya magani a raunika. Masu
karaya aka rinka gyarasu suna ihu bisa jin radadi da zogin
gyara.
Manyan mazaje kuwa, za ka ga sun yi shiru ko motsi basa yi. In
ba don albarkacin mata ba wadanda aka taho da su wannan
yaki da ba za a sami masu dawaniyar kula da lafiyar mutane ba
domin gaba dayan mazajen babu wanda bai jigata ba ainun,
wasu ma kamar ba za su rayu ba wasu kuwa sun gama zama
nakasassu ba zama su iya ci gaba da yaki ba.
A 6angaren su sarki Maharaz kuwa,bayan an kafa tantuna sai
sarki Maharaz, Hibru da Inmal suka taru a cikin tantin sarki
Maharaz kuyangi na sa musu magani a jikin raunikan jikinsu,
gimbiya Mulaifa ce da kanta take sawa Inmal magani a jikinsa
bata yarda wata kuyanga ta taba shi ba.
Bayan an tsaida jinin da ke zuba a jikinsu kuma sun ci abinci
sun sha ruwa sun sami 'yar nutsuwa sai sarki Maharaz ya ja
dogon numfashi sannan ya dubi sarkin yaki Hibru ya ce, "Ya kai
abokina yanzu a hangenka me kake ganin zai faru idan aka ci
gaba da wannan yaki?"
Koda jin wannan tambaya sai shima
Hibru yai ajiyar zuciya sannan ya dubi sarki Maharaz ya cc, "Ya
shugabana ni dai a ganina a Karshen yakin nan RAGAS za a yi
kowa da komai sai ya mutu, ka ga ke nan babu bangaren da zai
iya mallakar wannan takobi ta Saiful Lujara da ke karkashin
tekun nan tun da gashi muna kallon tekun da idanuwanmu
amma shiga cikinta ma ya gagaremu bare ayi laluben inda
takobin take."
Koda jin wannan batu sai Inmal ya yi murmushi saman ya dubi
Hibru ya ce, "Haba ya Abbana saboda me za ka yi waman batu,
ai har abada mutum ba ya fidda rai ga samun rabo muddin yana
numfashi a doron Kasa. Ni a rayuwata zuciyata ba ta taba
karaya ba bisa samun abin da zuciyata ke so. Na yi imani da
hakan dari bisa dari saboda haka na Kudurce a raina idan kowa
da komai zai hallaka a bakin wamnan tekun ya zamana saura ni
kadai jal lallai sai na lalubo takobin saiful Lujara a karkashin
wannan teku kodakuwa zan hallaka a kokarin hakan. Ai rai ba a
bakin komai yake ba muddin akwai biyan bukata".
Koda jin haka sai sarki Maharaz ya yi murmushi ya cc, "Da kyau
jarumin jarumai,
tauraron zamani, ka ci gaba da jajirccwa bisa wannan Kuduri
naka koda kuwa gaba dayan jama'ata zamu karc ya zamana
saura kai kadai jal. Ka sani ccwa idan har ka sami nasarar
mallskar wannan takobi ta Saiful Lujara sannan ka mallaki
mashin Galilil Haras da hular Lamsara ka ajiye abin tarihin da
babu wani mahalukin da ya ta6a ajiyewa a duniya,kuma sai ka
sami daukaka wacce babu wanda zai samu. Ya kai abin
alfaharina kuma mafarkina na gobe kayi iya yinka don ganin ka
cimma buri ka sani cewa rayuwarmu gaba daya a yanzu ta
dogara da iyakar kokarinka domin karfin sihirinmu da karfin
damtsenmu ba za su iya yin komai ba face kawai kara maka
Kwarin guiwa."
Sa'adda sarki Maharaz ya zo nan a zancensa sai Inmal ya cika
da tsananin mamaki ya dubeshi ya ce, "Ya shugabana ya ya ni
da nake yaro kankani a cikinku za ka ce rayuwarku ta dogara a
hannuna? Ka yi sani cewa ni kaina na tsorata da al'amarin sarki
Dujalu a lokacin da muka fara fafata yaki ni da shi, domin ban
ta6a ganin mutum mai tsananin karfin dantse kamar sa ba,
gami da zafin nama.
Sannan yana da matukar juriya da naci fiye da yadda nake da
su. Duk da cewar zuciyata bata taba karaya ba akan dukkan
al'amari amma a wannan karon akwai darsuwar kokwanto a
cikinta".
Sa'adda sarki Maharaz yaji wamnan batu na Inmal sai ya bushc
da dariya sannan ya dubi 'yarsa Mulaifa kuma ya dubi Inmal ya
ce, "Ai kuwa idan har nayi tsawon rai a waman yaki sadakin
aurenka na yata Mulaifa shi ne samun nasararka akan dauko
takobin Saiful Lujara a cikin Karkashin wannan teku. Idan har ka
kasa dauko wannan takobi to har abada ba za ka auri 'yata ba".
Koda gama wannan jawabi sai sarki Maharaz ya kishingida bisa
shimfidar da yake zaune ya lummshe idanunsa. Shima Hibru sai
ya yi koyi da abin da sarki Maharaz ya yi.Gimbiya Mulaifa da Inmal kuwa sai suka Kurawa jumansu idanu cikin tsananin
tashin hankali da fargaba. Nan take hawaye ya zubowa Mulaifa
ta rungume iNmal tana mai yi masa rada a kunne ta ce, "Idan
har kaunar da kake yi mini ta gaskiya ce duk yadda za ka yi ka
tabbatar da cewa ka dauko wannan takobi ta
Saiful Lujara. Idan kuwa ka kasa bana tsammanin ccwa zan ci
gaba da rayuwa a duniya".
Koda jin wannan batu sai idanun Inmal suka zazzaro yaji
hankalinsa ya yi mummunan tashi, bai san sa'adda jikinsa ya
kama tsuma ba yaji kamar ya tashi ya ruga da gudu ya dauki
kahon yaki ya busa domin a ci gaba da wannan masifaffen yaki.
Wannan shi nc abin da ya faru ga su Inmal bayan an fafata
azababben yaki tsakanin ruodunarsu da rundunar sarki Dujalu a
karo na farko a bakin tekun bahar Sufiya.
A CAN BANGAREN kuwa, bayan sun binne na su
su sarki Dujalu
gawarwakin kuma an kafa tantuna an duba
marasa lafiya kowa ya dawo cikin haiyacinsa
kuma an kafa tantuna sai sarki Dujalu ya
kadaita da yar uwarsa Hursiya a cikin tantinsa
inda ta rinka sa masa magani a jikin raunikan
da ke jikinsa. Koda ta ga raunikan sun kai guda
bakwai kuma duk masu zurfi ne, wasu ma sai
da ta dinke masa fatar sai zuciyarta ta karaya
bata san sa'adda ta fashe da kuka ba. Cikin matukar mamaki
sarki Dujalu ya dubi Hursiya ya ce, "Ya ke 'yar uwata ina dalilin
wannan kuka naki?"
Hursiya ta dago kai ta dubi sarki Dujalu cikin tsananin damuwa
ta ce, "Ya kai dan uwana ka sani cewa a duniya bani da kowa
face kai. Zuciyata ta karaya bisa ganin wadannan manyan
raunika na jikinka har ina ganin cewa abu ne mawuyaci mu
sami nasarar wannan yaki. Yanzu idan babu kai ya ya zan yi
rayuwa a diniya?"
Sa'adda Hursiya ta zo nan a zancenta sai sarki Dujalu ya kamu
da tsananin tausayinta har idanunsa suka ciko da Kwalla
sannan ya ce, Ya ke yar uwata kiyi sani cewa duk irin gumu da
bala'in da za a yi a wannan yaki a ba zan taba mutuwa ba
ammma bincike ya nuna mini cewa zan shiga mugun yanayi
kamar zan mutu da ni da babban jarumi na cikin abokan
gabarmu, wato wannan yaro Inmal dan sadauki Hibru.
Ni da shi duk ba zamu mutu ba amma duk irin yanayin da na
shiga sai shima ya shiga.A cikin binciken nawa na gani cewa
mutum hudu
ne kacal za su tsira da rayuwarsu a wannan yaki amma na kasa
gano ko su waye, ragowar mutum biyun bayan ni da Inmal. Abin
da nake so da ke shi ne, kafin a ci gaba da wannan yaki a karo
na biyu ki sulale ki bar wajen nan gaba daya ki koma can
nahiyarmu ki ci gaba da mulkin Kasarmu ta Hawarul din in da
muka baro mata, yara da tsofaffi, domin idan har baki koma ba
gaba dayan jama'armu za su shafe a doron kasa a manta damu
har abada. Idan har Inmal ya rigani dauko takobin Saiful Lujara, ki sani cewa hadimina aljani Baizurul Aufan na can a baya cikin
dajin Saurul yana jiranki domin tuntuni na shirya hakan.' Lallai
za ku yi wannan tafiya lafiya har ki isa gida babu wani tsautsayi
da zai sameki"
Sa'adda sarki Dujalu ya zo nan a zancensa sai Hursiya ta sake
fashewa da matsanaicin kuka kuma ta rungumeshi ta ce, "Ta ya
ya kake tsammanin zan iya tafiya na barka anan ana wannan
masifaffen yaki? Lallai ba zanje ko ina ba in ba tare da kai ba,
sai dai nima ajalina ya riskeni anan din. Ai sadauki Hibru ya yi
bayanin gaskiya da ya ce rayuwa ba ta da amfani idan babu
masoyi. Ka sani cewa mulki
da dukiya ba za su taba haifar da kwanciyar hankali ba a
rayuwata muddin babu kai a kusa da ni. Ka tuna cewa tun da na
taso ban san uwata ba kuma ban san ubana ba sai kai.
Babu wanda na shaku da shi a duniya sama da kai.
Babu irin jin dadin da baka bani ba a kullum kana riritani baka
son koda kuda ya sauka a jikina. Waye zai iya yi mini irin
wannan gata da ka yi mini?
Waye zai iya kare lafiyata kamar yadda ka kare kuma waye zai
soni kamar yadda ka soni? Na ka-na ka ne har abada ba zan
taba samun madadinka ba. Ina tabbatar maka da cewa idan zai
zamo ni kadai ce na rayu a filin yakin nan kuma na sami ikon
mallakar takobin Saiful Lujara, ba zan koma gida ba na ci gaba
da rayuwa sai dai na binne kaina a kusa da kabarinka domin
mutuwa ce kadai za ta iya kawar mini da bakin cikin rashinka."
Lokacin da Hursiya tazo nana zancenta sai shima sarki Dujalu
ya fashe da matsanaicin kuka kuma ya kankameta a kirjinsa
yana mai cewa'Hakika abin da ke shirin faruwa a gareni yana
neman ya zama dai-dai da yarda
rayuwar sadauki Shaddadu na birnin Kufa ta
kasance."
Koda jin wannan batu sai Hursiya tayi wuf ta janye jikinta daga
cikin na sarki Dujalu suka fuskanci juna sannan ta ce, "Mene na
ya faru ga rayuwar sadauki Shadaddu?".
Sarki Dujalu ya sunkui da kansa kas ya yi ajiyar zuciya sannan
ya fara ba ta labari kamar haka.
AWANI ZAMANI can baya, wanda
ya zo dai dai da zamanin sadauki
Hantaru na bimin Kisra,an yi wani azzalumin sarki a birnin Kufa
wanda ake kira da suna
Lafaru ibini Hurdas.
Sarki Lafaru ya mallaki dukiya mai tsananin yawan gaske, kuma
sai da ya shekara arba'in a duniya bai ta6a yin aure ba kuma bai
taba yin rashin lafiya ba koda kuwa ciwon kai na tsawon dakika
daya.
Sarki Lafaru ya kasance sadaukin sadaukai mai dakawa maza
gumba a hannu domin a tarihin rayuwarsa ya ziyarci yakoki
guda dari da ashirin yana samun nasara kuma
ko karce jikinsa ba a ta6a yi ba a wajen yaki.Saboda tsananin
jarumtakarsa, zafin namansa da kuma tsagwaron sa'a.
A rayuwar sarki Lafaru bai taba yin tsafi ba, kuma tsafi baya
cinsa, baya dogara da komai face tsagwaron karfin damtse. A kasarsa gaba daya ba a yin addini ko wanne iri, idan kuwa aka
kama mutum yana wani addini koda a 6oyene sai an kashe shi.
Sarki Lafaru na da wata muguwar al'ada ta yiwa mata fyade,
domin a duk sa'adda ya ga kyakkyawar mace in dai ya yi
sha'awarta ko matar wa ce sai ya mangareta ta sume sannan
ya biya bukatarsa da ita. Daga wannan rana sai ya sa a tsare
wamnan mace har tsawon wata shida sai an tabbatar da cewa
bata sami ciki da shi ba sanann zai sa a saketa.
Idan kuwa ta sami ciki ta ke zai sa a hallakata. Dalili kuwa shi
ne, ko kadan sarki Lafaru baya son ya sami magaji a duniya
saboda jarumtakarsa ta gado ce iyaye da kakanni, ma'ana
babansa ya kasance, shima kakansa haka yake kuma abin ya
biyo salsala tun sarkin kufa na farko.
Lokacin da sarki Lafaru ya sami tarihin wannan al'amari a cikin
kundin tarihin sarauta
na gidansu sai ya kudurce a zuciyarsa cewa shi ne zai zamo
sarki na karshe mai wannan baiwa ta jarumtaka da karfin lafiya,
don haka ba zai taba yarda ya haifi magajinsa ba.
Wani abin mamaki dangane da rayuwar sarki Lafaru shi ne a
duk shekara sau daya yake sawa a nemo masa budurwa wacce
babu kamarta a fagen kyawu a kasarsa. Ana kawota sai ya
sumar da ita ya biya bukatarsa da ita.Sai da ya shekara ashirin
akan karagar mulki yana wannan muguwar dabi'a. A cikin
shekara ta ashirin da daya ne al'amura suka zo da sauyi domin
a wannan shekarar ne aka kawo masa wata tsaleliyar budurvwa
mai suna Sharlis wacce tsananin kyawunta ya fi gaban
kwatance.
Da la'asar sakaliya sarki Lafaru na zaune a fadarsa an
kewayeshai ana fadanci sai ga Sharlis an shigo da ita. Nan take
gaba dayan mutanen da ke fadar suka rude suka dimauce bisa
ganin tsananin kyawun Sharlis. Shi kansa sarki Lafaru bai san
sa'adda ya mike tsaye ba jikinsa ya kama tsuma ya taka
kafafunsa ya nufi inda Sharlis ke tsaye sabanin yadda ya saba yi
a duk shekara, sai dai akai budur war
har gabansa.
Sarki Lafaru ya iso daf da Sharlis ya tsaya yana mai kura ma ta
idanu a lokacin da gaba dayan jikinta ke karkarwa saboda tsoro
kuma hawaye na zuba a idanunta. Sarki Lafaru ya daga
hannunsa da nufin ya make Sharlis domin ta suma ya biya
bukatarsa da ita amma sai ya kasa dukanta. Al'amarin da ya
matukar baiwa kowa mamaki ke nan a fadar aka mimmike tsaye ana al'ajabi. Koda ganin haka sai
kunya ta kama sarki Lafaru. Nan take ya yi tsawa ga jama'a ya
ce, "Kowa ya fice daga cikin fadar".
Cikin firgici jama'a suka fice da gudu ya zamana saura su biyu
kacal a cikin fadar.
Nan fa sarki Lafaru ya kamo Sharlis ya kwantar da ita akan
karagarsa ta mulki ya biya bukatarsa da ita. Faruwar hakan ke
da wuya sai yaji kansa ya sara ya kama ciwo.
Al'amarin da ya kama matukar razanashi ke nan kuma ya
harzuka. Kawai sai ya zare takobi zai sare Sharlis.
Bisa mamaki sai ya ga ko gezau bata yi ba bare ta firgita.Sharlis
ta dubeshi a fusace ta ce'Mene ne ya hanaka ka kasheni? Ai
gwara ka
kasheni domin na huta da bakin cikin da ka
dasa mini a zuciyata.
Ka yi sani cewa a lokacin da dakarunka suka je kamoni a can
kauyenmu na Bairul sai da suka kashe iyayena da duk mutanen
gidanmu sannan suka bunkawa gidanmu wuta kuma suka
kwashe duk dukiyar gidan saboda kawai mahaifina ya ce ba zai
bayar da ni ba.
Ka sani cewa yau shekarata goma sha takwas a duniya kuma
tun da aka haifeni ban taba fita ko ina ba daga cikin gidanmu
kai asalima ban taba ganin wani da namiji ba face mahaifina
domin babu maza a gidanmu sai mata.
A ranar da dakarunka suka kawo mana farmaki ne na ga maza
a rayuwata. Kaine namijin farko da ya sanni 'ya mace kuma
kaine za ka zamo na karshe domin bokan mahaifina ya tabbatar
mini da haka. Ya kai wannan sarki kayi sani cewa tun da aka
haifeni mahaifina ke 6oyeni saboda tsoron kada na fado
hannunka bisa muguwar dabi'arka da ka saba yi akan
kyawawan mata, ashe shuka ya yi a idon makwarwa.
Kuyangar mahaifina ce wacce ya aminta...
ashe shuka yayi a idon makwarwa domin kuyangar mahaifinace wacce ya aminta da ita fiye da kowa a duniya kuma itace wadda ta reneni har na girma taci amanarsa saboda kwadayin abin duniya ta labartawa dalkarunka batuna.Tabbas bukatarta ta biya ta sami dukiya mai yawan gaske ta siyar da mutuncina gareka.To kasani cewa sakamakon wannan cin zarafi dakayi mini daga yau burinka ya rushe lallai sai na haifa maka magaji,daga yau sai rayuwarka gaba daya ta sauya kai da samun cikakkiyar lafiya har abada,jarumtakar dakake takama da ita ta dakushe,duk dukiyar daka tara ta zalunci sai ta kare,sai ya zamana cewa babu mai fada aji a garin nan face ni Kafin sharlis ta gama rufe bakinta tuni sarki lafaru ya kai mata wawan sara da nufin ya cire mata kai.Bisa mamaki sai yaga takobin ta wuce ta cikin jikinta kamar ratsawar ba.
Koda ganin haka sai sharlis ta bushe da dariya sannan tace,"Ai tuni alkadarinka ya karye tun sa'adda ka kasa sumar dani lokacin dazaka tara dani.Bazaka iya kasheniba kuma bazaka iya cutar daniba domin daga yau tsafi yafara tasiri ajikinka.Abinda nakeso dakai kawai shine,ka rufawa kanka asiri kabar komai a zuciyarka bisa abinda yafaru yanzu tsakanina dakai.zaifi kyau kasa a kebeni a gidan sarautar nan inda babu mai ganina har izuwa lokacin dazan haife maka danka.Idan ka bini kamar yadda nakeso zan iya dawomaka da duk abinda karasa amma sai bayan dana yagirma ya gajeka,idan kuwa kayi mini taurin kai haka zan barka cikin takaici har izuwa karshen rayuwarka kuma ina tabbatar maka cewa bazaka maimaita shekarunka ba a duniya.wato bazaka shekara tamanin ba a duniya tunda yanzu ka cika arba'in dai-dai.Wannan shine furucina na karshe gareka yanzu saika sanya akaini bangaren dazan zauna acikin wannan gida naka. Lokacin da sharlis tazo nan a jawabinta sai sarki lafaru ya fusata ainun yarufeta da duka.Bisa mamaki saiyaji ashe iska kawai yaketa duka kawai,gata dai tsaye a gabansa tana tayi masa dariya amma ya kasa taba jikinta.Koda ganin haka sai sarki lafaru yakamu da tsananin bakin ciki yafashe da kukan takaici.Babu abinda yafiyi masa ciwo face ganin yadda 'ya mace ta gagareshi alhalin manyan mazaje ma yazame musu GUGUWAR ANNOBA,yazamo tamkar dodo a nahiyar gaba daya har anayi masa kirarida KURA MAI TARWATSA GARI!Yau gashi kura ta zama akuya domin bazata iya tsorata kowaba.Sai da sarki lafaru yadade a tsaye yana kukan takaici sannan sharlis ta daka masa tsawa tace,"zakayi abinda na umurceka dayine kokuwa sai na tara fadawanka da jama'ar gari na tozartaka agabansu kowa ya san cewa yanzu kai ba kura bane akuyace. Koda jin haka sai sarki lafaru ya kwalawa sarkin gida kira.Nan take sarkin gida yashigo da gudu yafadi gaban sarki lafaru yadubi sarkin gida yace"maza ka yiwa gimbiya jagora izuwa bangaren nan daba'a taba budeshiba
Sarki lafaru yace ina son yanzu-yanzu a bata bayin dazasu dinga yimata hidima kuma kada kowa ya kusanci inda take face kuyangin nata,Koda jin wannan umarni sai sarkin gida ya cika da tsananin mamaki bisa jin wannan sabon umarni wanda ya saba da al'adar iyaye da kakannin sarki. A tarihin gidan sarautar babu wani sarki da ya taba ajiye mace acikin gidan sai dai a wajen gidan sarautar amma yau sai gashi sarki lafaru yakarya wannan ka'ida.Bisa wannan daliline sarkin gida yatsaya nuku-nuku ya ki bin umarni.Aikuwa sai sarki lafaru yadaka masa tsawa,cikin rawar jiki sarkin gida yamike tsaye zumbur yayiwa sharlis jagora izuwa cikin gidan sarautar,sharlis ta waigo tayiwa sarki lafaru murmushin mugunta.Nan take sarki lafaru yafadi kasa yasake fashewa da kukan zuci don kada hadiman gidan sujiyo sautin kukansa. Daga wannan rana komai na rayuwar sarki lafaru ya sauya,kuma al'amura suka sauya gaba daya birnin ya zamana cewa matsafa sun sami yancin kansu suna iya yin harkokinsu a ko'ina kuma koyaushe sabanin da can da idan aka kamasu ana kashesu.Mutane suka rinka yin addinai iri-iri.a duk bayan kwana talatin ko arba'in sai sarki yakwanta rashin lafiya har sai an nemo likitoci sun kawomasa daukiwani lokacinma sai bokaye sun bada taimako sannan yake samun lafiya.Duk irin zaluncin da sarki yasabayi na kwacewa talakkawa dukiyarsu ya daina kuma har tsawon shekara ukku bai kara yiwa wata budurwa fyadeba.Gaba daya mutanen birnin kufa sai da suka cika da