Showing 27001 words to 30000 words out of 59226 words
Chapter 10 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
Cikin zafin nama Hibru
ya sunkuya kuma ya yi alkafira a kasa a karkashin Kafafun
dodon, a lokacin da hannun dodon ya bugi iska ya tafi ya share
wadansu manyan bishiyoyi guda bakwai da ke tsaye a jerc.
Gaba dayan bishiyoyin sai da suka
tun6uko daga cikin Kasa har jijiyoyinsu suka zube kasa saboda
tsananin karfin dantsen dodon. Kafin dodon ya juya bayansa
inda Hibru yake sai Hibru ya dankara masa sara,take tartsatsin
wuta ya tashi sakamakon haduwar takobin da gashin jikin
dodon. Kawai sai Hibru ya ga hayaki na tashi a gaba dayan jikin
takobin tasa, kuma ko ina a jikin takobin ya huje saboda tsinin
gashin dodon ne ya caccaketa.
Koda dodon ya juya bayansa ya yi arba da Hibru sai ya kai masa
cafka. Hibru ya yunkura domin ya goce, amma sai dodon ya
sami nasarar dankarsa kawai sai ya dagoshi sama ya wangame
bakinsa zai jefashi ciki ya lankwame.
Koda Inmal ya hango abin da ke shirin faruwa ga mahaifinsa sai
ya falfala da matsanaicin gudu irin wanda bai taba yi ba a
rayuwarsa kuma ya daka wawan tsalle ya dira akan cinyar
dodon ya kama kafarsa ya dinga hawa samansa tamkar
kadangare na hawa bango.
Kafin dodon ya jefa Hibru a cikin bakinsa tuni Inmal ya isa kan
kafadar dodon ya caka
masa takobin a cikin katuwar Kwayar idonsa.B& shuri dodon ya
saki Hibru ya fado kasa kuma y�� kurma ihu irin nasu na dodanni
a lokacin da Kwayar idon nasa ta fashe ruwan jini ya balle
tamkar an bude IDANTYAR RUWA?
Nan fa dodon ya haukace ya rinka kai naushi, bugu da taku da
hannaycnsa da Karafinsa ya zamana ccwa yana tarvwatsa
bishiyoyi da duwatsun dajin suna fashewa da ratattakewa. Duk
inda dodon ya kai takau da kafarsa sai ka ga kasa ta rufta tayi
rami zururu.In ba don Inmal na da matukar zafin nama ba da
tuni dodon ya tattakeshi shi da Hibru amma sai Inmal ya suri
Hibru tamkar ya suri dan yaro ya goyashi a bayansa ya falfala
da mzteznaicin gudu suka kasa tsere da dodon.Dama:tmi
shima sarki Maharaz ya cika wandonsa da iska ya tashi sama
da karfin sihiri ya ruga izuwa cikin daji.
Inmal ya ci gaba da gudu iya karfinsa amma da ya waigo sai ya
ga wannan dodo daf da shi. Babban abin da ya fi tayarwa da
Inmal hankali shi ne, takun kafafun dodon bisa kasa yana haifar
da girgizar kasa a dajin gaba daya,
kafin Inmal ya isa wurin ma sai ya ga kaser gabansa ta zabtarc
tayi rami, sai ya daka wawan tsalle ya tsallake ramin.
Shi kuwa dodon komai zurfin rami da fadinsa da ya daga
kafarsa daya sai ya shallakeshi.
Lokacin da Inmal ya fara wannan gudu ne ya lura da halin da
jama'arsu suka shiga,kawai sai gimbiya Mulaifa ta fado masa a
rai, nan take Inmal yaji dukkan tsoro ya gushe dage
Zuciyarse,kawai sai ya ga wamman gudun da yake yi bashi da
wani amfani gwara ma ya tsaya ayi dik abunm da za a yi.
Lokacin da Inmal ya fara wannan gudu ne ya lura da halin da
jama'arsu suka shiga,kawai sai gimbiya Mulaifa ta fado masa a
rai, nan take Inmal yaji dukkan tsoro ya gushe dage
zuciyarse,kawai sai ya ga wamman gudun da yake yi bashi da
wani amfani gwara ma ya tsaya ayi dik abunm da za a yi.
Koda gema aiyana hakan sai Inmal ya yiwa kafaraa birki ya
tsuginna kasa ba zato.Ai kuwa sai wannan dodo ya shallakeshi
bai sani ba. Cikin tsananin zafm nama Inmal ya yi jifa da Hibru
can gefe daya samnan ya sake daka tsalle ya haye kan dodon
ya rinka gudu a kansz kamar yadda ya yi dazu domin ya iss kan
kafadarsa.
Koda dodon ya fahimci nufinse sai ya rinka kai masa wawan
duka da hanaunsa,shi kuwa Inmal ya ringa tsalle yana gocewa
da kauccwa yana ta tsallc-tsalle a kansa. Abin da
ya baiwa Inmal mamaki shi ne, yadda wannan gashi na jikin
dodon mai tsini kamar kayoyi bai sossokeshi ba.
Abin da Inmal bai sani ba shi ne, akwai tsumin maganin kaifi da
tsini a jikinsa, kuma tun yana jarir mahaifinsa Hibru ya rinka
shayar da shi wannan tsumi.
Hibru na zaune a kasa dirshan yana kallon wannan gumurzu da
ake yi tsakanin dodo da Inmal. Al'amarin da ya matukar bashi
mamaki ke nan, domin ya san cewa shi kansa ba zai iya
wannan bajinta ba wacce Inmal ke yi domin zafin namansa ya
wuce gaban kwatance.
A dai-dai waman lokaci ne sarki Maharaz ya baiyana daf da
Hibru shima ya zauna kusa da shi yana kallon abin da ke
faruwa.
Sai da aka shafe sa'a uku ana bakin gumurzu tsakanin wannan
dodo da Inmal,babu irin kokarin da dodon bai yi ba akan ya
make Inmal ko ya damkeshi da hannu amma sai ya kasa
saboda tsalle-tsallen da Inmal ya dinga yi a kansa tamkar dan
biri akan bishiya.
Sai da Inmal ya galabaitar da dodon sosai sannan ya sami
nasarar sake soke daya idon ya fashe. Wannan karon da dodon
ya wangame
bakinsa ya kwarara ihu sai da gaba dayan bishiyoyin dajin suka
kakkarye suka zube Kasa. Kuma wani irin feshin wuta ne ya
rinka fita daga bakinsa yana haddasa gobara.Al'amarin da ya
dugunzuma hankalin su sarki Maharaz ke nan sai da sarki
Maharaz ya yi amfani da karfin sihiri wajen kashe wutar.
Lokacin da wannan dodo ya zama makaho wato duk idanun
nasa biyu Inmal ya fasa su sai ya kara haukacewa ya rinka duka
da fatali da komai, wato kan mai uwa da wa bi.Bai Kyale
duwatsu da bishiyoyin da suka farfado bama. Nan da nan ya
hautsina dajiin gaba daya. Ba shiri sarki Maharaz, Hibru da
Inmal suka falfala da gudu suka bar inda dodon yake suna gudu
suna waigen halin da dodon yake ciki. Sai da suka yi dan nisa
daga inda yake sannan suka tsaya suna hangensa..
Dodon bai daina tagagi da walagigi ba har sai bayan sa'a guda
sannan ya yanke jiki ya fadi kasa rikica! Kamar katon tsauni ya
fada cikin teku domin sai da dajin gaba daya ya yi girgiza.
Da ganin abin da ya faru sai sarkin yaki Hibru ya cire kambun
sarautarsa na sarkin yaki
ya mikawa Inmal ya ce, "Ya kai dana hakika kaine ka cancanci
da wannan kambu, amma ba ni ba".
Da jin haka sai sarki Maharaz ya karbi kambun daga hannun
Hibru ya daurawa lnmal da kansa a damtsen hannunsa ya
dubeshi cikin murmushi ya ce. Tabbas mahaifinka ya yi gaskiya,
kaine kafi cancanta da wannan kambu. Ya kai Inmal ka yi sani
cewa ko a cikin tarihin sadaukan da zamaninsu ya gushe ba a
taba samun sadauki mai karancin shekaru irin naka da ya yi irin
wannan bajinta ba.".
Gama fadin hakan ke da wuya sai ga wadansu dakarun sarki
sun rugo garesu da gudu a kasa suna haki. Da isowarsu sai
suka zube kasa, dayansu ya bude baki da kyar ta ambaci sunan
gimbiya Mulaifa yana mai nuni da hannunsa izuwa ga hanyar da
suka fito..!
Kafin kowa ya ce wani abu tuni Inmal ya falfala da azababben
gudu ya bi hanyar da aka nuna masa. Yana cikin gudun ne ya
hango keken dokin gimbiya Mulaifa a saman wannan rami mai
Zurfi, keken dokin na reto saura kiris ya subuce zuwa kasa.
A wannan lokaci Mulaifa ta farfado daga dogon suman da tayi,
ta rinka kwala ihu.Koda Inmal ya jiyo ihun Mulaifa sai ya kara
karfin gudunsa har ma yana daka tsalle yana kara dira gaba. A
dai-dai lokacin da ya yi tsallen karshe kafarsa ta dira akan bakin
ramin, kuma a sannan ne keken dokin ya subuce ya yi kasa zai
nutse izuwa karshen ramin. Nan take Inmal ya sake daka
tatsalle ya ruko keken dokin da hannu daya sanann ya ruko
dutsen da ke saman ramin da daya hannun nasa sai gashi
keken dokin na reto,shima Inmal yana reto a sama a lokacin da
Kwanjin hannunsa ya kumbura, jjiyoyin jikinsa gaba daya suka
tashi suka yi burdun-burdun. A dai-dai wannan lokaci ne
gimbiya Mulaifa ta daina ihu.! Tana daga cikin keken dokin sai ta
kurawa lInmal idanu kawai ta ta kame kuma ta kasa yin magana
saboda tsananin mamakin irin wannan' gagarumar bajinta da
ya yi.
Kwatsam! Sai ga su sarki Maharaz sun iso
wajen da gudu, sannan sai ga sauran gaba dayan jama'ar
rundunar. Duk wanda ya iso ya ga Inmal a sama yana reto kuma
yana rike da keken doki da hannu daya sai ya kame kamar gunki
saboda tsananin al'ajabi. Abin mamakin shi ne, wai shin wane
irin karfi ne da Inmal har da ya iya rike keken doki da hannu
daya alhalin dawakai uku ne a jikin keken dokin,nauyinsu ma
kadai ya isheshi bare bare kuma ga nauyin shi kansa keken
dokin wanda aka yi shi da karafa masu nauyi.
Koda isowar sarki Maharaz ya ga halin da Inmal yake ciki sai ya dubi Dakarun aljanunsa ya
daka musu tsawa ya ce, "Me kuke jira ne,maza ku kaiwa Inmal
dauki..
Nan take wadansu aljanu guda biyu suka kaiwa Inmal dauki
suka cafoshi tare da keken dokin suka yi saman ramin, sannan
suka kawosu gaban sarki Maharaz suka saukesu a hankali.
Kamar hadin baki sai sarki Maharaz da Hibru suka risina suka yi
sujjada ga jarumi Inmal. Koda ganin haka sai gaba dayan
dakarun tawagar ma suka yi jinjina a gareshi.
Ita kuwa gimbiva. Mulaifa tana fitowa
daga cikin keken dokin sai ta rungume inmal ta fashe da kukan
farin ciki. Al'amarin da ya sa gaba dayan jama'ar da k�� wajen
suka hau rafka tafi. Dajin gaba daya ya cika da tafin yana amsa
kuwa,.
Bayan Mulaifa ta janye jikinta daga cikin na Inmal ta koma gefe
daya ta tsaya sai sarki Maharaz ya zo gaban Inmal ya tsaya
yana murmushi ya dafa kafadarsa ya ce, "Ya kai jarumin
jarumai, kuma gwarzon zamani,hakika a yau na tsinke da
al'amarinka bisa ganin wannan gagarumar bajinta da ka yi, in ba
don kai ba, bamu san yadda zamu yi da wannan katon dodo ba,
domin koda zamu kashe shi sai da yawanmu sun hallaka. Bugu
da kari gashi a gaban idanuna ka ceci rayuwar 'yata a lokacin da
babu abin da zan iya yi ma ta tun da ina can wani wuri dabam.
Tsananin karfin gudunka da karfin jarumtakarka ne ya sa ka
sami nasarar ceto rayuwarta. Ya kai Inmal nayi maka alkawari
lallai zan yi maka sakaiya da lada irin wanda ban taba baiwa
wani ba".
Koda jin haka sai lnmal yai murmushi kuma ya yi godiya.
Nan dai sarki ya bada umarni aka shiga debo mutane da aljanu
wadanda suka mutu da wadanda suka raunana aka binne na
binnewa,wadanda za a yiwa magani aka yi musu magani.
Sai da aka kwana a wajen sanann da sassafe aka tashi aka
kimtsa aka ci gaba da tafiya.
Wannan karon sai su sarki Maharaz suka ga tafiyar tasu ta kara
sauri ainun, domin dawakansu da rakumansu suna yin wani irin
azababben gudu na ban mamaki.
Suna gifta dazuzzuka tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya. A
cikin kwanaki goma sha bakwai suka hango tekun bahar Sufiya
daga can nesa.
Tun daga nesan suka ga wadansu Kwari kanana bakake sun
cika sararin samaniya da kan tekun tamkar babu komai a wajen
sai su.
Koda Inmal ya hango wadannan Kwari sai ya cika da mamaki ya
dubi Hibru ya ce, "Ya kai Abbana wai shin wadancan tsuntsayen
wadanne iri ne? Belbelu ne ko Tsattsewala?".
Kafin Hibru ya budi baki ya ce wani abu sai sarki Maharaz ya
tari numfashinsa ya dubi
Inmal ya ce, "Ai wadanda abubuwan da kake hangowa sun cika
sama da kasa ba tsuntsaye bane, rudunar abokan gabarmu ce,
yanzu haka suna kan laluben inda takobin SAIFUL LUJARA take
ne a cikin kogin".
Koda jin wannan batu sai Inmal ya cika da tsananin mamaki
kuma yaji tsoro ya darsu a cikin zuciyarsa bisa ganin yawan
abokan gabar wanda idan bai ninka tasu rundunar sau uku ba,
zai gaza sau biyu ba.
Cikin matukar damuwa Inmal ya ce, "To yanzu ta ya ya muma
zamu iya laluben takobin a cikin wannan teku?"
Sarki Maharaz ya ce, "Ta hanyar afkawa abokan gabar tamu da
yaki, idan muka kawar da su sai mu shiga laluben takobin a
cikin kwanciyar hankali"
Koda gama fadin haka sai sarki Maharaz ya yi shiru bai kara
cewa komai ba, a sannan ne suka fara shaida dandazon abokan
gabar tasu suma su sarki Dujalu suka ankara da tasu tahowar.
Wohoho! Bala'i ba a sa masa rana. ldan masife ta durfafo, to fe
babu abin da ya isa ya tsaide ita face yar uwarta masifa.
Koda sarki Dujalu ya dago kai ya hango su sarki Maharaz sai ya
kwarara uban ihu ya dakawa dakarunsa tsawa yuna mai basu
umarnin su tafi su tari abokan gaba tun gabannin su Karaso
bakin tekum.
Da jin wannan umarni sai dakarun aljanu suka bude fuka-
fukansu guka nufi dandazon su Maharaz suna mugun ihu rike
da muggan makamai. Ihu nc wanda ka iya sabautar da
bil'adama su zauce domin gaba dayan tsuntsayen da ke wajen
ma wadanda ke shawagi a sama sai suku kama fadowa kasa
matattu. Halittun da ke cikin ruwa kuwa sai gani aka yi
gawarwakinsu na tasowa sama saboda masifar wennan inu na
aljanu.
Su kansu jama'ar sarki Maharaz in ba don shi saki Maharaz din
ya taresu da Karfin sihirinsa ba da nan take gaba dayansu za su
kurmance ko su haukace ko kuma duk su zube kasa matattu.
Lokacin da sarki Maharaz ya ga dakarun aljanu na sarki Dujalu
sun durfafo inda suke sai shima ya baiwa nasa dakarun aljanun
umamin su taresu. Ai kuwa suma sai suka yi sama suka ruga
kansu tamkar an cilla kibiyoyi.
Kafin kiftawar ido rundunar biyu sun hade a sararin samaniya
sun kacame da fitinannen yaki wanda ya fi gaban mai tunani ya
tunano bare mai misali ya misalta. Nan fa suma dakarum
biladama da ke kasa na kowanne 6angare suka falfalo da
matsannicin gudu ana kokarin a hadu.
Kaico! Inda ace mutum na nan a lokacin da wadannen runduna
biyu ta yunkura za a hadu ya ga irin tsanonin yawansu sai ya y��
tsammemin cewa gaba dayan mutanen duniya ne za su hade
da gaba dayan daboobin dunya.Ai kuwa bangare biyun na
haduwa a tsakiya aka ruguntsue da azababban yaki mai
dugunzumoa hankali da tafasa kwakwalwa.
Saboda jijigar da kasa tayi a wann��n r��na sai da gaba dayan
tekunan duniya suka hausine guka kana ambahiyar ruwa
saboda tekun bahar Sufiya ne no babbar cibiya na dukkanin
tekunan duniya.
Wohohol A wannan rana an yi gumurzu, dauki ba dadi, artabu,
turnuku, ruguntsuni da fafatawa irin wacce ba a taba yin
kamanta ba a duniye, kuma ba za a taba yi ba.
Sai da aka kwana aka yini ana ragargazar
mazajen aljanu da na biladama aka rinka asarar rayuka amma
komai kwarin idon mutum da iya kallon Kurillarsa bai isa ya iya
tantance 6angaren da ke samun nasara ba.
A duk sa'adda sarki Dujalu ya durfafi wurin sai dai ka ga fili, duk
inda ya sa gabansa sai ka ga maza na zubcwa tamkar guguwar
annoba ce ta fado daga sama. Haka ma a 6angaren su sarki
Maharaz duk inda sadauki Inmal ya durfafa sai dai ga yana
banke mutane da kirjinsa, hannaycnsa da kafafunsa suna
zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona,an rasa wanda zai iya
tsayar da shi.
Sarki Maharaz kuwa yana amfani da karfin sihirinsa ne kawai
domin duk inda yai numi da sandarsa ta tsafi sai dai ka ga
kawunan bil'adama na gutsurewa suna faduwa kasa. Sadauki
Hibri ma ba a barshi a baya ba domin shima ragargazar maza
yake yana ta yin ta'adi. A bangaren serki Dujalu ma akwai
wadansu zakwakuran mayakansa guda biyu wadanda ake kira
Matinu da Ratiju wadanda summa sun addabi jama'ar sarki
Maharaz, don duk inda suka sa gabansu sai dai kaga maza na
ratattakewa.
Lokacin da Mutinu da Ratiju suka hango irin mummunar barnar
da sarki Maharaz da Hibru ke yiwa jama'arsu sai suka yi KUKAN
KURA suka ruga garesu aka ruguntsume da wani masifaffen
yakin. Matinu ya tari sarki Maharaz shi kuwa Ratiju sai ya tari?
Hibru.Wani abin mamaki shi ne Matinu yana takama da a
karfin tsafi ne zalla ba wai jaruntaka ba shi kuwa Ratiju
tsagwaron jarumtaka ce da shi kawai sai gashi duk su biyun
sun tari dai-dai da su don haka sai fadan nasu ya zama abin
sha'awa kuma abin tsorO domin komai zai iya faruwa babu
wanda yake da tabbacin samun nasara akan abokim gwaminsa
saboda karfi yazo daya.
Lokacin da sarki Maharaz ya ga karfin sihirinsa ya zo dai-dai da
na Matinu sai ya cika da tsananin mamaki domin shi a zatonsa
babu mai iya karawa da shi a fagen yaki face sarki Dujalu
amma sai gashi daya daga cikiin yaran Dujalu ya bashi mamaki.
Abin da sarki Maharez bai sani ba shi ne,Sarki Dujalu ya boiwa
Matinu gabe dayan Karfin sihirinsa ne yanzu yana wannan yaki
ne da zallar karfin damtsensa.
Kamar yadda Inmal ya addabi dakarun Dujalu ya rinka ratsawa
ta cikinsa ta kowanne bangare yana ragargazarsu haka shima
sarki Dujalu ya addabi jama'ar sarki Maharaz tamkar an auna
barnar da suke yi tazo dai-dai.Ana cikin haka ne sarki Dujalu ya
hango irin mummunar barnar da Inmal ke yi sai hankalinsa ya
dugunzuma kuma ya cika da tsananin mamakin yadda Karamin
yaro ya sami irin wannan gagarumin karfi haka.
Cikin tsananin fusata sarki Maharaz ya tarwatsa mazajen da ke
gabansa ya falfala da gudun tsiya tamkar ana shara da tsintsiya
ya durfafi inda Inmal yakc. Ai kuwa sai Inmal ya dago kai ya
hango tahowarsa. Nan take shima Inmal ya tarwatsa mazajen
da suka lullu6eshi ya falfala da matsanaicin gudu yana banke
mutane da dawakai, rakuma da alfadarai da ke gabansa ya nufi
sarki Dujalu cikin dacin rai da kunar zuci gami da mugun nufi
domin su hadu. Ai kuwa suna haduwa suka kacame da mugun
yaki na ban tsoro da ban al'ajabi. Tamkar jikinsu ba na jini da
tsoka bane haka suka rinka kaiwa juna sara da suka cikin
tsananin juriya, zafin nama da bajinta. Sai gashi tsohon kashi ya hadu da sabon kashi,naci da naci, zuciya
da zuciya, kowannensu yaki yake yi iya karfinsa tamkar ba za su
taba dainawa ba facc an tashi duniyar gaba daya.Haka dai aka
ci gaba da wannan masifaffen yaki, har sai da rana ta fadi, gari
ya soma duhu. Kai saboda balain artabun da ake yi a sama da
kasa, wato aljanu nayi, mutane nayi sai da wata irin gagarumar
tsawa da walkiya suka addabi kowa, tartsatsin wuta kuwa ya
rinka fantsama yana haddasa gobara har a cikin tekun. Babu
wani bangare da ke shirin ja da baya a yakin. Mutane da aljanu
suka rinka zabga gumi, yunwa da kishirwa ta addabi kowa.
Gashi dai an zo da guzurin abincin kuma ga ruwan teku ana
gani amma sai ci da sha ya gagari kowa saboda bala'in da ake
ciki da mugun tashin hankalin da ake fuskanta. Ba shiri dan
dole kowanne bangare suka busa kahon janye yakin domin
tsananin duhu da hayakin wuta ya sa ba a shaida juna ha ta kai
cewa idanu sun rufe mnutane sun fara yakar yan uwansu ma
basu sani ba.
Koda jin sautin kahon na kowanne bangare sai duk aka ja da
baya aka daina yakin
tamkar daukewar ruwan sama a lokaci guda. A sannan ne
matsafa suka samar da hasken tsafi kowa ya iya ganin komai.
Kaico! Hakika yaki masifa.Da baiyanar wannan haske sai ga
gawarwakin mutane da aljanu zube a kas ko ina rututu, babu
inda mutum zai iya takawa da kafarsa face ya taka gawa. Kai
har akan ruwan tekun gawarwaki ne barjik babu adadi kuma ba
kyan gani. Jini kuwa gashi nan yana ta gudu da malala akan
kasa har ya jirkita ruwan tekun gaba daya yana neman rineshi.
Komai kallon Kurillar mutum bai isa ya iya tantance 6angaren
da aka fi yiwa barna ba. A