Showing 54001 words to 57000 words out of 59226 words
Chapter 19 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
matan da suke tare da su kyua, domin bambancinta da su kamar fari da baki ne.
Gimbiya Rahila ta samu guri ta zauna nesa kadan da inda su boka Muzafar suke zaune, ta fuskancesu sannan ta dubesu a nutse ta ce, Ba wani abu ne ya kawoni wajenku ba, sai domin mu gama maganarmu tun kafin mu isa can kogon darul ikisina, yanzu zan fada maku sharadin da zan gindaya maku tun kafin na taimka maku a wajen aljani Maraful Dauwas har ya amince ya biya maku bukatarku. Ina so ku saurara da kyau kuji bayanin da zanyi maku, domin ku fahimci manufata da kuma burina. Rahila tayi gyaran murya sannan ta ci gaba da magana da cewa Tun sa'adda mahaifiyata ke dauke da cika sai ta kasance mai tsananin farin ciki gami da doki bisa son ganin ranar da zata haihu, ba komai ne ya haddasa mata hakan ba face wata rana ta fito waje tana tsefe gashin kanta, a lokacin babu komai a jikinta sai wani guntun mayafi data daura iya girjinta zuwa gwiywoyinta, kamar yadda kuka ganni da tsananin kyau to haka mahaifiyata take, dan haka ita na yo gado.
Ba zato ba tsammani sai ga wani jibgegen aljani ma'abocin kyau ya bayyana tsulum a gabanta, cikin razana da firgici ta bude baki zata kwala ihu sai taji muryarta ta dishe a lokacin da ta ji jikinta ya mutu kuma ya kama karkarwa sabida tsananin tsoro, kuma gashi ta kasa guduwa tana tsaye cak waje guda, kawai sai wannan aljani ya dubeta yayi murmushi har kyawawan hakoransa suka bayyana da wushirya guda biyu a jikinsu sama da kasa, wadanda suka kara wa hakoran nasa kyau.
Aljanin ya dubeta ya ce kada kiji tsorona yake sarauniyar kyawawa, banzo fomin na tsorataki b sai domin yi maki albishir, ina mai sanar dake cewa wannan ciki da kike dauke da shi zaki haifeshi nan da cikar kwanaki goma sha tara, kuma abinda zaki haifa wata kyakkyawar jaririya ce wacce duk duniya ba za a samu mai kyawunta ba, face wata jariri da za'a haifa a gidan sarki Nashmir na birnin hindu. Rana daya za a haifi wadannan jarirai yarki da yar sarki Nashmir, kuma kyawunsu zai zamo daidai wato kunnen doki, idan har kina son wannan ya da zaki haifa tayi nisan kwana a duniya kuma ta kubuta daga sharrin aljanu wadanda za su yi sha'awar shiga jikinta dole ne ki dinga boye fuskarta da dukkan ilahirin jikinta har izuwa sa'ar da zata zama budurwa, idan kuma ba haka ba kuwa to ba zata yi tsawon rai ba, kuma sannan aljanu zasu rinka shiga jikinta suna lalata mata rayuwa har ta haukace ko ta hallaka sabida tsananin kyawunta.
Bugu da kari idan har kina son wannan ya taki ta samu daukaka da matsayi babba a duniya, dole ne ki aura mata mijin wannan yarinya yar sarkin birnin hindu zata aura.
Yake wannan matar sarki kiyi sani cewa Ni suna na aljani sautul baharu, kuma tun kina jaririya na kamu da tsananin kaunarki, amma saboda bana son na cutar da ke shiyasa ban shiga jikinki ba, domin idan har masoyi yana kaunar masoyinsa bil'adama ba zai iya cutar da shi ba, na kasance babban da a wajen sarkin bokayen aljanu na duniya, saboda haka duk wani sihiri na tsafi na duniya na gajeshi, kuma komai naake so a duniyar nan zan iya mallakarsa, amman bana son komai face na mutu da soyayyarki a zuciyata da kuma jin kyawawan kalamai daga bakinki, na sani cewa bai kamata aljani ya auri mutun ba, tabbatas inda ace ina da ikon sauya halitta daga aljan zuwa mutum da tuntuni nayi domin na samu damar aurenki, tun a ranar da mahaifiyarki ta haifeni na gani a wata rana da kika fito yawon shan iska, a wannan lokaci an shifideki akan gado kina cikin turaka, sai na tsaya daf dake na kura maki idanu, na dinga maki murmushi kema sai naga kina maida mani da martanin murmushin kin ta dariya. Mahaifiyarki na can nesa kadan da ke, koda ta hango abinda kike yi sai ta cika da mamaki domin babu kowa a kusa da ke, abinda bata sani ba shine kina ganina ina ganinki ita ce dai bata iya ganina, daga wannan rana kullum sai na ziyarceki sau bakwai domin kuwa sai na kalleki nake jin dadi a cikin zuciyata, duk ranar da ban ganki ba kuwa sai na yi zazzabi gami da ciwon kai, hakika so cuta ne domin tsananin kaunar da nake maki take take jefani a cikin wannan hali, haka dai na kasance a tare da ke dare da rana na zamo kamar mai tsaron lafiyarki, sau tari iyyaenki sun sha ganin abubuwan mamaki da dama, domin duk irin abin tashin hankalin daya durfafo gidanku sai aga an kawar da shi, kuma a rasa wanda ya kawar da shi din?
Haka dai kika fara girma har kika zama yar shekara bakwai, a sannan ne kyawunki ya kara fitowa karara, har mutane suka fara tsammanin ke ba mutum bace aljana ce, aljanu kuwa sai suka rinka kawo maki hari ni kuwa sai na rinka fatartakarsu na hanasu shiga jikinki, bisa wannan daliline na kulla gaba mai tsanani da sarkin sadaukan aljanu na duniya, wani aljani da ake kira da Barzuma ibn Kalsawar. Sai da muka kwana arba'in muna yaki ni da shi ya zamana cewa dukkaninmu mun suma sau saba'in da bakwai jikin mu yayi fatafata da raunika muka zube muna nufashi da kyar, anan take aljani Barzuma ya tunkuyi kasa ni kuwa sai nayi sa'a yan uwana sun zo giftawa suka ganni, cikin dimauta suka daukeni suka tafi da ni gida domin ayi jinyata, duk da ina cikin halin jinya amman ban fasa zuwa wajenki ba kullum sau bakwai nake zuwa gareki, ina tsaron lafiyarki dan kada wasu aljanun ko kuma mutane su cutar da ke. Ko sau daya ban taba bayyana a gareki ba dan haka kika girma kika yi aure kawo izuwa yanzu baki taba ganina ba, sai yanzu da nake maki wannan bayani. Kiyi sani cewa a ranar da aka daura aurenki da sarki sai da na suma sau uku saboda bakin ciki, kuma na kwana arba'in ina kuka da takaici ba ci ba sha, yanzu da naga zaki haihuwa sai naji soyayyar da nake maki ta tashi daga kanki ta koma kan yarki da zaki haifa, nayi alkawari zan ci gaba da tsaron lafiyar wannan ya da zaki haifa har izuwa karshen rayuwata, amman ina mai dada yi maki tuni da cewar lallai ki tabbar yarki ta auri mijin da yr sarki Nashmir zata aura anan gaba koda kuwa bakya raye, bani da wata bukata a wajenki face ki furta mani kalmar karshe ta kauna muyi bankwana domin ba zan sake bayyana ba a gareki, amman alkawarin dana dauka akan yarki lallai zan cika shi, kuma zan dinga bayyana a gareta ina taimakonta bisa dukkan abinda take son yi face wanda yafi karfina, wannan shine kalami na karshe a gareki yake abar kaunata, wadda nake kwana na tashi da begenta.
Koda Aljani Sautul Baharu yazo nan a zancensa sai idanunsa suka ciko da kwalla ya fara zubar da hawaye. Al'amarin daya karya zuciyar mahaifiyata kenan, nan take itama ta kamu da tsananin tausayinsa, ta zubar da hawaye sannan ta ce Ya kai babban masoyina hakika kaunar da ka nuna mani ba karama bace, tunda ga shi ka sallama rayuwarka domin tawa, inda da tsautsayi da tuni ka mutu sakamakon fafatawar da kayi da sarkin sadaukan aljanu wato Barzuma ibn Kalsawar, haka kuma gashi ka shekara ashirin da biyar kana kaunata da begena a cikin zuciyarka da karfin tsiya bata bari ta zugaka ka kashe mijin ba, ko kuma tasa ka saceni ka kaini can inda babu mai iya zuwa, lalla? kai masoyina ne na kwarai wanda har abada bazan taba mantawa da shi ba, na rantse da darajar iyayena ind ina da ikon suya halittata daga mutum zuwa aljana da nayi domin na aureka, na zama abokinyar rayuwarka ta har abada.
D jin wannan batu sai hawayen farin ciki ya zubo wa Aljani Sautul Baharu yace yi shiru haka ya masoyiyata hakika babu wata sauran kalma mai dadi da zaki furta mani wacce ta fi wannan, gama fadin hakan keda wuya sai aljani sautul baharu ya bace bat! Mahaifiyata ta neme shi sama ko kasa ta rasa, nan fa ta rude ta kama guje-guje a cikin gidan tana mai kiran sunansa, amman har ta gaji da yawonta ta hakura. Daga wannan rana mahaifiyata bata sake ganin aljani sautul baharu ba har ta bar duniya.
Ni ko tun ina da shekara tara a duniya na saba da shi, ya zamana cewa dare da rana muna tare, bamu taba rabuw ba, kuma duk abinda zanyi shine yake bani shawara, ban taba kaucewa maganarsa ba. Wata rana ina zaune ni kadai a cikin turakata sai kawai naga aljani Sautul Baharu ya bayyana a gabana cikin mugun yanayi, domin duk jikinsa sarane da takobi jini na kwarara daga jikin nasa, cikin firgici da dimauta na mike tsaye na rungumo shi alokacin daya yanke jiki yana shirin faduwa kasa, nna take fashe da kuka a lokacin da nake tambayarsa wanda yayi masa wannan mugun aikin.
Aljani Sautul Baharu ya bude baki da kyar a lokacin da numfashinsa ke sarkewa ya kura mani ido a lokacin da hawaye ke shatata daga cikin idanunsa, sannan yayi mani murmushin karfin hali ya ce yake yar babbar masoyiyata kiyi sani cewa ina farin ciki a yau daya kasance zan mutu a wannan kyawawan hannaye na ki, ba wani bane yayi mani wannan mugun aiki ba face mahaifin Barzuma Ibn Kalsuwar domin yq dauki fansar kisan da nayi wa dansa, farin cikina na biyu shine na sadu dake kafin raina ya fita dan haka yanzu take zan mallaka maki dukkan wani sirrin tsafina dana gada a wurin mahaifina, ina mai gargadinki da kada ki kuskura kiyi amfani da wannan sihiri face a ranar da wani gawurtaccen boka yazo wanann birni naku da nufin ya rabaki da mahaifinki, magnata ta karshe a gareki ita ce duk yadda zaki yi kiyi domin ki tabbar da cewa kin auri mijin da gimbiya Ramlatus siyam yar sarki Nashmir zata aura, ta haka ne kadai zaki iya samun babban matsayi da daukaka a duniya, yanzu na umarceki da ki bude bakin ki.
Koda jin haka sai na bude bakin nawa ba tare da wata gardama ba, nan take naga wani irin jan hayaki yana fitowa daga cikin bakin aljani Sautul Baharu yana shiga cikin nawa bakin, hasken na gama shiga sai jikinsa ya sandare komai nasa ya daina aiki. Koda ganin haka sai na rungumeshi na fashe da matsanancin kuka saboda tsananin shakuwa da shakuwar da nayi da shi, naji kmaar a sannan ne na rasa mahaifiyata. Na dade a cikin alhinin rashin Aljani Sautul Baharu bn samu nutsuwa b sai bayan wata uku.
Sa'adda Gimbiya Rahila ta zo nan a zancenta sai boka Muzafar da sarki Lafaru suka cika da tsananin al'ajabi, boka Muzafar ya ja dogon numfashi annan ya ce hakika Ruwa baya tsami banza, ai tunda naji kin fadi sirrina nasan cewa kina tare da sirrin tsafi mai karfin garske a jikinki, yanzu na ji labarinki sai kuma ki fada mana sharadin da kike son gindaya mana.
Tai murmushi tace ai nagama gindaya maku sharadina a cikin labarin dana baku, sharadin kuw shine bazan sa aljani Maraful Dauwas ya biya maku bukatarku ba face kun dauki alkawari cewa idn har bukatarku ta biya sarki Lafaru zai aure ni a ranar da ya auri Gimbiya Ramlatus siyam domin na samu matsayi da daukaka irin nata, tunda yanzu ni da ita munyi kunnen doki a fagen kyau.
Lokacin da boka Muzafar da sarki Lafaru suka ji wannan batu daga bakin Gimbiya Rahila sai suka dubi jjuna tare da yin shiru har izuwa tsawon yan dakiku, suka ma rasa abinda zasu ce, daga can sai boka Muzafar ya dago kai ya dubi Gimbiya Rahila ya ce ki bamu zuwa gobe muna da bukatar yin shawara.
Da jin haka sai Gimbiya Rahila ta yi murmushi sannan ta juya da nufin ficewa daga cikin tantin, har ta je bakin kofar fita sai ta juyo ta dubi sarki lafaru ta ce kada ka kuskura ka bayar da labarina ga sauran abokan tafiyarmu, domin bana son su san koni wace ce, kuma suga zahirin kyawuna da surata har sai mun isa kogon darul ikisina, tana gama fadin hakan sai ta fice daga cikin tantin ta bar boka Muzafar da sarki Lafaru a cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa kamar ruwa ya cisu.
Da sassafe su duka suka tashi suka kimtsa, jaruman biyar suka gyara makamansu kowa yayi damara sannan boka Muzafar ya dubesu daya bayan daya ya ce acikin ku waye zai wuce gaba yayi mana jagora a cikin wannan daji da zamu shiga?
Ko da jin wannan tambaya sai kowa yayi shiru aka rasa wanda zai wuce gaba, koda ganin haka sai sarki Lafaru ya ce ya kai wannan babban boka kayi sani cewa ai kaine kafi kowa cancanta da yin jagora a wannan tafiya, tunda kaine uban tafiya, kuma kafi kowa sanin hanya.
Boka Muzafar ya ce kwarai kuwa haka ne abinda ka fada, amman ni kaina ina shakkar abinda ke kan hanyar nan, dan haka ba zan iya wucewa gaba ba, face na samu wanda zai tayani jagoranci har na samu kwarin guiwa, caraf sai gimbiya Rahila ta ce ni zan tayaka jagorancin wannan tafiya.
Nan take Gimbiya ta wuce can gaba ta tsaya kusa da boka Muzafar, al'amarin da ya baiwa su sadauki Haiman mamaki kenan, Zarina ta dubi boka Muzafar ta ce wai shin ita waccan budurwar da tayi gangancin shigewa kn gaba wace ce ita? Me yasa tunda aka fara wannan tafiya take boye fuskarta da kuma jikinta? Wai shin ma mene ne amfaninta a wannan tafiya?
Boka Muzafar ya dubi Zarina ya ce Ya Zarina ai bai kamata ki tambayi kaza hanyar rafi ba, agwagwa zaki tambaya ki sha labari, babu wanda zai iya amsa maki wadannan tambayoyi naki face ita kanta.
Kafin wani daga cikin abokan tafiyar ya kara cewa wani abu, sai boka Muzafar ya ce in son duk wnada yasan shi ba jarumi bane ya tsaya a tsakiya, ku kuma jaruman ku rabu gida biyu, kaso daya su tsaya a baya, dayan kason kuma su tsaya a gaba.
Ba tare da wata gardama ba kuwa aka yi hakan, ya zamana cewa Lumaira, Masnur, mahaifiyar jarumi Imran sarkin Farisa da Sadauki Shaharan suka tsaya a tsakiya, Sadauki Haiman da jaruma Shadira suka tsaya a gabansu, Lumaira, Jarumi Imran da Zarina uwa suka tsaya a can baya, faruwar hakan keda wuya sai boka Muzafar da gimbiya Rahila suka wuce kan gaba suka nufi cikin dajin, bisa mamaki sai boka Muzafar yaga sarki Lafaru shine ke biye da su, al'amarin daya matukar bashi mamaki kenan ya juyo ya dubeshi gami da cewa ya kai abokina hin ka manta cewa yanzu kai ba Sadauki ba ne?
Da jin wannan tambaya sai Lafaru ya jinjina kai ya ce kawai gani nayi duk inda na tsaya walau a tsakiya, gaba ko baya ban isa na gujewa kaddarata ba, fatana kawai shine mu samu nasarar abinda muka fito nema... Kafin Lafaru ya gama rufe bakinsa sai kawai yaga sun shigo cikin wani mugun daji mai matukar kwarjini da ban tsoro, wasu irin dogayen bishiyune a cikin dajin masu kahonnin, a jikin kahonnin akwai kwarangal din kawunan bil'adama wadanda daka gansu kasan sun dade a sagale tsawon shekaru, domin har yana ta lullube wasunsu, a kasa kwarangalolin ne birjit babu adadi, ta kansu suka rika bi suna wucewa, da zarar sun takasu sai dai kaji suna kakkaryewa da rgujewa. Ganin wannan kwarangalolin ne yasa su Masnur suka firgita ainun jikinsu ya kama kyarma, tabbas inda zasu ji wani kwakkwaran motsi da nan take zasu saki fitsari ko sun runtuma da gudu, wani abun mamaki shine Lumaira da ta kasance makauniya bata firgita ba kamar yadda sauran suka firgita, kawai sai ta ci gaba da dogara sandarta tana mai laluben hanya, kuma tana amfanin da sautin sawun wadanda ke gabanta, sai da su boka Muzafar suka yi tafiyar sa'a daya da rabi cif sannan suka iso tsakiyar wannan daji mai ban tsoro, ba su hadu da komai ba kuma basu ji motsin komai ba koda kuwa kukan tsuntsu ne, kwatsam! Suna cikin tafiya sai suka ga wani abu kamar hayaki bakikkirin ya cika sararin samaniya kamar hadarine ya gangamo. Cikin razani kowa ya tsaya cak, jaruman suka daga makamansu suka tsaya suna jiran abinda zai biyo baya, kawai sai suka ga wannan bakin hayaki ya rikide ya koma siffofin wasu aljanu ababen firgitarwa, nan fa suka ringa durowa daga sararin samaniya. Aljanun suna da kawuna irin na birrai, kuma munana ne basu da kyan gani, gangar jikinsu kuwa siffar batoyi gareta, suna da kafafu da hannaye guda shida-shida, a jikin kowanne hannu da kafa akwai yatsu guda arba'in kuma kowanne dan yartsa yana dauke da farce mai tsananin kaifi da tsini tamkar adda sabuwar washi, ko dutse suka karta da faratan nasu sai dai kaga dutsen na rabewa gida biyu.
Koda su Masnur suka yi arba da wadannan dodanni sai suka yanke jiki suka fadi kasa a sume, saboda tsananin gigicewa, Lumaira ce kadai ta rage a tsaye itama sabida bata da idanune amman inda taga wadannan dodanni aljanun da babu abinda zai hanata sumewa.
Sadauki Haiman, jarumi Imran, Jaruma Shadira, Gimbiya Zarina, da boka Muzafar kuwa sai suka dubi junansu, cikin hadin baki suka kwarara uban ihu sannna suka ruga cikin aljanun suka hausu da sara gami da suka, amman sai suka ji kamar duwatsu suke sara, domin jikin aljanun ko kwarzanewa baya yi, duk sa'adda makaman su Haiman suka hadu dana aljanun sai dai kaga tartsatsin wuta yana tashi sama, al'amarin daya dugunzuma hankalinsu kenan ainun musamman ma d suka fara jaraba kkarfin sihirinsu sukaga shima yaki yin tashiri akan aljanun.
A daidai wannan lokacin ne aljanun suka fara mayar da martani suka fara kaiwa jaruman sara da faratan hannunsu domin su nakastasu, kuma suna ki masu suka a fuska dan su lalata masu idanu. Haka dai suka ci