Showing 24001 words to 27000 words out of 59226 words

Chapter 9 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

a dalilin
ganin gawarta da ya yi shima ya hadiyi zuciya ya mutu.
Ka tuna cewa babu wani mahaluki da nake soa wannan duniya
sama da Sarki Kusaidu,gashi ka kashe matarsa Zarifa a dalilin
ganin gawarta da ya yi shima ya hadiyi zuciya ya mutu.
Ka tuna cewa yanzu na rasa mijina, kuma na rasa kakana boka
Sulbaini da mahaifina,wanda ya rage mini kawai ita ce
mahaifiyata da kai,kuma yanzu na tsaneka kamar yadda na
tsani dukkan makiyana a duniya.Na san za ka yi mamaki bisa
yadda aka yi na san duk abin da ka aikata a birnin Kisra, amma
idan kayi tunani ba abin mamaki bane tun da matsafa basu kare
ba a doron kasa. Tun daga ranar da ka bar nan birin ka tafi
?zuwa birnin Kisra har ka je ka kashe boka Ardusa, sannan ka je
ke kashe Zarifa kawo izuwa barowarka birin Kisra duk na gani a
cikn madubin tsafi.
Koda na gama ganin wannen al'amari sai na fashe de
matsanancin kuka na kamu da Babban bakin ciki kuma nan
take naji duniyar ta yi min kunci bani de bukater na ci gaba da
rayuwa Bisa wannan delili ne na sha guba a ranar de ka iso nan
birnin Kisra.
Wanann shi ne kelamaina na karshe a gareka ya kai dana. Ina
mai yi maka bushara da cewe rayuwar duniya be ta da wani
dadi idan har babu masoyi. Tabbas ka zame mini bakin takobi,
kumna bakin kumurci mai mugun dafi. Ina mai shawartarka da
ka bi rayuwar duniya a sa��nu kuma ka sani cewa baka da
babban makiyi a rayuwarka sama da zuciyarka tun da ba za ka
iya sarrafata ba. Ka sani cewa a duniya bebu abin da ya fi
soyayya karfi de
dadi, kuma babu abin da ya fita wahala da hadari. Har abada ba
zan koma Kisra ba..."
Sa'adda Hantaru ya zo nan a karatun wasikarsa sai ya sake
fashewa da matsanaicin kuka ya rungume gawar Salimat a
kirjinsa ya yi ta kuka kamar ba zai taba dainawa ba. Da Kyar da
sidin goshi kuma da rarrashi gami da lallami aka banbare gawar
Salimat daga hannunsa, sannan aka haka kabari aka binneta.A
bakin kabarin nata Hartaru ya kwana yana kuka har gari ya
waye rana ta take. Saboda tsoron fushin Hantaru sai aka rasa
wanda zai zo ya rarrasheshi. Hatta Shaulat ma kasa zuwa ta yi.
Lokacin da Hantaru ya gaji da kuka har ya zamana cewa ruwan
hawayensa ya kafe kuma muryarsa ta dashe, kuma
numfashinsa na sarkewa sai ya sulale kasa sumamme. Sai da
Shaulat ta debo ruwa ta watsa masa sannan ta bashi a baki ya
sha sannanj ya dawo cikin haiyacinsa.Koda ya nutsu sai ya
mike tsaye ya fice daga cikin gidan Shurem ya durfafi gidan
sarki kai tsaye,yana tafe yana tangadi kamar wanda ya sha giya
ya bugu saboda tsananin
yunwa da kishirwar da ke jikinsa gami da
dumbin bakin ciki.
Da zuwan Hantaru kofar gidan Sarki sai ya ga kan mahaifiyarsa
Zarifa a cake jikin itace. Al'amarin da ya matukar firgitashi ke
nan ya cika da tsananin mamaki. Shi dai a saninsa ya binne
wannan kai a can cikin daji a lokacin da babu wanda ya ganshi.
Abin tambaya anan shi ne, wane ne yaje ya tono kan ya kawoshi
nan? kuma ya ya akayi aka san inda kan yake?
Ba zato ba tsammani, sai Hantaru ya hango gimbiya Larziya ta
fito daga cikin gidan Sarki ita kadai tana sanye da wata farar
doguwar riga mai shara-shara wacce ke baiyana gaba dayan
kyakkyawar surar jikinta.Fuskarta a cike take da annuri kuma ta
goya hannayenta a gadon bayanta.
Koda ganinta a cikin wannan hali sai Hantaru ya cika da
tsananin farin cikiya yunkura zai ruga da gudu izuwa gareta
kawai sai yaji ta daka masa tsawa ta ce, "Dakata!Anan inda
kake ya kai masoyina".
Cikin matukar kaduwa da mamaki Hantaru ya tsaya cak a inda
yake ba tare da ya
yi gardama ba. Kawai sai ya ga hawaye ya zubo daga cikin
idanun gimbiya Larziya sannan ta dubeshi ta ce, "Ya kai
masoyina abin begena dare da rana,kayi sani cewa na yaba da
tsananin kokarinka bisa kokarin cika alkawarin da ka daukar
mini kuma na tabbatar da cewa kana kaunata fiye da komai a duniya.Sai dai kash! Baka sami nasarar cika mini
burina ba kuma baka da laifi ko kadan,murmushin da ka ga nayi
maka dazu shi ne murmushin karshe tsakanina da kai, kuma shi
ne na bankwana. Lallai ban ga amfanin zamana a duniya ba tun
da na kasa cika alkawarin mahaifiyata wanda na yi rantsuwa da
soyayyata a gareta a akansa. Kayi hakuri ya kai masoyina kuma
ka gafarta min bisa tafiyar da zan yi na barka, ka sani cewa idan
ma na zauna ba zan yi nisan kwana ba domin ciwon zuciya ne
zai kasheni.
Da wannan furuci nake maka bankwana na karshe. Idan har
akwai wata rayuwar bayan ta duniya ina fatan mu sake
saduwa".
Koda gama fadin hakan sai gimbiya Larziya ta fito da
hannayenta daga bayanta sai ga wata sharbebiyar wuka a
hannunta. Koda
Hantaru ya hango wannan wuka sai ya falfalo da matsanaicin
gudu domin ya hanata aikata abin da take nufi. Amma da yake
bakin alkalami ya riga ya bushe kafin ya iso gareta da tazarar
taku uku kacal, tuni ta soka wannan wuka a cikinta, kawai sai ta
sulale kasa matacciya.
Hantaru ya fada kan gawar Larziya ya fashe da kuka, ko kadan
ba a jin sautinsa kuma wanda babu hawaye.
Bayan Hantaru ya dade yana kuka sai ya zare wannan wuka
daga cikin Larziya ya hau cakawa jikinsa. Abirka da jikin tsohon
sadauki mai tarin sihirin tsafi sai wukar ta kasa hudashi. Nan fa
Hantaru ya zama kamar mahaukaci ya rinka wawuro komai
yana makawa a jikinsa don ya kashe kansa ya huta da bakin ciki
amma duk abin da ya cakaa cikin nasa sai ya ki tasiri.
A wannan lokacin babu kowa a gidan sarki domin gaba dayan
mutanen gidan sun tafi gidan Shurem don yin gaisuwar
mutuwar Salimat.
Nan take Hantaru ya dauki gawar Larziya ya koma da ita gidan
Shurem inda ya iske
Sarki da sauran jama'ar gari,
Koda sarki ya hango Hantaru dauke da gawar Larziya sai ya
fashe da matsanaicin kuka kuma nan take Kwakwalwarsa ta
tabu ya kama surutai irin na mahaukata. Gaba dayan jama'ar da
ke wajen sai da suka afshe da matsanaicin kuka saboda
tsananin tausayin Hantaru da Sarki.
Sannu a hankali Hantaru yazo da gawar gimbiya Larziya kusa
da kabarin mahaifiyarsa Salimat ya ajiye gawar. Kawai sai ya
mike tsaye yaje inda dokinsa ke daure ya dauko takobin Saiful
Lujara. Koda jama'a suka ga ya zare takobin daga cikin kufenta
sai suka firgice suka kama guje-guje da iface-iface.Kawai sai
Hantaru ya dubi jama'a ya yi wani dan guntun murmushi sannan
ya caka takobin takobin ta lume ta faso gadon bayansa.
Hantaru ya tafi kasa luu! Ya durkusa bisa guiwoyinsa ba tare da
ya fadi kasa ba ya zama gawa. Amma har a wannan lokacin
murmushi na fuskarsa bai guseh ba.
Faruwar hakan ke da wuya sai takobin Saiful Lujara ta zare
kanta daga cikin Hantaru ta yi sama ta luluka izuwa cikin
gajimare ta
6ace 6at! A sannan ne kuma gaba dayan jikin
Hantaru ya sandare ya zamo gunki.
Har yau, har kwanan gobe idan mutum yaje birnin Darul
Mahabul ya ziyarci gidan Shurem zai ga sadauki Hantaru cikin
siffar gunki ya durkusa a gaban kabarin Salimat da kabarin
matarsa gimbiya Larziya da murmushi a fuskarsa..
LOKACIN DA SARKI DUJALU ya zo nan a labarinsa sai ya ga
idanuun
Hursiya sun cika sharkaf da hawaye saboda
tsananin tausayi.
Tsawon yan dakiku daya daga cikinsu bai ce uffan ba. Daga can
sai Sarki Dujalu ya dubeta ya ce, "Ya ke 'yar uwata yanzu me
kika fahimta a cikin wannan labari na Hantaru,kuma wane irin
darasi kika samu?".
Koda jin wannan tambaya sai Hursiya tayi ajiyar zuciya ta ce,
"Hakika na fahimci cewa a duniya babu wani abu mai hadarin
gaske sama da soyayya, domin za ta iya sa mutum ya aikata
abin da bai dace ba kamar yadda sarki Kusaidu ya hadiyi zuciya
ya mutu saboda
ganin an kashe matarsa Zarifa da yadda Salimat ta sha guba ta
mutu saboda mijinta Sarki Kusaidu ya mutu da kuma yadda
sadauki Rabbasu ya murdewa kansa wuya ya mutu saboda ya
fuskanci cewa ba zai taba samun masoyiyarsa ba Larziya. Uwa
uba kuma shi ne,Hantaru wanda ya sallama rayuwarsa don
kyautata wa masoyiyarsa amma sai gashi a banza ya kashe
kansa bayan ya sha bakar wahala kuma ya sami daukakar da
babu wanda ya sami kamarta a wannan zamani amma kuma
daukakar bata amfane shi da komai ba.
Na yi koyi darusa da dama a cikin wannan labari, musamman
akan, duk abin da mutum zai so to ya soshi saisa-saisa kada ya
zurfafa.'Abu na biyu kada mutum ya bari zuciyarsa ta kawatu da
son kudi ko matsayi da yawa domin.zai iya hallaka kowa domin
ya sameta ko da kuwa dan uwansa na jinine kamar yadda
Zarifa da Marifa suka taso a cikin kiyayyar juna alhalin sun
kasance 'yan uwan juna na jini uwa daya uba daya.
Abu na uku mafi muhimmanci shi ne,daukar alkawari bisa abin
da mutum bashi da tabbacin zai iya cikawa. Tun da farko inda
Hantaru bai dauki alkawarin zai yi duk abin da Larziya za ta
umarceshi da yi ba da ba zai je birnin Kisra ba har yai aikin da
zai zo yai nadamarsa ba, amma saboda idanunsa sun rufe akan
soyayyarta sai ya amsa dukkan muradinta.
Ya kai dan uwana kayi sani cewa idan zan ci gaba da lissafo
maka darasin da ke cikin wannan labari sai gari ya waye ban
kare ba."
Koda jin wannan batu sai sarki Dujalu ya bushe da dariya ya ce,
"Ai wadannan darussan ma kadan ne akan wanda ke cikin
labarin sadauki Shaddadu na birnin Kufa da kuma labarin
sadauki Hulkas na birnin Romaniya".
Koda jin wannan batu sai Hursiya ta goge hawayen idanunta da
sauri ta dubi Sarki Dujalu cikin murmushi ta ce, "Ina rokonka da
ka bani labarin sadauki Shaddadu na birnin Kufa domin na ji irin
abubuwan al'ajabin da ke cikin tasa rayuwar".
Koda jin wannan batu sai sarki Dujalu ya sake bushewa da
dariya a karo na biyu ya ce;Daga kanki sama ki duba ki gani,
mene ne wancan?".
Cikin sauri Hursiya ta daga kanta sama
sai ta ga ashc har alfijir ya keto. Al'amarin da ya matukar ba ta
mamaki ke nan bisa yaddaa aka yi suka shafe sa'oi masu yawa
haka a zaune tana sauraron labari ba tare da ta gaji ba ko kuma
barci ya dauketa ba."
Koda sarki Dujalu ya fahimci cewa Hursiya tayi mamaki matuka
bisa tsawon lokacin da suka shafe yana ba ta labarin Hantaru,
sai ya mike tsaye ya ce, "Ya ke 'yar uwata ki sani cewa labarin
sadauki Shaddadu ya ninka na sadauki Hantaru yawa sau
biyu,sai dai kawai na gajarce miki shi saboda haka sai mun
sami isasshen lokaci anan gaba. Yanzu sai ki tashi da sauri ki
koma can tantinki domin kiyi wanka kiyi kalaci nan da dan
lokaci kadan wannan runduna tamu za ta ci gaba da tafiya
domin mu isa tekun Bahar Sufiya akan lokaci".
Gama fadin hakan ke da wuya sai sarki Dujalu ya juya ya nufi
inda tantinsa yake.Cikin sauri itama Hursiya ta mike tsaye ta
ruga izuwa na ta tantin.
Ko rabin sa'a ba a yi ba gaba dayan rundunar su sarki Dujalu
suka gama kimtsawa,aljanu suka kwashi mutane da dukkanin
kayayyakinsu suka bude fuka-fukansu suka
tashi sama suka fara tsala matsanaicin gudu suna masu
tunkarar tekun bahar Sufiya.
Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin sarki Dujalu da yar
uwarsa "Hursiya bayan ya gama bata labarin sadauki Hantaru
sun kuma kintsawa sun ci gaba da tafya sun tunkari kogin
bahar Sufiya don dauko takobin SAIFUL LUJARA.


ALAMARIN RUNDUNAR Sarki
Maharaz kuwa, lokacin da suka baro
birnin Darul Mahabul sai suka wanzu suna
wata tafiya ta ban al'ajabi, wacce ta baiwa
kowa mamaki, dalili kuwa shi ne, saurin
tafiyar ya wuce misali, domin gani suke yi
kamar suna shafe tafiyar kwana guda a cikin
abin da bai kai rabin sa'a ba.
Shi kansa sarki Maharaz yana mamakin al'amarin amma da ya
tuno da jawabin da ubangijinsa Darbuza ya yi masa cewar zai
gajarce musu nisan wannan tafiya sai ya daina mamakin komai,
hankalinsa ya kwanta.
Sadauki Inmal ko yaushe yana daf da keken dokin da Mulaifa ke
ciki, baya yarda a
sami wata tazara a tsakaninsu don tabbatar da tsaron lafiyarta.
Duk bayan 'yan dakiku kadan sai Mulaifa ta yaye labulen keken
dokin ta leko wajen sun hada ido da Inmal gami da yiwa juna
murmushi.
Haka dai aka ci gaba da wannan tafiya ba sassauci face idan
dare ya yi a yada zango. Wani lokacin ma in dai akwai hasken
farin wata ba a yada zango sai dai a ci gaba da tafiya.
Hakika masu iya magana sun yi gaskiya da suke cewa, "Idan ka
ga ki gudu, to sa gudu ne bai zo ba'. Kai tsaye wannan runduna
ta su Sarki.Maharaz ta rinka ratsa dazuzzuka tana wucewa,
komai yawan 'yan fashi ko muggan dabbobin daji ko muggan
aljanu da zarar sun jiyo takun sawun wannan runduna wacce ke
haddasa karamar girgizar kasa saboda tsananin yawansu sai
ka ga wadannan muggan halittu sun falfala da gudu sun nemi
��amuka sun shiqe sun 6uya domin sun san cewa GABA DA GABANTA, aljani ya taka wuta.
Lokacin da wannan runduna ta iso cikin dajin Sauratul Auzur
dama sarkin yaki Hibru da sarki Maharaz ne akan gaba, don
haka sai
sarki Maharaz ya ja linzamin dokinsa ya tsaya cak. Nan take
kuwa kowa ya yi koyi da shi,aka yi tsit tamkar babu mai
numfashi a wajen.
Sarki Maharaz ya shaki numfashi sannan ya dubi gabas da
yamma, kudu da arewa sannan ya daga kansa sama ya sauke
ya dubi kasa. Kawai sai ya yi ajiyar zuciya ya ce,Tabbas abokan
gaban gatbarmu sun wuce ta cikin wnanan daji kimanin kwanaki
biyu rak!da suka wuce, kuma sun fafata kazamin yaki da daya
daga cikin irin mugayen halittun da ke cikinsa.
Ya ku jama'ata kuyi sani cewa masifi da ke cikin wannan daji
sun fi gaban tunanin bil'adama ko aljan, don haka ba lallai bane
yawanmu, jarumtakarmu da karfin sihirinmu ya Kwace mu,
amma tun da har abokan gabarmu suka samu nasarar wuce
lallai ina sa ran cewa muna zamu iya wucewa,sai dai bai zamo
lallai ba dukkaninmu mu iya wucewa ba a raye, don haka sai
kowa ya gyara damararsa kuma ya yi iya kokarinsa domin ceton
rayuwarsa".
Koda gama fadin haka sai sarki Maharaz ya dubi sarki yaki
Hibru ya ce, "Ya kai
abokina ai sai ka wuce kan gaba domin a wannan dajin babu
batun karfin sihiri sai dai amfani da tsagwaron karfin damtse da
hikima gami da basira".
Da jin wannan batu sai Hibru ya yi murmushi sannan ya
Kwalawa Inmal kira.Inmal ya zaburi dokinsa ya rufa inda Hibru
da sarki ke tsaye. Hibru ya dubi Inmal ya ce, "lna son ka
kasance kusa da ni." Inmal ya gigirza kai alamar cewa ya bi
umarni. Nan take Hibru ya sakarwa dokinsa linzami ya wuce
gaba,cikin sauri Hibru ya take masa baya sannan sarki da
sauran jama'a.
Koda fara wannan tafiya a cikin dajin Sauratul Auzur sai kowa
hankalinsa ya tashi ganin irin yanayin dajin yadda komai a
cikinsa ya kasance a cikin siffar ban tsoro, sannan kuma tunda
suka fara tafiya a cikin dajin ba su ga halitta ko daya ba koda
kuwa kananan Kwari da tsuntsaye, kuma basa jin sautin komai
face sautin takun sawun dawakansu da rakumansu.
Sai da aka shafe sa'a guda ana tafiya ba a ga komai ba,
kwatsam! Sai aka yi kicibus da gawar katuwar halittar nan
wacce ta danne
sarki Dujalu aka rasa yadda za a yi a zaroshi daga karkashinta
har sai da tsoho Shurkaib ya zo da shawarar yadda za a iya
kubutar da shi.
Koda ganin wannan halitta sai aka yi cirko-cirko ana kallonta
cikin tsananin al'ajabi bisa ganin tsananin girmanta da siffarta.
Nan take sarki Maharaz ya sauka daga kan dokinsa ya zo gaban
halittar ya tsaya, kawai sai ya dafa gawar halittar da hannunsa
na hagu sannan ya rintse idanunsa. Nan fa ya rinka ganin duk
abubuwan da suka faru tsakanin halittar da rundunar su sarki
Dujalu tun daga lokacin da suka fara artabu da halittar har
izuwa lokacin da sarki Dujalu ya sami nasarra kasheta ta
danneshi kawo izuwa sa'ar da aka zaroshi daga karkashin
dabbar da Kyar.
Gama ganin wannan al'amari ke da wuya sai sarki Maharaz ya
bude idanunsa ya dubi Hibru ya ce'Anan gaba kadan zamu iya
haduwa da wata muguwar halittar mai kama da wannan. Idan
har muka sami nasarar halakata ba zamu sake haduwa da
komai ba har mu fita daga cikin wannan daji".
Koda jin wannan batu sai Hibru ya girgiza kai sannan ya zare
takobinsa. Da ganin haka
sai shima Inmal ya zare tasa. Ganin aka ne ya sa gaba dayan
sauran Dakarun suka kama zare takubbansu. Karar zare
takubban nasu ya cika dajin gaba daya ya amsa kuwwa. Ba tare
da 6ata lokaci ba aka ci gaba da ratsa dajin.
A wannan lokaci kowa ka dubaa sai ka ga ba a cikin nutsuwa
yake ba saboda fargaba da tsoron abin da za a iya haduwa da
shi. Sai da aka sake shafe sa'a guda ana tafiyar sannan
kwatsam aka yi arba da wani garkeken dodo mai tsananin
tsawo, fadi da kauri. Saboda tsawon dodon ya kere gaba dayan
bishiyoyi,duwatsu da tsaunikan da ke dajin.
Dodon na da Kwala-Kwalan idanuwa jajaye kamar an gasa dan
buda a cikin wuta,k��ma girmansa ya kai na kwan jimina. Yana
da wawakeken hanci tamkar an bude kofar gari. Fadin bakinsa
kuwa da zurfinsa tamkar rijiya hakar mutanen farko. Saboda
fadin dodon ya cika hanyar gaba daya babu ta inda za a iya
wuce face ta karkashin kafafunsa da ya dan warasu.
Gaba dayan jikin dodon a murde yake,kuma kwarin fatar jikinsa
tamkar da dutse aka yi ta. Jikin nasa duka a lullube yake da
gashi,
kuma wani irin gashi ne mai tsawo da tsini tamkar allurai aka
lillika.
Koda dodon ya yi wani irin gurnani sai gaba dayan mutane da
aljanun rundunar suka firgice suka dimauce. Da yawansu basu
san sa'adda suka saki makamansu kasa ba suka juya da baya
da gudu. Kai ba ma su ba, hatta dawakai da rakuma firgicewa
suka yi suka tarvwatse suka kama gudu a cikin dajin.
Wasu a garin gudun ne ma suka rinka fadawa cikin mugayen
ramuka suna hallaka,wasu suka rinka fadawa kan kayoyi da
itatuwa suna cakewa. Wadanda kuwa basu sami damar
quduwa ba sai suka rinka zubewa kasa sumammu.
Sarki Maharaz, Hibru da Inmal ne kadai basu firgice ba amma
suma sun tsorata da ganin wannan dodo kuma sai aka rasa
wanda zai karasa inda dodon yake.
Lokacin da dodon ya ga mutum uku raklA gabansa tamkar an
ajiye kadangaru a gaban mikiya, sai shi kansa ya cika da
mamakin su Hibru, kawai sai ya tsaya yana kallonsu suma suna
kallonsa jikinsu na tsuma.
Gimbiya Mulaifa kuwa, lokacin da jama'a
suka firgice, sai dawakan keken dokinta suka juya da baya da
gudu a dimauce suka nufi wani rami mai zurfin gaske. Mulaifa
ta rinka Kwala ihu tana neman a taimaka mata, amma da yake
iface-iface ya yi yawa a wajen babu wanda ya tuna da
al'amarinta tun da nafsi-nafsi ake yi. Ai kuwa sai dawakan suka
fada cikin wannan rami, karshen keken dokin ne ya makale a
jikin wani dutse mai gwafa daga sama ya kama reto. Tuni a
wannan lokaci gimbiya Mulaifa ta suma a cikin keken dokin da
ke reto a sama sakamakon tsananin razanar da tayi bisa ganin
wannan rami mai zurfi da ta fada.
Tsawon 'yan dakiku ana kallon-kallo tsakanin wannan dodo da
su Hibru,amma sun rasa abin da ya kamata su yi. Daga can sai
Hibru ya yi ta maza ya rugo da gudu izuwa kan dodon. Dodon ya
kawo masa mangari da hannunsa guda.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login