Showing 51001 words to 54000 words out of 59226 words

Chapter 18 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

shi baya sonta. Abinda bata sani ba shine shim ya kamu da tsananin kaunarta amman daya tuno da alkawarin da ya daukar wa mahaifiyarsa sai yaga ya zama dole ya cire sonta dgaa cikin zuciyarsa.
Sai da suka shafe sa'a bakwai suna tafiya a cikin sararin samaniya bisa aljani Marhabul Zaurus sannnan suka iso birni Farisa, take kuwa suka sauka a cikin wani kayataccen gidan sarauta. Koda ganin wannan gidab sarautar sai su sarki Lafaru suka cika da tsananin mamaki, suka kama kalle kalle da waige waige tamkar mutanen kauye domin ko a labari basu taba jin ginin mai girma da kawatuwa kamar wannan ba, ginin fadar gaba daya anyishine da tubalun lu'u lu'u, ba a dora komai ba, kuma duk inda mutum zai taka a cikin gidan sai dai ya taka yakutu babu inda wani wuri mai kasa, komai ka gani na amfani hatta kayan dawakai da zinare aka yi su, duk inda mutum ya duba a cikin gidan sai dai yaga barori da kuyangi sunata kai kawo da hidima a cikin gidan, kafin su sarki Lafaru su sauka daga kan aljani Marhabul Zaurus sai kawai suka hango sarkin farisa da yar uwarsa Gimbiya Zarina sun taho garesu cikin tsala ado na gaban kwatance, suna sanye da wadansu kurayen tufafi iri daya, abinda ya fara daure wa su jarumi Imran kai shine ganin yadda sarkin Farisa da yar uwarsa Gimbiya Zarina suke matukar kama da juna, inba dan Sarkin Farisa ya kasance d namiji ba da sai mutum yace hasana d husaina ne. Sarkin Farisa da gimbiya Zarina suka tunkaro inda su jarumi Imran suke fuskokinsu cike da annuri suna t murmushi kamar wadnda aka yiwa bushara da samun mulkin duniya. Tsananin kyawun Gimbiya Zarina ne ya fara dimauta Sarki Lafaru, yayi ajiyar zuciya sannan ya cw a cikin zuciyarsa, Oh hakika duniya da fadi take, kuma abin cikinta yawa gareshi, tabbas wanda baiyi tafiya ba bai more kallo ba, unda muka fara wannan tafiya duk inda muka riski mace mai kyau da mun kara gaba sai mug wacce ta fita kyau, to wai shin ya kyawun Gimbiya Ramlatus siyam zai kasance akan kyawun wadannan mata da nake haduwa da su yanzu, ashe kuwa idan har na auri Gimbiya Ramlatus siyam nasan sai nafi kowa samun matsayi a duniya, a daidai lokacin da sarki Lafaru ke wannan zancen zuci ne su gimbiya zarina suka iso daf da su. Koda Zarina ta hada ido da jarumi Imran sai taji zuciyarta ta buga da karfi saboda kwarjininsa da kuma kyawunsa, dan hkaa sai ta yi sauri ta kauda kanta ga barin kallonsa, ta dubi jaruma Shadira da Lumaira matar Sadauki Haiman,bisa mamaki sai ta ji ta kamu da kishi akansu, duk da cewar tasan ta fisu kyau nesa ba kusa ba, cikin matukar farin ciki Zarina ta yi wa boka Muzafar barka da zuwa ta ce Lale marhabun da babban boka mai share mana hawayenmu kayi sani cewa tun jiya nida dan uwana ba mu rintsa ba, saboda farin ciki da dokin zuwanku bisa wannan gagarumar tafiya dake gabanmu, dan haka yanzu mun gama kintsawa ssi tafiya kawai.
Cikin murmushi boka Muzafar ya dubi Gimbiya Zarina ya ce an gaisheki ya mai ilimin daji, kece kika san dabbobin daji da sharrinsu, kuma kece sarauniyar mafarauta ta duniya, ina mai sanar dake cewa abokan tafiya sun hadu, saura mutum daya jal kuma ba wani bane face sadauki Shaharan bn Lauwal na birnin Hairussalas shine ma'abocin gudu, yanzu sai kuyi harama mu tafi domin isa can birnin Hairussalas kafin dare yayi mana.
Da jin haka sai kowa ya hau kan aljani Marhabul Zaurus ya zauna shikuwa sai ya bude fuka-fukansa yayi sama yana mai tsala azababben gudu cikin gajimare yana keta giza-gizai tamkar gudun tauraruwa mai wutsiya. Aikuwa a cikin sa'a uku kacal suka iso birnin Hairussalas suka tsaya a kofar gidan sadauki Shaharan, da saukarsarsu sai suka ga sadauki Shaharan a gaban dokinsa wanda yake gasar gudu da shi, dokin na durkushe bisa kafafunsa. Koda sadauki Shaharan yayi arba da su boka Muzafar sai ya cika da tsananin farin ciki, ya ruga da sauri ya tarbi boka Muzafar suka rungume juna, Shaharan ya janye jikinsa daga jikin na boka Muzafar sannan ya dubi su sarki Lafaru dake zaune a bisa aljani Marhabul Zaurus nan take kuma ya ha?a idanu da Gimbiya Zarina, kawai sai yaji zuciyarsa ta buga da karfi, har bai san sa'ad da yayi mata murmushi ba, ita kuwa sai ta hade fuska ta kauda kai ga barin kallonsa, ta dubi jarumi Imran shima sai ya hade mata fuska kuma ya sunkuyar da kansa kasa.
Shaharan ya juyo ya fuskanci boka Muzafar ya ce ga dukkan alamu naga abokan tafiya sun gama haduwa?
Boka Muzafar yayi murmushi ya ce kwarai kuwa daman kai kadaine ka rage dan haka sai ka taho mu tafi.
Shaharan ya dubi boka Muzafar cikin damuwa Sannan yayi nuni izuwa dokinsa ya ce yanzu ya zamu yi da wannan doki nawa har mu dauke shi mu dirashi akan wannan aljanin?
Koda jin wannan tambaya sai boka Muzafar yayi murmushi ba tare da yakara cewa komai ba, sai kawai ya nufi inda dokin ya ke da zuwa sai ya sa hannayensa biyu ya ciccibo dokin tamkar ya dauki buhun harawa, yaje ya dorashi akan aljani Marhabul Zaurus sannan shima ya zauna.
Koda ganin irin sadaukantaka ta boka Muzafar sai kow ya cika da mamaki, bisa ganin cewa yayi amfani ne da tsagwaron karfin damtsensa ba wai karfin sihirinsa ba, ba tare da bata lokaci ba shima sadauki Shaharan ya zauna akan aljani Marhabul Zaurus. Nan take ya sake bude fuka-fukansa ya tashi sama ya luluka a cikin gajimare, babu abinda zai baiwa mutum mamaki face yadda aljanin ya iya dauke mutane har kusan goma sha daya da kuma doki guda daya akansa, amman kamar bai dauki komai ba yake jin kansa, saboda girmansa da kuma karfin damtsensa, sai da suka shafe sa'a hudu suna tafiya a sararin samaniya dayansu baice uffan ba, a wannan lokacin Lumaira ta dora kanta a saman cinyar mijinta Sadauki Haiman suna yi wa junansu wasa da gashin kai, Shadira na rungume da dan uwanta yaro Masnur yana shinfide a bisa cinyarta ta kura masa idanu kawai tana murmushi, shikuwa jarumi imran yana kwance akan kafadar mahaifiyarsa tana gyara masa dogon gashin kansa tana daure masa a baya sabida yawansa da kuma santsinsa. Gimbiya Zarina da dan uwanta Sarkin Farisa kuwa sun lulluba a cikin mayafi guda sakamakon iskar dake kada suturun jikinsu marasa nauyi kamar ana hura balo. Shiko sadauki Shaharan yana zaune daf da dokinsa yana shafa wuyan dokin kuma yana satar kallon Gimbiya Zarina, da yaga zata juyo su hada ido sai yayi saurin kawar da idanunsa.
Ana cikin wannan hali ne kwatsam sai hadari ya taso aka fara wata irin iska mai sanyi sosai gamk da walkiya da tsawa mai furgitarwa, wacce tasa yaro Masnur ya farka a firgice.
Koda ganin haka sai boka Muzafar ace da aljani Marhabul Zaurus yayi masu rumfa. Nan take aljani Marhabul Zaurus ya lullube su da biyu Daga cikin fuka-fukansa tamakar an kifa kwarya akansu, nan take suka daina jin sanyi kuma suka tsira daga barazanar sakkowar ruwan sama da ta tsawa wacce ka iya masu lahani, duk da cewa Aljani Marhabul Zaurus ya kifesu da fuka-fukansa basu tsinci kansu a cikin duhu ba, domin boka Muzafar ya samar masu da haske ta hanyar tsafi. Sarki Lafaru na zaune gefe daya kusa da boka Muzafar ya yi tagumi yana mai tunani gami da zulumi.
Koda boka Muzafar ya ganshi a cikin wannan hali sai ta kamu da tsananin tausayinsa saboda haka sia ya matso kusa da shi ya zauna suka fuskanci juna, boka Muzafar ya dubi Lafaru ya ce Ya kai wannan sarki wai shin tunanin me kake yi ne haka mai zurfi?
Sa'adda sarki Lafaru ya ji wannan tambaya sai ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan ya ce Ya kai wannan sadaukin boka mai ban al'ajabi, kayi sani cewa a halin yanzu babu abinda nake tunani da zulumi face halin da birni na ke ciki, da kuma abinda zai faru nan gaba idan kwanaki arba'in suka cika idan sarki Nurwas ya zo da dakarunsa na yaki da nufin ya rushe mulkina ya haye kan karagata.
Koda jin wannan batu sai boka Muzafar ya bushe da dariya sannan ya ce Ya kai Lafaru ka kwantar da hankalinka tunda kana tare da ni, nayi maka alkawari har muje kogon darul ikisina mu dawo babau abinda zai taba mulkinka da dukiyarka daja baro acan birninka, domin wannan halifa naka d muka bari zai iya tafuyar da kowa da komai hatta matarka sharlis wacce ke kokarin ganin bayanka ita da dan da ta haufa maka, yanzu bari na nuna maja halin da birninka ke ciki.
Nan take boka Muzafar ya zura hannu a cikin rigarsa ya dauko madubin tsafinsa ya shafeshi da hannun hagu, sai ga hoton birnin Kufa ya bayyana, aka nuno sarki Lafaru na zaune bisa karagar mulki, fadawansa sun kewayeshi ana tafiyar da harkokin mulkin, suna mamakin yadda aka yi sarki ya samu lafiya, har ma yana masu karyar cewa wai daya daga cikin likitocinsa ne ya bashi wani magani mai kyau, yana shan maganin kuma ya samu sauki nan take.
Koda ganin wannan al'amari sai Sarki Lafaru ya cika da tsananin mamaki irin karfin sihirin boka Muzafar, domin shi dai gashi tare d boka Muzafar amman kuma gashi can a birnin kufa tare da fadawansa tamkar shi din ne ba wani ba.
Boka Muzafar ya sake shafar madubin tsafinsa da hannun hagu take hoton komai ya bace ya mayar da madubin cikin aljihun rigarsa, sannan ya dafa kafadar sarki Lafaru ya ce Ka saki ranka tamkar tsumma a randa, nan da cikar kwanaki arba'in zan nuna maka yadda za a fafata a yakin da za a yi tsakanin tsakanin jama'arka da na sarki Nurwas, kuma ina mai tabbatar maka d cewa halifanka ba zai bka kunya ba.
Koda jin wannan batu sai hankalin sarki lafaru ya kwanta, har fuskarsa ta fadada da murmushi ya dubi boka Muzafar yayi masa godiya.
Boka Muzafar ya dubeshi yace akan me zaka yi mani godiya, bayan nine da babban riba idan muka samu nasara bisa abinda muka fito nema.
Koda jin wannan batu sai sarki Lafaru ya ji zuciyarsa ta karaya, kawai sai ya dubi boka Muzafar cikin yanayin damuwa ya ce Ya kai wannan boka maganar da Gimbiya ta fada mana kan batun Aljani Maraful Dauwas ta jefa ni cikin tashin hankali da wasi wasi, ka fa tsaya kayi naxari akan al'amarin sosai, masoyiyar aljani maruful dauwa ita kuma gimbiya Rahila mutum ce kawai dai kammaninsu ne yazo iri daya, babu yadda za'a yi gimbiya Rahila ta debe wa Aljani Maraful Dauwas kewar Gimbiya Rashmin wanda babu aure a tsakanin mutum da Aljan, shin kayi tunanin sabuwar maganar da zamu je wa da aljani Maraful Dauwas da ita? Domin ya amince da bukatarmu har ya yarda ya sati mana gimbiya Ramlatus siyam.
Yayin da boka Muzafar ya ji wannan tambaya sai hankalinsa ya tashi, yayi shiru bai ce komai ba har zuwa tsawon yan dakiku, can ya dubi inda gimbiya Rahila ta ke sharar baccinta kmaar ma bata da abinda ke damunta, daman tunda aka fara wannan tafiya da ita bata da wani aiki sai bacci, kuma bata fira da kowa ba, sannan ko yaushe tana rufe da jikinta da kuma fuskarta da mayafi. Wasu ma daga cikin abokan tafiyar tata basu ga fuskarta ba, kuma basu san amfaninta ba a wannan tafiyar. Su boka Muzafar da sarki Lafaru ne kadai suka san amfaninta a wannan tafiya.
Lokacin da sarki lafaru ya ga boka Muzafar yayi shiru ya shiga tunani mai zurfi kamar ba zai daina ba, sai ya dafa kafadarsa, boka Muzafar ya dago da sauri kuma a razane kamar wanda ya farka daga mummunan mafarki, sannan ya dubi sarki Lafaru cikin matukar damuwa ya ce ya kai Lafaru ka yi sani cewa har a yanzu banyi tunanin wata sabuwar magana ba da zamuje da itq wajen Aljani Maraful Dauwas ba, amman nayi bincike a hallarar tsafina naga cewa Bamu da wani zabi face mu nemi taimakon gimbiya Rahila, domin tabbas tana da magana sahihiya wacce zata iya gamsar da aljani Maraful Dauwas har ya amince ya fito daga cikin kogon darul ikisina, har yaje ya sato mana gimbiya Ramlatus siyam, inda matsalar take shine bamu san irin sharadin da gimbiya Rahila zata shinfida mana ba.
Kafin sarki Lafaru yace wani abu sai kawai suka ga Gimbiya Rahila ta mike zaune ta yaye mayafin data rufe fuskarta da shi, kawai sai ta dubi boka Muzafar tayi masa murmushi mai kama dana mugunta sai ta koma ta kwanta ta sake lullube jikinta gabadaya ta kwanta ta ci gaba da baccinta.
Boka Muzafar ya gyada kai sannan ya dubi Lafaru ce wannan yarinyar ba karamar hatsabibiya bace, ya zama dole muyi hankali da ita.
Haka dai su boka Muzafar ssuka ci gaba da tafiya a bisa aljani Marhabul Zaurus dare da rana har suka shafe kwanaki 16, sannan boka Muzafar ya umarci aljani Marhabul Zaurus da ya sauko kasa domin a yada zango a huta, ba tare da gardamar komai ba kowa aljani Marhabul Zaurus ya saki fukafukansa ya yowa kasa ya sauka a cikin wani katon daji mai yawan duhuwa, duk inda mutum ya kalla sai dai yaga kyawawan koramai, bishiyu da manyan duwatsu ababan sha'awa, sannan ga tsutsaye iri iri suna kuka mai dadi irin wanda ke tausasa zuciya ya gusar mata da dukkanin wata damuwa, cikin tsananin farin ciki gabadayansu suka sauka daga kan aljani Marhabul Zaurus, suka kama tattaki domin su wasa kafafunsu, kumq su huce gajiyar zaman da suka yi a waje daya.
Koda boka Muzafar yaga wasu daga cikinsu na kokarin nausawa cikin wannan daji, sai ya kwala masu kira, gaba dayansu suka dawo gabansa suka tsaitsaya. Muzafar ya dubesu daya bayan daya ya ce Ya ku abokan tafiya kuyi sani cewa wannan daji da muke ciki shine dajin karshe wanda daga shi sai wandannan dazuzzuka guda 5 masu mugun hadari. Shi kanshi wannan daji abin tsoro ne domin akwai mugayen aljanu a cikinsa rukuni uku.
Rukuni na farko sun kasance yan fashi masu tare mutane da aljanu su kwace masu dukkanin dukiyarsu, sannan su rabasu da dukkanin matansu, basa yin kisa amman kum sai sun nakasta mazajen gabadaya, sun maishe su guragu ko makafi ta hanyar gutsure masu kafafu da kuma kwakule masu idanu. Karfin sihirin tsafi ba zai kwacemu ba a hannunsu face tsagwaron karfin damtse, zafin nama da karfin gudu da jarumta.
Rukuni na biyu kuwa wadansu masifaffun aljanu ne wadanda suka ksance dangin mayu, da farko idan suka kama mutane suna shanye jinin jikinsu ne, sannan sai su rinka cinye sassan jikinsu da kadan kadan, gaba bayan gaba.
Rukuni na uku kuwa wadansu zakwakurarun mayakan aljanu ne kimanin su miliyan arba'in da uku dauke da muggan makaman yaki, su dai wadannan aljanu babu wani makami da zai iya tasiri a jikinsu har yayi masu rauni ko kuma ya sokesu su mutu, sannan kuma idan zasu shekara suna yaki ba zasu gaji ba, idan mutum yana so ya tsira daga sharrinsu sai dai ya ratsa ta cikinsu da zababben gudu yana bankesu da karfin tsiya, kuma yana kare harin da zasu dinga kawo masa, har sai ya isa karshen dajin sannan za su rabu da shi. Kuyi sani cewa ba zamu iya ketare wannan daji ta sama ba, dole sai dai mu ketareshi ta kasa tare da aljnai Marhabul Zaurus, domin duk abinda ya keta tq sama take yake konewa ya murmushe ko mene ne shi. Idan har muna son tsura da rayuwarmu yayin ratsawa ta wannan mugun dajin sai dai mu hada karfi da karfe mu yaki wadannan mugayen aljanu, ya zamana cewa mun taimaki juna tamkar uwa daya uba daya muke. Amman fa duk da haka bani da tabbacin cewa duk da haka zamu fita daga wannan daji a raye ko kuma cikin koshin lafiya, domin komai zai iya faruwa ga kowannenmu, yanzu babu abinda ya kamacemu face mu kafa tantuna mu kwana anan tunda duhu ya soma, zai fi kyau mu shiga cikin wannan daji ido na ganin ido, domin wadannan mugayen aljanu sunfi gani da daddare.
Koda jin wannan jawabi sai kowa ya shiga taitayinsa aka shiga zulumi gami da fargaba, musamman wadanda suka kasnce ba jarumai ba kamar mahaifiyar sadauki Imran, yaro Masnur, Lumaira, sarkin Farisa da sarki Lafaru. Su kuwa sauran jaruman sun saurari bayanin sarki lafaru ne kawai, amman gani suke kamar zasu iya ratsa dajin ba tare da sun sha wata muguwar wahala ba. Kamar yadda Muzafar yake bayani, Kasancewar sun halarci yakuna da dama a rayuwarsu, abinda suka manta shine wadannan aljanu da suke cikin wannan daji ba irin aljanun da suka saba gumurzu da su bane, wadannan aljanu ne na musamman masu sadaukartaka da karfi na ban al'ajabi gami da mugun naci.
Ba tare da bata lokaci ba aka kafa tanti kuwa ya shiga nasa tantin shida dan uwansa, Gimbiya Rahila kadai ta shiga nata tantin ita kadai, amman boka Muzafar da Sarki Lafaru ma a cikin tanti daya suka zauna. Muzafar da Lafaru na cikin cin abinci kenan sai kawai Gimbiya Rahila ta fito daga nata tantin ta nufi tantin nasu inda taga aljani Marhabul Zaurus yana rangadi a tsakanin tantinan nasu dan tabbatar da tsaro. Kai tsaye gimbiya Rahila ta kutsa kai zuwa cikin tantin su sarki Lafaru, koda ganinta sai suka cika da tsananin mamaki, boka Muzafar ya dubeta ya ce Ya ke Rahila ene ne ya kawo ki cikin tantinmu a wannan lokaci?
Sa'adda Gimbiya ta ji wannan tambayar sai ta yi murmushi sannan ta cire mayafin da ke jikinta da farin kyallen data rufe fuskarta da shi, nan take kyakkyawar fuskarta da kuma surar jikinta suka bayyana a fili karara.
Boka Muzafar da sarki Lafaru suka bude baki suka kame, kuma suka kura mata idanu ashe ganin farko da suka yi mata ganin tsoro ne kuma tana lullube da fuskarta da jikinta shiyasa basu ga bauwar da Allah yayi mata ba, yanzu ne suka tabbatar da cewa Gimbiya Rahila ta fi gaba daya yan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login