Showing 36001 words to 39000 words out of 59226 words
Chapter 13 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
muyi maka kisan mummuke irin wanda zamu zare maka ruhin numfash a sannu da sannu.Ina tabbatar maka cewa baka da tudun tsira,baka da mafaka ko maboya duk irin mugun tanadin da muka shirya akanka ni da mahaifina sai ya tabbata a kanka kuma bazaka fara dandana azabarmu ba sai bayan 'dana ya girma.Yanzu menene ya kawoka wajena?"Sarki Lafaru yai ajiyar zuciya sannan yace,"Nazo ne naga dana da kika haifa?"Koda jin haka sai Sharlis ta bushe da dariya sannan ta murtuke fuska sannan ta ce,"Zanyi maka alfarma guda daya zaka ganshi yanzu sau daya amma bazaka sake ganinsa ba sai ranar da zai kasheka." Koda gama fadin haka sai tayi nuni da hannunta izuwa kofar wani daki sai kofar dakin ta bude wani kyakkyawan yaro dan shekara uku yafito daga ciki yana sanye da fararen tufafi na alhariri,riga da wando kuma yayi damarar yaki,da wata karamar takobi ta wasan yara daure a qugunsa.Koda yaron yaga sarki Lafaru a gabansa sai ya zare wannan takobi tasa ya rugo da gudu izuwa kan sarki Lafaru ya kawo masa duka.In ba dan sarki Lafaru ya goce ba da sai ya kwada masa takobin a fuska. Cikin sauri Sharlis ta ruke yaron sannan tace "Wannan shine danka SHADDAD Kuma na kulla gaba a tsakaninku irin wacce har abada baza ta gushe ba. Kullum sai na nuna masa fuskarka a madubin tsafi kuma sai fuskar taka ta rika barazanar cutar dashi, shi yara a duk sa'adda yaga fuskarka shima sai yayi kokarin cutar da ita.Da wannan furuci nake yimaka sallamar karshe,sai nan da wasu shekaru zamu sake ganawa". Koda gama fadin haka sai Sharlis da Shaddad suka bace bat tamkar basu taba wanzuwa ba a cikin falon.A wannan lokaci ne sarki Lafaru ya fashe da kukan bakin ciki bisa ganin yanda aka hadashi gaba da dansa na cikinsa. Cikin matukar sanyin jiki da tsananin bakin ciki ya fita daga cikin wannan gida yakoma can turakarsa inda yaci gaba da tunani da zarya ya rasa abinda zai fissheshi a rayuwa.A wannan dare bai runtsa ba har asuba tayi a sannan ne wata dabara ta fado masa take kuwa barci ya sace shi bai sani ba sai da gari ya waye rana ta take sannan ya farka. Cikin hanzari sarki Lafaru ya tashi yaje yayi wanka sannan yaci ado tamkar babu wani abu dake damunsa yawuce fada ya zauna akan karagar mulki aka ci gaba da harkokin mulki kamar yanda aka saba yana ta nishadi da walwala abinsa.Lokacin da ya rage baifi rabin sa'a ba a tashi daga fadar sai sarki Lafaru ya bingire daga kan karagar mulkin ya fado kasa yana shure-shure da numfashi sama-sama kamar zai mutu. Cikin gaggawa Dakaru suka daukeshi suka kaishi cikin turakarsa aka kwantar dashi akan gado sannan aka kirawo likitocinsa suka shiga ayyukansu amma har tsawon sa'o'i ba a samu nasarar shawo kan lalurar sarki Lafaru ba.Koda ganin haka sai aka tura aka kirawo gaba daya sabbin bokayen da sukayi shuhura a garin domin su bada tasu gudunmawar.Nan fa bokayen suka rinka shiga cikin turakar sarki daya bayan daya kowanne nayin iyakar kokarinsa amma babu nasara. " Sa'adda boka na tara ya shiga sai ya dubi sarki Lafaru dakyau sai yayi murmushi sannan ya dubi gaba dayan hadiman sarki dake cikin turakar ya ce, "Kowa ya fita ya bashi wuri." Ba tare da gardamar komai ba kuwa suka fice. Fitarsu ke da wuya sai bokan ya karanta wasu dalasimai na tsafi ya tofa a kowacce kusurwa ta dakin sannan ya dubi sarki ya ce, "Tashi zaune ya shugabana. Na sani cewa babu wata rashin lafiya a tare dakai, wanda kake nema yazo, nine mai share hawayenka.
Koda jin wannan bati sai sai sarki ya mike daram ya dubi vokan cikin alamun tsoro da fargaba ya ce Mene ne tabbacinka na cewar babau wanda zai ji abinda za mu tattauna a yanzu.
Da jin wannan tambaya sai bokan ya ce saki ranka kamar tsumma a randa ya shugabana, ka sani cewa na tsaface wannan daki da muke ciki yadda ko makiyarka sharlis bata isa taji abinda zamu tattauna ba. Yanzu kuma duk matsalolin da kake ciki zan iya warware maka su idan har kabi umarnin da zan fada maka. Amman fa bisa sharadi guda daya, sharadin kuwa shine bayan bukatarka ta biya zaka raba kasarka da kuma dukiyarka kaso biyu ka bani kaso daya, idan ka kuskura ka saba alkawari zan lalata dul kariyar dana baka, abokiyar gabarka da danta su samu nasara a kanka.
Sa'adda boka ya zo nan a zancensa sai hankalin sarki lafaru ya tashi domin yanzu dai ga mafita da waraka sun zo masa, to amman mene ne amfanin warakar tunda zai raba kasarsa da dukiyarsa biyu ya bada rabi, ai idan hakan ta faru daukakarsa ta ragu a idon sauran sarakai.
Amman daya tuna cewa idan fa bai yi hakan ba karshenta ne fa ya rasa komai. Lokacin da sarki lafaru ya gama wannan nazarin a cikin zuciyarsa, sai ya dubi bokan cikin nutsuwa ya ce Wai shin da farko ma wane ne kai? Shin yanzu kana nufin ka ce zaka iya dawo mani da sadaukantaka ta wacce sharlis ta rabani da ita? Kuma zaka iya bani nasara bisa yakin da zanyi da sarki Narwas nan da cikar kwanaki arba'in, kuma ka kareni daga sharrin sharlis da danta na yanzu da kuma shekarun gaba masu zuwa.
Koda bokan ya ji wandan nan tambayoyi sai ya bushe da dariya ya ce Ko shakka babu duk zan iya yin irin wadannan abubuwa kuma ni kadaine a nahiyar nan zan iya, musamman idan ka yi la'akari da yadda duk nasan matsalolinka, da kuma yadda nasan sirrin abokiyar gabarka sharlis wacce ke shirin daukar mummunar fansa a kanka. Da farko dai ni suna na boka Muzaffar Bn Munzur, kuma ni haifaffen birnin Kisra ne, amman bisa wata bukata tawa na bar mahaifata na bazama duniya, yau shekara arba'in kenan da barina gida, ban sake komawa ba kuma har yanzu bukatata bata biya ba, sai idan na biya maka taka bukatar sannan kai kuma ka cika mani nawa alkawarin da ka daukar mani, kada kayi tsammanin cewa mulki da dukiyar da zaka bani sune bukatar tawa, ko kadan ba su bane, bukatar tawa wani babban sirri ne wanda duk wanda ya same shi sai ya fi kowa da komai matsayi a duniya, a iya bincikena na gano cewa lallai sai na mulki rabin kasarka, sannan na mallaki rabin dukiyarka, to a lokacin ne zan kai izuwa wannan matsayi. Yanzu sai ka saurareni da kyau dan kaji umarnin da zan baka idan har kana son karfin damtsenka ya dawo kafi karfin wulakancin da sharlis da kuma danta zasu yi maka a nan gaba, nan da cikar shekaru goma sha biyar.
Ya kai wannan sarki da farko dai ina son ka sani cewa idan har kana son ka karya asirin da sharlis ta yi maka, har karfin damtsenka ya dawo kuma ya zamana cewar tsafi b zai sake tasiri a jikinka ba, sai ka auri budurwar data fi sharlis kyau a cikin watanni biyu masu zuwa nan gaba, ita kuwa wannan budurwa duk duniya a halin yanzu babu wata ya mace data kaita kyau ana kiranta da suna Ramlatus siyam.
Ramlatus siyam ta kasance yar sarki Hindu na yanzu wato sarki Nasmir Bn Hayat wabda babu wani matsafi da ya fishi karfin sihiri a duniya, kuma babu wani sarki da ya fishi yawan zakwakuran mayaka wadanda suka siyar da rayuwarsu dan bauta masa, kai bama mayakansa ba hatta mutanen kasrasa suna bauta masa ne, saboda tsananin tsoronsa da suke ji.
A duniya babu abinda sarki Nasmir yake so sama da yarsa gimbiya Ramlatus siyam, sabida haka ne ma ya bata tsaro na musamman a gidan sarautarsa da karfin sihiri, sannan kuma ya zuba dakaru kimanin miliyan dubu daya na aljanu suna shawagi a saman gidan nata dare da rana dan tabbar da tsaro. A kasan gidan kuwa ya zuba dakaru miliyan dubu daya na biladama suna gadi, tunda aka haifeta aka sata a cikin wannan gida, wanda girmansa ya kai na wannan birni na Kufa. Gabadaya ita da mahaifiyarta da barori masu yi masu hidima babu wanda ya kara shiga gidan ko ya fita face shi kanshi sarki Nazmir. Babu yadda sarki Nashmir ya amince ya baka yarshi gimbiya Ramlatus siyam domin ka aura, sai dai mu sato ta bai sani ba. Sato gimbiya Ramlatus siyam kuwa daidai yake da mutum yayi kundubala a cikin rami mai zurfin kafa dubu, ya kai wannan sarki idan har ka samo sa'ar auran gimbiya Ramlatus siyam to a ranar da ka kwanta da uta a wannan lokaci ne sihirin daya shiga jikinka zai karye, sannan karfin damtsenka zai dawo. Ka sani cewa koda karfinka ya dawo ba zaka iya yiwa sharlis da danta komai ba, kuma wannan da data haifa sai ya girma ya zama gawurtaccen sadauki da babu kamarsa a duniya karfin damtse dana sihiri, kuma babu wanda zai iya tunkararsa har ya hanashi halaka ka, face yar da zaka haifa da gimbiya Ramlatus siyam nan da shekara daya idan har ka samu nasarar auranta a cikin watanni biyu masu zuwa. Hanya daya zamu bi mu samu haduwa da gimbiya Ramlatus siyam kafin cikar watanni biyu masu zuwa, hanyar kuwa ita ce dole ne muyi shiri ni da kai mu tafi kogon darul iksina dake can karshen birnin sin domin mu sadu da aljani Maruful dawwas, domin shine kadai aljanin da zai iya sato mana gimbiya Ramlatus siyam aga can birnin Hindu, kuma ya ganota gaemu cikin kwanaki ashirin da biyar kacal! Amman ka sani cewa kafin mu isa can kogon darul ikisina daga nan sai munyi tafiyar kwanaki talatin da uku, kaga kenan idan ka hada da kwanaki ashirin da biyar da aljani Maruful dawwas zai yi ya kawo mana gimbiya Ramlatus siyam akan lokaci, kuma idan har aka gota kwanaki sittin koda yini daya ne to fa aurenka da ita bazai taba yiwuwa ba, ka sani cewa akwai tashin hankali gami da bal'ai iri-iri akan dazuzzukan da zamu ketare kafin mu isa kogon darul ikisina, inda aljani maraful dawwas, ina mai tabbatar maka da cewa mu biyu kacal face da taimakon asu manyan jarumai guda shida wadanda suma basu da wani buri face suje kogon darul ikisina omin debe tsumin wannan maganin da zai warkar da masoyansu daga cutuka daban daban. Dukkanin wadannan jarumai sun kasa zuwa wannan kogo na darul ikisina saboda dole sai da ni dinnna sannan zasu iya zuwa, kasancewar ni kadaine nasan hanyar da za a bi aje wannan kogo na darul ikisina anan cikin duniya, ni kuma nayi al?awarin cewa bazan jeba duk da cewa idan naje zan samu damar cika babban burina na duniya, sai a yanzu da matsalarka ta taso sannan na san cewa burina zai cika, idan har na taimakeka matsalarka ta kau kuma ka cika alkawarin daka daukar mani, wadannan jarumai abokan tafiyarmu duk suna zaune ne a kasashe daban daban, amman duk zan iya kaimu wurinsu cikin kwana daya bisa taimakon wani babban hadimina mai suna Shaibatul Barbus. A halin yanzu duk duniya babu wani aljani da ya ke da gudun Shaibatul Barbus da zafin namansa face aljani maraful dawwas, har ma shi ninka Shaibatul Barbus sau goma a komai, shine dalilin daya sa zai iya shiga fadar sarki Nashmir ya sato gimbiya Ramlatus siyam ba tare da ya halaka ba.
Jarumi na farko abokin tafiyarmu shine Sadauki Haiman wanda ke zaune a birnin Misra, ahalin yanzu duk duniya abu jarumin da ya kai Haiman iya sarrafa takobi, domin idan yana rike da takobinsa yana iya sare kawunan mutane ko aljanu guda dubu a cikin dakika biyar, dan haka komai yawan dandazon dabaru in har ya shigesu sai ya trwatsa su, ka yi sani cewa a cikin daji na farko da zmau riska kafin mu isa kogon darul ikisina akwai wadansu mugayen maridai wadanda adadinsu ya kai miliyan dubu, wadannan maridai saboda tsananin tsawonsu idan mutum ya daga kai ya kallesu sai yaga kamar sun hade d sararin samaniya. Komai yawan runduna ta aljanu idan tazo giftawa ta saman wadannan maridai sai sun cafcakosu sun ciccinyesu, babu wanda zai iya tarwatsa wadannan maridai har mu samu ratsawa ta cikinsu mu wuce ta cikinsu face Sadauki Haiman, amman fa wannan ba yana nufin cewa ya zama wajibi dukkaninmu mu tsallake sharrin maridan, komai zai iya faruwa ga dayanmu, domin tsafi da karfin jarumtaka ba zasu cecemu ba face sa'a da tsananin rabo.
Fiye da shekaru dubu baya mutane da aljanu suka daina ratsa wannan daji, Sadauki Haiman na da wata kyakkyawar mata guda daya wacce aljanu suka shafeta ta makance, babu irin neman magani da bai yi ba domin idanunta su bude amman abu ya gagara, sai daga baya ya gano dole sai na rakashi izuwa kogon darul ikisina ya debo wannan tsumin maganin ya baiwa matarsa ta wanke fiskarta sannan zata warke. Wani abun mamaki shine Lumaira matar Sadauki Haiman tun tana jaririya wannan lalura ta makanta ta sameta, dan haka bata taba ganin kalar iyyaenta, danginta da mijinta ba, kuma ba baiwa Haiman auren Lumaira ba sai bisa alkawarin komai dadewa sai ya nema mata magani. Sau bakwai sadauki Haiman yana zuwa wajena akan batun tafiya kogon darul ikisina sannan yana mani alkawarin zai biya dinare dubu, amman sai nake fada mashi lokacin tafiyarmu bai yi ba, lallai idan lokacin tafiyarmu yayi zan nemeahi da kaina.
Abikin tafiyarmu na biyu ba kowa bane face Jaruma Shadira ta birnin Baitul Halwal, a halin yanzu duk duniya bau wanda ya fi jaruma Shadira iya harbi d kibiya, domin tana iya harba kibiyoyi guda dari a cikin dakika Ashirin, tana da wani irin kwari na musamman mai harba kibiyoyi Ashirin a lokaci guda. Tsananin zafin naman jaruma Shadira yafi gaban tunani, acikin daji na biyi da zamu wuce kafin mu isa kogon darul ikisina, akawai wasu mugayen burirrika kimanin guda dubu dari hudu, wadanda suke yawo a sama tamkar tsuntsaye domin suna dauke da fuka-fukai, kuma suna da zara-zaran farata masu tsananin kaifi da tsini, wanda da zarar sun cafi wuyan mutum sai dai kaga sun cisge masa kai, tabbas jaruma shadira ce kadai zata iya tarwatsa mana wadannan mugayen burirrikan har mu samu damar ratsawa da wannan daji mu wuce, wannan baya nufin dukkaninmu zamu iya tsallake sharrin burirrikan dukkaninmu face sa'a da kuma nasara. Jaruma Shadira tana da wani dn uwa nata wani karamin yaro mai kimanin shekaru tana ana kiransa da suna Masnur, tunda aka haifi Masnur bai taba magana ba, kuma shima aljanu ne suka shafeshi aka tabbatar da cewa bazai tab warkewa ba face an debo wannan tsumin maganin na cikin kogon darul ikisina an bashi ya sha.
Jaruma Shadira tana matukar kaunar Masnur fiye da komai a duniya, domin su goma sha daya ne a wajen mahaifinsu, amman mutum tara duk sun mutu saura su biyu kacal, sakamakon wani azababben yaki da aka yi a kasarsu, wanda aka kashe kaso takwas cikin kaso goma na jama'ar kasar gaba daya. A wannan ya?i ne su jaruma Shadira suka rasa iyayensu da dukkanin danginsu, saboda haka Shadira ta dauki alkawarin cewa ko da zata rasa rayuwarta sai ta nema wa dan uwanta magani, domin babban burinta shine taji ya budi baki ya ambaci sunanta kafin ajali ya risketa, bisa wannan daliline ma yasa jaruma Shadira taki yarda ta yi aure duk da cewa ta kasance kyakkyawar budurwa abar kwatance.
Abokin tafiyarmu na uku shine jarumi Ishran Bn Suhairu wanda ke zaune a birnin Istim, a halin yanzu duk duniya babu wanda ya fi jarumi Ishran iya sarrafa sanda, domin idan yana yaki da sanda a hannunsa komai yawan abokan gaba dayansu bazai iya taba jikinsa ba, sabida zafin namansa da kuma karfin dukansa, kuma yana iya shafe kwana biyu yana yaki ba tare da ya nuna alamar gajiyawa ba.
A cikin daji na uku da zamu wuce kafin mu isa kogon darul ikisina akwai wadansu mugayen tsuntsaye wadanda adadinsu ya kai kimanin dubu dari biyar da arba'in. Kaifi da tsini baya tasiri a jikin wadannan tsuntsaye, haka ma karfin sihiri, sai dai a makesu da sanda ko icce, idan wadannan tsuntsaye suka karci jikin mutum da faratansu ko kuma da tsinin bakinsu take wajen zai zama gyambo har da tsutsa, babu wanda zai iya trwatsa mana wa?annan tsuntsaye mu iya ratsawa ta cikin dajin face Jarumi Isran Bn Suhairu. Isran yana da mahaifiya wacce ta tufa tukuf ainun, ammnan tunda aka haufeta bata taba taka kafafunta ba, domin a lankwashe suke kamar lauje, kuma itama aljanu ne suka shafeta, babu irin neman maganin da ba a yi ba, amman abu ya gagara, sai daga baya bikaye suka tabbatar da cewa sai an shafa mata ruwan wannan maganin na kogon darul ikisina annan zata warke ta iya mikewa. Isran yayi alkawari koda zai rasa rayuwarsa sai yaje kogon darul ikisina ya debo wannan magani, sau tara Isran yana zuwa wajena akan na rakashi kogon darul ikisina, amma sai na fada masa yayi hakuri sai idan lokacin tafiyar tamu yayi zan nemeshi da kaina.
Abokin tafiyar mu na hudu ba kowa bane face Gimbiya Zarina ta birnin Farisa, a halin yanzu duk duniya babu wanda ya lakanci sanin sirrin daji sama da Gimbiya Zarina, domin tafi kowa kwarewa a iya farauta da sanin sawun ko wace irin dabba gami da hadarinta. A cikin daji na hudu da zamu ratsa kafin mu isa kogon darul ikisina akwai mugayen dabbobin daji wadanda suke lambo da buya, sai dai kawai mutum yaji sun dira a jikinsa sun turmusheshi, kafin ya ankara sun halakashi, akwai hanyoyi da wurare a dajin wanda dabbobin basu isa su bi ba, wadannan hanyoyine kawai mutum zai bi ya iya tsira daga sharrin wadannan dabbobin, domin dabbobin dake wannan daji basa jin sara sa suka kuma tsafima baya tasiri a jikinsu. Gimbiya Zarina ce kadai zata iya fitar damu daga cikin wannan daji.
Sarkin Farisa ya kasance dan uwa ne a wajen Zarina, kuma tagwaye aka haifesu tamkar an tsaga kara haka suke a kamanni, sannan sun kasance kyawawa ne na gaban kwatance, tunda sarkin Farisa ya girma ya zama saurayi bai taba sha'awar ya