Showing 45001 words to 48000 words out of 59226 words

Chapter 16 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

kuka tare domin tunda aka haifi Gimbiya Rahila bata taba rabuwa da mahaufinta ba daidai da rana daya, dare da rana suna tare har ta girma ta cika budurwa face makwanci idan dare yayi.
Ko da ganin yadda sarki da Rahila ke kuka rabuwa da juna sai tausayinsu ya kama boka Muzafar da sarki Lafaru har basu san sa'adda idanunsu suka cika da kwalla ba.
Nan take boka Muzafar ya ji yayi nadama bisa wannan babban buri da yasa a gabashi, tunda ga shi a sanadinyyar haka ya zama bakin takobi mai raba mai masoya. Boka Muzafar ya tuna cewa shifa a yanzu bashi da kowa a duniya iyayensa sun mutu tun yana yaro dan shekara 6 matarsa ta mutu a lokacin da ta zo haihuwar fari, dan cikin nata ma sai ya zo a mace, to tun daga sannan bai sake marmarin yin aure ba, bugu da kari tun yana karami aka kmashi a matsayin bawa, aka daukeshi daga garinsu na asali aka tafi da shi can wata nahiyar da ban da shi da dangin iya balle na baba.
A lokacin ne aka siyar da shi ga wani shahararren boka wanda yayita bauta a gareshi har ya shekara ashirin da biyar, a sannan ne mai gidan nasa ya mutu ya gaji sirrinkan tsafinsa saboda tsananin biyayyar da yayi wa mai gidan nasa.
Koda boka Muzafar ya tuna cewa shifa yanzu bama zai tuno asalin inane mahaifarsa ba, balle ya tuno da danginsa ba, sai ya koma can gefe daya ya hada kai da gwiywa ya kama kuka. Yana cikin wannan hali ne yaji an dafa kafadarsa, koda ya dago kainsai yaga ashe sarki Lafaru ne tsaye a kansa, koda Lafaru yaga hawaye a cikin idanun boka Muzafar sai jikinsa yayi sanyi sannan ya ce da shi Y kai wannan shu'umin boka kuma sadaukin boye ina dalilin wannan kuka naka alhalin ga shi bukatarmu ta biya, mahaifinta ya hakura zai bamu Gimbiya Rahila.
Koda jin wannan tambaya sai boka Muzafar ya yi ajiyar zuciya sannan ya share hawayensa ya ce Ya kai abokin tafiyata, ka sani cewa duniya babu ranar bakin ciki kamar ranar rabuwa da masoyi, hakika na kamu matuka da tausayin wannan sarki da yarsa, bisa yadda zasu yi rabuwar dole ba a son ransu ba, kuma hakan ne ya tuno mani da asalina na kasancewata maraya, wanda ma ba zai iya tuno mahaifarsa ba bare danginsa, hakika kaddara ta yanke mani kauna da farin cikin rayuwa wanda har abada bazan samesu ba domin kowa ya bar gida gid ya barshi.
Yayin da sarki Lafaru ya ji haka sai shima ya tuna cewa shima fa yanzu bashi da kowa face mulkinsa sai kuma dukiyarsa da ya baro a birnin Kufa, nan take ya sake tunawa yau fa saura kwanaki arba'in yayi yaki da sarki Nurwas na birnin Zaruk kuma ga shi gashi yanzu ya bar kasar, to wai shin yanzu za a yi wannan yakin ko kuma ba za a yi ba? Idan kuma aka yi yakin suwa za su samu nasara?
Shin wannan halifa nasa wanda boka Muzafar ya kirkira zai iya kare birnin daga sharrin sarrki Nurwas da dakarunsa? Shin da gaske ne idan basu samu nasara ba bisa abinda suka fito nema ba shida boka Muzafar dansa Shaddad zai girma ya zama babban makiyinsa har kuma ya kasheshi?
Sarki Lafaru yana cikin wannan tunani ne Gimbiya Rahila da mahaifinta suka zo kansa suka tsaya, cikin hanzari boka Muzafar da sarki Lafaru suka mike tsaye suna masu fuskantarsu.
Sarkin ya dubi boka ya ce ya kai wannan Sadauki mai jarumtaka ta al'ajabi, kayi sani cewa ban kasance boka ba, dan haka ban san irin aikin da yata zata yi maku ba? Amman da ganin fuskokinku baku yi kama da makaryata ba kuma ba zaku kasance masu kin cika alkawari ba, abu daya nake zargi akanku bai wuce rashin aldalci ba ga duk wanda ke karkashinku sannan zaku iya yin komai dan ganin bukatarku ta biya. Ni dai yanzu ga yata nan na damkata amana a hannunku bana bukatar na ji abinda zaku yi da ita, amman ina son ku kasance masu rike alkawari ku dawo mani da ita lafiya kamar yadda kuka yi alkawari da farko. Idan kuwa kuka ci amanata to kuma amana zata ci ku.
Koda gama fadin haka sai sarki ya sake rungume Gimbiya Rahila a kirjinsa tare da fashewa da matsanancin kuka itama kawai ai ta kama kukan, da kyar suka kasi juna kana daga bisani suka yi bankwana. Daga nan sarki da dakarunsa suka juya suka shige cikin birnin na su.
Sarki na waigen yarsa gimbiya Rahila yana mai zubar da hawaye, haka itama, haka dai suka ci gaba da daga wa juna annuwa har suka kule.
Ba tare da wani bata lokaci ba, boka Muzafar sarki Lafaru da gimbiya Rahila suka fito daga cikin wannan birni inda suka iske aljani Maraful Dauwas a zaune yana jiransu. Nan take duk su ukun suka haye bayan aljani Marhabul Zaurus shi kuwa sai ya bude fuka-fukansa ya tashi sama ya luluka a cikin gajimare sannan ya tsaya cak a cikin iska.
Koda ganin haka sai boka Muzafar ya daka masa tsawa tare da cewa Me kake nufine da zaka tsayar da mu cak a sararin samaniya?
Cikin razana da biyayya aljani Marhabul Zaurus ya rusuna ya ce Ya shugabana ai baka fada mani inda zamu je ba, umarninka nake jira?
Koda jin haka sai boka Muzafar yayi ajiyar zuciya sannan ya ce Yanzu mun hau mataki na farko a wannan gagarumar tafiya da ke gabanmu, saura mataki na biyu wanda shine tafiya zuwa dauko abokan tafiyarmu. Ya kai Marhabul Zaurus na umarceka daka kaimu birnin Misra domin mu sadu da sadauki Haiman, kafin Boka Muzafar ya gama rufe bakinsa tuni aljani Marhabul Zaurus ya dubi bangaren kudu ya falfala da matsanancin gudu cikin gajimare tamkar tauraruwa mai wutsiya.
Tunda aka fara wannan tafiya hira ta barke tsakanin sarki Lafaru da boka Muzafar, ita kuwa gimbiya Rahila sai tayi shiru kawai ta kishingida kamar tana yin bacci idanunta a lumshe bata tanka masu ba.
Sarki Lafaru ne ya fara yin gyaran murya sannan ya dubi boka Muzafar ya bushe da dariya, al'amari da ya baiwa boka Muzafar mamaki da haushi kenan, ya dubeshi a fusace ya ce ina dalilin wannan dariyar ta ka?
Sarki Lafaru ya hadiye rai sannan ya ce Gani nayi ni da kai duk mun kai shekaru dari a duniya amman hr yanzu bamu da kwanciyar hankali, sannan muna da buri mai tsauri a cikin zukatanmu, kamata yayi ace a yanzu muna cikin rayuwar farin ciki da nutsuwa tare da iyalanmu.
Da jin wannan batu sai boka Muzafar ayi murmushi sannan ya ce Ai shi rai da kake ganinsa baya rabuwa da buri, daga lokacin da mutum yayi aure babu abinda zai fara tunani sama da haihuwa. Idan ya samu haihuwar sai kuma ya fara tunanin tara dukiyar da zai baiwa dansa, idan tafiya tayi tafiya aka tara abin duniya ya taru sosai sai a fara hangen mulki, idan mulkin ya samu sai a fara hangen daukaka, a lokacin da daukakar ta samu zaka ga tsufa ya fara zuwa, to a Sannan ne lafiya zata yi karanci dan haka sai kaga kullum a cikin neman lafiya ake, wani har ya mutu ba zai samu lafiyar ba, wani kuma sai kaga yau da lafiyar gobe kuma babu, haka dai rayuwa zata kare amman buri bai kare ba walau yaro matashi ko tsoho.
Koda boka Muzafar ya zo nan a jawabinsa sai Gimbiya Rahila ta yi caraf ta tari numfashinsa tare da cewa Wanne abu mutum zai yi domin ya iya sarrafa zuciyarsa da kwadayin burika?
Boka muzafar ya amsa mata da cewa babu wani abu mai kore burika daga cikin zuciya face ya dauki hakuri, kuma ya rike gaskiya da amana, idan har yayi hak to samu da rashi ba zasu dameshi ba.
Rahila tayi murmushi ta ce nda kunyi aiki da wannan maganar da ka fada yanzu da bazaka rabani da mahaifina ba domin kuje ku bayar da ni ga aljani Maraful Dauwas na maye gurbin masoyiyarsa gimbiya Rashmin.
Koda jin wannan batu sai boka Muzafar da sarki Lafaru suka zazzaro idanu cikin tsananin mamaki suka kasa cewa komai, tsawon yan dakiku su dukansu sunyi shiru daga can sai boka Muzafar yayi ajiyar zuciya ya ce Yake Gimbiya Rahila ya akayi kika san wannan al'amari namu alhalin baki kasance matsafiya ba, haka shima mahaifinki bai kasance matsafi ba?
Rahila ta girgiza kanta cikin alamun takaici sannan ta ce Ashe baku yi mamaki ba lokacin da na bayyana tsulum a tsakiyarku ba sa'adda kai da mahaifina kuke shirin kaurewa da yaki, a cikinku babu wanda yaga ta inda na fito kawai nasan kun ganni ne tsulum a tsakiyarku, to ka sani cewa bana tsafi amman ina mu'amala da matsafa, kuma suna sanar da ni duk irin abinda zai faru gareni a yanzu ko a nan gaba. Kuma suna bani taimako, inda ban san abinda zai faru a gareni a cikin wannan muguwar tafiya da zamuyi ba da bazan biyoku ba, ku sani cewa a cikin wannan tafiya da zamuyi zamu sha bakar wahala wacce zamu gwammace mutuwa da rayuwa, amman a karshe wasu daga cikinmu burinsu zai cika, wasu kuma zasu samu nakasa wacce zasu mutu tare da ita, wasu kuma gabadaya ma zasu rasa rayuwarsu, ina mai shawartarku da kada kuyi mani tambaya bisa bayanin dana yi maku, domin ko zaku kasheni b zan iya amsa maku tambayar ba, daga yanzu bazan kara cewa uffan ba har sai mun usa wadannan mugayen dazuzzukan guda biyar, wadanda sai mun ratsa ta cikinsu ne sannan zamu isa kogon darul ikisina lallai acan ne zaku sake tsinkewa da al'amarina, abu na karshe da zan fada maku shine kunyi babban kuskure da har kukw tunanina a matsayina na bil'adama zan iya maye gurbin aljana, ai kama da wane bata wane, ina mai shawartarku daku sauya tunani gami da shawara bisa magana daya wacce zaku je wa da aljani Maraful Dauwas da ita har ya amince ya biya maku bukatarku, idan kuma kun kasa tunanin hanyar da zata fissheku ni ina da dabara wacce dole ne aljani Maraful Dauwas ya amince yabi umarninku, amman bazan furta maku ba face kun dauki alkawarin cewa nima xaku biya mani wata bukata tawa ta musamman, ku sani cewa kuna da isasshen lokaci nayin tunani gami da shawara daga yanzu har izuwa sa'ad da zamu isa kogon darul ikisina.
Koda gama wannan dogon bayank sai Gimbiya Rahila ta koma ta kishingida ta kama bacci abinta, tamkar a cikin turakarta take.
Boka Muzafar da sarki Lafaru kuwa sai suka sunkuyar da kawunansu kasa suka fada kogin tunani saboda tsananin mamakin al'amuran da suka ji daga bakin Gimbiya Rahila. A daidai wannan lokaci ne suka fuskanci cewa Aljani Marhabul Zaurus na sakkowa kasa wne, koda suka leko kasa sai sukaga ashe har sun iso birnin Misra. Nan take Marhabul Zaurus ya durfafi wani katon gida kayataccen gaske irin na sarakai, ya sauka a tsakiyar farfajiyar gidan, acikin wani tafkeken lambu wanda ke cike da furanni iri-iri masu dadin kamshi, sanann kuma a wani bangaren kayan marmarine kala-kala kamar irin su inibi, baure, fasa dabur da dai sauransu. Tsuntsaye kuwa gasu nan kyawawa iri-iri wank kalarma mutum bai taba ganin irinsa ba.
Nqn take sarki Lafaru da gimbiya Rahila suka kamu da tsananin sha'awar wannan gida, domin ya isa a kirashi da aljannar duniya. Da saukar aljani Marhabul Zaurus a cikin wannan kayataccen labu sai boka Muzafar ya sauka daga kansa da sauri sannan ya yafito gimbiya Rahila da sarki Lafaru da hannu yana mai yi musu nuni da su biyoshi a baya. Ba tare d gardamar komai ba kuwa suma suka sauka daga kan aljani Marhabul Zaurus suka bi bayan boka Muzafar da sauri.
Boka Muzafar ya dinga kuntsawa ta hanyoyi daban daban ta cikin lambun kamar tafiyar ba zata kare ba a haka dai har suka iso bakin wani katon daki, tun kafin su iso kofar dakin suka hango wata tsaleliyar budurwa mai tsananin kyawu na ban al'ajabi ta fito daga cikin wani daki tana dogara sandar zinare a hannunta. Kallo daya Gimbiya Rahila tayi wa budurwar ta tabbatar da cewa ta isa a yi kwatancenta a bangaren kyawu domin tasan cewa dolene ta ruda maza. Budurwar tana sanye da wata riga doguwar riga launin ruwan kwai ta siliki, wanda aka yi wa ado da zanen furanni na ruwan zinare, takalman dake kafarta kuwa da lu'u lu'u aka yi su, shima launin ruwan kwai, gashin kanta dogo ne da ya zuba har kan gwiywarta kamar zai shari kasa, kuma ya kasance bakikkirin sai sheki da walwali yake yi. Tana da daradaran idanuwa wadanda idan ta dubi mutum da su sai yaji kamar zai shide saboda tsabar kyawunta, hancinta dogone kuma siriri kai kace lika mata shi aka yi, bakinta kuwa dan kankani ne kamar da alkalami aka zanashi, kirjinta a ciki yake shi kuma cikinta a shafe yake kamar bata taba cin komai ba a duniya, kugunta kuwa kirar kalangune ya fashe, mazaunanta nada tudu sosai, kafafunta sirarane kuma tana da zararan yan yatsu na hannu da kafa, tana da dunguniya mai tudu kuma kafafun nata a mike suke sambal babu karkata ko kadan, kkaurin jikinta madaidaicine fatar jikinta kuwa kamar idan ka latsa jini ne zai tsattsafo saboda haske, Kash! Sai dai duk tsananin kyawu wannan budurwa abu daya ne tawayarta, bakomai bane illa makanta.
A lokacin da budurwar ta tunkaro inda su boka Muzafar suke, Gimbiya Rahila ta gane cewa makauniya ce, saboda ganin yadda take laluben hanya da sandar hannunta, tana xuwa daf da su boka Muzafar sai ta tsaya fuskarta na kallon gefe tayi murmushi sannan ta ce Lale marhabun da manyan baki masu daraja, ku zo mu karasa wajen masoyina.
Koda jin wannan batu sai Gimbiya Rahila da sarki Lafaru suka cika da tsananin mamaki, na yadda akayi ta san da zuwansu da kuma yadda akayi ta tsaya a daidai inda suke alhalin bata gansu ba tunda ba ido ne da ita ba.
Kamar budurwar ta san abinda Sarki Lafaru da gimbiya Rahila ke wasi-wasi a zukatansu kawai sai ta dago kai a karo na biyu ta yi murmushi sannan ta ce Kada kuyi mamaki bisa tsayuwata anan daf da ku, domin ina amfani da numfashi ne ba idanu ba, ko mutum, aljan ko dabba idan suna nesa da ni koda tazarar takai ta kamu arba'in ina iya jin numfashinsu wannan ba tsafi bane baiwace kuma da ita aka haifeni tun ina jaririya. Yadda aka yi kuwa nasan da zuwanku shine Masoyina ne yayi bincike a cikin hallarar tasfinsa ya hangoku. Ku yi sani cewa yau nida masoyina muna cikin farin ciki mara misaltuwa, saboda sanin cewa lokaci yayi da zamu cika burinmu, mu kuma yaye bakin cikin daya addabemu tsawon shekara da shekaru.
Koda gama fadar haka sai budurwar ta juya tayi masu jagora har izuwa cikin wannan babban dakin, da shigarsu cikin wannan daki sai Rahila da Lafaru uka zama cikakkun yan kauye saboda ganin irin kayan alatun da aka shirya a ciki, nan take sarki Lafaru ya gane cewa fadarsa bata wuce akurki akan wannan ba, kuma kayan kawar da aka zuba a dakin zasu iya siyen na fadarsa sau dari, zaune akan wata kujera ta jauhari sadauki Haiman ne, kunyangi da barori sun kewayeshi suna yi masa hidima, wasu fifita suke masa da mafifici na gashin dawisu, wasu kuwa gyara masa kayan jikinsa suke yi, wata kuyanga na tsaye a gefe guda sai kirari take masa tana cewa Hutawarka lafiya sadauki mai kamar sarki, gaisheka abul saifu, kaine kafi kowa iya sarrafa kai, jan gwarzo kake zakin dawa, kaine fasa taro tarwatsa runduna, komai yawan runduna indai kaizo kai zaka zama Gwarzo.
Da shigar su sarki Lafaru sai sadauki Haiman ya mike cike da farin ciki ya ruga wajen boka Muzafar suka rungume juna sannan ya kama hannunsa ya kaine har kan karagarsa suka zauna.
Nan da nan kuyangi suka kawo wa Sarki Lafaru abinci da abin sha iri-iri na alfarma suka kimtsa cikinsu. A wannan lokaci duk bayan dakika biyu sai gimbiya rahila da Sarki Lafaru sunyi satar kallon Lumaira matar Sadauki Haiman saboda mamakin tsananin irin kyawunta. Koda satki Lafaru ya kwatanta kyawun sharlis dana Lumaira sai yaga kamar baki da fari ya hada wato Lumaira ta yi wa sharlis fintin kau, nan fa Sarki Lafaru ya shiga zancen zuci yana mai cewa Yanzu n bbanda rashin godiya irin na Sadauki Haiman akan me zai damu dole sai ya nemo wa Lumaira maganin wannan ciwo na makanta tata, dubi irin daular da yake ciki, sannan duk da cewa makauniya ce tafi masu idanun kyau gami da ban sha'awa, gata bulbul kamar tsada, ya za a yi ina matsayinta na yarda har wani abu ya dinga sosa mani zuciya a wannan duniya.
Ita gimbiya Rahila irin wannan tunani sak ta yi a cikin Zuciyarta, tamkar sun hada baki ita da sarki Lafaru.
Bayan anci abinci an gyatsene sai Sadauki Haiman ya dubi boka Muzafar ya ce Mene ne abin yi?
Boka Muzafar ya ce ku muke jira kugama shiri mu cigaba da tafiya, da jin haka sai Sadauki Haiman yayi murmushi ya ce Ai mu yau kwananmu ashirin da gama shiryawa, daman ku kawai muke jira ku iso.
Gama fadin hakan keda wuya sai Haiman ya mike tsaye ya kama hannun Lumaira wacce ke zaune daf da shi ya tasheta tsaye suk nufi hanyar fita. Cikin hanzari kuyangi suka debo wasu jakunkuna guda biyu na guziri suka bisu a baya.
Sarki Lafaru, Gimbiya Rahila da boka Muzafar basu tsaya bata lokaci ba suma suka bi bayansu, gabadayansu suka dunguma izuwa inda suka bar aljani Marhabul Zaurus suka hau kansa suka zazzauna, amman sai gasji kamar bai dauki komai ba saboda fadin gadin bayansa da kuma girman halittar jikinsa.
Nan take boka Muzafar ya dubi aljani Marhabul Zaurus ya ce maza ka kaimu gidan jaruma Shadira ta birnin Baitul Haiward, kafin boka Muzafar ya gama rufe bakinsa tuni aljani Marhabul Zaurus ya bude fuka-fukansa ya luluka sama. Tafiyar sa'a uku kacal yayi ya iso birnin Baitul Haiward ya sauka a kofar gidan jaruma Shadira. Cikin hanzari suma suka sakko daga aljani Marhabul Zaurus,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login