Showing 33001 words to 36000 words out of 59226 words

Chapter 12 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt

matukar mamaki bisa ganin halayyar sarki ta sauya a lokaci guda.Kai bama mutanen birninba hatta sarakunan sauran kasashe dake makwabtaka dashi.Dama dukkan sarakunan suna tsananin tsoron sarki lafaru suna biyayyar dole agareshi domin duk shekara sai kowannensu yakawo haraji maiyawa gami da bayi. Lokacin da'aka sami shekara ukku da samun sauyin al'amura ga sarki lafaru sai wani sarki da ake kira Nurbas wanda ke mulkin kasar zaruf yakawo haraji da bayi.
Dama can shi sarki nurbas gawurtaccen matsafine mai taurin kai kuma yanada zakwakuran mayaka ababan dogaro.A lokacin da sarki lafaru ya aika masa da sakon ya aiko da haraji sai yayi taurin kai ya bijirewa umurnin.Nan take sarki lafaru yayi shirin yaki shi kadai ya shiga birnin zaruf ya rinka ragargazar dakaru har sai da ya shiga cikin fadar sarki Nurbas aka rasa wanda zai iya kawar dashi.Koda sarki Nurbas yaga karfin tsafinsa yaki yayi tasiri akan sarki lafaru kuma ya tabbata kasheshi zaiyi ya mallake kasarsa sai ya fadi kasa yana kuka da tuba yayi ta neman gafara,kuma yayi alkawarin cewa duk shekara zai rinka bayar da harajinsa da bayi sama dana kowanne sarki.Koda ganin yadda sarki Nurbas ya wulakanta agaban fadawansa da jama'arsa kuma ya mika wuya sai sarki lafaru yafasa kasheshi ya bushe da dariya yafice daga cikin fadar yatafi abunsa.SARKI Lafaru na zaune a fadarsa,fadawa sun kewayeshi ana tafiyar da harkokin mulki sai ga manzo daga kasar zaruf dauke da wasika.Da zuwan manzon sai ya zube kasa ya kwashi gaisuwa cikin alamun tsoro duk jikinsa na karkarwa ya mikawa magatakarda wasikar shikuma ya warware wasikar yafara karantata a fili kamar haka; Takarda daga sarki mai cikakken iko wanda a halin yanzu ya sami yancinsa Sarki Nurbas na birnin zaruf. Zuwa ga makaskancin sarki wanda a halin yanzu yazama akuya ba kuraba..."Koda magatakarda yazo nan a karatun wasikar sai muryarsa ta sarke kuma hannunsa yakama karkarwa saboda tsoron kada sarki ya huce haushi akansa bisa abinda yakaranto na kaskanci.Lokacin da sarki lafaru yaji irin wannan cin mutunci da sarki Nurbas yayi masa a wasika sai ya kamu da tsananin takaici yaji kamar zuciyarsa zata faso kirjinsa ta fado kasa,yatuna irin tsananin tsoronsa da sarki Nurbas keji ada ,amma yanzu shine harda zaginsa cikin wasika.Cikin karfin hali da barazana sarki lafaru ya dakawa magatakarda tsawa yace maza kaci gaba da karanta wannan wasika muji karshenta nan take magatakarda yaci gaba da karatun wasika muryasa na rawa kamar haka;Yakai sarki lafaru mai birnin kufa kayi sani cewa a halin yanzu tsirara nake kallonka babu sutura a jikinka,dalili kuwa kayi sake har sharlis 'yar boka Narwas ta karya alkadarinka.Nasan cewa kamanta da kowanene boka Narwas to kayi saurare dakyau yanzu zan tunamaka shi domin kasan cewa tsohon abokin gabarkane wanda ya mutu da bakin cikin daka turamasa amma kuma sai gashi 'yarsa sharlis zata dauki fansa akanka.
Nan take magatakarda yaci
gaba da karatun wasika muryasa na rawa kamar
haka;Yakai sarki lafaru mai birnin kufa kayi sani
cewa a halin yanzu tsirara nake kallonka babu
sutura a jikinka,dalili kuwa kayi sake har sharlis
'yar boka Narwas ta karya alkadarinka.Nasan
cewa kamanta da kowanene boka Narwas to
kayi saurare dakyau yanzu zan tunamaka shi
domin kasan cewa tsohon abokin gabarkane
wanda ya mutu da bakin cikin daka turamasa
amma kuma sai gashi 'yarsa sharlis zata dauki
fansa akanka.yakai wannan sarki kayi tunani
izuwa kimanin shekaru ashirin baya,a shekarar
daka hau mulki bayan mutuwar mahaifinka sarki
Hurdas. bayan an nada Sarki
lafaru a matsayin sabon sarki,akwai wata rana
da ya tafi rangadi izuwa kauyukan kasarsa har
tsawon kwana arba'in yana kewaye kauyukan
kamar yadda kowane sabon sarki keyi idan ya
hau karaga bisa al'ada.Kauyen daya ziyarta na
karshe shine kauyen Bairul. Da isarsa kauyen
sai ya umurci dukkan attajiran garin dasukawo
masa gaba dayan dukiyarsu.gaba dayansu sai
suka cika umurnin face mutum daya wani
takadarin boka mai suna Narwas wanda kowa
ke shakkarsa a garin.Boka Narwas bai amsa
kiransa ba kawai sai yayi zamansa a gidansa
kuma ya aiko gidan hakimin yace a gaya masa
cewa bazai amsa kiransaba kuma bazai bada
komai ba daga cikin dukiyarsa,koda yaji wannan
batu sai ya harzuka yasa akayi masa jagora
zuwa gidan boka Narwas Da zuwansa ya iske
boka Narwas a kofar gidansa yarike kugu yana
jiransa domin yasan cewa lallai yana
tafe,saboda boka narwas ya yarda da kansa a
fagen tsafishiyasa yake ganin bazaka iyayi masa
komai ba kuma a tunaninsa zai iya hallaka sarki
lafaru farat daya. Da zuwan sarki lafaru sai boka
narwas yafara watsa masa wutar tsafi,bisa
mamaki sai yaga gashi dai wutar ta zuba jikinshi
amma sai takasa konashi.Cikin fusata yaci gaba
da watsa masa abubuwan sihiri kamar
kibiyoyi,macizai da kunamaiamma duk sai suka
ki yin tasiri akansa.Nan take sarki lafaru ya
shako wuyansa da hannu daya ya dagashi
samasai gashi yana kakarin mutuwa idanunsa
sukayi kulu-kulu kamar zasu fado kasa
kafafunsa na wutsil-wutsil a sama,kawai sai ya
fyadashi da kasa ya baje wanwar a sume.Kafin
boka narwas ya farfado daga dogon suman
dayayi sai yasa aka shiga gidansa aka kamo
iyayen boka narwas da matarsa gami da wata
kanwarsa kyakkyawar gaske mai suna lasirat
dakuma 'ya'yansa guda ukku kananan yara biyu
mace daya.A wannan lokaci matar narwas tana
dauke da tsohon ciki haihuwa ya kogobe,amma
saboda wulakanci a kasa dakarunsa suka rika
janta suna fincikarta tana ihu tamkar suna jan
mushe Bayan anzo da
iyalan boka Narwas gaban sarki lafaru sai yasa
aka daddauresu a jikin dirkar gini,shikuwa boka
Narwas yasa aka dagashi sama aka daureshi
sannan aka watsa masa ruwa ya farfado.Koda
Narwas yabude idonsa yatsinci kansa daure
ajikin dirka kuma yaga dukkan iyalansa da
iyayensa a daure sai hankalinsa ya dugunzuma
yakurma uban ihu yafara kokarin kwance daurin
da akayi masa da karfin tsafi amma sai tsafin
yaki yayi tasiri.Koda ganin haka sai sarki lafaru
ya bushe da dariyar mugunta sannan ya
murtuke fuskarsa kamar an aiko masa da sakon
mutuwa yakama gashin kan narwas ya finciko
baya da karfi,yayi ihu sakamakon zafin
dayaji,kawai sai ya tofamasa yawu a fuska
yabude baki cikin kakkausar murya yace.;Ya kai
wannan makaskancin boka kayi sani cewa kayi
babban kuskure har da kake zaton zaka iya
bijire mini.Yanzu kayi laifi har guda biyu.Na
farko ka karya dokar kasata kayi tsafi wanda
hukuncinsa kisa ne akanka.Na biyu nabaka
umurnin ka kai min dukiyarka kaki kaiwa.Ka sani
cewa kaine mutum na farko daya kawo raini a
cikin mulkina kuma yakarya dokata saboda haka
bazan kasheka ba sai dai na nuna misali akanka
domin ka zamo darasi akan masu sha'awar
jaraba taurin kai a garemu.Lallai zan dandana
maka azaba irin wacce ba'a taba dandanawa
wani ba kuma zan cusa maka bakin ciki a
zUciyarka wanda har karshen rayuwarka bazaka
sami natsuwa da kwanciyar hankali ba".Koda
gama fadin haka sai sarki lafaru ya zaro wata
sharrbebiyar wuka daga kugunsa sannan yayiwa
mahaifin boka Narwas da mahaifiyarsa kisan
wulakanci ta hanyar yanke makogoransu yanka
daya a lokaci guda.Take jini yai tsartuwa daga
wuyansu ya wanke fuskar boka Narwas.Narwas
ya tsandara ihu kuma ya fashe da matsanaicin
kuka.Yana cikin wannan bakin cikine sarki
lafaru yakamo wadannan 'ya'ya nasa guda
uku,wato kananan yara ya take wuyansu da
kafafunsa daya bayan daya suna ihu yayi musu
yankan rago.Gaba daya mutanen dake wurin sai
da suka zubar da hawaye do tausayi.Shi kuwa sarki lafaru ko ajikinsa wai an mintsini
kakkausa. Yayin da boka
narwas yaga irin kisan wulakancin da yayiwa
'ya'yansa,sai nan take ya haukace yakama
sambatu.Hakan baisa sarki lafaru ya hakura
ba,sai ya kamo wannan kanwa tasa kyakkyawar
budurwa,wato lasirat ya maketa ta fadi kasa
sumammiya.A gaban jama'a ya murkusheta ya
biya bukatarsa da ita,sannan itama yayi mata
yankan rago.Tun sa'adda matar Narwas taga
yanda sarki lafaru ya kashe 'ya'yanta ukku sai ta
sulale kasa sumammiya bata farfado ba sai
bayan yakashe lasirat.Ai kuwa tana bude ido
tayi arba da gawar lasirat a gabanta sai ta kwala
ihu.Nan take nakuda tazonata.kawai sai sarki
lafaru ya kura mata ido yana ta kyalkyala dariyar
mugunta kuma yahana kowa ya taimaka
mata.Sai da ta shafe sa'a biyu tana nakuda
sannan ta haifo tsaleliyar 'ya mace a gaban kowa.Da kanta ta yanke cibi ta goge jinin jikin Jaririyar.Jaririyar ta kama tsala kuka har ta
yunkura zata baiwa jaririyar nono sai sarki lafaru
ya kwace jaririyar daga hannunta ya cillata cikin wata katuwar kwata wacce ke cike da ruwa.Nan
take jaririyar ta nutse izuwa can kasan kwatar
kuma gashi ruwan kwatar mahada ne na kogin
garin.Koda matar Narwas taga ya jefa 'yarta
cikin wannan kwata sai ta sulale kasa
sumammiya.Da ganin haka sai sarki lafaru yasa
aka dinga yiwa boka Narwas azaba iri-iri har sai
da ya suma sau bakwai sannan aka
kyaleshi.Nan take sarki lafaru yasa aka yashe
komai na gidansa ba'abar masa ko tsinke ba har dabbobisa sai da aka kwashesu daga cikin garke,gonakinsa kuwa yasa aka konesu sannan
aka gine wajen aka rufe ba shiga ba fita.A
sannanne sarki lafaru ya hau dokinsa yai
tafiyarsa izuwa birninsa na kufa.Yakai wannan
sarki,tun daga wannan lokaci baka sake tambayar labarin boka Narwas ba. Babban kuskuren da kayi shine barin Narwas a raye.

Bayan wata ukku da haukacewar boka narwas wani dan uwansa yazo daga wata kasa dabam yayi masa magani ya warke daga cutar
hauka.Wannan 'ya tasa jaririya da aka jefa cikin kwata bata mutuba.Ruwa yataso da ita
sama. wani masunci ya tsinceta ya reneta har izuwa tsawon shekara bakwai a wannan lokaci tuni Narwas ya kara samun ilmin tsafi ninkin wanda yake dashi a da sau dubu kuma yayi bincike yagano 'ya tasa da aka jefa cikin kwata bata mutu ba tana hannun wannan masunci don haka sai yaje ya karbo 'yarsa yaci gaba da renonta kuma ya bata dukkanin sihirin tsafinsa ya horar da ita bisa tafarkin dazata dauki fansa akanka.Ba wata bace wannan 'ya tasa face SHARLIS Budurwar dakayiwa fyade bayan dakarunka sun kashe mahaifinta da mahaifiyarta sun kawota fadarka.Dama boka Narwas yagayawa sharlis cewa alkadarinka bazai taba karyewaba sai a ranar dakayi mata fyade daga wannan rana sadaukantakar ka zata gushe kuma tsafi zai dinga tasiri a jikinka sakamakon sihirin dake cikin jikinta yafi naka.Nasan zakayi mamaki bisa yadda akayi duk nasan wannan al'amari,amma idan kayi la'akari da cewa nima tsohon bokane mai nacin bincike da yawan neman karin ilmi bazakayi mamaki ba.Yakai wannan sarki kayi shiri domin gani nan tafe izuwa kasarka nan da cikar kwana arba'in.Lallai idan nazo sai na kwace duk dukiyar daka mallaka abakacin harajin danayi ta baka a baya bisa dole kuma sai na kaskantar dakai kazama bawa mai kula da turken dokina.Bazan kasheka ba sai dai ka jira ranar da sharlis zata dauki fansa a kanka bisa abinda kayiwa mahaifinta.Ina yi maka albishir da cewa a halin yanzu sharlis na tare da danka data haifa dan shekara ukku kuma tasa masa suna shaddad.Nasani cewa tunda kasa aka kai sharlis bangarenta a cikin gidan sarautarka baka taba ziyartarta ba kuma baku sake ganin juna ba.Lallai abinda kake gudun ya faru sai ya faru,wato sai ka haifi dan da zai gajeka kuma sai ya fika shuhura a duniya kuma shine zai zamo babban makiyinka wanda zai dauki fansar abinda kayiwa kakansa.Lokacinda magatakarda yazo nan a karatun wasikarsa sai kawai aka ga sarki lafaru ya bushe da mahaukaciyar dariya.Cikin shammace ya zare takobinsa ya sare kan wannan manzo da ya kawo wasikar
Nan take sarki lafaru yasa aka rubuta wasikar raddi,a cikin wasikar ya karyata duk abinda sarki nurbas yayi bayani cewar har yanzu alkadarinsa bai karye ba,sadaukantakarsa na nan kuma yana jiran isowarsa su gwabza yaki domin a bambance tsakaninsu a gane wanda yake karya.Da aka gama rubuta wannan wasika sai aka hadata tare da gawar manzon daya kawo wasikar farko a cikin akwati aka tafi dasu izuwa birnin zaruf.Sa'adda fadawan sarki lafaru da sauran jama'ar gari suka ji hukuncin da sarki lafaru ya yanke akan bayanin da wasikar sarki Nurbas yayi saisuka shiga wasi-wasi.Wasu suka fara tunanin cewa har yanzu alkadarin sarki lafaru bai karyeba duk da cewa yanzu ana yin tsafi kasarsa kuma yana yin rashin lafiya sabanin da.Dalilinsu na yarda da hakan shine inda sarki lafaru yasan duk abinda sarki Nurbas yayi bayani gaskiyane.To da ba zai taba yarda ya mai da masa da wasikar raddiba. Abinda basu sani ba shine,sarki lafaru kundunbala kawai yayi,saboda taurin zuciya da ki fadi ne irin nasa yaki yarda ya nuna gazawarsa domin kada talakkawansasu sami damar da zasu ci mutuncinsa su wulakantashi bisa mulkin zalincin da ya yi musu.Amma a zahiri yaji a jikinsa cewa duk irin jarumtakar da yake da ita a da yanzu bashi da kaso biyu cikin kaso darinta.Lokacinda fada ta watse sai mutanen gari suka tafi suna fadin albarkacin bakinsu bisa abinda ya faru a fada dangane da wasikar sarki Nurbas ya aiko da ita da kuma wasikar raddi wacce sarki lafaru ya aika masa da ita. Wannan abu daya faru sai ya jefa shakku a zuciyar dakarun yaki na kasar ya zamana cewa basuda tabbacin cewa zasu sami nasara idan akayi wannan yaki da birnin zaruf,kuma basu da tabbacin bazasu samu nasararba.Dole ne su zuba ido kawai su jira ranar daza ayi wannan yaki sugani idan har yanzu jarumtakar sarkinsu na nan tunda shine abin dogaronsu.Al'amarin sarki lafaru kuwa,bayan fada ta watse sai ya shiga cikin turakarsa ya zauna yayi tagumi cikin tsananin bakin ciki,yana tunani da mamaki bisa yanda al'amura suka sauya masa.

Al 'amarin sarki Laffaru kuwa,bayan fada ta watse sai yashiga cikin turakarsa yazauna yayi tagumi cikin tsananin bakin ciki,tunani da mamaki bisa yadda al 'amurra suka sauya masa a cikin shekaru ukku kacal.Nan take ya tuno da irin tsananin jarumtakarsa ta yanda shi kadai yana iya yakar gari guda ya cisu da yaki,ya tuno da irin yadda gaba dayan sarakunan dake kasashen da suke makwabtaka suke tsananin tsoronsa tare da yin biyayya a gareshi amma gashi yau an wayi gari an sami daya daga cikinsu yana aiko masa da zagi dakuma gadarar ayi yaki.Nan take hawayen takaici ya zubo masa.Sarki Lafaru yaci gaba da tunani bisa makasudin faruwar wadannan al 'amurra wato haduwarsa da sharlis.Nan take bayanin wasikar sarki Nurbas yasake fado masa a rai cewar a halin yanzu Sharlis ta haifae danta kuma 'dan shekara uku a duniya sannan zai zamo abokin gabarsa ya dauki fansar abinda yayiwa kakansa.Sarki Lafaru bai san sanda zancensa na zuci ba ya fito fili ba ya ce, "Ya za a yi 'dan cikina yazamo abokin gabata?Lallai idan nabari wannan yaro yagirma nagama tozarta a duniya.Yanzu ya za a yi na salwantar da rayuwar sharlis da wannan yaro data haifa kuma ya za ayi nayi mugun tanadi bisa wannan yaki dazamuyi da sarki Nurbas nan da kwana arba 'in na sami nasara akansa don natsare mutuncina da darajata a idanun jama'ata da sauran sarakunan kasashen makwaftaka? " Lokacin da sarki Lafaru yazo nan a tunaninsa sai hankalinsa ya dugunzuma fiye da komai ya tabbatar da cewa yana cikin TSAKA MAI WUYA domin GABANSA TSINI NE,BAYA SIYAKI.Yanzu dai gashi yana zaune da abokiyar gabarsa cikin gidansa kuma babu yadda zai yi da ita.Abu na biyu kuma yana cikin barazanar sarki Nurbas wacce idan har bai sami mafita ba nan da kwana arba 'in zai rasa dukiyarsa,mulkinsa da darajarsa a duniya gaba daya.A iya rayuwar sarki Lafaru bai taba jin yayi nadama ba bisa irin rashin imanin dayake ma mutane ba da mulkin zaluncinsa sai a wannan karon saboda da inda bai ci zarafin boka Narwas ba da duk wannan sauyin al 'amurran na rayuwarsa bazasu faruba.Haka dai sarki Lafaru yaci gaba da kukan takaici gami da tunani yakasa zaune ko tsaye cikin tsananin fargaba da tashin hankali har dare ya raba sosai yakasa barci.Yana cikin wannan hali ne wata dabara ta fado masa ya ce da kansa, "Ai masu iya magana sunce ta inda aka hau tanan ake sauka.Me zai hana naje wajen Sharlis na yaudareta ta hanyar neman gafararta bisa abinda nayiwa mahaifinta kuma na bata dukkanin abinda take bukata na daga dukiya domin ta taimaka mini na samu nasarar yaki akan sarki Nurbas inyaso nima daga baya sai nashiga neman ilmin tsafi a sirrance kafin dana ya girma nasami sihirin dazan iya ganin bayansa shi da mahaifiyarsa ".Koda gama aiyana hakan sai sarki Lafaru ya fice daga cikin turakarsa ya nufi bangaren da Sharlis take a cikin gidan sarautar a wannan tsohon dare.Da isar sarki Lafaru gidan da Sharlis take sai ya iske kofar gidan a bude wanwar kuma gaba dayan dakarun dake gadin gidan a kwance suke suna ta shara barci,al 'amarin da ya matukar bashi mamaki kenan.Nan take zuciyarsa ta buga da karfi yaji tsoro ya darsu a ransa amman sai yai ta maza ya kunna kai izuwa cikin gidan ya wuce kai tsaye izuwa wani babban falo,da shigarsa cikin falon sai ya iske gaba daya tagogin falon guda goma sha biyu a bude suke kuma babu kowa a cikin falon har kuyangin dake yiwa Sharlis hidima kuwa.Sarki Lafaru yaci gaba da lekawa cikin sauran dakunan gidan guda bakwai amma duk inda ya leka sai yaga wayam babu mutum a ciki sai kayan sai kayan alatu kawai da aka tanada a ciki.Cikin matukar damuwa da sakar zuci ya dawo cikin gidan in yaso ya bayar da cigiyar Sharlis a tafi nemanta a cikin gidan sarautar.Wata zuciyar tace dashi anya kuwa Sharlis ba ta yi hijira ba daga gidan gaba daya?Ai tunda yanzu tana da karfin sihirin tsafi babu abinda bazata iya yi ba. Gama aiyana hakan keda wuya sai yaji wata irin iska mai karfi ta taso irin wacce ke tsorata mutane sannan iskar takulle tagogin falon gaba daya sannan fitilun dake kunne a cikin falon suka mutu,wani irin duhu yamamaye idanun sarki Lafaru tayanda ko tafin hannunsa baya iya gani kuma har a sannan iskar naci gaba da kadawa,daga can kuma sai yaji an bushe da wata mahaukaciyar dariya.Duk da cewa sarki Lafaru yagane muryar dake dariyar hakan bai hana yaji zuciyarsa ta buga da karfin gaske a karon farko a rayuwarsa yaji tsoro ya shigeshi.Daga can sai dariyar ta dauke iskar dake kadawa ta tsaya cak sannan haske ya mamaye falon.Sarki Lafaru yayi arba da Sharlis cikin shigar fararen kaya zaune akan wata karagar mulki,sarki Lafaru ya daka mata tsawa ya ce menene na son ki tsoratar dani?Sharlis ta bushe da dariya sannan tace ina so na nuna maka nafi karfinka ta ko ina baka da wata dabara dazaka iya tsallake sharrina.Kada ka yaudari kanka yakai wannan sarki domin tuni alkadarinka ya karye kuma har abada jarumtakarka bazata taba dawowa ba.Na sani cewa sarki Nurbas ya tunamaka da kisan wulakancin dakayiwa kakannina kuma kaso ka hallakani tun ina jaririya amma dayake ina da nisan kwana a duniya sai da na rayu.Yanzu gashi lokaci yayi dazan dauki fansa a kanka to ka sani cewa ramuwar gayya tafi ta gayya ciwo.Sharlis taci gaba da cewa da sannu zan dauki wannan fansa a kanka yadda zaka dandana azababbiyar wahala irin wacce waninka bai taba sha ba,sannan ka dandana dacin bakin ciki marar tukewa.A karshe ni da dana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login