Showing 15001 words to 18000 words out of 59226 words
Chapter 6 - MAZAN JIYA Littafi Na Biyu Rubuta Labari Abdulaziz Sani Madakin Gini.txt
da kallo cikin murmushi kawai.
(Hallau dai kuna tare da Shuraih 99%)
Bayan sarki da Larziya sun shige cikin gida sai fadar ta watse kowa ya kama gabansa. Saboda tsananin ?oki da murna Hantaru bai yi barci ba a wannan dare, a yadda ya ga rana haka ya ga dare, wato dai ya jera kwana biyu ke nan bai yi barci ba.
Da gari ya waye, tun da sassafe zuri'ar Shurem suka cika gari da kade-kade da bushe- bushe gami da raye-raye suka yi ta walima a gida- gida, unguwa-unguwa, ya zamana cewa Ana a bushasha da abinci da abin sha iri-iri a ko ina cikin birnin Darul Dulshul bisa samun nasarar ?auko takobin Saiful Lujara.
Haka dai aka ci gaba da wannan shagalin biki har izuwa yammaci. Bangaren zuri'arsu Rabbasu kuwa banda kuka da bakin ciki babu abin da suke yi, domin sun yi asarar abubuwa uku.
Abu na farko da suka rasa shi ne, shugabansu wato mahaifin Rabbasu sannan sun rabu da kambun gasa wanda ke hannunsu tsawon shekara da shekaru. Abu na na uku shi ne, magajin shugabansu wato sadauki Rabbasu jarumin da babu kamarsa a gaba daya nahiyar. La'asar nayi sai fada ta sake cika ta batse jda ama'a fiye da taron da aka yi na safe, wannan karon ma gaba daya birnin ne ya cika da baki daga sauran makotan birane saboda jin cewa za a daura auren gimbiya Larziya da jarumin da yaje har kogon Mazubatul Dulshul ya dauko takobin Saiful Lujara.
Tun ana baiwa baki masauki har sai da takai cewa an daina basu domin babu. A wannan rana mutanen birnin Darul Habul sun yi matukar al'ajabi domin basu taba ganin cikowar jama'a ba a garinsu irin haka. Abin da basu sani ba shi ne, fiye da kaso saba in na cinkoson jama'ar ba mutane bane aljanu ne daga sassa na duniya suka zo a cikin siffar mutane domin kawai su ga jarumi Hantaru sadaukin da ya yi gagarumar bajintar da ta gagari dukkanin sadaukan duniya tsawon shekaru dubu uku da suka gabata.
Zan ci gaba.
Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp.
MAZAN JIYA
Littafi na biyu 2
Part F
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
Ba tare da 6ata lokaci ba aka daura auren sadauki Hantaru da gimbiya Larziya a gaban miliyoyin jama'a kuma aka ?ankawa Hantaru kambun gasa ya ?aurashi a hannunsa, ai kuwa fadar gaba daya ta rude da shewa gami da tafi har kowa yaji kamar kunnensa zai dode.
Nan dai aka cigaba da shagalin biki aka yi ta watsa dukiya gA maroka da mabukata. Abinci kuwa sai da ya zamo ga shinan kamar shara aka rinka yin bolarsu tsibi-tsibi saboda an rasa yadda za a yi dashi.
Kowa a garin sai da ya cika da mamakin irin wadatar da aka samu a wannan rana domin abin yafi karfin iyakar bajintar Sarki, kai da gani ka san cewa akwai sa hannun aljanu. Haka dai aka ci gaba da shagalin biki amma har dare ya soma ango bai ga amaryarsa ba domin tunda aka ?aura aurensa da ita sai aka shigar da ita cikin gidan sarauta aka killaceta a cikin turakarta aka yi ta tsala ma ta ado iri-irk, idan a ka yi wannan sai a ga bai yi ba a sake yin wani har sai da aka yi kala saba'in.
A na saba'in ne matan da ke yin adon suka gamsu gaba ?ayansu cewar ya yi. A wannan lokaci dare ya fara tsalawa don haka sai aka dauki amarya cikin hanzari aka kai ta gidan su Ango. Bayan masu kak amarya sun watse sai ango ya shigo ?akin amaryarsa yana sanye da tufafi masu tsadar gaske na alhariri.
Da shigar Hantaru cikin dakin sai ya iske amaryarsa zaune a gefen gado ta sha lullu6i fuskarta a rufe.
Cikin matukar farin ciki ya karasa gareta fuskarsa cike da murmushi ya kasa rufe baki. Hantaru ya zAuna daf da Amaryarsa sannan yasa hannayensa biyu ya yaye labulen da tayi.
Koda ya yi arba da fuskarta sai hankalinsa ya dugunzuma ainun, ya dubeta cikin tsananin mamaki ya ce, "Ya ke masoyiyata abar begena dare da rana ina dalilin zubar Wannan hawaye na idanunki? Ki sani cewa yau rana ce ta farin ciki ba ta bakin ciki ba. Ina son ki gaya mini abin da ke damunki ko mene ne shi in dai ina da ikon kau da shi, sai na kawar da shi."
Sa'adda gimbiya Larziya taji wannan batu sai tayi ajiyar zuciya tayi shiru kamar ba za ta ce komai ba, daga can sai ta daga kai ta dubi Hantaru ta ce, "Ya kai mijina hakika baka san komai na ba domin baka san labarina ba kawai ka zo garin nan ne a matsayin bako kana ganina ka kamu da kaunata. Ina son na sanar da kai cewa ina cikin wani bakin ciki tsawon shekaru wanda duk duniyar nan babu wanda zai iya kawar mini da shi face kai.
Ka saurari labarin da zan baka yanzu da kunnen basira domin ka fahimci matsalar da kuma babban burin da ke gabana." Sa'adda Larziya ta zo nan a zancenta sai tayi shiru gami da ajiyar zuciya sanann ta ci gaba da labari Kamar haka
"Mahaifina bai taba yin soyayya ba da wata ya mace har ya hau karagar mulkin wannan birni na Darul Mahabul kuma sai da ya shekara hudu akan karaga bai yi aure ba. Al'amarin da ya dami fadawansa kenan da sauran al'umman gari ke nan suka dameshi akan batun lallai ya kamata ya yi aure domin ya tsare mutuncinsa da masarautar gaba ?aya.
Lokacin da mahaifina ya ga jama'a sun matsa ainun akan wannan batu sai ya tara dukkan jama'ar gari ya ce, "Idan har ana son ya yi aure dole ne ayi abu biyu. Abu na farko dole ne a samo masa kyakkyawar budurwa wacce babu kamarta a gaba daya nahiyar kuma dole ne a shirya gagarumar gasa irin wacce ko a tarihi ba a taba yin kamarta ba". Sa'adda sarki ya gama jawabi sai hankalin kowa ya dugunzuma aka rasa wanda zai ce kala.
Daga can sai Wazirin sarki ya mike tsaye ya dubi sarki ya ce, "Ya shugabana hakika ka zo mana da baban al'amari wanda ba zamu iya saurin yanke hukunci ba face ka bamu lokaci mu yi tunanin mafita.
Dole ne mu nemi manyan bokayen kasar nan domin su yi mana bincike bisa wannan al'amari".
Koda jin haka sai sarki ya yi murmushi sannan ya ce, "Ya kai waziri na baka wuka da nama akan kaje ka zartar da komai amma ka sani cewa kwana goma sha hudu kacal na baka". Koda gama fadin haka sai sarki ya mike tsaye ya shiga cikin gida, a sannan ne fadar ta watse kowa ya kama gabansa.
Al'amarin Waziri kuwa, bayan ya bar fada sai ya kira wadansu
manyan hadimansa amintattu guda hudu ya basu wasika suka
yi hawa izuwa manyan garuruWan birnin guda hudu akan su je
su gaiyato manyan bokayen da ake takama da su.
Su kuwa bokayen da ake takama da su a cikin birnin Darul
Mahabul guda biyu ne kawai wato boka Sulbaini da mahaifin
Rabbasu suma sai WAZiri ya kirasu ya sanar da su cewa, "Ya
tura a kirawo sauran bokaye kasar guda hudu domin a ZAuna
gaba daya a tattauna akan matsalar sarki.
Koda jin haka sai Sulbaini da baban Rabbasu suka yi murmushi,
Sulbaini ya ce, "Ya kai waziri ai ka wahalar da kanka ne kawai
domin mu kadai mun isa mu fadi hanyar da ZA a bi a warware
matsalar sarki, to amma masu iya magana sun ce ba a
kwacewa yaro garma kuma dan hakin da ka raina shi ke tsone
maka ido. Babu mamaki wani daga cikin wadannan bokaye
yazo da wani abin wanda yafi namu don haka zamu jira isowar
sauran bokayen hudu"
Sa'adda waziri yaji wannan batu sai yai murmushi sannan yayi
godiya ga su boka Sulbaini ya sallamesu. Bayan kwana tara
daidai sai ga wadannan bokaye sun amsa kiran Sarki.
Da zuwan su sai waziri ya tara su a cikin gidansa tare da su
boka Sulbaini sannan ya yi bayanin abin da yasa aka tara su
kuma aka bukaci kowannensu ya fadi tasa shawarar.
Daya bayan daya sai bokayen suka rinka nuna hoton budurwar
da sarki ya kamata ya aura da inda take da kuma irin gasar da
ya kamata ayi ta neman aurenta, a cikin madubin tsafi. Ya yin da
bokan farko ya nuna tasa sai waziri ya kidime domin gani yake
kamar a duniya ma kaf ba za a sami kamar ta ba, amma da
boka na biyu ya nuna tasa sai ya ta fi ta waccan nesa ba kusa
ba.
Haka abin ya kasance bi da bi ta biyu ta fi ta farko, ta uku ta fi ta
biyu, kuma ta hudu ta fi ta uku. Lokacin da aka zo kan baban
Rabbasu sai ya nuna wata kyakkyawar budurwa wacce ?uk ta fi
sauran kyau ya ce, "Wannan sunanta Zarifa kuma yar wani
babban attajiri ce a birnin Kisra, tabbas a gaba dayan wannan
nahiya babu mai kyau kamarta a can birnin Kisran ma tana da
masoya da yawa 'ya'yan sarakai da 'ya'yan manyan sarakai da
ya'yan manyan attajirai da kuma 'ya 'yan manyan bokaye.
A halin yanzu an rasa wanda za a baiwa ita daga cikin masoyan
nata, amma komai na hannun sarkin Kisra, shi ake jira kawai ya
yanke hukuncin akan ta. ldan har sarki ya sami nasarar auro
Zarifa za a shirya gasar Jarumtama ta musamman a tsakanin
manyan mayaka domin Su debewa jamaa kewa a lokacin da
ake shagalin bikinsa.
Lokacin da waziri ya ga Zarifa a cikin madubin tsafin Baban
Rabbasu kuma ya gama sauraron jawabin Baban Rabbasu sai
ya ude, kuma ya cika da tsananin al'ajabi ya ce, "Na rantsed
darajar iyayena babu wata nahiya da za aje a SAmi kyakkawar
mace kamar wannan Zarifan, don haka lallai zan kaiwa sarki
labarinta domin ya shirya da kansa yaje ya nemi aurenta a can
birnin na Kisra. Koda jin haka sai boka Sulbaini ya bushe da
dariya, al'amarin da ya matukar baiwa kowa mamaki ke nan a
wajen, aka yi tsit ana kallonsa kawai. Daga can sai boka
Sulbaini ya tsuke bakinsa ya murtuke fuska sannan ya nutsu ya
dubi kowa daya bayan daya ya ce,
"Akwai wata budurwar wacce idan ba ta fi Zarifa kyau ba sai dai
su yi kunnen doki sunanta Mafira, kuma 'yar uwar Zarifa ce uwa
daya uba daya suke, wato Hassana da Hussaina ne amma ita
Mafiran tun da aka haife ta bata taba fita ba daga cikin gidansu
domin dare da rana babu abin da take so face ta Zauna a cikin
lambun gidansu tana kallon tsuntsaye da kananan dabbobin
daji. Idan ka ga ta fita daga cikin wannan lambu sai idan lokacin
barcinta ya yi" Koda Sulbaini ya zo nan a ZAncensa sai ya fiddo
madubin tsafinsa ya ajiye a gabansu waziri kuma ya shafeshi
da hannun dama. Take fuskar Mafira ta baiyana akan madubin
da kuma dukkan surar jikinta. Koda ganinta sai waziri da sauran
wadannan bokaye hudu suka rude fiye da lokacin da suka ga
Zarifa domin a zahirin gaskiya Mafira ta fi Zarifa tsawo da
yalwal gashi.
Boka Sulbaini ya ci gaba da bayani ya ce, "ldan har sarkinmu ya
sami nasarar auro Mafira za shirya gasar kamo barewa
tsakanin zuri'ar makera da zuriar mafarauta na wannan birni
kamar yadda aka saba yi a kowacce shekara domin a taya sarki
murnar wannan biki nasa.
Da jin wannan batu sai waziri ya sake rudewa ya rasa hukuncin
da zai yanke akan budurwar da sariki ya kamata ya zaba
tsakanin Zarifa da Mafira. Baban Rabbasu ya murtuke fuskarsa
zuciyarsa ta kama tafarfasa saboda kishi da bakin ciki akan
boka Sulbaini ya zo da abin da ya zama kishiyar nasa.
Lokacin da boka Sulbaini ya ga baban Rabbasu na kumbure-
kumbure da bata rai sai shima ya murtuke fuskarsa kamar an
aiko masa da sakon mutuwa, har ma jikinsa ya kama tsuma,
al'amarin da ya firgita waziri ke nan da sauran wadannan
bokaye hudu domin sun san cewa idan wadannan hamshakan
bokaye biyu suka kacame da fada ba karamin bala'i ne zai faru
ba, wata kila ma sai gidan gaba daya ya rushe ko kuma ya kama
da wuta.
Koda waziri ya fahimci haka sai ya mike zumbur ya dubi boka
Sulbaini da Baban Rabbasu ya ce, "Yanzu ina son gobe da safe
ku hallara a fada, domin kowannenku ya nunawa sarki fuskar
budurwar da ya zaba masa in ya so sai sarki ya Zabi wacce ya fi
So da kansa."
Koda jin haka sai boka Sulbaini da boka Zaharu suka mike tsaye
suka tafi ko sallama babu. Kashe gari kuwa da sassafe sai ga
boka Sulbaini da boka Zaharu a fada, sun hallara.
Bayan sun zube kasa gaban sarki sun kwashi gaisuwa sai
waziri ya maida bayani bisa duk abin da ya faru jiya a gidansa
tsakanin sa da su boka Zaharu. Sa'adda Sarki ya ji wanann
bata'u sai ya cika da matukar farin ciki yai shiru yana tunani har
tsawon 'yan dakiku.
Daga can sai ya yi gyaran murya ya ce, "Ya ku wadannan
manyan bokaye na birnina abin takama a gareni, ku yi sani
cewa bana bukatar ku nuna mini fuskokin wadannan yan mata
guda biyu.
Abin da nake so da ku shi ne, ku yi shiri ni da ku da waziri da
kuma wasu tsirararun dakaruna za mu yi tafiya izuwa birnin
Kisra. Ina son kowannenku ya yi amfani da iya karfin sihirinsa
domin na sami nasarar auro budurwar da ya za6a mini.
Duk wanda ya bani sa'ar dana auri Zabinsa lallai zan yi masa
kyauta ta musamman kuma Zan bashi girma na musamman a
cikin masarautata. Ina so ku gane cewa a cikinku bani da gwani
ko abin so sai wanda kokarinsa ya sa na auro budurwar da ya
zaba mini. Da wannan furuci nake sallamarku domin ku je gida
ku yi duk shirin da ya kamata. Lallai i yanzu ZA mu kasance
masu jiranku anan fada".
Koda Sarki ya gama wannan jawabi sai ya mike tsaye ya shiga
cikin gidan. A sannan ne boka Zaharu da boka Sulbaini suka
kalli juna cikin harara a lokacin da idanuwansu suka kada suka
yi jawur kamar an gasa dan buda a wuta.
Daga can sai kowannensu jikinsu ya kama tsuma kamar za su
kaure da fada har wani irin tiririn hayaki ne ke fita daga cikin
kunnuwansu, baminsa da hancinsu. Koda ganin wannan
al'amari sai hankalin gaba ?ayan jama'ar da ke fadar ya
dugunzuma aka fara mimewa ana ficewa da sauri. Shi kuwa
waziri sai yai sauri ya kama hannun boka Sulbaini ya jashi suka
fice daga cikin fadar yana jansa da hira cikin lafazi mai taushi
domin ya sanyaya masa zuciya.
Nan take waziri ya sa aka kawo keken dokinsa suka shiga ciki
tare suka ZAuna sannan aka ja suka tafi. Sai da waziri ya kai
boka Sulbaini har kofar gidansa yana tausar zuciyarsa akan
kada ya daka ta boka Zaharu su yi fada tun da idan suka yi fada
sai sun dagula hankalin kowa a garin kuma sai kwanciyar
hankali da zaman lafiya ya yi karanci. Sa'adda boko Sulbaini ya
ji wannan batu sai ya yi murmushi ya ce, "Ya kai waziri kayi sani
cewa kiyayyar da ke tsakanina da boka Zaharu ta gado ce
domin tasowa muka yi muka ga iyayenmu da kakanninmu na
yinta. Ina tabbatar maka da cewa har abada ba zamu daina
wannan gaba ba face dayanmu ya ga bayan ?aya ko kuma idan
mun yi RAGAS. Bugu da kari ka sani cewa ni daga zuri'ar
Makera na fito shi kuwa daga zuri'ar mafarauta yake, gabar da
ke tsakanin wannan Zuri'a biyu ta fi shekara dari ana yinta kuma
har duniya ta nade ba za daina ba. Ni kam zan yi iya kokarina na
ga cewa ba mu yi rigima ba ni da shi a cikin wannan birni namu
face idan ta kure babu yadda zan yi"
Nan dai Waziri ya yiwa boka Sulbaini sallama ya tafi gida. A
daren Wannan rana babu wani mahaluki da ya yi barci a cikin
birnin Darul Mahabul saboda wata irin tsawa mai firgitarwa aka
rinka kwadawa a Sararin samaniya har tartsatsin wuta yana
zubowa kasa.
Duk wata dabba mai rai ko shuka idan wannan tartsatsin wuta
ya fado ma ta, nan take take konewa kurmus. Duk wani mai
tsautsayi da ya sake ya fito waje kuwaa wannan dare sunansa
gawa. Kai ba ma mutane ba hatta Aljanun da ke ZAune a birnin
saida suka yi hijirar dole a wannan dare suka bar cikin garin
suka koma can nesa da gari cikin dazuzzuka basu dawo ba sai
da gari ya waye. Ba komai ne ya haddasa duk wannan bala'i ba
face fishin da su boka Sulbaini suka yi da juna.
Wato a cikin daren ne suka rinka aikawa junansu da masifu iri-
iri amma maimakon masifar ta sauka a kansu sai ta rinka
kwamarzuwa da yar uwarta a sama cikin sararin samaniya tana
zubowa kasa kan mai uwa da wabi. Kashe gari kuwa da safe,
Sarki, Waziri da Dakarun rakiya mutum dubu biyu suka yi hawa
cikin shigar yaki mai kwarjini da ban sha'awa Sannan aka tanaji
guzuri mai yawa bisa kan rakumi dari biyu sanann aka kimtsa
wadansu kuyangi guda goma wadanda za su yi wa sarki
hidima a cikin tafiyar. Sarki bai fito ba daga cikin gida sai da
boka Sulbaini da boka Zaharu suka iso.
MAZAN JIYA
Littafi na biyu 2
Part G
Na Abdulaziz Sani m gini
Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey
Ciki na sani kuma na zo ne domin na taimakeki na biya miki
bukatarki".
Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Zarifa kuma ta cika
da dumbin farin ciki. Ba tareda fargabar komai ba Zarifa ta
zauna daf da boka Ardusa ta kura masa idanu tana mai
sauraron abinda zai fada ma ta.
Boka Ardusa yai murmushi gami da gyaran murya sannan ya ce,
"Ya ke ma'abociyar kyawu,tauraruwar kyawawa, ina son ki sani
cewa na san baki da wani buri wanda ya fi ki daukaka a duniya
fiye da dukkan sauran mata, kuma kina son kimallaki dukiyar da
babu mai kamarta.
Tabbas idan kika yi abubuwan da zan umarceki sai bukatarki
tabiya.
Yanzu nazo gareki a sirrance lallai ki rike sirrin kada ki kuskura
ki gayawa wani wannan sirri na zuwana wajenki koda bukatarki
ta biyane idan kuwa kika fadi sai dan da za ki haifa yazamo?
sanadin ajalinki".
Koda jin haka sai Zarifa ta ja dogon numfashi ta ce,'Ai kuwa ba
zan taba gayawa wani wannan sirri ba".
Boka Ardusa ya ce,' Na san kin yi mamakin yadda aka yi na
kawo kaina wajenki, to amma ba abin mamaki bane idan kika yi
la'akari da matsayina a yanzu na bokan da yafi dukkan bokayen
duniyar nan karfin sihiri, amma kuma ina
daga cikin talakawan bokayen. Yau shekarata ashirin da biyar
ina bauta a karkashin wannan masarauta ta birnin Kisra kuma
akwai alkawari mai nauyi tsakanina da dangin su Sarki Kusaidu
cewar ba zan daina bauta a garesu ba sai bayan shekara
hamsin, kin ga ke nan a gaba akwai shekaru ashirin da biyar.
A ka'idar wannan alkawari