Showing 24001 words to 27000 words out of 87228 words

Chapter 9 - YARO DA KUDI Complete Hausa Novels by Binta Umar Abbale .txt

a kaci sa'a ya cire


Kwafa dady yayi A fili yace "ai naci kabar sarqar taka da daga yau kabar sakata sai dai ka se wata"


Shiru Nasir yayi kawai yana cin Abinci,
Shi yarasa gane kan dadynshi yanzu kamar shi sai a ce masa ga yadda zai yi"




Yace"idan ka gama kaje katawo dasu Maryam ,za mu tafi tare dasu domin suma "yaya nane"




Hade Fuska Nasir yayi tamau!lallai yanzu ,zasuyi rigima da dady ,in har yace shine zai dauko yarinyar ,shi Sam ba yaso ya hada tafiya da ita,




Yayi shiru


Dady yace"ka fahimci wace Maryam nake Magana kuwa"




"A'a yafada yana wani ya mutse fuska!


Maryam da kanneta "Na gurin Malam Ya'u




"Dady sai ni ne dole zan je in kiransu?
Yafada cikin bacin rai!
Yaci gaba da cewa "meye ma Alaqarka dasu dady"
Dan Allah ka kyalesu ,dole za ai ta tambayar yaran waye a gurin tunda dai an San ba naka bane"


Dady yace"babu ruwanka ,kawai ka tashi ka je kai min Abinda Na saka"




Momy tace"bara Na kira Aunty sai ta turo su kawai ba sai yaje ba"
Domin Momy bata son bacin ran Nasir ko kadan




Dady yace"shi nake so yaje ya tawo da su ai kannensa ne"


Sai mom din tayi shiru ganin dady yafara hasala domin tana mugun gudun bacin ran mijin NATA






Mikewa yayi ,yana kallon Dadyn nasa yace"Afuwa my dady Na tafi"


Sai Mom ta saki fuska tana dariya"


Dady ko kara shan kunu yayi har sai da Nasir din ya fice daga farlour




Ya kalli Momyn yace"narasa Abinda yarinyar nan Maryam tayi masa Na fuskanci basa shiri"




"Wallahi kuwa Ashe kai ma ka fuskanta, gashi yarinyar nada hankali da nutsuwa"




"Kwarai kuwa Dady yafada yana saqa wani Abu cikin zuciyarsa ,a game da lamari,Amma ya barwa zuciyarsa,






Duk suna zaune ,guri guda bayan sun gama karya wa tsaf dasu Mussaman Nafi'u da Miftahu ,suna cikin do gayan kaya Na wata lafiyaryiyar shadda,har da hula,dama tun Asubah Alh Hussein ya fadawa Ya'u cewar a shirya yara zai je dasu wani guri


Shiyasa yana shigowa yafawa Aunty Dan haka tana sauke Abin kari ta mayar da ruwan Wanka.
Ta shiryasu tsaf


Maryam ce kawai take Wanka yanzu,


Nasir ya shiga da sallama,
Duk suka Amsa,ya Dan tsaya daga waje yana karewa farloun nasu kallo,Arrama Yau yace"Nasiru ya katsaya nan ,kashigo mana"
Aunty tace"rabu dashi ,ai yasan shi mai Laifi ne a gurina"




Bai yi Niyar shiga ba Amma jin furucin Aunty yasa kawai ya daga Labule fuskarsa a sake ya shiga ,
Wanda yayi dai dai da fitowar Maryam daga dakinsu Jikinta sanye da riga doguwa mai zubin "Yar kanti rigar tafitar mata da duk wani hallitar ta hannuta riqe da gyale tana kokarin nan nade kanta dashi ,batan ta nannade gashinta,yarinyar tayi kyau ba Dan ka Dan ba,
Nasir ya riqa jin gabanshi yana faduwa lokacin da sukayi ido hudu da ita,sai ya nemi yawo yarasa a bakinshi ,da kyar ya Aro dauriya da jarunmta a saka a zuciyarsa ,yakarasa ya zauna kujera,
Yace"Aunty A she laifi nayi ,Afuwa Na tuba "
Yafada yana sakin dariya,
Yace kai Na bisa wuyana Aunty"




"Wallahi Nayi fushi da kai Nasir,yau sharabon ka daka shi go min,ai INA jin tun ranar da kadawo ko"


Yace"Aunty Na manta"
Wallahi pls Aunty ,kai miftahu zo ka tayani bata hakuri"




Miftahu ya taso yana dariya,yace Aunty kiyi hakuri kinji Uncle yana da Kirki


Sai tafashe da dariya ,Malam Ya'u ma ya saka dariya yana mamakin zaro zance irin Na miftahu








*BINTA UMAR ABBALE*




_MARUBUCIYAR_


*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
_in kana bukatar cigabanshi ga number nan_
08089965176
[09/04, 15:10] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—






*✍🏻Writting by*
_*BINTA UMAR*_
*MAMAN ABDUL WAHABU*






*πŸ…Ώ42*


_BISSIMILLAHI_




Aunty tace"ai nayi hakuri tuntuni Miftahu,Uncle din naku ne wani'sain bai da kirki"


Nasir ya gyara zama fuskarsa a sake yace"ki dai yi hakuri Aunty ni din ne sai a hankali wallahi tun da nadawo bana zama kwananan ma za'a bude sabon Asibiti Na"


Aunt tace"kai masha Allahu Dan gidana Allah yasa s fara Aiki a sa'a Allah ya tsare da tsarewarsa"




Malam Ya'u ma cikin Farin ciki yace "Na tayaka murna Nasiru,Allah ya tsare ka daga sharrin mai sharri"


"Ameen Ameen ,Nasir din yafada yana Dan satar kallon Maryam dake tsaye gefan Aunty.


Malam Ya'u yace"kaga yanzu sai ka fito da matar Aure ko domin shine cikar mutum"




"In sha Allahu ,Arrama munanan muna dubawa a dai tayamu da Addu'a"






"Addu'a kullum cikin yi muku ita muke Nasiru ,zamu kara a kan wacce muke yi"




"To Alhmdullhi ,Allah yasaka da Alkairi Arrama Allah ya ja kwana"


"Ameen Ameen"Arrama Ya'u yafada yana jin dadin yadda Nasir din yake daukar maganarshi babu raini ko daya"yace"ina abokin ka Anwaru?


Dariya Nasir yasa yace"tunjiya rabo Na dashi Amma yanzu zan yi kiranshi a waya"


"To to Masha Allah ,ka mikamin gaisuwata"


"Insha Allah zaiji"
Nasir din yafada yana kokarin tashi tsaye.


Aunty ta bugawa Maryam harara tace"tsayuwar me kike nan gurin kina ganin mutane kin gagara gaishe su.




Maryam ta gyara tsayuwa tana kallon Uncle din tace"Aunty nazo zan gaidashi naga kuna hira shine Na dakata tukkuna"
Tsaki Aunty taja ,tana hararata
Maryam ta gyara Murya idonta kansa tace " Ancle Ina kwana"?


Saurin dauke kanshi yayi daga kanta ,yana tafiya yace"lafiya Maryam ya kk? Kamar gaske yayi furucin.
Maryam tace "lafiya lau Uncle"
Yace"dady yace Ku fito zamuje Anguwa"
Tace"to Uncle"
Ya kalli Aunty yace"sai mun dawo Aunt


Mikewa tayi ta biyo bayanshi tana musu addu'oi iri iri tace"yanzu zasu tawo ai Maryam ce tafiye shirishirta"
Ya saki fuska kamar babu wani kulli cikin zuciyarsa yace"ki kyaleta Aunt kowa da irinshi ,Amma dai kar sukara minti goma basu fito ba"


Aunty tace"in sha Allah"


Yayi mata sallama ya fice daga bangaran nasu.


Dady Na tsaye a harabar gurin hannunshi ruqe da key din mota yau ba ya sha'awar a tukashi shi dakanshi zai yi drevin .
Nasir yakara so gurin zai karbi key din ,dady yace Ina su ke,"?


"Gasunan fitowa dady"


"Masha Allah"


"Dady kawo key din mana"


"Aa yau sha'awar dreving nake je ka huta kawai"




Dariya Nasir yasa yana mamakin rigimar dad din shi


Kawai sai ya wuce ya Nufi Motar Dady ya bude yayi zamanshi ,
Yana wani mugun jin haushin yarinyar ganin yadda take bata musu lokaci dady yayi shiru sabida baya son laifinta ko Dan,Wanda in da shi yayi haka da tuni dady ya balbaleshi da fada.




Can ya hangi tawowarsu ita dasu Nafi'u ,yayi saurin dauke kansa,yana jin wani yamm! A jikinshi,nan da nan jarabarsa ta motsa domin shigar da yarinyar tayi ta tafi dashi,yau babu hijab ga qirjinta a waje yana gani ta cikin Riga,kamar su tsone mai I do a tsaye!!
Ya riqa takurewa jikin mota yana sauke Numfashi ,gaskiya yarinyar nan ta cuceshi,
Suka karaso motar tare da Dady yana ta jansu da wasa,ya bude musu ,bayan motar suka shiga,


Shima ya shiga ,ya kalli Nasir Wanda ke zaune ido nshi a lumshe.


Yace"kai layarka kuwa"?


Ido guda ya bude domin bayason dady ya fahimci halin da yake ciki ,yace "lafiya dady kai na ne yake Dan ciwo kadan"
Dady ya tada mota ,yace"zaka fara tsirface tsirfacen naka ko,? Daga haka sai dai in nemeka in rasa gurin taro ka fakaice da ciwon kai!! Wai Kai meyasa baka son mutanene?




Murmushi yayi Na gefan baki yana cije lebe,shi kadai yasan halin da yake ciki Dan idan jarabarshi ta tashi bata sarrafuwa ta dadi. In bai kwar ba,yanzu tunaninshi ma yadda zai je ya zauna tsawon Awanni gurin taron batare da ya rage Abinda yake tsinkolunshi a mararshi ba,


Yace "Sorry My dad ,Da gaske nake fa yanzu nan nafara jin jiri kasan bana son zafi ko hayaniya"


Dad yace"sai ka nemi guri guda ka zauna ,Amma yau komai Abinka sai ka zauna an tashi a taron nan dakai"


Kwanciya ya gyara cikin motar still idonshi Na rufe yace"To dady duk Abinda kace haka za'ayi"


Maryam tayi tsuru a baya ita da qannenta tana jin maganganun da da Uba ,gefe tana mamakin Ashe Uncle yasan darajar iyayenshi,ganin duk Abinda dad dinshi yace baya musa masa,






*BINTA UMAR ABBALE*




_MARUBUCIYAR_
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
_in kana bukatarshi ga number nan_
08089965176
[10/04, 15:13] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?




πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—






*✍🏻writting by*
_*BINTA UMAR*_
*MAMAN ABDUL WAHABU*






*πŸ…Ώ43*






_BISSIMILLAHI_






Ma keken guri ne cike da Mutane maza da mata yara da manya ko wannensu zaune cikin kujera cikin manyan rumfuna
Gefe kuma motoci ne manya manya kowa ya aje tashi hatta "yan matan dake gurin kowacce da tata motar,kana ganinsu kasan "yan matane masu Amsa sunansu gurin ilimi da Arziqi gami da wayewarka ,gasunan dai kowa da irin shigarshi ta rashin kamun kai ,kowacce tana hurawa "Yar uwarta hanci tamkar ba a gurin taron Sada zumunchi suke ba.




Motar Dady ta shiga gurin
A nutse yayi parking yafito yana gaigaisawa da jama'a cikin barkwanci kamar yadda yasaba


Nasir yafito daga mota yana wani ya mutse fuska,gami da bin gurin da kallo a dage!!


Hanifa dake zaune can nesa ta hangi fitowarsa ,gabanta yafadi ,domin tazata bazai zo gurin taron nasu ba sabida taga ba kasa fai yake zuwa bah.
Sauri tayi ta mike tana gyara rigar jikinta ,wacce tafito mata da duk wani sassa Na jikinta, da wani mitsayacin takalmi mai tsayi ,ta nufi inda Nasir din ke tsaye jingine jikin mota,fuskarshi babu yabo babu fallasa,yana kallon dadynshi yana gaisawa da jama'a cikin farin ciki
Ta karasa gurin cikin wata irin tafiya ta daukar hankali duk wani sassan jikinta yana motsawa mussaman qirjinta,


Tun daga nesa ya hangi ta wowarta gurin yayi saurin dauke kansa yana ya mutse fuska,cikin ransa yace yarinyar nan zatazo ta takurani yanzu




Ashe Mubina ta ga lokacin da Hanifa ta mike domin tarar Nasir din,ranta ya baci in da A kwai wacce ta tsana bai wuce Hanifa ba duk da tana a matsayin "Yar uwarta ,sabida tana son Abinda take mugun so,
Sai kawai ita ma ta mike tsaye cikin yanayin shigarta ,ta durfafi inda suke tsaye,




Hanifa ta karasa gurin fuskarta a sake ta ke gaida Dady har da tsugunawa ,Dady Ya Amsa cikin farin ciki yace"ina Babanki yake"
"Gashi can zaune ai kai kadai a ke jira dady a fara gabatarwa"


Dady yace"masha Allah"


Ta karasa kusa da Nasir cikin iyayi da kwarkwasa tace"Ya Nasir dama talaka Na ganinku ,Yaushe kadawo daga ,America ne?


Fuskarshi ya Dan saki kadan yana bin ta da wani kallo irin nasu Na"yan duniya ,yace "Me zaki min kike nema Na ,? In kin damu dani ai kina da number Na meyasa Baki kirani ba"




Farin ciki ya lullube Hanifa ganin yadda Nasir ya ke kulata ,ta matso daf dashi kamar zata rungumeshi tace"haba my Love ka manta ne ,Amma kasan ina kiranka ,ba ka dagawa ne ko kuma in ka daga kace baka gane ne number ba"




Numfashi ya sauke a hankali yana lumshe ido jin wani irin mugun kamshi da Hanifa take bugawa ,Wanda yakara saka shi cikin wani yanayi gata tsaye daf dashi ta turo masa kirjinta.




Yace"karya kike yaushe kika kirani a waya kika ce kece har da zan kashe miki waya"


Cikin mamaki take kallonsa tace"kadai manta ne ,Amma najima INA kiranka ka Na nuna baka gane wacece ba"




Tabe baki yayi yace"mybe lokacin karatu ya sha min kai"


Dady ya waigo yana kallonsu fuskarshi a sake yanajin dadin yadda Nasir yake sakewa da "yan uwansa yanzu,ya kalli Nasir din yace "ina su Maryam din"




"Suna cikin mota dady"




Dady ya bata rai! Yace"sai ka barsu cikin mota haka ake baza ka jagorancesu ba"owk yi musu magana su fito cikin "yan uwansu
Dady yafada yana tafiya




Ranshi a bace ya bude mota yanawa Maryam wukantaccen kallo fuska a hade yace"Ku fito"


Cikin tsarguwa Maryam ta bude mota suka fito ita da qannenta a darare take bin gurin da kallo


Gaban Hanifa yayi muguwar faduwa ganin wacce tafito daga bayan motar dady yarinyar Maigadin gidansu Nasir ce,yarinyar da tayiwa muguwar tsana sabida tarin baiwar da Allah ya aje mata,
In taje Hutu gidansu Nasir har bataso yarinyar ta shiga part din momy sabida yadda take jin wani mugun kishinta gashi momyn tai ta ji da ita,wannan ne dalilin da yasa ta tsaneta.!








*BINTA UMAR ABBALE*


*MARUBUCIYAR*


*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
08089965176
[12/04, 03:03] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?






πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—




*writting by*
_*BINTA UMAR*_
*MAMAN ABDUL WAHABU*






_ALLAH MAI JI NE KUMA MAI GANI NE_






*πŸ…Ώ44*




Hanifa tabi Maryam da wani irin kallon Wulakacin tana tabe baki tace"My love wannan fah"? Ina ce yarinyar mai gadin gidan Ku ce ko"?


Domin ya ba kantawa Maryam din rai yace"Eh ita ce mana, ke kin ga tana kama da Family namu ,duba da kyau Yarinya kamar zabiya"


Hanifa ta sheqe da dariya tace"wallahi my Nasir baka da kyau,eh ko da yake Maganarka haka take domin irinsu in ka giftasu sai kaji har qarni suke"


Tabe baki Nasir yayi bai ce komai ba yana hangen karasowar Mubina gurinsu,
Cikin zuciyarsa yace "ke ma kizo duk zan iya daku shashashai kawai , ni Sam! Bana wani sha'awar Auran zumunchi daku"


Maryam Na jingine jikin mota kanta a kasa tana jin duk irin cin mutumcin da suke mata ,idon ta ya Tara hawaye tana ta kokarin mayar dasu,sabida bata bukatar zubowarsu gurin,dalili kuwa tasan in dady ya gani ran Nasir ne zai baci,,
Dama sai da tacewa Aunt bata son zuwa gurin Ta balbaleta da fada wai bata son mutane,ita kuma wulakaci take gudu.




Mubina ta karaso gurin ta hararar Hanifa ,Tace"Sarki shishigi da kwala kai har anzo Neman magana ko"?


Hanifa tai mata nata kallon Na Tara saura kwata tace"ke kai sarkin shishshigi ,ke ko kunya bakiji ba kinzo gurin Mijin kanwarki a haka,Dan Nasir Mijina ne ba Na wata "yar iskar ba"


Tofa!!
Baki yasan Abinda zai fada Amma bai San Abinda za'a mayar masa ba.


Shareta kawai Mubina tayi sabida ta Riga tasan halin Hanifa da muguwar rashin kunya,yanzu sai ta zage babu Abinda ya dame ta.


Tun kafin tace komai Nasir yace"my Aunt Ina kwana? Yafada cike da zolaya da Neman magana


Aiko jakar hannunta ta kwala masa tana harararsa cikin so da kauna tace"Wai tuntuni bana ce ka dai na ce min Aunty ba"


Yana dariya yace"kamar yaya in dai Na kiranki da Aunty bayan nasan ke din Aunty Na ce tunda kin girme ni, in haka ne kuwa ban zama *YARO* Mai biyyaya ba"


Dariya Hanifa take yi tana kallon Mubina da tayi kici kici!! Da fuska a sabila da ta tsani Nasir ya kira ta da Aunty a cewarta girman da tayi mishi ai bai taka kara ya karya ba,du du du ko shekara daya bata bashi ba.




Tace"please Bana so kawai tunda nace bana so ka daina kirana da haka ,kawai ka zabi sunan da ya dace dani ka kirani dashi"




Hanifa tayi karaf!! Tace "wane suna zai kiraki dashi bayan sunanki Aunt Mubina,ai irin wannan sunayen da kike mafarki ,sai da ya kira ni dasu".




Nasir yana tsaye yana kallonsu Fuskarshi dauke da Murmushi,gefe kuma yana mamakin haukansu ,wai son shi suke,duk su biyu shi kwata kwata bashi da ra'ayin Auran zumunchi,Ba wai Dan basu yi mai ba dukkaninsu babu ta yarwa Dan sun Amsa sunansu Na mata masu Aji da kyawu ga ilimi uwa uba nasaba da tarin dukiya




Mubina taja tsaki tana kallon Hanifa a dage! Tace"bani da lokacinki ni ke kike haukanki"


Ta kama hannun Nasir tace "muje ga guri can Na tanadar maka,sweetyna"


Babu wata damuwa ya bita,sunyi taku Uku ya tuna da.su Maryam
Shaf! Ya manta dasu wallahi


Ya jiyo yana kallon gurin,tana tsaye jikin mota ita kadai har yanzu kanta a kasa ta kasa dagowa ,Amma duk tana jin Abinda suke yi


Yace"ke!! "
Tayi sauri ta dago kanta gami da zuba masa idanuwanta masu rikitashi,sai yayi saurin yin kasa da nasa idon gabanshi yana faduwa,
Yace"ina su Nafi'un suke"?


Sai tafara waige waige domin ita duk a zatonta suna gurin a tsaye suna wasa,


Babu su babu dalilinsu sun shiga cikin Jama'a


Da sauri! Ya fizge hannunshi daga Na Mubina ,ya karasa jikin motar da take jingine ,yayi mata rumfa ,har tana jiyo hucin numfashinsa,yace"Wallahi ki nemo kanneniki kar ki sake ki sako sunana a gurin Dady ,shashashar yarinya kina can kina kallon Munafurci da kauyanci kin saki yara a wannan gurin ,to duk in da suke ki shiga ki lalubo su"


Maryam ta diridirce sai raba ido take a gurin tanaso ta hango su Nafi'u ,babu su babu Alamar su.
Tuni hawaye yafara zuba daga idonta.


Mubina ta karaso gurin ,tana kallon Maryam,cikin izgilanci ta kalli Nasir tace"Wannan fah daga ina"!!






*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_


*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
08089965176
[23/04, 23:57] +234 808 996 5176: πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—




*✍🏻Written by*
_*BINTA UMAR*_
*MAMAN ABDUL WAHABU*






*ZAMANI WRITES ASSOCIATOIN*🀝🏻






_KABI DUNIYA SANNU SANNU YADDA KA DAUKE TA HAKA ZATA DAUKE KA ,DUNIYA BUDUWAR WAWA ,ALLAH KASA MUGAMA LAFIYA_








_BISSIMILLAHI_






*πŸ…Ώ45*




Hanifah ta karaso gurin tace "kin gama da mu ne ,yarinyar maigadin gidansu ce,tazo kalan dangi"




Tsaki Mubina taja Tanawa Maryam kaskantaccen kallo tace"to waya gayyace ta zuwa nan in banda shishshigi irin Na talakawan daji ,Malama ki zauna a Matsayinki bama bukatar bara gurbi cikin danginmu"
Vrystupid!! Tafada tana wani ya mutse fuska


Maryam ko hankalinta baya Kansu da duk Abinda suke tana can Neman "yan uwanta,kokarin barin gurin take batare da tace musu komai ba,Mubina "Yar zafin kai! Ta janyo ta da qarfi gami da tsinka mata mari tace" kamar ni "Yar me gadi ina mata Magana ta shareni Dan raini to yau zan nuna miki matsayin ki,tafada tana kokarin kai wa Maryam din duka.
Abdul latif yayi saurin karaso wa gurin yana hararar Mubina ,yace"ke dai anyi babbar kwabo wallahi me tayi miki kike dukanta"?


Shiru Mubina tayi tana kauda da kai sabida tasan Halin Abdul yanzu sai ya ramawa Maryam din.


Ya kalli Nasir Wanda yayi kicin kicin! Da fuska yace" nan ka gayyato ta azo a ci mata mutumci,? Wai me yasa baka da kirki ne"?




"Mtssss!! Nasir ya ja yace" kaga dallah Malam kar ka dame ni ,Kaje ka tambayi Dady dalilin zuwanta gurin Ashe kai ma ka fahimci bata da Alaqa da nan din ,zakazo kana min surutu a kai,yana gama fada yayi tafiyarshi ya barsu tsaye a gurin




Abdul ya kalli su Hanifa yana harara yace"wallahi babu ruwanku da yarinyar nan nasan halinku,in dai kuka yi mata wani Abin ,Allah sai Na saba muku"


Cikin kunkuni Mubina tace"Tsabar shishshigi ne kawai in son ta kake kafito kafada,ka daina boyewa"
Tayi tafiyarta itama Mubina tsaki taja tayi gaba ta barsu tsaye a gurin.




Abdul ya kalli Maryam dake goge hawaye yace" kiyi hakuri kinji Maryam ,ki riqa taka tsan tsan da Nasir da Abokanshi ,babu ke babu su Hanifa,tunda sun girmeki nasan halinsu basu da kirki"




Cikin sanyin Murya tace"Nagode Ya Abdul Allah ya saka da Alkairi,


"Babu komai ,yace wuce mutafi ko"


Tayi diri diri tana kara goge hawayenta,tace"su Nafi'u ne suka bace cikin gurin nan tun dazu ban gansu ba"




"Subahannallahi"


"Garin yaya"


"Wallahi muna tsaye a tare a gurin ,nan"


"Owk karki damu kinji ko mybe sun shige

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login