Showing 69001 words to 72000 words out of 87228 words
Chapter 24 - YARO DA KUDI Complete Hausa Novels by Binta Umar Abbale .txt
ma saura kiris ta katse ya daga batare da yace komai ba.
[06/06, 01:50] +234 808 996 5176: [03/06/2019 1:18 PM] ®Binta Umar Abbale: [03/06/2019 9:22 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*104*
Mubina kamar ta fashe da kuka tace"Yanzu Nasir ni kake wulakantawa, nafi sati daya ina kiranka a waya Dan wulakanci kaki dagawa sai yanzu ka gadama"
Tsaki yaja yace"kinga Malam karki dameni, tunda dai na amince shikkenan kuma mai kikeso nayi miki ku so kike in aje aiki in tsaya dan kin kira waya ina sauraron shirme da shiri ririta, karki kara yimin makamanciyar magana irin wannan ya karashe maganar yana Jan tsaki a karo na biyu
Jikinta ne yayi sanyi sosai dama tasan za'ayi haka dashi
Itama sai tau fada tace" kasan bazan jure wannan rashin mutumcin naka ba wallahi
[03/06/2019 1:17 PM] ®Binta Umar Abbale: Kashe wayar yayi kawai bai tsaya sauraronta ba zuciyarsa sai zafi takeyi ,sakkonin yake dudduba wani kiran ya kara shigowa wannan baby ce katse kiran yayi nan ma ya cigaba da abinda yakeyi , sai da yaga duba sakkonin sannan ya kira Sofia a waya cikin turanci suke magana, nan ya ke tambayarta yaya aiki dafatan komai babu matsala.
Basu jima suna magana ya kashe waya,
Ya dade kafin bacci ya dauke shi, biyar saura Na asubah ya tashi har an idar da sallahr asubah duk jikinshi a mace yakeyin komai, tun jiya da Momy tafada mishi labarin auran Abdul da Yarinyar jikinshi yayi sanyi nan falo ya zauna yana Jan carbi Momy na sama bata sakko ba Har bacci ya dauke shi bacci mai tartare da damuwa da wahala gami da gajiya
Momy ta sakko kamar ko daushe cikin kwalliya, ta tsaya suna magana da Uwani mai aiki, Uwani tace" naga uban gidana yana bacci a farlo ,Momy ta cikin sauri ta juya tana kallon farlon Nasir ta hango kwance cikin kujera bacci yake sosai da sosai
Wani irin tausayinsa ne ya kama Momy sai ta zauna kusa da kafafunsa tana kallonsa cikin tausayi da kauna irin ta uwa da danta , shi kam bai San ma abinda yake faruwa bacci mai nauyi ne ya daukeshi.
[03/06/2019 2:21 PM] ®Binta Umar Abbale: Sai wajan karfe tara da rabi ya tashi , yana bude idonshi ya saukesu kan Momy, cikin mamaki ya mike zaune yana mika ya kalleta gami da cewa "Momy bacci nayi anan"?
"Bacci kayi sosai Myson" Momy tafada tana kallonshi
Agogon hannunshi ya kalla yana mamakin yaya Akayi bacci ya daukeshi a nan batare da ya shirya ba
"Momy bari in yi wanka " yafada yana mikewa
"Sai ka fito My son"
"Ok Momyna"
Cikin sauri ya kammala komai ya fito ,Momy tace"kazo ka karya yau nasa Uwani tayi maka kunun gyada gashinan yaji madara"
"Ok Momy"
Kai tsaye daining din ya nufa Momy ts hada mishi yaji madara sosai tace"ko in zuba maka abinci ne"?
"A'a Momy kunun ma ya isa"
"Kadaure kaci ko yaya ne"
"Momy wannan ma ya'isa kinsan yanayin cikina yanzu sai ya rikice
"Amma dai yau karkayi ciye-ciyen kayan zaqin nan don Allah"
Momy tafada gwanin tausayi
Dariya yake yace"insha Allah Momyna"
Mikewa yayi yana gyara links din hannunsa, yace"zan wuce Momy amma kafin in tafi zan shiga asibitin in ga abinda yake faruwa"
Momy tace"to Allah ya kiyaye hanya a gaida "yan uwa da abokan arziqi, har waje ta rakoshi Giss yana tsaye yana jiran fitowarsa,
Yayi sauri ya karbi wata karamar dake hannun Nasir din , ya bi bayanshi inda motarshi take Momy sai addu'a take ta zabga masa , Tony ya bude masa motar ya shiga da Sauri ya rufe ya zagaya ya bude mazauninshi ya zauna gami da kunna mota suka fice daga gidan
Maryam ce take bin titi a nutse tana sanye cikin atamfa riga da zani mai kalar ja tayi amfani da mayafi kalar atamfar, takalmin dake sanye a kafarta mai tsine ne sosai sabida haka a nutse take tafiya, Maryam najin takaicin tafiyar nan sabida kafin ta fita babban titi akwai tafiya , sosai yawanci dama duk da motoci suke fita in ba lalura ba babu Wanda zaka gani yana tafiya da kafa cikin Estet din tunda guri ne Na wane da wane, so take ta fita babban titi domin ta samu Napep , tayiwa Momy Alkwari zataje yau hospital din, amma in taga da wulakanci bazata jura ba
[06/06, 01:51] +234 808 996 5176: [04/06/2019 9:18 PM] ®Binta Umar Abbale: [04/06/2019 7:26 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*105*
Tun daga nesa ya fahimci ita ce sai yace ma Tony yaja motar a hankali har suka iso daf da ita, Nasir ya bawa Giss umarni ya fita yayi mata magana da yawonshi, batare da bata lokaci ba Giss ya bude Mora domin cika umarnin da aka bashi.
Maryam gabanta yayi wata muguwar faduwa ganin Giss ya tari gabanta domin baza ta taba mancewa da wannan fuskar ba ,gabanta yana faduwa tace"Lafiya malam kazo ka tare min hanya"?
Cikin yanayi hausarshi yace" oga ne ya bada Umarnin haka"
Cikin mamaki ta tsaya tana kallon motar , ahankali glass din motar yake yin kasa fuskar Nasir ta ban yanna, ya dago kanshi gami da kallonta, ita kuwa gabanta ya rika faduwa tamkar qirjinta ya tsage
Kai tsaye yace"ina zaki je"?
"Ina zakije"?
Maryam ta maimaita maganar cikin mamaki!
Fuskarshi ta kalla taga ya hade fuska tamau!
"Ai kena a kayi"
Maryam tafada kai tsaye
Banzan kallo yayi mata gami da cewa" makaryaciyar banza da wofi, zaki tafi gantali kin dai"
Yafada yana mata wani kallon gani-gani
Maryam ranta yayi mugun baci amma sai ta dake kawai ta kama hanya zata wuce batare da tace komai ba
Nasir yayiwa ma Giss alama ya shigo su tafi dama so yakeyi ya bata mata rai kuma yayi nasara
Haka Tony yazo ya wuce ta fuuuuuu da mota,
Zuciyarta ta dinga wani zafi, tanaji kamar ta juya ta koma gida kawai amma in ta tuno tayiwa Momy alkwari sai zuciyarta ta karaya
Haka ta fita babban titi ta samu Napep ta hau kai tsaye (N Alhussen Specialyst Hospital)
A waje tace ya sauke ta tafito tana gyara zaman mayafinta sannan ta bude handbag din ta tafito da kudinshi ta bashi, sannan ta wuce ciki
Tana shiga taga motashi a harabar gurin a aje Tony a jingeni da ita ,sai gabanta ya ruqa faduwa da tasan nan zaizo wallahi da babu abinda zai kawo ta ,tasan yau za'ayi wulakanci a asibitin
[04/06/2019 8:32 PM] ®Binta Umar Abbale: Kafin tagama tunani sai ta hangi Nasir din ya fito tare da Dr Sofia da wasu "yan mata uku a bayansu, kai tsaye gurin motarshi suka nufa sai tayi saurin kauda kanta tana diri-diri kamar ta ruga a guje
Mamaki ya kamashi ganinta a asibitin zuciyarshi yace tazo kenan.
Ganin sun tsaya suna magana ne yasa ta karasawa gurin da suke din cikin turanci tace"sunana Maryam Arma Ya'u
Ta mika Dr Sofia hannu suka gaisa
Dr Sofia ta rika tunanin kamar ta San wannan fuskar sabida kwata-kwata kammanin Maryam din bace mata sukayi
Dr Sofia ta duba takkadun da suke hannunta tana duba sunan domin sai yaga kamar sunan daya, tabbas hakane, tadago kai tana kallonshi gami da cewa "ita ne wannan kenan"?
Daga mata kai yayi kawai yana kokarin barin gurin batare da ya kalli inda Maryam din take tsaye ba kai tsaye motar ya shiga Giss yabi bayanshi Tony yaja suka fice
Kallon kallo ake tsakanin Maryam da Sofia domin sai yanzu Sofia ta gane Maryam din
Cikin turanci tabasu umarnin da su biyo bayanta
Haka suka bita har Maryam din
Nan Dr Sofia tabawa "yan matanan biyu uniporm ko wacce tasan matsayinta, sannan ta kalli Maryam a qasqance
Tace" Ke kuma zaki na mana goge goge da aike-ake a nan in kinga zaki yi to ,za'a biyaki naira Dubu hamsin"
Shiru Maryam tayi tana tunanin kaskancin yayi yawa wato ita ce zata zama Clenar a asibitin bayan tana ganin akwai masu goge -goge a hospital din ba
[04/06/2019 9:17 PM] ®Binta Umar Abbale: Cikin turanci tace" Ok, yaushe zan fara aiki"?
Dr Sofia ta kalleta cikin mamaki ganin Sam ranta bai baci ba ko kadan tace" ranar Monday mai zuwa"
Cikin turanci tace "amma ina naiman alfarma guda daya"
Sofia tayi mata wani dan iskan kallo tace "wani irin alfarma ko fara aiki bakiyi ba"
Cikin nutsuwa tace"zanyi aure a wannan satin ina naiman alfarmar zuwa bayan sati guda sai in fara aiki"
"Wannan kuma bani zaki tambaya ba sai ki bari in Oga ya shigo sai kiyi mishi magana"
Dr Sofia tafada tana kokarin wucewa.
Maryam ta bita da kallo kawai har ta shige wani daki
Girgiza kai tayi kawai itama ta bar gurin tabbas yazama dole ta nemi wannan alfarmar gurin Nasir, zata jure duk irin wulakancin da zai yi mata
Nasir kuwa yana fita daga hospital din kai tsaye birnin kudu suka nufa
Sai biyar Na yamma ya baro garin a mutukar gajiye yake in banda ciwo babu abinda jikinshi keyi sabida yadda yayi zurga zurga a garin tunda mutan garin suka ji labarin zuwansa suke ta turereniyar zuwa karbar zakka gaskiya mutane sunji dadin zuwanshi
Duk da haka bai koma gida ba sai da ya je gidan bursina nan ma yayi musu rabon kayan abinci sosa nan ma yayi rabon kudi kamar babu gobe sosai Media suke su suji ta bakinshi yaki cewa uffan, har ya gama ya fito suka biyo bayanshi yaki tankawa, sai kawai suka rika daukarshi a photo
Momy na zaune a harabar gidan kamar ko da yaushe suna hira da Maryam motar Nasir ta shigo cikin gidan
Tony yayi parking da sauri ya fito ya budewa Nasir mota ya fito duk jikinshi sanyi kalau,
Momy tayi saurin mikewa tsaye tana kallonshi ganin yadda yaron nata ya fada lokaci guda duk lebanshi ya bushe , idanshi sun kankance sai lumshewa yake
Tun kafin ya karaso Momy ta cimma sa ta rike hannunsa suka nufi part dinta tana tambayarshi abinda yake damunshi
Maryam ta bisu da kallo sai taji wani mugun tausayinsa ya ratsata ji take kamar tafashe da kuka ta Dade a gurin tana ta tunanin Nasir din ga kudi ga komai ga jin dadin amma daga gani bashi da kwanciyar hankali shekarunshi basu kai ba Allah ya Dora masa jagoranci yanzu Wanda suke ci a karkashinsa Allah yayi yawa dasu, ita kanta zata fadi alkairinshi, shidai barshi da mugun halinshi
[04/06/2019 9:30 PM] ®Binta Umar Abbale: Jikinta a sanyaye ta mike daga gurin itama ta nufi bangaransu
A kujera ya zube Momy ta zauna tana kallonshi har yanzu hannunsa na cikin nata
"Momy nayi wata muguwar gajiya wallahi jikina ciwo yake"
Nasir yafada yana lumshe ido
"Kayi yawo ne a rana My son"?
"Ko daya Momy hayaniyar mutane ne kawai"
"Kai fa baka son hayaniya ko myson"?
Momy sosai kuwa, ga media suka dameni lallai sai nayi musu magana ,Momy to ince musu me"?
"Gwara da kayi shiru yafi"
Momy tafada
Ta cigaba da cewa "kazo kaci abinci ko'
"Momy bari inyi wanka yau zan baki mamaki zanci abinci sosai"
Mikewa yayi ya nufi bedroom dinshi
Momy tace "sai ka fito My son"
"OK Momy"
Momy ta mike itama jin ana kiran sallahr magariba
[06/06, 01:51] +234 808 996 5176: [05/06/2019 10:45 AM] ®Binta Umar Abbale: [05/06/2019 10:18 AM] ®Binta Umar Abbale: [05/06/2019 9:32 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*106*
Ban garan su Hajiya Rakiya mahaifiyar Abdul kuwa taja tunga ta kafe tayi rantsuwar Abdul ba zai auri Karuwa ba sabida taji labarin cewar yarinyar "yar iska ce , shi kuma Mahaifin Abdul yayi rantsuwar mutukar yana raye a duniya sai anyi wannan aure, yau Abdul ya diro garin cikin farin ciki da annasuwa sosai yake shiri amma yana zuwa ya tadda tashin hankali a gidan Hajiya tace masa mutukar ya sake ya auri Maryam to sai ta tsine masa
Duk yadda zaiyi ya fahimtar da ita taki ta saurareshi sabida
Haka yake cikin tsananin tashin hankali
Ban garan Mubina kuwa shiri take sosai da sosai burinta ya cika zata auri Nasir ita dai Allah ya sanya mata kaunarsa
Yanzu Hanifa bata da babbar makiyya kamar Mubina wacce suke Uwa daya uba daya gaba sukeyi sosai da sosai
Bangaran Nasir kuwa babu wani shiri da yake Harkokin shi kawai yakeyi batare da ya saurari Mubina ba gashi gone daurin aure
Aunty ita da Yaya Rabi Na zaune a falo suna kara duba kayan lefen Maryam Yaya Rabi tace"gaskiya yaron nan yayi kokari sosai duba saitin a kwatu har dozin ,o ni "yasu yarinyar nan ina zata kai kaya"
Aunty ta sauke ajiyar zuciya tace"wallahi ni jikina ma yayi sanyi ji nake kamar a kwai wani al'amari da zaifaru"
"Babu abinda zai faru sai alkairi ki kwantar da hankalinki"
"Allah yasa a gama hidimar bikin nan lafiy....
Kafin ta karasa suka dinga jin sautin tafiya kwas kwas kwas
Hajiya Rakiya tare da Hajiya Mairo babbar kawarta suka yi sallama cikin gidan
Aunty ta amsa tana kokarin mikewa tsaye kafin ta mike din sai gasu sun shigo sai falo Yaya Rabi tace"maraba lale marhabin sannunku da zuwa"
Hajiya Mairo ta yi wani mugun shan kunu tana kallonsu dai-dai sai ya mutse fuska take
[05/06/2019 9:55 AM] ®Binta Umar Abbale: Aunty tace"Bisimillah mana Ku shigo ga guri ku zauna"
Hajiya Mairo tayi mata wani dan iskan kallo na raini tace"ai Baku da gurin da zamu zauna anan mutsiyata fatararru"
Yaya Rabi tace"to Hajiya lafiya mai ya faru"?
"Au tambayar abinda ya faru kike mutsiyata talakawa masu gadon talauci"
Shiru Yaya Rabi tayi kawai tana kallo Hajiya Mairo ita kuwa Hajiya Rakiya takasa cewa komai sai kallon banza take watsa musu
Hajiya Mairo tace" gargaji mukazo mu yi muku wannan Umarni muke Baku mutukar kaka sake a kayi wannan auran wallahi sai kun gwammace kida da karatu babu arziqi zaku kuma garinku Na gado, wato kunga dukiya idanku ya rufe shegu fatararru to in abinda kuke bukata kenan, zamu yanke muku talauci
Yaya Rabi ta numfasa tace"to duk munji abinda kuka fada Hajiya mu bamu isa mu hana abinda Allah ya hukunta ba idan yarinyarmu matar yaron nan ce, mu baza mu hana abinda duk Allah ya hukunta ba,
Maganar zaku yanke mana talauci kuma wannan babu mutumin da ya isa ya Yankewa mutum talauci sai Allah, sabida haka kullum cikin godiyar Allah muke da ya barmu a wannan yanayi na talauci , kuma bamu cewa nema gurin uban kowa ba
[05/06/2019 10:43 AM] ®Binta Umar Abbale: Hajiya Mairo ta zabura tana nuna Yaya Rabi tace" ke mutsiyaciya zagina zakiyi ne , mutukar kika sake kika zageni wallahi sai kin qare rayuwarki a kurkuku"
Aunty tayi wani murmushi mai ciwo tace "Don Allah kuyi hakuri Hajiya duk abin bai kai na haka kuyi hakuri don Allah kuje Ku jawa yaronku kunne tunda shi ne yakeso mu bamu ce dole ba"
Hajiya Mairo ta bude jakar hannunta ta fito da damin kudi ta watso shi cikin farlo tace" Ku diba gashinan mutsiya ta kawai in kunne yaji jiki ya tsira,
Kafin su an kara har sun fice daga gidan
Shiru Na tsawon mintina goma babu Wanda yayi magana tsakanin Ya Rabi da aunty.
Ya Rabi ta numfasa tana kallon aunty tace"wannan wace irin masifa ni Rabi"
Aunty tace"kinga abinda nake fada miki ko Yaya"
"Dama tun safe jikina yake bani akwai wani abu da zai faru gaskiya ina ganin in da matsala sai a hakura yanzu ki duba kiga irin cin mutumcin da mutanan nan suka zo suna mana"
"Kul wannan ba huruminki bane, wannan al'amari Allah ne ya hukuntashi kuma da marigayi Alh mai gidan nan, sabida haka sai cika mass burinshi wanda ya bari"
Aunty tafashe da kuka tace"wallahi ina tsoran rashin mutumcin wadan nan mutanan"
"Duk abinda zasuyi suje suyi, baxa su taba hana Allah ikonshi ba sabida haka ki kwantar da hanlalinki"
"To shikkenan Allah ya sanya alkairi"
Aunty tafada tana goge hawaye
****
A mutukar gajiye Maryam ta dawo gida ga wata irin yunwa da ishirwa sun addabeta , sabida haka ko da tadawo din ruwa ta nema tasha sannan ta kwanta tana sake-sake tarasa inda zata tsoma ranta taji dadi
Wayarta ta dauka ta rike hannunta tunani take ta kirashi ko kar ta kirashi Dan gaskiya baxata taba zuwa gurinshi wai ta tambayeshi wani abuba shiyasa tayi dabarar satar numbarsa a wayar Momy.
[05/06/2019 12:54 PM] ®Binta Umar Abbale: Wata zuciyar tace ki kirashi kawai ki gani ai a wayane
Zuciayrta na dar-dar ta danna numbarshi, sai da kusa tsinkewa sannan ya daga, tare da yin sallama
Maryam ta sauke ajiyar zuciya jin muryarshi nan da nan jikinta ya soma rawa sai tayi shiru tamkar ruwa ya cinyeta
"Hello"
Nasir yafada daga bangaranshi,shiru ba'ayi magana ba sai faman ajiyar zuciya yake ji
Number wayar ya duba sabuwa domin ba'ataba kiranshi da ita ba
Kashewa yayi kawai yana kokarin ajewa wani kiran ya kara shigowa
Aje ta yayi kawai har ta katse, wani kiran ya kara shigowa a karo na uku
Sai da takusa tsinkewa ya dauka, ranshi a bace yace" da wa nake magana ne"?
Maryam ta sauke numfashi tana sauke ajiyar zuciya tace" Nice"
"Kewa"?
Yafada kai tsaye domin kwata-kwata bai dauki muryar ta ba
Shiru tayi tana inda-inda
"Mtsssss"
Yana kokarin kashe wayar
Tayi sauri tace"Maryam ce"
Yanzu ya fahimci wacece
Mamaki yakeyi a'ina yarinyar nan tasamu numbarsa
"Wacece Maryam"
Yafada yana ya mutse fuska
Shiru tayi
"Ok zan kashe waya tunda babu abinda zakice"
"Dama dazu naje anyi min intarvio kamar yadda kafada, to shine nake naiman alfarma Sofia tace Lallai sai dai in tambayeka"
Maryam tafada batare da tayi masa bayanin wacece ita
Tsaki yaja yace"wai wace banza ce take min magana yaya ina tanbayarki wacece ke kina min maganar banza ko an gayamiki bani da abin yi ne"
"Maryam ce uncle"
Tafada tana jin mugun bacin rai
"Ok Maryam Ya'u maigadi"
Yafada cikin izgili
Itama cikin izgili tace "eh ita ce"
Sabida tasan yayi hakane domin ya bata mata rai
''Okey Maryam wace irin alfarma ce kike nai ma"?
Yafada yana sakin murmushi Lallai yarinyar bata da kunya gaskiya wato yana fada tana fada lallai wuyanta ya isa yanka.
Shiyasa yakeso yasan wace irin alfarma ce wannan
[06/06, 01:52] +234 808 996 5176: [05/06/2019 4:28 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*67*
Cikin nutsuwa Maryam tace"dazu munyi magana da Dr Sofia cewar zan fara aiki ranar Monday, sai na nemi alfarmar cewar inaso abari zuwa litinin ta sama, sabida a cikin wannan satin zanyi aure shine tace sai na nemi izini daga gareka"
Shiru yayi yana sauraron muryarta jikinshi yayi bala'in sanyi muryata ta kashe masa jiki sosai, da kyar yayi gyaran murya yace" duk abinda Dr Sofia tafada miki hakane in kina bukatar yin aiki a wannan hospital din zaki bi doka ni babu ruwana da wani