Showing 57001 words to 60000 words out of 87228 words
Chapter 20 - YARO DA KUDI Complete Hausa Novels by Binta Umar Abbale .txt
hukumcin da ya yanke tace" OK za'ayi duk abinda kace,sai kadawo"
Nasir ya shige motarshi ranshi a bace
Dr Sofia ita da Security din suka nufi cikin Asibitin
Suna zaune shiru kowa yana sakawa da kwancewa ,mussaman Malam Ya'u yana tunanin mai nene mifita a rayuwarsu Suka ji an turo dakin an shi go
Cikin bada Umarni Dr Sofia ta nuna Maryam da hannu tamkar wacce tayi gagarimin laifi cikin turanci tace "kuyi waje da ita"
Kafin Momy tayi magana tuni sunyi kan Maryam suna zare ido
Momy ta daka musu tsawa tace"kar Wanda ya kuskura ya taba ta wallahi ranku zai baci"
Daya daga cikinsu yace"Madam umarni ne daga oga"
"Ok Umarni ya baku Nasir din cewar kuzo Ku fita damu"?
Duk cikin turanci suke maganar.
Yace"No ita kadai yace mu fita da ita"
"To shikkenan Momy tafada rai abace tace nice Mahaifiyarshi ,ba Maryam ya kora ba ni ya kora kuma zan fita yanzu"
Dr Sofia tace"Mom kiyi hakuri , wan can yarinyar ya bada umarni a fitar masa ,ba ke ba please mom
Momy tace "rufe min baki bana son zan can banza"
Malam Ya'u dake tsaya jikinsa a sanyaye duk da bayajin turanci amma ya fuskanci abinda yake faruwa ba mai dadi bane ,gashi yaga ana nuna "yarshi da hannu Allah yasa bata wani laifi tayi ba
Ya tari Momy wacce take ta faman fada da turanci,yace duk da dai bana fahimtar abinda kuke cewa Hajiya ina ganin abin duk bai kai na daukar zafi haka ba,ina ganin tunda Baban gida yasamu lafia zamu bar asibitin nan mungude da karamchi Allah ya kara girma"
Momy ta sauke ajiyar zuciya tace "ai ko baka fada dole zamu bar asibitin nan yanzu, shi kuma Nasir din zaizo ya same ni"
Abin mamaki duk da tsawar da Momy tayiwa Sucurty din ,ta kuma ce musu ita mahaifiyar Mai asibitin ce ,hakan bai sa sun kauce daga kanta ba su tsaye kikam ! Suna jira ta tashi. Ita ko Maryam Sam abin bai mata ciwo ba domin tasan Dan ya bata mata rai ya yanke wannan hukunci, sai ta kalli Momy tace "kiyi hakuri Momy wallahi ni kaina narasa wace irin qiyyaya uncle ke min amma babu komai"
Momy tace"ai ke zan bawa hakuri Maryam kinji ,babu komai zaizo ya same ni, tafada tana mikewa tsaye tana gyara zaman hijab din ta
Su aunty ma mikewa sukayi ,Yaya Rabi tana kokarin tashin Mahaifin nata, Malam Ya karaso gurin ya tasheshi ya mike jikinshi babu kwari sosai ,sai ya jin ginar dashi a kafarshi suka na kokarin fita daga dakin
Suma suka biyo bayansu kowanne da rai a bace, Dr Sofia ko babu abinda ya dame ta, haka wannan Sucurty suka tasasu a gaba har sai da sukaga sun fice daga asibitin sannan suka dai na binsu sai kace wasu masu laifi.
[06/06, 01:46] +234 808 996 5176: [26/05/2019 9:16 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*91*
Wannan abu da Nasir yayi ya 6ata ran Momy sosai, tunda take dashi bai taba mata abinda ya ta6a mata zuciya ba irin na yau,kwata-kwata ta lura Nasir bai san darajar dan'adam ba ko kadan ,giyar kudi tana dibanshi ya nawa kowa kallon kaskanci,amma wannan karon dole ta nuna masa bacin ranta, rai a bace suka karasa gida,dukkaninsu suka fito daga motar bayan Momy tayi parking,kai tsaye part dinta ta nufa ,batare da ta tsaya a gurin ba domin wani irin nauyi da kunyar mutanan takeji, gashi dai kullum Nasir din zai yi musu rashin mutumci amma sabida karamci da dattako basa nuna wani bacin rai a tare dasu,
To bayan Momy ta wuce Malam ya shiga da Baban gida wajansa ,su aunty suka gyara masa ko ina ,sannan suka fito,suka barshi tare da Malam Ya'u suna hira ,Baban gida ya kalli Ya'u yace"dama a kwai maganar da nadade inaso muyi da kai"
Malam Ya'u ya gyara zama yana fuskanta Baban gida cikin girmamawa yace"ina sauraron ka Baba"
Baban gida ya sauke ajiyar zuciya cikin alamu na marasa lafia yace"lokaci yayi da za'a ce ka tsaya da kafarka ma'ana ka dai na ci a karkashin wani , tun lokacin da Marigayi Alh yana raye naso ka karbi kasuwanci kamar yadda shi Alh ya so a lokacin ,kai ka nuna kafison ka zauna a bakin get ko"
"Kwarai kuwa Baba ni kai na sai yanzu nasan na tafka babban kuskure wallahi"
Baban gida yace"dama ba wani abin ake gudu ba sai mutuwa"
"Kwarai kuwa Baba"
"Yanzu abinda za'ayi a kwai wata gona ta can garinmu albasu zan siyar da rabi sai in baka kudin ka fara juyawa ko yaya kace"
"To madallah Allah ya saka da alkairi,wallahi nima tuntuni nake shawarwarin yaya za'ayi"
"Abinda za'ayi kenan ai "
Baban gida yafada yana gyara kwanciyarsa
Nan dai Malam Ya'u yayita godiya suka tsayar da maganar cewar zasuje can albasu garinsu Baban gida domin a siyar da gonar sabida sauran "yan uwanshi duk suna can shine kawai yafito nai man abinci cikin gari a wancan zamanin har ta kaishi da yin aure ya haifi su Yaya Rabi da aunty Lokacin da mahaifiyarsu ta rasu aunty da girmanta a lokacin Yaya Rabi a kayiwa aure ,to bayan rasuwar mahaifiyar tasu sai auntt ta cigaba da kula da mahaifinta har lokacin da ta auri malam Ya'u
Malam Ya'u ya gyara masa kwanciya ya mike ya fito cikin farin ciki ya nufi bangaransu,
Ya na zuwa ya sanarwa da aunty halin da a ke ciki
Suma sun goyi da bayan haka sabida dama tun dazu abinda suke tattauna kenan
Maryam tana kicin tana aikin hada musu abinci ita ma taji dadin wannan lamari dama burinta bai wuce ta dai na ci a karkashin Nasir ba ,Dan rainin hankali.
[26/05/2019 9:38 PM] ®Binta Umar Abbale: Nasir kuwa sai wajan sha biyu na dare ya shigo gida.
Kai tsaye part dinshi ya wuce domin yayi wanka ga wata irin yunwa yana ji
Momy tana falo tana jiran dawowarsa ,tana jin shiguwar motarsa ta mike ta nufi part din nasa.
Fitowarshi kenan daga toliet yana tsane kanshi,Momy ta tura kofar dakin nashi ta shiga da sallama
Abin ya bashi mamaki ganin Momyn shi da daddaran nan ,sai ya tsaya yana kallonta ta karaso ta zauna gefan gadonsa ita ma shi take kallo kamar yadda take kallonsa
Yace"Momyna lafiya dai ko"?
Tace "lafia lau tunda gani ka ganni Allah ya dawo dani gida bayan korar karan da kasa akai mana"
Cikin namaki yaje ya zauna kusa da'ita yace"Momy waye yayi miki korar kare,ban fahimci abinda kikecewa ba"
Tace"dazu bayan fitarka waye ya turo Sucurty suzo su wulakanta Maryam"
Momy"wacece Maryam"
" Ok zakayi min rainin hankalin da kasaba ko"?
Momy tafada a fusace!
Dauke kai yayi yana nazari na minti biyu yace"Momy please ban fahimci me kike nufi ba wallahi , dazu dai nasan nasa Dr Sofia tasa ka Sucuty su fitar da yarinyar nan ganin tana nema tayi mana katsaldan a kan aikinmu ,ba na son bacin rai shiyasa na yanke wannan hukunci"
Momy ta hararashi tace"wannan ba hukumci bane wulakanta mutum ne abinda kayi Sam Baka kyauta ba, kamar ni ince musu ,su kyaleta suka qi ,ji sukayi mana tsaye a ka har sai da sukaga mubar asibitin sannan suka dai na bin mu sai kace wanda mukayi gagarimin laifi"
Ranshi ya baci jin abinda Dr Sofia tayi kafin ya tafi sai da yafada mata ga yadda zata yi
Yace" Kiyi hakuri Momy ba laifinsu bane ,ni na isa in sa a kore ki Momy ke nake gani nake jin sanyi a zuciyata Momy nayi missing din Dady Sosai ,kwalla ta taro a idanshi yana kokarin mayar da ita,amma sai da ta fito ,ya sa Dan ya tsanshi daya yana daukewa
Ita ma Momy zuciyarta ce ta karye sabida Nasir ya fama mata mikin da yake cikin zuciyarta ,sai tafara goge hawaye
"OK" "OK Momy yi shiru na dai na please ki dai na Dan Allah"
Nasir yafada yana marai rai cewa
Cikin kuka Momy tace"My Son Bakajin magana ko,ka manta wasiyyar dady din ka"
[06/06, 01:46] +234 808 996 5176: [27/05/2019 1:19 PM] ®Binta Umar Abbale: [27/05/2019 10:35 AM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*92*
Momy ta cigaba cewa My son baka kewar mahaifinka, da ka kayi missing din nashi da gaske da baza ka wofintar da wassiyar shi ba, nima kanaso ka dora hawan jini ,ko ka kasheni in na mutu ka huta ai"Momy ta karashe maganar tana goge fuskarta.
Nasir hankalinshi ya tashi sai ya rungume ta sosai yake kokawa da zuciyarsa sabida bayason hawayen da yake kokarin dannewa su zubo masa har Momyn ta gani hankalinta ta tashi,yace "a'm Sorry Momy bazan karaba ki yafe min, ni kaina ,Wasu abubwan da nakeyi ba'a son raina ba ,amma Momy kar kira zubar min da hawaye dan Allah"
Tausayinsa ya kamata ance tsakanin da da uwa sai Allah
Ta shafa kanshi kamar yaro tace"Na yafe maka ,amma Dan Allah kar kara wulakanta mutanan ,kaga mahaifinka har ya bar duniya tsakaninsa dasu mutumci ne,kuma duk Wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimakeshi"
"Momy ki kwantar da hankalinki insha'allahu zanyi kokarin ganin na faranta miki"
Momy tace"yawwa Allah yayi maka albarka"
"Ameen Momyna"
Tace"kaci abinci kuwa,domin jikina yana bani bakaci abinci ba"
"Uhum Uhumm Momy Wallahi banci ba yanzu hakama yunwa nakeji sosai"
Nasir yafada tamkar wani yaro karami
Momy ta Dan mari fuskarsa tana dariya tace"ai halinka zama da yunwa sai da kai tafaman cin biscut sai kace wani yaro"
Dariya yayi har fararen hakoranshi suka bayyana ,kasan habarshi ya loba yana kanne mata ido daya yace"Momy nifa har yanzu yaro ne a gurunki"
Momy ta girgiza kai kawai tana murmushi tana tuno hirarsu da dady kafin rasuwarsa inda yake son yara kananu,
Ta kalleshi tace"Myson inaso ka haifa min yara da yawa kaji ko"
Shiru yayi fuskarshi dauke da murmushi yace"Momy ni a tsarina banason taron yara wallahi a kwai damuwa"
Momy ta harareshi tace "albarkace damuwa my son"?
Yayi murmushi yace" Momy da gaske nake wallahi da daya ko biyu sun isheni"
"Baka isa ba"Momy tafada, tacigaba da cewa kai dai kawai ka nemi zabin Allah"
"Insha Allahu Momy,Allah ya kawo masu albarka"
"Ameen amee"
Tace"tashi ka kimtsa muje kaci abinci"
Ya mike tsaye yace" Momy muje kawai haka
Mikewa tayi itama suka fita.
Momy ta hada masa abinci sosai tasashi a gaba sai da yaci ya koshi sannan ta kyaleshi yaje kwanta
[27/05/2019 10:56 AM] ®Binta Umar Abbale: Washe gari da wuri ya tashi ya kimtsa tsaf cikin yanayin shigarshi irin ta jiya kwana biyu abin ya motsa mishi,ya fito ya tadda Momy zauna cikin kujera tana duba wanni littafin turanci fuskarta manne da farin tabarau
Ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace"Kwana biyu kuma abin ya motsa maka ne"
Yayi murmushi gami da zama kusa da ita yana gyara wata katowar hula ta sanyi mai uban tsada yawanci turawa ne suka fi amfani da ita mussaman da sanyi, yasanya ta a kanshi har sai da rufe masa kunne , hannuwanshi ma safa ce kalar hular ,yace "Momy yau garin antashi da sanyi wallahi kinsan banason wannan yanayi duk jina nake a takure"
Momy tace"shine ka jibga riguna a jikinka haka"
Dariya yayi yace"yeah Momy to ke ya kikaga wankan"?
Momy ta tabe baki tace"babu laifi dai"
Yana dariya yace" Momy in a America nake ,wannan dressing din nawa ,mai tsada ne sai nasamu wanda zai'siya,
Momy tace"ai ban ce komai ba"
Yace"nan din ma bari kiga in fita ,yadda zan hada Gslow mussaman Na mata"
Dariya Momy tayi tace"baka da dama My son ,zan so inga Sirika ta,wai ko da Hanifa za'ayi ne ko da Mubina wacce kazaba a cikinsu"
Nasir ya hade fuska yana turo baki kamar wani Yaro yace"Momy rabuda Wa "yan nan "yan iskan yaran dan Allah"
"Yan uwanka ne "yan iska "? Momy tafada cikin mamaki
"Yes " Nasir yafada ya cigaba da cewa
Momy in ba iskanci ba wai a gurin taro Mubina ta mike ta kefadawa dady tana sona ko kunya ba taji cikin jama'a"
"Laifi tayi kenan dan tace tana sonka"?
"Momy nifa a tsarina bana son in auri shashashar mace Mara kamun kai ,shiyasa ma har yanzu ban fara dubawa cikin matanmu nan domin babu abinda suka iya sai shirme da kazanta gami da shafa man bleecing"
Momy dariya take sosai ganin yadda Nasir ya hakikan iya gaskiyarshi
Shima yana dariya yace"Allah kuwa Momy inajin haushin "yan matan wannan zamani kiga sun dage suna shafe shafen banza,karshe ya jawo musu cuta,nafison mace naturel "
Momy ta tabe baki tace "to ai sai kaje kauye ka nemo mata ina ganin can zai fi maka"
[27/05/2019 1:36 PM] ®Binta Umar Abbale: Ya mutse fuska yayi yace"haba Momy kauye fa kikace,ni nayi kala da matan kauye yanzu"?
Momy tace "au matan kauyen kalarsu daban take da ta "yan birni,ashe bakasan sunfi tarbiya ba, in ka amince sai insa Uwani ta duba maka a garinsu kaga Uwani kyakykyawa ce gata bafulatana"
Dariya yayi kawai yana girgiza kai yace"Momy kenan indai zaki iya zama da'ita shikken ki samomin"
Dariya tayi tana nunashi da hannu tace"dubeshi kamar gaske"
Cikin dariya dai ya mike ya nufi dainnig teble yace"da gaske ne mana"
Momy ma mikewa tayi tabi bayanshi tafara hada masa kalaci suna hira cikin so da kauna irin ta uwa da danta,yace"Momy mun kammala komai fa Dan gane da bude Hotel dinmu ni da Abbas yanzu kawai za mu tanadi ranar da zamuyi bikin budewa,bayan haka kuma munyi odar Motoci Masu kyau Sosai da nagarta suna gareji ,kiyi mana addu'a Allah yasa mu fara a sa'a"
Momy tace"Allah ya dafa muku yayi riko da hannuwanku yasa Ku fara a sa'a"
"Ameen Momy"
Miftahu ne yayi Sallama ya shigo cikin falo, yana sanye jallabiya mai ruwan tuka kanshi da hula irin ta Larabawa, yaron yafara girma yanzu yana shekara sha Uku zuwa sha hudu ,cikin nutsuwa ya karaso yana gaida Momy
Momy ta amsa fuskarta a sake ,ya mikawa Nasir hannu gami da cewa "uncle barka da asubah"
Nasir ya bashi hannu sukai musabaha tace" ka tashi lafiya Boy"
Miftahu yayi dariya jin sunan da uncle din ya kirashi dashi yace"lafiya Lou uncle"
"Masha Allah"
Nasir yafada yana cire hannusa ya cigaba da cin abincinsa
Ya kalli Momy yace"Dama Baba ne yakeson yayi magana dake"
Momy tace" to kace ya shigo mana, in banda abin Malam Ya'u sai ya aiko ka, ai anzama daya"
[06/06, 01:46] +234 808 996 5176: [27/05/2019 6:28 PM] ®Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*93*
Miftahu ya fita domin ya sanar da mahaifin nasa abinda Momy tace.
Tare suka shigo falo Momy ta mike daga kan kujerar cin abinci tace "Yanzu malam har sai ka turo yaro yayi maka iso sannan zaka shigo"?
Tafada tana nuna masa gurin zama, Malam Ya'u ya zaune cikin kamala da dattako yana murmushi yace"ai dole ne hakan domin haka shari'a tace" Momy tace"e kayi gaskiya Malam"
Malam Ya'u ya gyara zama sosai yana fuskantar Momy yace"Hajiya wata muhimiyar magana ce nake tafe da ita"
Momy tace "To Allah yasa ta alkairi ce ,ina sauraronka"
"Hajiya inaso kiyi wa magana ta kyakykyawar fahimta wallahi ban shirya wannan Abu da wata manufa ba,sai Dan ina ganin haka shine mafita a gare ni"
"Babu komai Malam ina sauraron ka"
"Dama na yanke shawarar cewar zan bar aiki anan zan shiga kasuwa in sha Allah"
Momy tayi shiru tana tunani a cikin zuciyarta,dama tasan wannan lokacin yana nan zuwa
Ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa tace"Masha Allah arrama ,bazan hanaka ka fita nema ba ubangija Allah yabada masu amfani"
Cikin farin ciki malam yace"ameen Hajiya nagode da fahimta ta da kikayi"
Momy tayi murmushi tace"ai nasan gaskiya Malam wallahi babu komai"
Duk wannan abin Nasir Na zaune yana cin abinci yana jin duk abinda suke cewa ,kala bai ce musu ba,har Malam ya tashi yanawa Momy sallama sannan ne ya hangi Nasir din yace"A'a Nasiru baka fita ashe"?
Nasir ya dago kai yana kallonshi babu yabo babu fallasa yace"e arrama yanzu dai nake kokarin fita"
"To masha Allahu,Allah ya tsare"
"Ameen ameen Arrama"
Nasir yafada ya cigaba da cin abincinsa
bayan Momy tace "My son kana jin yadda mukayi da arrama ko"?
"Eh Momy inaji"
"Owk to yanzu kai mai zaka ce"?
"Momy mai zance kuwa ,ni banason takurawa mutum dama shine ya ga zai'iya ko yau ya bar aiki zan samu get man, karki damu zan fitar da kudi in bashi hakkinshi,kuma dukkanin dawainiyar da ake mishi ba za'a fasa ,sai dai in shine yace" baya bukata"
"Haka yayi Allah yayi maka albarka"
"Ameen" Nasir yace ya mike bayan ya gama karyawa yana duba agogo yace"Momy zan fita kuma inaji sai dare zan shigo"
"To Allah ya tsare"
"Ameen Momyna"
Yafada yana kokarin fita
Kai tsaye motarshi ya nufa
Maryam na tsaye kusa da Baban gida dake zaune kan bainci ,jiki yayi karfi ,sai tsokanarsa takeyi, ta hangi fitowar Nasir gabanta ya yanke ya fadi ,sai tayi saurin dauke kanta ta cigaba da magana da Baban gida amma duk da haka gabanta sai dukan uku-uku yake ,sabida yadda taga Uncle din yayi mata wani mugun kyau gaskiya kayan sun mishi kyau sosai
[27/05/2019 6:55 PM] ®Binta Umar Abbale: Gashi Malam baya guri ga get a rufe, ga Nasir ya tawo da mota zai fita yaya kenan"?
Baban gida ya mike cikin rashin qarfin jiki yafara kokarin bude get din,
Maryam tayi sauri ta dakatar dashi ta hanyar mayar dashi ta zaunar kan bainci tace"haba tsoho jikinka babu qwari ina kai ina iya bude kofa,ka kyalemu mu masu jini a jika, tafada tana dariya
Shima dariyar tayi yace"kaji ja'ira kamar wacce zata iya"
Kai tsaye gat din ta nufa cikin karsashi gami da jarumta tafara kici-kicin budewa,
Nasir tun kafin ya karaso ya hange ta tana kokarin budewa
Tsaki yaja kawai yana dariya domin shi dariya ma yarinyar tabashi gaskiya yana ganin karfin halinta
Sai ya tsayar da motar gami da zuge glass din ta zuro kanshi dai-dai sai tin da Baban gida yake zaune yace" Baban gida barka da asubah"
Baban gida ya fara kokarin mikewa yana amsawa Nasir yace"ba sai ka tashi ba ma, yaya karfi jiki"
"Alhmdullhi Nasiru Allah yayi maka albarka,ya jikan alh Huseen ameen"
Nasir yace"ameen ameen" ya mayar da glass din motar yana dannawa Maryam Hon wacce ta hakikance tana faman tura get amma kamar wacce take tura dutse kwata-kwata yaki motsi ,sai gumi take yankawa.
Dariya kamar ta kashe Nasir a cikin mota ,yana sane yake ta faman danna Hon babu ji babu gani
Maryam ta juyo a fusace tana danna masa harara taja tsaki ta cigaba da abinda takeyi,shiko yana ganin abinda tayi sai ya kara danna hon da karfin gaske
Ya bude motar ya fito a fusace, ya nufi gurin , yana zuwa kawai ya buge hannunta daga jikin get din yace"dallah matsa mana a guri kinsan baza ki'iya budewa kika batawa mutane lokaci idoit"
Maryam jikinta a sanyaye ta dinga kallonshi tana galla masa harara sai