Showing 84001 words to 87000 words out of 87228 words
Chapter 29 - YARO DA KUDI Complete Hausa Novels by Binta Umar Abbale .txt
taja gami da cewa"rashin imanin naka akan ta ya tsaya kenan yarinyar da bata da wani kwarin kirki
[16/06/2019 2:20 PM] Binta Umar Abbale: Momy ta cigaba da cewa"ina Mubina take? Kafin daurin auranka da Maryam da Mubina s kafara mai yasa baka kwatanta adalci ba my son"
"Momy Mubina zagina tazo tanayi daga dawowata gida tana gwada min iko ni da gidana,shiyasa na koreta ita kuma wannan kin manta kece kika aje min ita a part dina, ni ba nine na kirata ba"
Girgiza kai Momy tayi na rashin abin fada tace"da na kawo maka ita cewa nayi ka kaita part dinta ai, ban ce kayi mata komai ba"
Cikin mamaki Nasir din yake kallon Momynshi ganin yadda ta fututtuke tana fada,Maryam fa matarshi ce yana da damar ya taketa a ko ina,
Shiru kawai yayi mata tana fada ta cigaba da cewa"yanzu ka duba musu yarinya babu wata matsala in ceko"?
"Momy babu Matsala fa, komai normal ki kwantar da hankalinki, Ita fa ba yarinya bace kamar yadda kike tunani"
"Maryam din guda nawa take my son"?
Momy tafada
Tabe baki yayi yana duba agogon hannunshi yace"Momy ni a gurina ba yarinya bace,
Shiru Momy tayi tana jin tsoran kar ya yanko mata maganar da zata kallanshi"
Tace"yanzu bacci tskeyi ko me"?
"Momy kin tambaye ni fa na baki amsa,tana can akwance tana bacci amma takasa tafiya, sai tale-tale takeyi, yana sane yayi mata wannan maganar domin ta rabu dashi da tambaye-tambaye
Aiko Momy hankalinta ya tashi sai ta mike tsaye tana kokarin hawa sama domin ta dauko gyale,
Yace"Momy ina zakije ne"
Ta tsaya tana kallonshi gami da cewa"muje in ga jikin yarinyar mutane myson nasan halinka"
"Mikewa tsaye yayi ranshi a dan bace yace" Momy ni ba gida zan koma ba ofis zan wuce,mutane na can na jira na, Na lura kin dai na sona yanzu sai wannan "yar"
"A'a My son jirani in fito ai soyayyarka ita ce ta shafi iyalinka"
Tafada lokacin da take hayewa sama,dakko gyale
Ficewarsa yayi ranshi a bace ganin rawar jikin da Momy take a kan Maryam sai kace itace autar mata,ko kuma a kanta haka ta taba faruwa,sai yaji wani mugun haushinta ya kamashi, sabida haka yana fitowa ya nufi mota,Giss dake tsaye kofar da zata sadaka da cikin falon ya rufa masa baya
Yana shiga mota ya bawa Tony umarnin tafiya tun kafin Momyn ta fito,har sun fice daga gidan.
[18/06, 02:40] +234 808 996 5176: [17/06/2019 9:40 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*122*
Sai bayan sha biyu na rana Maryam ta farka daga nannauyan baccin da ya dauketa,babu laifi taji dadin jikinta ba kamar dazu ba,da kyar ta mike tsaye ta nufi kofar fita daga dakin Nasir din, kai tsaye part din ta ta nufa,
Har yanzu key din na jiki kofar in da barshi budewa tayi kawai ta shiga cikin tsananin mutuwar jiki, sam bata tsaya ta karewa falon kallo ba,ta nufi daya daga cikin dakunan da suke cikin kayataccan falon
Toleit ta nufa ta hada ruwan zafi ba sosai ba, ta shiga ciki,wani zafi ne ya ratsata sosai amma ta daure ta zauna,sai da ta jima a ciki sannan ta daina jin zafin gurin.
Har wani bacci ne yake kokarin fizgarta sabida yadda takejin dadin zama cikin ruwan zafin
Da kyar ta fita daga ciki ta hada wani ruwan ta yi wanka sosai ta tsarkake jikinta , tafito a daddafe,ta kimtsa,sai sannan tayi sallahr Asubah,takaici da bakin ciki duk sun cika mata zuciya, sabida yadda Nasir yayi mata asarar Sallahr asuba babu abinda ya dameshi
Nasir yana ofis amma duk hankalinshi ya na kan Maryam,in ya tuno da yadda ya bar ta sai yaji gabanshi yana faduwa, haka dai yake daurewa yana sauraron abokan kasuwancin su, wasu baki ne suka zo daga Nijar, domin su duba sabbin motocin da suka shigo dasu abinda ya dauke masa hankali kenan.
Amma yana samun sukuni ya samu ya kunna wayarshi domin kiranta
Nan ya tuna ashe bashi da number ta
Sai ya ajiye wayar jikinshi a sanyaye zuciyarshi tana saka masa kawai ya tafi gida,yasan yarinyar tana bukatar taimako,
Adaddafe dai ya bari biyar na yamma tayi ya hada inashi inashi ya bar Abbas da jama'a ya gudu gida
Da sauri ya bude part din nashi ya shiga so yakeyi kawai yayi tozali da ita, amma sai yaga wayam babu kowa, har yanzu bed shirt din nanan kaca-kaca da jini kamar yadda ya fita ya barshi.
Kofa ya nufa da sauri wata zuciyar tace masa me kakeyi haka ne, Nasir kar ka manta kaifa babban yaro ne da ko wace mace take kaunarka,sabida kyau kudi da wayewa ko ta ina kayi zarra mai zai sa ka rika yin rawar jiki kan wata bagidajiyar yarinya mutukar ka sake ta gane son da kake mata ka shiga uku,sabida haka ka kiyaye.
Nan take yadawo nutsuwarshi yaji wata tsanar yarinyar ta darsu cikin zuciyarsa mussaman da ya tuno abinda ya faru tsakaninta da Nasir, mamaki yake ma yaya akai ma ya kwanta da ita,daga yau ya daukarwa kanshi alkwarin bazai sake kula ta ba.
Wanka yayi ya fito ya zauna gefan gado daga shi dai towol ga lokacin sallar magariba yayi,amma a halin yanzu babu abinda yake bukata in ba sex ba,
Wayarshi ya dauka yana laluben number Mubina,dole ya rage zafi.
Mubina na ganin shi ne sai taqi daga wayar har ta katse,wai ita nan jan'aji
[17/06/2019 9:51 PM] Binta Umar Abbale: Bai yi zuciya ba,sai ya kara kiran wayar,a qa'idarshi baya kiran mace a waya sau biyu lallai yau Mubina ta ciri tuta
Sai da takusa katsewa sannan ta dauka tana ya mutse fuska tace"Ya aikai ne"?
"Ya'akai ne"
Ya maimai ta maganar cikin mamaki, wato Mubina tun kafin tafiyar tayi nisa raini ya fara shigowa,
Cikin bacin rai yace"ban sani ba, ki sameni a dakina,Mtssss"
Yafada yana Jan tsaki
Wani farin ciki ne ya lullubeta a fili tace"wallahi bazan je xoba zaka san nafi waccan daraja da wayewa"
Saki yakeyi yana duba agoge ganin har Angara
K
Kiran sallahr magariba, ya zira g
Duguwar riga mai yankakken hannu ya fita,kicibus sukayi da Mubina ta shigo cikin wasu kaya masu tsananin fidda surar mutum
[19/06, 00:26] +234 808 996 5176: [18/06/2019 7:24 PM] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*123*
Tare masa hanya tayi tana kokarin hanashi tafiya zuwa massalaci, yace"meye haka zaki tare min hanya"?
"Ka kirani kuma kana kokarin tafiya ka barni"
Tafada tana lumshe masa ido,
"To hanani zuwa massalacin zakiyi,? Meya sa lokacin da nayi kiranki baki zoba sai yanzu"
Fada yana kokarin fita
"Ok kaje kadawo ina jiranka"
Tafada tana zama cikin kujera,
Babu abinda yace mata ya fita, ya barta ko tunanin sallah ba tai ba
Sai da yayi sallahr isha'i sannan ya shigo gidan zuciyar tana bashi shawarar ya shiga ya duba Maryam wata zuciyar ta hanashi ai in ya shiga,gurinta girmansa yafadi,kawai ka rabu da ita tunda dai ka nuna mata matsayinka,
Kawai ya wuce part dinshi ya san Mubina tana nan tana jiransa.
Mubina na zaune tana kallo ya shigo ya sameta
Yace"kinyi sallah"?
Girgiza kai tayi tana wani irin fari da idanta
Jikinshi ya hau kyarma ganin yadda take ban karo masa kirji
Yace"kiyi sallah ki zo ki sameni muyi soyyaya"
Yafada yana kanne mata ido
Girgiza jiki tayi cikin kwarewa tace"wace soyyaya kuma bayan ka gama soyewa tun jiya"
Dariya yayi yana nunata da hannu yace"tabbas jiya na soye kurmus yau ma zan soye,ina fatan kwalliya zata biya kudin sabulu"
"Ba na san wulakanci fa"
Tafada cikin bacin rai
Tabe baki yayi yace"wane wulakanci ana maganar gaskiya,kin san ni bani da rufi kuma bana gulma, duk wacce tafi tes cikinku sai nafada"
Yana gama fadar maganar ya shige dakinshi,
Jikinta ne yayi sanyi lallai iskanci Nasir ya girmi hankalinta yanzu ita yake fada ma wannan maganar
Aikuwa yau zata bashi mamaki
Part din ta ta koma taje ta hada magani da madara tasha,ta markada kankana ta hada da madara ta shanye,sannan ta dauko wani magani a wata roba ta bude ta lakato dan mitsitsi ta yi matsi dashi sannan ta mayar da murfin ta rufe
Ta dauki wani cingam ta sa a bakinta tana taunawa, kai tsaye part din Nasir ta nufa
Yana zaune gefan gado dagashi sai Karamin wando jikinshi duk a murmude power dinshi duk ta bayyana. Hankalinshi na kan desktop din shi yana dubawa
[18/06/2019 7:55 PM] Binta Umar Abbale: Mubina ta shiga dakin tana zabga wani mugun kamshi,Wanda ya sashi dago da kanshi babu shiri ya bita da wani kallo har ta karaso kusa dashi ta zauna tana tauna cimgam kas-kas cike da kwarewa
Nan yaji wani mugunwar sha'awar ta kamashi kamshin da takeyi yayi bala'in tafiya da imaninshi,
Gadon ya hau sosai ya jawota tafada jikinshi,jiki na kyarma ya fara cakudata itama tana mayar masa f
Da martani,kan kace kwabo Nasir ya gigice ya fita daga hankalinshi, sai ya karama himma da abinda yakeyi
Mubina ta saki jiki suna soyewa kawai taji yana ambatar sunan Maryam tun kafin aje ko ina.
Bakin ciki ya turnuketa ta dinga yunkurin tureshi daga jikinta, yaki turowa sabida tsabar bakin ciki kawai sai tafashe da kuka,shi kuwa bai fasa tara da ita ba kuma bai fasa kiran sunan Maryam ba
Mubina taci wuya hannun Nasir amma ba kamar Maryam ba,duk da cewar ya sameta cikkakiyar budurwa to amma ko kafar Maryam bata kamo ba, sabida babu jini ko kanki kan bedshirt din,ba kamar Maryam ba da jini ya bata gadon tamkar an yanka kaza mai rai da lafiya.
Bayan yadawo nutsuwarshi sai ya mike gami da sauka daga bed din ya barta kwance cikin halin bakin ciki da damuwa
Wankanshi yayi ya fito ya kimtsa jikinshi, ya tsaya kanta,yace"ki tashi kije ki tsarkake jikinki amarya"
Ranta ya baci ta yunkura zata mike a zafafe, sai ta koma ta kwanta tana kwalla gami da jin wani mugun radadin zafi a gabanta,
Amma duk da haka bata hakura ba,race"Allah ya isa tsakanina dakai Yaron nan wallahi ban yafe maka ba,kana kwance dani kana karuwa dani sannan kana kiran sunan wata shigiya yarinya mai kama da mayya,kayi na farko kayi na karshe"
Tafada tana matsar kwalla
Dariya yake yana kallonta, ya wani zakuda kafada,alamar abin bai da meshi ba yace" yau na nuna miki ruwa ba sa'an kwando bane,yau kinga aikin karamin yaro kamar yadda kika fada, babu ruwani ni,nasan da kanki zaki zo ba sai na nemeki ba"
Kallo kawai ta bishi dashi tana mamakin rashin kirkinshi, tasan bakin ciki kawai zata kunsawa kanta mutukar tace zata sa damuwarsa a cikin zuciyarta
Tana kallonshi ya zauna kan Sofa,yana ciye-ciyen kayan zaqinshi babu abinda ya dameshi,yana ci yana duba wayarshi
Da kyar ta mike zaune ta lalubi mitsitsiyar rigarta ta sanya, ta sauko daga bed din cikin jigata,ta nufi kofa tana wata irin tafiya tamkar mai koyo tata.
Dariya yake mata kasa-kasa har ta ficr daga dakin nashi, a fili yace"babu wani taimako da zan miki da girmanki,kawai ya cigaba da abinda yakeyi
Mubina da Maryam ko wacce ta shiga halin ni"yasu, ko wacce tana jiyar kanta, tsawon kwanaki bakwai babu wacce ya kara saurara sabgar gabanshi kawai yakeyi.
[20/06, 14:33] +234 808 996 5176: [6/20, 09:33] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*124*
Babu abinda yake fito da ita daga part din ta kullum a kulle,yau tsawon kwana takwas kenan,duk wani abu da take nema da akwai a ciki, kamar babu abinda ya taba shiga tsakaninta da wani da namiji yadda ta girgije tayi shar, suna waya da Momy kullum tana tambayarta lafiyarta, bata taba fada mata abinda yake faruwa tsakaninta da Nasir ba
Abinci dai-dai cikinta take girkawa kullum in ta zauna ci sai ta tuno Amanar da Momy ta bata ta Ancle wata zuciyar tace mata taje ta sameshi, inda yake ta gani ko yana cin abinci,sai kuma wata zuciyar tace mata Nasir dai ba yaro bane hausawa sukace lafiya itace take boya, kwata-kwata yanzu bata kaunar ta ganshi sabida wani irin mugun tsoransa take ji
Mubina ma gefe taja tana jiyyar kanta sam bata kara marmarin sake haduwa da Nasir din ba
Yana tsaye a gaban drssing mirrow yana taje sumarshi wacce taji mayuka masu uban tsada tayi wani bakikkirin da ita har wani nan nadewa yake fuskarshi tayi wani haske kana ganin shi da yanayin fatarshi kasan yana hutawa,
yana sanye da wasu uban suit masu masifar tsada wanda sukai mishi uban kyau,ya zauna gefan bed din shi yana daura takalmi, wayarshi ce tayi kara, Abbas
"hello"
yafada gami da makale wayar da kafadarshi ya cigaba da daure igiyar takalmin
daga daya ban garan Abbas yace"ka fito ne,kasan kafin muwuce airport dole zamu sallami mutanan dake jiranmu"
"kaga Malam ban fitoba ma ina gida, ko na fito ma babu wanda zan saurara wallahi kaji na rantse kawai kayi kokari ka sallami jama'a kafin in karaso,sabida tsabar iskanci sai ka dinga barin mutane wai lalai sai nazo sannan"
ganin yadda Nasir yake masa masifa yace"kaga saurara min Malam kwana biyu in kazo ofis ba ina lure da kai baka tsinana komai sai aukin tunani ko na meye oho maka ni dai nafada maka akwai jama'a suna jiranka kuma tun jiya suka zo daga ghana sabida haka sai kafito"
kashe wayar yayi yana jan tsaki babu abinda yace da Abbas din kawai ya cigaba da shirinshi
tsaf ya shirya ya dauki wata karamar jaka irin ta mata fiya
kai tsaye part din Mubina ya nufa sai zabga wani mugun kamshi yake
Mubina na zaune a falo tana kallo tana braekfarst tana sanye da kayan bacci bata cire ba,yayi sallama gami da shiga ciki
[6/20, 09:56] Binta Umar Abbale: Gabanta ne yafadi lokacin da ta ji kamshin turarashi kafin ta ankara ya shigo falon cikin sallama fuskarsa babu yabo babu fallasa
tunda ya shigo take binshi da wani kallon wanda ita kadai tasan ma'anarshi yau yayi mata wani kwarjini ga wani uban kyau da yayi, fuskara take bi da kallo yana tsaye yana kallonta ji take tamkar ta je tai tata shafa kwantacan gashin da yabi kewayayyiyar fuskarshi ya kwanta yai sosai sai kyalli yakeyi abinka da farin mutum.
kallonta yake yana jira yaga zata gai dashi koko har yanzu girman kan yana nan
kamar tasan tunanin da yake kenan tace"kanina sai ina kuma da alama zakayi tafiya ne"
"Eh zan je America zamu ni jirgin 12:00 pm ni da Abbas , zamu dawo ranar ita yau so ki kula da kanki ,babu ruwanki da waccan yarinyar ko wacce ta zauna ma tsayinta"
"Ok shikkenan sai kadawo da kake min maganar babu ruwana da waccan " yar talakawan yo ni dama meye runawa na da ita,ita kanta tasan cewar ruwa ba sa'an kwando bane"
"Oho miki"
yafada yana kokarin fita,sai yai saurin dakatawa gami da juyowa ya wani sha kunu sosai yace"wato bani da matsayin da zagi gai dani ko a matsayina na mijinki sabida kin rai nani"
diriricwa tayi tana kallonshi har zatace masa kai ne ai zaka gaidani tunda kasa kake dani,sai wata zuciyar ta kwabeta sabida tuno karanta dashi sati daya da ya huce
Tace"to ka shigo ka tsaya a tsaye ko zama kakiyi ta yaya zan gai daka"
kallonta yayi yace"ok shikkenan na lura har yanzu baki dauke ni a matsayin miji ba,amma insha Allahu in na dawo zan nuna miki matsayinki"
yana gama fadar maganarsa ya sa kai ya fice daga falon,
kai tsaye part din Maryam ya nufa.
[20/06, 20:55] +234 808 996 5176: .[6/20, 12:06] Binta Umar Abbale: *YARO DA KUDI*
*125*
Shiru falon nata tamkar babu wani mahalukin da yake rayuwa ciki tana cikin bedroom dinta a kwance wani irin zazzabi ta tashi dashi mai shiga kashi gabobinta duk ciwo suke mata,tana kwance kan bed ta kudundune jikinta cikin bargo sai rawar dari take,ta rika jin motsi kamar anshigo falon,
yunkurawa tayi tana kokarin mikewa zaune,shikuma ya sako kai dakin.
saurin dauke kanta tayi gabanta yana dukan uku-uku kwata-kwata bata tsammaci zuwanshi ba
idanshi a kanta har ya karaso kusa da ita
babu zato taga ya dago kanta dake kasa yana karewa fuskarta kallo
lokaci guda yayi kicin-kicin da fuska gabanshi na wata irin faduwa, Allah yasa kar zarginsa ya tabbata
sakin fuskar tata yayi gami da cewa"zanyi tafiya zuwa America sai rana ita yau zan dawo ki kula da kanki, bayan haka kuma na lura da abinda kike kunshewa kallo guda da nai miki sabida kafin in dawo ki ki samawa kanki mafita sabida kin san bazan taba karbar dan da ba nawa ba"
bai saurari abinda zatace ba kawai ya sakai ya fice daga dakin.
Tana kwance tana binshi da kallo har ya kari maganarshi ya fice tana mamakin furucinsa
itama tafara zargin wani abu gabanya ya dinga dukan uku-uku da sauri ta diro daga bed din ta nufi toliet ta dauko pt ta dauki fitsarinta ta fara kokarin gwadawa,Addu'a take Allah yasa kar zarginta ya zama gaskiya
Aikuwa Allah bai amsa mata ba domin positive ya nuna mata,zaman dirshan tayi a toilet din jikinta na kyarma,ranar da aka kawota gidan nan ranar tagama al'ada aranar tai wanka,kuma ranar ta dauki ciki,innalillahi wa inna ilayi raji'un
Kuka ne ya kufce mata tanayi tana mai-mai ta innalilahi dama rabo ne ya kawota gidan Nasir gashi ya fahimci ciki ne da ita tun ba aje ko ina ba, tasan sarai baya kaunar haihuwa ita kam ko zama da kasa zata hade baza ta yadda ya zubar mata da ciki ba
nan ta karaci kuke kukenta ta mike tayi wanka tafito ta shirya tsaf, ta dauki aniyar yaqi da Nasir duk abinda zai biyo baya zata dauka domin bazata yadda ya zubar mata da ciki ba.
[6/20, 16:21] Binta Umar Abbale: Tunda Nasir ya tafi basu hadu da Mubina ba ko wacce na gurinta, yau kwananshi biyar saura kwana biyu ya dawo kenan,
Mubina suna waya dashi kullum in bai kirata ba ita zata kirashi wani lokacin in "yan wulakancinsa suna kusa sai yaqi dagawa ku kuma yafara neman fada babu arziqi take masa sallama,ta aje wayar.
Maryam ko jikinta yaqi dadi kullum cikin zazzabi take ga jiri babu damar ta dade a zaune in ta mike tsaye sai jiri ya kusa kada ita, haka dai take daddafawa ta sha magunguna abin sai a hankali
Misalin karfe hudu na safe na yamma jirginsu Nasir ya sauka a filin saukar jirage na Malam Aminu dake kano,
Yaranshi Tony da giss suna hango fitowarshi daga jirgi suka nufeshi da sauri ko wanne fuskarsa dauke da murmushi na murnar dawowar oga
rungumeshi sukai suna dariya,shima dariyar yake sannan suka nufi inda motarsu take,
Giss yace" Boss ina Abokinka ne,naga tare kuka tafi"
"yana can na barshi yana hado mana kaya mybe gobe ko jibi ka ganshi"
Tony yace"Boss ina muka nufa ne"
hutawa yake so yayi yasan in ya je gida yanzu Momy bazata