Showing 39001 words to 42000 words out of 87228 words

Chapter 14 - YARO DA KUDI Complete Hausa Novels by Binta Umar Abbale .txt

yadda ya iya dole ya sanya safa a hannuwanshi yaje ya dakko kayan aiki,




Maryam ko tana kwance tana kuka bakin ciki kamar ranta zai fita,uncle ya cuceta ,ganin yadda ya ke kalle mata jiki.
Har yanzu hannuwanta na qirjinta ta kare,wai bataso ya gani.




Cikin rashin imani yazo ya tankwabe hannun a karo na biyu fuskarshi a murtuke, ya ciro wani abu mai tsayi yana da dan kaifi, ya daga mata Brest guda ,inda ya hango wata labcececiyar kwalba ta makale a gurin jini na fita, Ya sanya wannan abin ya fara aikinshi




Maryam ihu take kurmawa kamar ranta zai fita ,shi ko babu abinda ya dameshi ,sai da ya ciro kwalabar sannan ya sanya auduga a gurin ya tsane jinin dake fita, a gun ,ya cire ya dauko wani magani ,shima ya sanya auduga ya dangwalo ,ya manna a gurin ciwon cikin rashin tausayi! Maryam ta fasa kara jin wani mugun radadin zafi yana tsirga mata a ko wane sassan jikinta ,riqe masa hannu tayi ,tana kuka tace"please uncle ka kyaleni haka,kar ka kashe ni ,na tuba ancle wallahi bazan fadawa dady komai ba"


Share tayi ya cigabah da aikin shi,yanda yayi wa kasan Brest din nata haka yayiwa saman kafadar ta,inda ya ciro wata katuwar kwalba,yana ji tana kuka gami da rokanshi yaki saurara mata,sai da yayi dressing din gurin yadda ya kamata,sannan ya sanye plasta ya manne gurin tsaf!
[05/06, 19:00] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*




*67*




Yana gama aikinshi ya matsa daga gurin , zuciyarshi sai faman tafasa takeyi, key din shi ya dauka ya fice daga ofis din sai huci yakeyi shi kanshi yarasa wace irin masifa wannan kishin yarinyar kamar ya kashe shi duk wata sha'awar ta da take damunshi ya neme ta yarasa.




Maryam tashi tayi da kyar ta lalubi rigarta ta saka ,sai faman kuka takeyi ta sauko daga kadon a hankali ,taje ta dauki hijab dinta ta saka,ita ma ta fita ,dady ya daga kai ya kalli Nasir lokacin da ya fito ,hankalin shi ya tashi,ganin Nasir din yana muzurai,yace"kai lafiya kuwa"?
Ina Maryam din"?




Kafin yace komai Marym ta fito tana goge fuska ,dady ya saki ajiyar zuciya, yace"sannu Maryam kinji ko,yanzu mai yake miki ciwo"?






Dady ya bata tausayi ganin yadda ya damu da lamarinta ,sosai dattijon yake burgeta,itama tana bala'in kaunarsa kamar yadda yake kaunarsu,tace "babu komai dady sai dai zugi da nake ji,shima nasan maganin da'akasa a gurin ne,"




"To
Masha Allah ,Maryam Allah yakara kiyayewa kinji"


"Ameen dady nagode"
Maryam tafada kanta a sunkuye




Yace"shige muje mota kinji naga wancan yafito yana zare ido kamar mara gaskiya,dafatan dai bai miki komai ba"?




Kanta a kasa tace"dady babu abinda yayi min"




"Yawwa Allah yayi miki albarka, dady tafada cike da tausayin yarinyar.




Nasir na cikin mota yana jiran su ranshi duk a dagule yake,dady ya matsa lallai sai sunje duba Anwar yana ganin in yaje zai iya karasa shi mutukar sukai ido biyu




Dady ya bude mata kofa, yace"shiga ki zauna kinji, cikin jin kunya Maryam tace"dady da kanka,ai zan iya budewa"




"Nasani ai na hutassheki"


Babu yadda ta iya tashiga bayan motar tana jin nauyi sosai Lallai Alh huseen samun kamarshi a duniyar nan sai an tona.




Dady ya bude kujerar gaba kusa da Nasir din ya zauna ko kallonshi bai yi ba.






Nasir din ma haka,ya kunna mota suka bar hospital din






Dady yayiwa Nura waya suna wane asibiti'"?




Nura yace suna Malam Aminu, kai tsaye yace"ma Nasir din su wuce Malam Aminu




Bai ce masa komai ba ya cigaba da dreving din shi






Maryam ta dago kai cikin rashin sa'a suka hada ido dashi ,yai mata wani banzan kallo ,tayi saurin yin kasa da idonta, a zuciyarta tace"ban taba ganin mugun mutum kamarka ba,mai zuciyar fir'auna"




Anwar ya na kwance a gadon asibiti,bayan likita ya duba shi, sosai shima ,sai da a kayi masa dinki a fatar lebanshi inda Nasir ya fasa sai gwiwarshi da kafadarshi, Gaskiya Nasir yayi masa lahani sosai,sai nuffashi yake fitarwa na wahala,yana tunanin irin Wulakacin da rashin mutumchin da zai yiwa Nasir ,in ya far fado.
Dady yayi Sallama dakin da Anwar din yake kwance, likita a kansa,nan suka gaisa da dady cikin mutumchi da girmamawa. Likitan ya juyo yana kallon Nasir ,shima Nasir din ya kalleshi , Dr Dini ,ya ce" kai Nasir Alhussen ,dama kana duniyar nan"?




Nasir ya saki fuska kamar bashi bane mai nukufurci nan yace"ya akayi ne dini, inanan wallahi, kace har ka fara aiki kai"




"Dr dini ya saka dariya gami da rungume Nasir din yace"gaskiya naji dadin ganinka Nass ,sosai kasan bayan shekaru biyar da suka wuce da rabuwarmu a america,na dawo nan na karasa karatuna a jami'ar bayaro wallahi to ban dade da kammalawa mahaifina ya samamin aiki a wannan asibitin, dama kai ai ka dauko karatu mai zafi sosai ,ina fatan duk ka kammala"?




Cikin sakin fuska Nasir din yace" sosai kuwa,kasan duk abinda nasa agaba Allah yana taimakona, yanzu zancan da nake maka ma ranar Monday zan fara aiki a sabon asibitina,an kammala komai, da komai,




"Alhmdullhi na taya ka murna mutumina bukatar ka ta biya, Allah yasa a fara a sa'a


Nasir ya bashi hannu suka tafa ,suna dariya, Dr dini, ya kalli Maryam dake rabe a bayan Nasir tana zare ido,yace"kai! Mutumina kace kananan kana shagalinka"




Nasir ya dinke fuska ,yana nuna masa dady, nan da nan Dr dini, ya shiga hankalinshi domin kwata kwata ya manta da dady, dady kuwa duk yana kallon su, bai ce komai ya wuce gurin Anwar dake kwance ,yana kallonsu wato Nasir bashi da mutumchi , wallahi sai ya tona masa asiri gurin mahaifinshi.
[05/06, 19:00] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*




*68*
Dady ya
karasa kusa da Anwar din gami da dafa kafadunsa,yace"sannu Anwar,wato kun girma,ba kusan kun girma,har yanzu Baku dai na shirme,ba ko"?






Anwar ya ya mutse fuska yana kokarin mikewa zaune, yace"dady , a rayuwata babu wanda ya tabayi min wulakanci irin wanda Nasir yayi min dazu,amma ko dame yake taqama dashi wallahi sai na rama"




Dady yace"wannan kuma abinda ya shafeku ne, babu ruwana kuje Ku kashe kanku ,sai dai duk Wanda yayi kisa a tsakaninku ,to kar ya saka sunana, yanzu abinda nakeso dake ,kagayamin mai nene ya haddasa wannan rigimar"




Anwar ya ya mutse fuska yana jin radadi a jikinshi yace"dady ka tambayi Maryam duk zata fada maka dalili,yarinyar nan tun safe kuke nai manta ,ko"?




Dady yayi saurin daga kai gami dacewa kwarai kuwa,mai yafaru"?






Ya zakuda kafada,gami da nuna Nasir da hannunshi yace"to ga Wanda ya sace ta nan ya kaita can guest house din shi da gina can bayan gari,inda yake kai"yan matanshi, can ya kaita zai lalata, dama ya Dade yana hakonta,shine na gan ta tafito daga gurin tana kuka, nayi sauri na sata a mota na, shine fa ya biyo mu wai sai ya kashe ni"
Dady ,bai yi mamaki ba sabida dama ya zargi haka , ya daka wa Anwar din tsawa gami da cewa ,"ka fadamin cewar Ya keta mata haddi kokuwa,mutukar kayi min karya domin kare shi ,kai dashi sai nayi shari'a daku"






Anwar ya tsorata da ganin yadda dady yake huci yace"Dady waqa abakin mai ita tafi dadi ga Maryam din nan ka tambaye ta,zata fada maka komai"




Ya juyo yana fuskantar Maryam din yace"hakane maganar Anwar ko kuwa"?


Maryam ta diririce batasan sanda ta daga kai ba




Dady yayi salati ya sanar da ubangiji yana bin Nasir da kallo wanda yayi tsaye ,yana kallonshi ko gezau bai yi ba,sai dai abinda ya bashi mamaki bai wuce ,Maryam ba wato ita sharri zatayi mishi,Sam! Hakan bai dameshi ba


Dady ya ce"Nasir kaci amanata kaci amanar malam Ya'u ,to bari kaji wallahi summa tallahi,baka da mata sai Maryam,ka rubuta ka ajiye,




Anwar sai da ya kusa wuntsilowa daga kan bed sabida bai yi tunanin irin wannan hukuncin dady zai yanke ba,


Shiko Nasir ko a jikinshi ,Lallai da akwai rigima mutukar dady yace ,zai aura masa yarinyar ,dan shi yanzu wata irin tsana yake mata , amma can kasan zuciyarshi kishi,yana tsunkulinshi in ya tuno lokacin da Anwar ya danneta a mota,yana wasa da Brest din ta.
Sai yaji kamar ya kashe kansa ya huta.
[05/06, 19:01] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*


*69*




Babu fargabar komai yace"dady ka kwance wannan rantsuwar taka, kasan halina in nace banason abu ba na so sabida in ka ce lallai sai na zauna da yarinyar nan ,zakaji kunya sabida yadda na tsaneta haka na tsani mutuwa ta bana kaunar in bude ido in ganta,






A fusace dady ya tsinka masa mari,ya ce wato ina fada kana fada ko Nasir,turawa sun bataka da rashin kunya,ko su ai da suka Baku "yancin kai,ba sai wa iyayensu rashin mutumcin da kake yi min Nasir,nafada na kara fada mutukar ni na haifeka ,to baka da matar Aure sai Maryam,in yaso in an kai maka ita ka kashe ta,dan naga alama zaka'iya




Dr dini dake tsaye yana sauraronsu ,sai yanzu yafara gane inda maganar take ,sai ya ruqa bawa dady hakuri yana tausar zuciyarsa ganin yadda ya hasala,sai fada yakeyi.




Nasir na tsaye kanshi ,a kasa yayin da ya zube hannunwanshi cikin aljihun wandan dake jikinshi 3 qutar ,ranshi yana masa zafi mutuka ,tunda yake da dadynshi bai taba fudda hannu ya mareshi ba tun korociyarshi,kawo wa girmanshi, amma yau in baiyi qarya ba, yau ya mareshi sau uku a kan yarinyar da bai San asalinta ba,




Fuskarshi a murtuke ya ke kallon dady dake ta balbala masa fada,yace"dady ,kasan bana karya ,bana boye abinda yake zuciyata, nace kar ka kulla wannan lamari ,ok kai ne a ciki ,duk abinda ya biyo baya kar ka tambaye ni yana gama fada yayi nufin barin dakin ranshi a mugun bace.






Dady ya bishi yana zagi,yace "duk abinda zakayi kaje kayi,aure kai da Maryam babu fashi,na fada maka,idan andaura auran ka kasheta ,kagani in ban sa an kasheka ba kai ma, zanga abinda kake taqama dashi,ka lalata yarinya ,daga baya ka kawowa mutane maganar banz.....kuka Maryam ne ya katsewa dady Fadanshi,ya waigo a fusace,gami da cewa"Maryam in dai ina raye bazaki wulakanta, zan cika Alkawarin da na daukarwa mahaifinki tun bakizo duniya ba






Da rarrafe ta karasa kusa da dady din ta ruqumqume kakafunshi tana gursheken kuka, tace"dady please ka janye wannan maganar da kafada a kai na da Uncle, dady ka dai na zaginshi kana ai batashi, dady uncle yafi mu gaskiya, fa tun da yace bayaso kar kayi masa dole"
Ya buga mata tsawa gami da cewa"rufe min baki shashashar yarinya ,kawai ,kema tsoro yake baki,ya cuceki ,kina rufa masa asiri,baxan janye ba,duk abinda zakuyi kuyi,kinji na fada miki"


Maryam na kuka tana rokan dady a kan irin zagin Nasir din da yakeyi ,tace"dady Uncle bai yi min komai ba asali ma yaje taimakona ne, lokacin da wannan can yayi nufin cutar dani a motarshi,tafadi maganar tana nuna Anwar da hannunta .




Dady ya buga mata tsawa a karo na biyu yace" ki kiyaye ni nafada miki ,ni zaki fadama halinshi, Anwar bazai yi masa sharri ba, sabida yasan halinshi,idan kema zaki bijeremin kamar yadda yayi min shikkenan,nasan dai tarbiyarki ba irin tashi bace,




Tausayi dady ya lullube ta sosai tace"dady kayi hakuri bazan bijirewa umarninka ba,Amma ina rokan alfarma ka janye maganar hadamu da Ancle nayi maka,alkwarin yi maka biyyaya ga duk namijin da kazaba min ,amma ba Nasir ba.




Dady yaji babu dadi da jin furucin Maryam zuciyarshi tace"wata kila itama yarinyar tana gudun mugun halin danka ne,shiyasa take kuka,kar ka shiga hakkinta,




Jiki a sanyaye ya kalleta yace"ok naji maganarki Maryam, kiyi shiru kin jiko bazan cutar da ke ba domin jin ki nake tamkar yar da na haifa a jikina, kiyi min alfarmar auran Nasir kinji ko, zuciyata tana bani a kwai alkairi a auranku sosai,kece zaki zama silar kintsuwarshi"
[05/06, 19:01] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*




*70*




Maryam ta mike tsaye tana share hawaye ,tace"dady kai ne zaka dinga yi masa addu'a dady ka dai na yi masa mugun baki,domin bakinka yana da dafi a gareshi , kasan shiriya ta Allah ce"




'To
Maryama na dai na, kinji dama duk a kanki ne,abinda nakeso dake shine kifadamin gaskiyar abinda ya afku a tsakaninku dashi,shin maganar da Abokinshi yafada haka take a kanki"?




Maryam bata iya karya ba,nan ta zayyanewa dady komai tun lokacin da tafito daga gida ,da yunkurin cutar da ita da Nasir din yayi Allah ya taimaketa ta gudo,ta kare maganar da cewa,amma Sam baiyi min fyade ba kamar yadda kake nufi dady"






Dady yace"na yadda da duk abinda kikace Maryam domin ba kya karya ke sabida haka na janye maganar da nafada a kanki,ke da Nasir din ,bazan miki dole ba,kwanaki Abdul latif yaron kanina yazo min damaganar yana son ya aure ki ,nace ya bari in sanarwa da mahaifinki tukkuna ,Na lura dama ke dashi kuna shiri ko?






Maryam ta sunkuyar da kanta cikim jin kunya. Ta daga kai alamun haka ne dady yayi murmushi yace"To masha Allah ,Allah ya nuna mana,ke kuma Allah yayi miki albarka"






Anwar ji yake tamkar ya kashe dady sabida tsabar bakinci ki yana iko da abinda banasa ba, ai yarinyar ba"yarsa bace ,ba "yar waninsa ba ,da zai riqa yanke hukumci a kanta,Abdul din banza da hofi,ko Nasir ne ya aureta ba yajin zai iya hakura batare da ya kashe ,shiryawar dake damunsa ba








Ya zakuda ,yanawa dady wani irin kallo na raini,yace "haba! Dady wannan ba girmanka bane,eh!! Yawa!! Fa kakeyi kakyale yarinya ta mori kuruciyarta,kai tsaye zakace zakayi mata aure, gaskiya in hakane nine yafi dacewa in aureta ,sabida Nina fi Kowa sanin ta sabida haka ka cire hannunka daga kanta ,tunda dai ba "yarka bace!


Cikin rashin kunya da rashin mutumchin da suka saba Anwar yakewa dady magana




Dady mamaki ya kasheshi yakasa furta komai ,Lallai dama hausawa sunce naka shike ba da kai,yanzu inda Nasir na ganin girmanshi ,ai Anwar bazai sami kafar zaginshi ba, ranshi yayi mugun baci,bai ce komai ba ya nufi hanyar fita daga dakin
Babu zato Anwar yaji saukar mari! A kuncinshi, Maryam ce
Sai huci! Take dama a kufule take dashi.


Ya dago kanshi ,cikin sauri yana mamakin ta ,idonta masu kama dana mage ta zuba masa tana watsa masa wani mutsiyacin kallo.
Tace "ko da maza sun kare a duniya bazan taba auranka ba ,Dan iska macuci azzalimi ,ba gwaramin Uncle din sau dubu ba a kanka, to bari kaji ,abinda bakasani ba dady yana da iko dani ,ba kamar yadda kake zato ba, duk abinda ya zartar a kaina da ni da iyayena,daidai ne sabida haka ,duk abinda ya umarce ni dashi ,shi zanyi,tana gama fadin haka,ta sakai ta bi bayan dady din.






Anwar ko ya jima hannunshi dafe da kuncinshi ,yagaza tabuka komai ,tunani yakeyi ya'akayi har ya tsaya yarinyar nan ta mareshi,lallai ta tarowa kanta bala'insa da sharrinsa sai ya kulla mata!! Sai ta gwamace ba'a haife ta ba.






Babu motar Nasir a gurin tuntuni yayi tafiyarshi, sabida haka Nura drevar yana ganin fitowar dady ,yayi sauri yaje ya bude masa mota ya shiga ,yana jin wani Bacin rai a jikinshi,yayi sanyi da'alama hawan jininshi ne yakeso ya tashi Maryam ta shiga bayan motar itama dady yabawa Nura umarnin tafiya,Nura yace",rankaya dade zan kai office ne"?




"Aa Nura muje gida kawai nafasa zuwa ,bana jin dadin jikina,baya gahaka ma lokaci ya kure,mubarwa gobe, kawai"






Nura ya ja motar suka bar gurin yana mamakin abinda ya canja dady ,yanzu yanzu sabida ya lura dashi ranshi a bace yake,




Maryam ma haka, sai ta rika bashi hakuri, tamkar ta fashe da kuka.




Yace"nayi hakuri Maryama karkiyi kuka kinji ko,muje gida ,ki huta ,Allah zai sakamiki duk Wanda ya cuceiki






Maryam tafashe da kukan da take boyewa tace"Dady nifa nayafewa Uncle sabida dama babu abinda yayi min Uncle ba ya taba laifi a gurina, don Allah ka daina fadar haka,komai ya wuce ka kwantar da hankalinka"
[05/06, 19:01] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*




*71*




Haka suka sauka gida Maryam na tausar zuciyar dadi,da kalamai masu sanyi,ya riqa shi mata albarka, Nura nayin parking ya fito da sauri yazo ya bude masa kofa ,dady ya yunkura ya fito yanajin wata hajijiya a kanshi,kan kace kwabo ya yanke jiki yafadi a gurin ,yana fidda numfashi sama sama,Malam Ya'u dake kokarin mayar da get ya rufe ya tawo da sauri,yana fadin subahannallahi Alh" ya karaso gurin suka kama dady shida Nura ,suka shiga dashi gida,bai San inda kansa yake ba,Maryam ko sai kuka takeyi sosai




*innalillahi wa'inna ilayi rajiun*
Shine abinda Malam Ya'u yake ta nanatawa ,sai gumi ne yake karyo masa
Momy na zaune cikin kujera tana duba wani littafi ,taga an shigo mata da dady ranga ranga, hankalinta ya tashi ,ta mike da sauri,har littafin yana faduwa,kan fisu karaso ta karasa ,tace"Nura lafiya mai yasameshi,lafiya lau ya fita fa"




Nura yace"wallahi Hajiya kalau muka fita dashi kamar yadda kika fada sai yanzu kuma naga ya fito daga asibitin da muka akai Anwar abokin Nasir hankalinshi a tashe"


Cikin gigita Momy tace"mai yasami Anwar din ,ina My Son ,ta na nufin Nasir,


Nan Nura ya warware mata komai da abinda yafaru,Momy ta fashe da kuka ,tana kallon Maryam tace "yanzu da abinda zaku saka mana dashi kenan Malam Ya'u, yarinyar ka ta zame mana annoba, yanzu a kwai abinda dady zai nema a gurinki ki kasa yi masa"




Malam Ya'u ya diri-ririce sabida bai fuskanci inda maganar tata ta dosa ba,yace Hajiya ban fahimci maganarki ba"




Momy na kokarin hawa sama cikin tashin hankali tace"ai baza ka fahimci komai ba Malam Ya'u mungode da wannan Abu"




Dady yana ta kokarin magana ya kasa sabida yadda bakinsa ya harde maganar bata fita sosai , Maryam takarasa kusa dashi tana kuka wai ko zataji mai yake cewa,duk da haka bata fahimchi komai daga abinda yake fada ba.




Tana kuka ta rirruqe masa kafafu tace"dady ka yafemin in nice na bata maka rai ,wallahi zanyi maka biyayya dai dai gwargwado,


Nan Malam Ya'u ya fahimchi Wato Maryam din ce dalilin bacin ran sa, bai yi wata-wata ba ya gaura mata mari! Yace "wato kece kika haddasa masa tashin ciwonsa ko, abinda tun kafin kizo duniya bai tashi ba,sai yanzu ta dalilinki ,mai kikayi masa wanda yasa ranshi ya baci wane umarni ya baki ,da kika kasa bi,kin cika butulo Maryam ,mutumin da ya hana kowa fita nemanki yace,shi zai je ,shine zaki saka masa da haka!




Maryam kuka take kamar ranta zai fita tanabawa Mahaifinta hakuri,shiko sai faman fada yake Mata,tun da take dashi ,bai taba dukanta ba,ballantana ya yi mata fada,sai yau"


Cikin tsawa yace"kifadamin mai nene dalilin da ya haddasa masa wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login