Showing 42001 words to 45000 words out of 87228 words
Chapter 15 - YARO DA KUDI Complete Hausa Novels by Binta Umar Abbale .txt
tashin hankalin"?
[05/06, 19:01] +234 808 996 5176: *YARO DA KUDI*
*72*
Kafin Maryam tace komai Momy ta sauko daga sama hannunta ruqe da kwalayen magungunan dady,ta mikawa Nura, tace bude ka bashi ko kallon inda Malam Ya'u yake ba tayi ba,taje ta dauki wayarta ,tana neman number Nasir,hankalinta a tashe,
Fitowarshi kenan daga toilet ,ya ga kiran Mom din kin daga wayar yayi har ta katse wani kiran ya kara shigowa nan ma yaqi dagawa sabida yasan dady ya fada mata duk abinda ya faru,a tunaninshi ,za tayi masa fada ne,
A takaice dai sai da momy ta kira sau kusan biyar sannan ya daga wayar kafin yace komai tace"ka kyaura Son" kaji ko wato ni zaka ki dagawa waya ,ko babu laifi, ina so duk inda kake kazo yanzu,dadynka babu lafiya ciwonshi ya tashi,gashi nan bai San wanda yake kanshi ba"
Dama abinda nake ta gudu kenan"
Gabanshi ya fadi,! Amma sai ya share yace"mom kin manta ya kore ni a gidanshi ne,banaso inzo wani Abu ya faru ni dashi,sabida dama dazu ba rabuwar kirki mukayi ni dashi ba"
Momy ta sanya kuka tace"wato har yanzu kanaan kan vakanka ko My Son,sai kace bakasan halinshi ba,da fifita bare a kan nashi kayi hakuri kazo kaji ko"
"Owk Momy ki dai na kuka dan Allah ganinan zuwa kinji kar inzo kina kuka,yaya jikin nashi"?
"Yananan bai San wanda yake kansa ba kasan dama in ciwon nashi ya tashi haka yake masa"
Nasir ya kashe waya cikin sauri ya saka ,kayanshi ya fito ya shiga motarshi,bai nemi rakiyar su Joy ba shi kadai ya tafi ,yana bala'in kaunar mahaifinshi sosai kawai halinshi ne ba ya so ,dady n nashi fadanshi yayi yawa gami da shiga abinda babu ruwanshi shiyasa ,suke yawaita fada dashi,
Masu tsaron gurin ne suka bude mass get din ya shiga yayi parking gurin a je motoci, ya fito ,yana amsa gaisuwarsu ,sama-sama ya shige ciki.
Dady ya gani kwance kashir6an kamar baya numfashi, duk sunyi tsaye a kanshi,yay in da Maryam take gurfane kusa da kafa fun shi,ta rirruqe masa kafafau tana kuka,
Hankalinshi ya tashi ,da sauri ya karasa gurin,ya fincike Maryam din ya wurgar da ita gefe guda. Yana zaginta da turanci yace"idan so kike ki kashe shi ai ba ta wannan hanyar ba ,sabida kowa zai gane ki, Ke mayya ce,ubanki ne shi da zakizo ki rirriqe shi,ko kina da alaqa dashi,wallahi duk maytarku kurwar dady daci gareta"!!
Maryam na kuka ta kara komawa kusa da dady domin Sam bata fahimci abinda Nasir din yake nufi ba burinta kawai taga dady ya mike ,yana magana tafada masa cewar ta 'amince da auran Nasir din,domin duk a ganinta ,ita ce dalilin da ta haddasawa dady tashin ciwonsa
Dady yana kallon Nasir yana motsa baki ,sabida tun lokacin da yaji muryarshi ya bude ido, yanaso ya fada mashi ya dai na zaginta
Malam Ya'u kam hankalinshi ya tashi jin furucin Nasir din a kan Maryam shifa duk sunbi sun rikitashi ya kasa fahimtar komai
Nasir ya kamo kafadun dadyn nashi idonshi jazir sai sauke ajiyar zuciya yakeyi ,ya sanya gefan rigarshi yana goge masa gumi, ya kalli Nura wanda ke tsaye riqe da kwalayen magani,yace "dauko min fresh milk a frij"
Da sauri Nura ya tafi,yaje ya dauko. Nasir ya balle Murfin ,ya fara kokarin sawa dady Abaki,
*innalilahi wa'ina laiyi raji'un*
Yadda yake saka masa fresh milk din haka yake dawo wa sam bayq zama a bakinshi ,ballanta a saran zai zauna a cikinshi, Momy tuni ta karaya da dady sai kuka takeyi ,shima Nasir din daurewa kawai yakeyi,
Dady ya kama hannun Nasir ya riqe tamau!! Yana kallonshi, shima nashi hannun ya riqe ,yace"dady please ka tashi muna bukatar ka,ga Momy na tana kuka,dady in nine na bata maka rai kayi hakuri ,bazan kara kaji,yadda ya fadi maganar sai ka tausaya masa
Alamun tsayuwar motoci suka riqa ji ,dama Momy tuni tayiwa"yan uwanshi waya aiko sai ga su sun shigo farlo din hankali a tashe, Mahaifin Hanifa ,ya bugawa Nasir tsawa yace"burinka ya cika ,Nasir babu tamtama kai ne ka yi silar tashin ciwonshi ,kasan sarai ba ya San damuwa,in ka kashe shi sai nayi shari'a da kai"!
Nasir da ba'a fada masa ya kyale ,ya kalli Uncle din nashi sheqeqe ,yace"in har dady ya mutu ,to kwananshi ne ya kare bawa bai isa ya kashe wani ba, in lokacin mutym yayi dole ya mutu,sabida haka kar ka kuma dora min,ai ba Ku fini jin ciwonsa ba"
Dukkaninsu mamakinsa suka yi to amma dake sun San halinsa ,babu Wanda yakara cewa ufan a cikinsu,suka kama Dan uwansu , da nufi tafiya asibiti
[06/06, 00:44] +234 808 996 5176: [15/05/2019 1:57 PM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*
*73*
Hankali a tashe Malam Ya'u ya karaso gurin da nufi kama Alh Huseen ,Nasir ya daka masa wata muguwar tsawa tamkar bai san daga inda yake ba tace"karka kuskura ka ta bashi Malam ,duk wani surkule irin naku na fulani kaje ka kwance ,shi sabida dama na lura tun tuni kuka asirce dady ,shiyasa kwata-kwata bayason Bacin ranku kai da iyalinka, sabida haka ka rubuta ka aje ,zamanka a gidanan ya kare"
Mahaifin Hanifa yace"kayi min dai-dai Nasir dama nima tuntuni nake zargin haka, dole subar gidan nan,ni ina zarginsa gurin rashin lafiyar dan uwanmu,dole ya bar gidan domin ba mu hada zuri'a dashi ba ,
Malam Ya'u yayi tsamo-tsamo tamkar Wanda a ka watsawa ruwa a jiki ,sai gumi ne yake zuba a jikinshi, lokaci guda ya muzanta,bakinshi yana rawa yace"ku fahimce Alh babu wannan abu mai muni a tsakanina da Alhji Huseen sai alkairi,uba na dauke shi ,babu cutarwa tsakanina dashi sabida yayi min abinda bazan taba mantawa ba a rayuwata"
"Rufe mana baki dattijon banza da Wofi"!! Nasir ya katseshi cikin tsageranci ,yana masa wani banzan kallo"
Maryam ranta yayi mugun baci! A gabanta Nasir yake kiran Ubanta da dattijon banza Lallai bazata lamunta ,dole a kwai ranar da zata amayarwa da uncle duk cin mutumchin da yake mata
Duk wannan abinda yake faruwa Dady ya naji ,ranshi yana mugun zafi,da irin rashin kunyar da Nasir yakeyi,anrasa mai tsawatar masa ,a cikin "yan uwanshi,sabida sunajin tsoransa,wanan yana nuna cewar ko mutuwa yayi haka zasu wofintar da jininsa,tabbas zumunci bai ce haka ba tunda shi ba haka ya musu ba
[15/05/2019 2:18 PM] Binta U Abble: Tari! ne ya sarqe shi ya riqayi babu kakkautawa ,nan da nan suka mayar dashi suka kwantar,Nasir ya nufi frji da sauri ya ciro ruwa mara sanyi sosai yazo ya na sama a baki,
Dady ya ki karba ,idanunshi tsaye kan Malam Ya'u, yana kallonshi ,da kyar ya daga hannunshi da yayi masa bala'in nauyi yayi masa alama yazo gareshi ,Malam Ya'u ya karasa kusa dashi jikinshi a sanyaye,yace "sannu Alh Allah ya baka lafiya"
Dady ya bude baki da kyar yace"Malam Ya'u ko bayan babu raina ban amunce ka bar gidanan ba ,shashen da kake ciki na mallaka maka shi ,halak malak, sannan , inaso kayi min wannan alfarma ga amanar Nasir nan na damka maka ita a hannunka kar ka wofintar da shi,ka cigaba da yi mishi addu'a Nasir naka ne dama can "
Malam Ya'u yace"na karbi Amana Alh ko da ranka ko babu jinnika ba abin gudu bane a gareni,in sha Allahu zaka tashi ka cigaba da rayuwa, nagode da karamchin ka a gareni ubangiji Allah ya biyaka da aljanar fiddausi"
Cikin zuciyarsa yace ameen,sannan ya kamo hannun mahaifin Abdul latif ya ruke gam! Yace"ni Hussen in dai na isa da kai da abinda ka haifa ,ina so ko bayan babu raina ,ka daura auran Abdul da Maryam,domin ina sha'awar hada zuri'a da ta Ya'u, da naso Nasir ne ya samu wannan garabasa domin auran kamilar mace irin Yarinyar dace,dukkaninku baza Ku fahimchi haka ba sai nan gaba, Nasir ya fadamin qeqe da qeqe ban isa dashi ba ,kuma bazai bi umarnina ba, sabida haka da wannan bakin cikin zanmu a rayuwata ,Nasir nagode nagode, nagode, tari ya rurnikeshi,!!
Hankalin Nasir yayi mugun tashi, kaddai ,dady ya sauki maganar su ta dazu da zafi haka,har ta janyo masa tashin ciwonsa,shifa yafadi hakane kawai dan ya bata masa rai, amma kwata-kwata-ba gaskiyar abinda yake zuciyarshi ba kenan,
Kafin ya dawo daga tunanin nashi,yaji Momy ta rusa ihu,yayi da Mahaifin Mubina,yake Fadin *innalillahi wa'inna ilayi raji'un*
Dady ya amsa kiran Ubangiji
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [16/05/2019 9:26 AM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*
*74*
Nasir ya fasa wani ihu yayi kan dadynsa ya ruqunqume shi,kuka ya kece masa ,cikin dimuwa da fitar hayyaci ,yake fadin *innalillahi wa'ina ilayi raji'un*
Dady kar ka mutu, bakace ka yafe min ba, dady ka tashi in fada maka abinda yake zuciyata duk kanin abinda nafada maka abaya ,karya nakeyi wallahi,dady ina mutukar kaunarta ,har a cikin zuciyata,dady in kayi min haka ina zan sanya rayuwata pls dady karka yimin haka rayuwata nima tazo karshe ban da amfani a duniyar nan,kafadamin mai kake bukata nayi maka shi yanzu!!! Nasir kuka yake sosai da sosai ,duk ya gigice yafita hayyacinsa, in banda gumi babu abinda yake zuba a jikinsa,yabi ya rungume gawar dady ya hana kowa ya kusance shi,da kyar! Malam Ya'u ya karaso gurin gami da dafa kafadar Nasir din cikin dauriya da jajircewa ya ce"kayi hakuri Nasiru Allah Ubangiji ya amshi Alh cikin aminci da yaddarsa, ya mutu yana kalamar shahada,yanzu babu abinda yafi bukata da kai sai addu'a kaji"
Nasir ihu! Yakeyi yana sambatu da'alama kwakwalwarsa a lokacin ta daina aiki,domin kwata kwata bai ji abinda Ya'u yake fada ba.
Maryam ko yanke jiki tayi tafadi, ta suma!!!
Kafin kace kwabo gidan ya hautsine da hayaniya, tuni Nura ya fita ya sanar da Sucurty da ke waje abinda ke faruwa a cikin gida,
Aunty ko tana bangaransu duk wannan abin da yake faruwa bata sani ba tana kchin tana hidimar Dora abincin rana,taga Malam ya shigo mata da yarinya ranga ranga,
Salati ta tafka tana tambayarsa abinda ya faru ,sabida dama tasan da batan da Maryam din tayi na awanni biyar da suka wuce,Malam Ya'u yace"babu lafiya Suwaibah ,muna cikin tashin hankali,Allah yayiwa Alh rasuwa
Gigicewa aunty tayi domin duk a zatonta mahaifinta yake nufi ,sabida tasan shima ba shi da koshin lafiya.
Kuka ta fashe dashi tace "shikkenan baba wahala ta kare"
Ganin bata fahimci abinda yake nufi ba,yasa ya tsaya yayi mata bayanin komai,aunty ta rika salati tana sanar da ubangiji,da gudu tayi dakin ta zaro hijab tana ,nanata innalilahi a fili,take tambayar mai ya sameshi,shiru Malam yayi mata shi dai yana ta tasbihi cikin zuciyarsa, tare suka shiga farlou, har yanzu Nasir na rungume da gawar Mahaifinshi ,yanzu. Ya dai na zubar da hawayen sai kukan zuci yakeyi kwata kwata ya hana kowa kusantar gawar ,har Momy dinsa, dake kusa dashi ,ita kuma a lokacin Allah ya sanya mata juriya,kwata kwata idanunta sun bushe ,babu hawaye ko days,amma kana kallonta kasan tana cikin dimuwa! Da tashin hankali
[16/05/2019 9:43 AM] Binta U Abble: Tace"My Son shiyasa kullum nake fada maka ka kiyaye bacin ransa ,sabida kasan yana da lalura,kaki ji ,ko ka gani yanzu yazo ya tafi ya barmu mai zakace min ,my son ,mai zakace min!!
Momy tafada muryar ta tana karkarwa,
Aunty tazo ta dafa kafadar Momy tana zubda hawaye tace"Hajiya Kiyi hakuri kinji,dama Allah ya kaddara lokacin Alh yayi yanzu bawa bai ta kashe wani ba face sai lokacin sa yayi, kiyi hakuri ,kiyi mishi addu'a Allah ya jikanshi Hajiya Allah ya sanya mana hakurin jure rashinsa da mukayi.
Sai lokacin hawaye ya kecewa Momy ,tafadi a gurin ragwajb ,tana kuka, cikin tashin hankali da damuwa take fad in"innalillahi wa inna ilaihi raji'un
Aunty tazo ta dafa kafadar Nasir tace"dan gidan aunty kayi hakuri kaji ko ka fawwalawa Allah kowa na hakane,don Allah ka saki kyale Alh ayi masa suttura ,duk wannan abinda kakeyi bazai sa dawo mana dashi ba"
Nasir ya zubawa aunty ido yana kallonta ,bakinsa dai motsi yakeyi ,da kyar ya samu ya finciko maganar ,yace"aunty dady ya mutu,!! Wancan yarinyar ,ce tayi sanadi ni babu ruwana,sabida lafiya kalau na tafi na barshi da'ita,sabida haka ,duk yadda zanyi sai nayi gurin ganin na wulakantata ,tunda tayi sanadin kashe min mahaifi.
Aunty Sam!! Bata fahimchi maganarsa ba ,ta lura kwata kwata baya cikin hankalinshi,tace"eh nima Na amince Auncle ka dauki mataki kan wanda ya zalunce ka,amma yanzu abinda nakeso dakai ka saki Alh ayi mishi suttura kaji ko"
Nasir yayi zakwado!! Yana bin dady dake rungume a jikinshi da kallo vakinshi sai motsi yakeyi,yanzu wai da gaske ne dady shi ya mutu !! Ina karya ne!
Abinda ya fada kenan da karfi!! Sai ya fara Jan numfahi!! Da karfi ,kan kace kwabo ya afka kan dady din nasa ya suma!!!
Guri ya hargitse da salati,Ya'u yazo ya janye Nasir ,daga kan dady,yayinda "yan Uwan dady din suka samu damar janye dan uwansu,domin sutur tashi,
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [16/05/2019 8:45 PM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*
*75*
Momy ta kidime tayi kan Nasir din tana kuka sosai ,tamkar wacce tasamu tabin hankali take cewa "My son kai ma zaka tafi ka bar ni ne, ta kamashi sai jijjigashi takeyi tana kuka da sauri Malam Ya'u yazo da ruwa mai sanyi cikin gora ya bude ya watsa wa Nasir din ,cikin zuciyarsa yana ta nanata Kalmar innalilahi
Nasir ya mike a zabure!! yana dube dube babu dadynshi a gurin ya mike da sauri ,jiri! ya debeshi ya yar kan kujere ,sai ya dafe kanshi da hannunshi guda,ya na furta,kalame "Ya Allah!!
Momy da aunty sai tausarsa sukeyi,kar ma dai aunty taji labari,shidai idanunshi suna rufe,kwata-kwata hankalinshi da tunanunshi baya kansu,zuciyarsa take fada masa kayi rashin mahaifinka har abada Nasir,sai ya karyar da wuyanshi jikin kujera ,hawaye yana zirarowa daga idanunshi da suke rufe,
Kankace kwabo mutuwar Alh Huseen ta karade birni da kewaye sabida dukkanin wanda ya kwana ya tashi a garin kano da kewaye babu Wanda bai sanshi ba idan ma baka taba ganinshi ido da ido ba to za ka ganshi a jarida ko gidajan TV ko tashoshin yada labarai,sabida yadda yayi suna gurin taimakon marayu da nakassasu gami da taimakon talakawa ,Sam dukiyarshi bata rufe masa ido ba sabida haka ,kofar gidan damqam! Take da jama'a duk suna jira a fito dashi domin suyi masa rakiya zuwa ma kwancinsa na gaskiya ,sai jaje sukewa juna suna ta fadar alkairinsa, dayawa daga cikinsu hawaye suke sharewa domin sun gaza daurewa sabida sunsan ba karamin rashi sukayi ba,
Addu'oi Ya'u ya dukkufa yana ta tofawa Nasir ,duk domin ya samu zuciyarsa ta sanyaya, cikin hukumcin ubangiji ya bude idonshi ,ya na binsu da kallo daya bayan daya, kimanin minti biyu,ya mike tsaye cikin nutsuwa ,aunty tayi saurin riko hannunshi,sai Malam Ya dakatar da ita ,yayi mata alamar ta rabu dashi, kai tsaye dakinshi dake farlo ya nufa ,ya bude ya shiga gami da rufo kofar,Momy tabishi da kallo zuciyarta ,tana tsinkewa
Toleit ya bude ya shiga ya dauro alwala ya fito ya kwabe kayan jikinshi, ta cire sarkokin da suke wuyanshi,hade da barimar dake manne a fatar kunnenshi,ya bude katuwar siff dinshi,ya ciro wata jallabiya fara kar da ita ya sanya a jikinshi bayan ya sanya gajeran wando,ya dauki carbi mai ma dan nai
Lokacin da ya fito anfito da dady,"yan uwa suna ta yi mishi addu'a Momynshi na gurfane gaban gawar tana kuka sosai da sosai, cikin jarumta yazo ya janyeta ya zaunar da ita kan kujera, bai cewa kowa komai ba,yafara kokarin daukar dady,ganin haka yasa jama'ar da suke gurin suka mike dama shi suke jira ya fito yayi masa addu'a ,sai suka kama masa makarar ya Dora a kafarshi, suka fita bakinshi dauke da addu'oi iri-iri yana nai mawa dadynshi rahamar Allah.
[16/05/2019 9:05 PM] Binta U Abble: Nan Aunty ta zauna ita da saura jama'a suna ta tausar Momy,kwata-kwata ta manta da Maryam da a ka kai mata ita ranga ranga,sai ganinta sukayi tafado farlo din tamkar zautacciya sai zare ido takeyi dama ga su tubarkallah,
Ta rika bin ilahirin farlou n da kallo, cikin zuciyarta take fadin Allah mafarki takeyi ba gaske bane abinda ta gani cikin mafarkin ta.
Mata tagani zazzaune ko wacce cikin hijabi ga carbi a hannu,da kyar! Ta samu ta furta,kalarmar da ta fito daga bakinta, Tace"aunty wai da gaske dady ya mutu,wani mummunan mafarki nayi,
Kafin aunty tace komai,Momyn Mubina ta daka mata tsawa ,cikin tsantsan kyama tace" waye sa'anki a gurin nan da zakizo kina mana maganar banza da wofi ko an fada miki ana wasa da mutuwa ne,shegu mayu! Kun kasheshi kun huta ,mutsiyata, kawai masu mugun abu, sarakan surkulle, Allah wadaran talaka Wanda zaka dauko shi daga rana kai ya mai da kai cikinta, dukiyar Alh kukewa to Baku da gado da ita ,ehe!!
Maryam tayi tsaye bakin kofa tana ji da kallon ikon Allah, ita kwata kwata magangan nun Momy Mubina sam basu dameta ba,illah jin ciwon rashin dady da radadin yadda takasa bin umarninsa na auran tilon danshi wato ancle din ta,har ya koma ga ubangiji ,yanzu ita yaya zatayi da rayuwarta,gashi tanaji a gabanta dady ya bar wasiyar cewar a daura mata aure da Abdul latif duk da tasan ,ba haka yaso ba a zuciyarsa ya mutu ne da burin ganin ya aura Mata Uncle
Hajiya Rakiya wato mahaifiyar Abdul kenan ta rika watsa aunty mugun kallo na tsana, sai tabe baki takeyi,sabida dama can ita macace mai mutukar izza gami da taqama,ta tsani talaka Sam! A rayuwarta shiyasa ko inuwa bataso ta hada dashi, macace "yar mulki ko shi Mahaifin Abdul din hakuri yake da'ita.
[06/06, 00:45] +234 808 996 5176: [17/05/2019 4:00 PM] Binta U Abble: *YARO DA KUDI*
*76*
Maryam ta zube nan bakin kofar kuka ya kufce! Mata sosai take yi har da majina,a nan Nasir ya cimma ta, da ya lura ita ce a gurin ka wai ya sanya kafarsa yayi ball da ita,ya yi shigewarsa ciki batare da ya waiwayo ba, ihu ta kurma lokacin da kanta,ya bugu da bango ,ta dafe gurin hawaye wani na bin wani ,dakinsa ya shiga ya fito rike da dadduma ,babu Wanda ya kula a cikin mutanen da suke farlo din ya sakai ya fice Maryam tayi sauri ta bashi hanya ganin yadda ya taho gadan gadan ,
Haka dai akayi zaman makokin dady Auntt da Maryam suna kunsar Bakin ciki gurin mutane domin kowa ya daura mutuwar dady din a wuyansu,gefa guda kuma ga wasiyar da dady ya bari cewar kar su bar gidan,
Nasir kuwa wani irin ya dawo mai shiru shiru sai