Showing 87001 words to 87228 words out of 87228 words
Chapter 30 - YARO DA KUDI Complete Hausa Novels by Binta Umar Abbale .txt
barshi ba,kai tsaye yace mu wuce can gest house dina idan na huta sai muje gurin Momy"
"Ok Boss"
lumshe idanshi yayi yana jin wani irin a jikinshi tsigar jikinshi sai tashi takeyi in ya tuno da wani abu wanda shi kadai yasan ko menene shi
Tony da Giss ne suke ta faman yi masa hira wani ya amsa wani ya share shi kadai ya san abinda yake damunshi tsawon kwanaki bakwai din nan da yayi dauriya kawai yake,amma bazai je ya kashe kanshi ba,tunda shi dai ga yadda Allah ya halliceshi
"Boss mun karaso"
Giss yafada bayan ya bude mashi kofa
a hankali ya bude idanshi wadanda suka kada sukayi jajazir dasu ya fito daga cikin motar,Giss yayi saurin yin gaba yaje ya bude mashi kofa yana jiran karasowarshi,
sai da ya shiga sannan ya bi bayanshi hannunshi rike da karamar jakarshi da ya tafi da ita
bayan ya aje jakar sai ya fito ya barshi domin yaji dadin hutawa
yana zama gefan gado wayarshi ta fara kara
wayar ya kalla ganin Momynshi ce yasa ya dauki wayar yana sauke ajiyar zuciya,
"Momah"
yafada muryarshi kasa-kasa
Itama ajiyar zuciyar ta sauke tace"Myson ya naji muryar ka kamar na mara lafiya,uhum? ina nan zaune ina jiran karasowarka, kace karfe hudu zaku sauka ko"?
Gyara murya yayi ya san halin Momynshi yanzun nan sai ta tada hankalinta, yace"Momy mun sauka, yanzu haka ina gesthouse dina,ina hutawa bayan sallahr magariba zan shigo"