Showing 6001 words to 9000 words out of 87228 words

Chapter 3 - YARO DA KUDI Complete Hausa Novels by Binta Umar Abbale .txt

Maryam din
Kallonsa Nasir yayi yace Sunanta Maryam Ashe?!!




*MRS AHAMAD GWADABE*
[23/04, 14:58] +234 808 996 5176: πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—




*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)




*πŸ…Ώ13*




Eh Ai tun jiya nayi mata hudubah da sunan maihafiya ne.
Ayya sunan Mom dina ne fa Nasir yafada fuskarsa a sake Malam Ya'u yace masha Allah kaga yarinya ta ci sunan kakaninta Allah ta rayata shine Abinda Nasir yace kawai ya ciga da cewa yau saura wata biyu fa in tafi America a can zan qarasa karatuna Cikin fatin ciki Malam Ya'u yace Allah yabada sa'a Nasiru yabada Abinda a katafi naima Dan Allah idan kaje ka kula da tarbiyar ka kar ka dauki dabi'un "yayan Nasara Allah ya tsare mana ka.Nasir yace karkadamu Alaramma in Sha Allahu zamu kiyaye a dai tayamu da adu'a a wan can lokacin idan Nasir yana maka magana sai ka rantse yayi shekaru ashirin sabida nutsuwarsa da yadda yake fitar da lafazi cikin hikima,
Lokaci n da Mom din Nasir taga babyn da Suwaibah ta haifa taji tana kaunar yarinyar Karin farin cikinta jin sunanta a kasawa yarinyar Dan haka shatara ta arziqi ta hadowa baby da uwar ta duk cewar Momyn bata da sakin Fuska da Jan mutane Amma darajar wannan baby yasa tashiga har bangaran su ya'u ta Abin Arziqinta tace ita tanason baby in zasu bata dariya Ya'u yayi yace ai dama takice Hajiya tuntuni Nasir ya karbar miki ko yanzu kikeso sai ki dauka Momy tayi murmushi tace A'a a dai bari tayi kwari tukkuna taga ma karbar nonon mahaifiyarta sannan sai in karba idan na karbeta yanzu yaya zanyi da Aiki na.
Kwarai kuwa hakane inji malam Ya'u yace to Allah ya kaimu lokaci Nan Momy ta tafi ta barsu suna tattauna maganar Ya'u yace ni mai mutannan zasu nema a duniya in hanasu mutukar ina dashi zan basu rai nane kawai bazan iya basu bah Suwaiba tace kwarai kuwa ai duk inda mutanan kwarai suke sun kai sosai.


Kafin suyi Ar'bain Baby Maryam tayi wata irin qiba yarinyar tahada uban kyau kamar "yar turai ko Larabawa a gurin Momy take wuni duk randa babu Aiki duk sanda Nasir ya shi go ya tadda ita A hannu Momy sai yace Momy Wannan Yarinyar kika dauko ? Momy tace gata kuwa kana gani My son Wallahi haka kawai nake son ta Yakan ta6e baki a wancan Lokacin yace kinga ni ko Momy Sam yarinyar batai min Ba Wallahi dariya Momyn take a lokacin tace kai yarona wannan baby n ai tana da kyau maiye laifinta. Daga kafada yakeyi yace babu ruwana da kyanta Momy kune kuke ganinshi yayi wucewarsa ciki har sai Momy ta mayar da ita zai fito yasake suyi hira da ita Sautari zai shigo ya tadda 'ita a bedroom din Momy kwance kan bed tana kuka in Momy na toilet haka zai tabe baki ya juya yafita baya ma karasowa dakin balle ta sa ran zai dauketa.










*MRS AHAMAD GWADABE*
[23/04, 14:58] +234 808 996 5176: πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—






*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)






*πŸ…Ώ14*




Watan Maryam Uku a duniya Nasir ya tafi America karatu tafiyar da ta sauya masa rayuwa ta sauya masa kyawawan halayensa yaje ya hadu da Abokai "yan "yan masu kudi Sosai da turawa su ka koya masa shaye shaye da Neman mata da duk wasu ta'adu na Nasara Abu daya zai ce ya riqe Wanda Allah ya tai makeshi bai yarba sallah ko da Ba a lokacinta bane yanayi baya bari ya kwanta baiyi Ba sai da yafara hankali ne yake yakice komai idan lokacin sallahr yayi yaje yayi sai wata baiwa da Allah yayi masa ta a zumin litinin da Alhamis bai yar Ba domin tun yana gida yakeyi tare da Malam Ya'u to Abin ikon Allah bai dai naba duk shagalarsa ranar littinin da Alhamis sai yayi yake jin dadi,
Shekararshi takwas a can yadawo gida domin Hutu kafin ya koma ya cikashe shakuru hudu Fannin duk wata matsala da take damun mata ya ke karanta Sosai ya ke binkice a kan Matsololin da mata ke Fuskanta ta kowane 6angare kama daga gurin haihuwa gurin daukar ciki sankar Nono sanyin Mahaifa; Sanyi Mara; da shi kanshi HedeQuaetar din Babu Abinda baiyi binkice a kai Ba shiyasa yasan mata iri iri yake yi musu kallon Nasanku ciki da bai kamar yadda yafada Ba ko wace mace yake kwanciya da ita sai ya hango wani Cabin;
Lokacin da yazo gida Maryam tana shekara Tara a Duniya. Yayi mamakin girman Yarinyar sai bai CE komai Ba ko ya shiga bangaran Aunty tashi yasha tar6a sosai ta dinga INA a saka INA a je dashi tayi mishi girki na Mussaman ta aje gabanshi yayi murmushi yace Aunty na Abinci nan yayi yawa fa .tace kaci kabar saura Nasir Lailai girma yazo kaga yanda kazama wani kato kuwa mai turawan suke baka haka,? Yace babu komai Aunty yanzu yaranki nawa ga wani boy nan shima naki ne yafada ya na nuna wani yaro dake kwance kan kujera bazai wuce wata biyar Ba,
Dariya Aunty tayi tana zubah masa Abinci tace Nasir junior kenan ai ta kwaranka ne sunanka a sa bayan tafiyar nasamu yara UK' suna makaranta tare da yayarsu yanzu zaka gansu ai lokacin tashinsu yayi,






*MRS AHAMAD GWADABE*
[23/04, 14:58] +234 808 996 5176: πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—




*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)




*πŸ…Ώ15*


A kwan kafin ta rufe baki sai ga Maryam tare da kannata sun shigo cikin kayan makaranta Nafi'u shine yake bin Maryam sai Miftahu ya kasance ita ce mace kawai a cikinsu Nasir yayi mamakin girman Yarinyar Kallo guda yayi mata ya dauke kai Amma yayi mamakin ganin yanayi idontan nata ya Dan rissina Ba kamar tana jariri yaba Amma fa yananan da kalarsa bai sauya Ba Aunty tace gaka "yan halak Ba dama yanzu nake CE maka zasu shigo. Gyara zama yayi yace Masha Allah Aunty na kin Tara basawa Haka Ashe babu baby girl dina Dariya Aunty tayi tace Allah bai kawo Ba Nasir ka ganta kenan Maryam yace naganta Aunty ta girma yarinyar gaskiya dariya Aunty tayi tace haka kowa yake cewa Sam batayo jikin Fulani Ba ita kam tana da rusheshen jiki Masha Allah ta kalli su Maryam da suke tsaye suna kallon Nasir kamar sun sami Tvi suna mamaki waye wannan domin su kam basu ta6a yin baqo haddade Dan gayu irin shi domin Fatarshi ma Abin kalloce sabida gogewa jikinshi kwata kwata babu datti yana sanye cikin qananun kaya As'useal sai murmushi yake musu Aunty tace kai Nafi'u kai ne kullum mai tambaya ta waye Uncle Nasr yau dai gashi nan a gabanka kun tsaya kuna kallon mutane babu gaisuwa har dake da girmanki tafada tana harararta. Washe baki Nafi'u yayi yakara sa kusa da Nasir ya tsuguna yace sannu Uncle ya hanya kullum Aunty na bamu labarin ka da kirkinka Sai naji nima ina sonka ina son ganinka kullum sai nasa Aunty tayi min labarinka. Dariya Nasir yasa ganin yadda Nafi'u yake zubah sai kace wata tsohowar radio sai kawai ya daukeshi ya daura saman cinyarshi yace yayi boy Naji dadi nima ina sonka daga yau kazama Abokina mu daura ya mika masa ya tsansa daya da sauri ya sanya nasa suka makale da juna suna dariya Nasir nayi mishi irin Gaisuwarsu ta Nigogi da hannu shima A she ya iya sakamakon kalla da sukeyi a TV ganin haka yasa Miftahu tawowa shima yana Dariya wai shima sai Nasir yayi mishi irin Abinda suke da Yayanshi Nafi'u Aunty ko sai dariya take musu kan kace kwabo Nasir ya zage sai kyalkyala dariya yake dama shi A kwai San yara ko a can ma haka yake 6ata lokaccinshi cikiin "yayan turawa suyi ta wassanni
Qaramin Hijab din dake wuyanta tacire ta zauna kusa da Aunty ta'aje Jakarta kusa da ita cikin sanyi Muryarta tace Aunty wan an ne Uncle din dama?
[23/04, 14:58] +234 808 996 5176: πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸŽ—πŸ΅
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—


*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)






*πŸ…Ώ16*




Aunty tace Shima Maryam gashi nan kina wata takwas ya tafi karatu can kasar waje gashi nan yazo Hutu zai koma Amma Cikin Sanyi muryarta dai tace Uncle ina kwana kazo Lafiya ya hanya? Duk lokaci guda tayi mishi wannan tambayar yana can yana wasa dasu Nafi'u ya tsin kayi Muryarta a Dan sakaye ya dago kai Ya kalleta sai kuma ya yi saurin Mai da kansa kansu Nafi'u yace Lafiya lau Na sameku Lafiya Maryam? Dake yarinyar tana da wayyayan kai tace lafiya Lou Uncle. Daga bai ce mata kala ba suka cigaba da shirmansu shi dasu Nafi'u gefe guda kuma yana satar kallonta ganin yadda ta tube hijab babu Abinda ya dauki hankalinshi jikinta sai kyawun fatar ta da Wuyanta domin Maryam dai irin Masu cikkaken jiki ce bata da rama ko daya wuyanta har wani guru yayi Fatar luwai luwai tamkar wacce take rayuwa a kasashen waje Cikin zuciyarsa yace Ammafa yarinyar tana da kyan jiki da da ni fatarta zatayi Laushi sosai Wata zuciyar tace masa bama Fata Ba kadai wancan gurin na zaiyi taushi sosai tabbas za'a sameshi a cike Dam domin duk wasu A lamu ya hango a Dan kallon da yayi mata na Munti daya kar Ku manta dama nace daku Nasir Fanni Mata yake karanta da Binkice a kansu Dan haka gane kalar ko wace mace bazai masa wahala ba , Ya Mike yana kallon Aunty yace zan Dan shiga in kwanta Aunty Nagode Tace A,a ai bakici Abincin bah ko daya Murmushi yayi yace baki lura bane lokacin da naci Amma ki aje min idan an jima zanshigo in dauka Mikewa Aunty tayi tace a,a Ba zai haka Ba bara Maryam tabi ka dashi kawai da zafinsa kafi sakewa kaci nan fitinnanun yaran nan sun hanaka kaci Yana kallon A gogo dake daure hannunsa Mai wata irin sarqa yace OK Auntyna babu komai nagode Momy ma tanasan yanzu tana kan hanya time din da wowarta daga gurin Aiki yayi. Eh Ai kam yau juma'a bata dadewa take dawowa Ai tana ma kokari Aunty tafada tana harhada kayan Abinci cikin wani kwando mai kyau Shi kam Nasir tuni ya fita daga bangar Dan Ba zai iya zama jiran yarinyar bah Aunty tace Maza bi bayanshi da Abincin kinga ko Uniporm dinki Baki cire Ba kin tsaya shirme Maza ki dawo kin San a kwai isilamiyya ko
Karbar kayan Abinci n tayi da Sauri tabi bayanshi INA! Ai tuni Nasir ya shige part dinsa Sai ta dinga diri diri dan bata San in da yayi Ba tafi minti biyar a gurin a tsaya kamar ta koma da Abincin sai kawai ta karasa can bakin Get gurin Kakanta Baban Gida da Mahaifinta tsakanin Bakin Get din da Ai nihin cikin gidan A kwai "yar tafiya gaskiya tunda gidan Ba nawasa bane domain har kwalta ce a shimfide a wasu guraran .tana ajiyar zuciya takarasa gurinsu Malam Ya'u na ganinta yace ina zakije da kayan Hannuki ? A Nutse tace Aunty CE tace in kai wa Wani Nasir tace nabi bayanshi gashi ban San inda ya shiga kafin Malam Ya'u yace komai Baban gida ya mike yana dariya yace muje in nuna miki gurinshi sokowa kawai nama Fasa auran dake tunda Ba kya ganewa"




*MRS AHAMAD GWADABE*
[23/04, 14:59] +234 808 996 5176: πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸŽ—πŸ΅
*YARO DA KUDI*
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—






*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)




*πŸ…Ώ17*




Dariya tayi tana sun kuyar da kai Dan idan da sabo tasaba da irin wannan tsokanar da Baban gida yake mata na kaka da jika,


Part din Nasir ya Nuna mata yace ki shiga yana ciki kinji ko Tace to" Shi kuma ya juya ya koma Bakin Get din,


Tafi minti goma tana Aikin buga kofar dakinshi nashi shiru ba'abude Ba cikin gajiya ta zauna gefe tanaji kamar ta koma kawai wata zuciyar tasa ta daukar dutse ta fara bubbuga kofar dashi da qarfin gaske'


A hargitse Nasir yafito daga toilet daga shi sai gajeran wando jikinshi duk kumfa yana Fadin Wane Mahaukacin ne yake min wannan Dan iskan bugun kofar tamkar zai fasa min kune Dan iskanci ,shi duk a zatonshi irin Abokananshi na nane suka fara zuwa su dameshi jin cewar ya shigo kasar , kan yabude kofar sai mita yake yace ko waye basai ya kirani a waya ba meye amfanin Wayar tawa Mtsssss


Yana bude kofar yayi Arba da Maryam tsaye hannuta riqe da kwandon kayan Abinci Fuskarta ta nuna Alamun kosawa


Shi har ga Allah ya Manta da cewar Aunty tace yarinyar tabiyo shi da Abinci Wallahi sabida haka Wani banzan kallo yabi ta dashi yana ta6e baki yace ke wace irin daqiqiyar yarinyace iyi zakizo kinawa mutane bugu irin na Mahaukata Sabida gidadanchi irin naki


Kallonsa Maryam take cikin Mamaki sabida yadda yake yabata Mamaki ganin yadda yanzu nan a gurunsu yake ta dariya da wasa dasu Na'fiu Amma dubi yanzu yana kokarin zaginta,


Dake yarinya ce mai sanyin Hali sai tace dama Aunty ce tace in kawo maka Abinci Uncle kayi hakuri,"




Mtssss yaja yashige cikin dakin ya barta nan tsaye , ganin ya tafi ya barta sai kawai ta ajiye kwandon nan tayi nufin fita ranta a 6ace duk da take yarinya bata kaunar mutum mai wulakanci tana da gudun "yayan masu kudi sosai Dan ko A skull dinsu bata sakewa dasu kasancewar duk makarantar babu Dan talaka makarantace ta "yayan wane da wane Dan Alhji Huseen ne duk yake daukar nauyinsu ita da qannata,




Cikin tsawa yace ke mai kama da jinsun ifiritu dawo nan ki kwashe kayan Abinciki da dai bake kika kawo min sai inci, Ni Wallahi tsoro kike bani maza fice min daga daki yafada yana dauke idonshi a kanta lokacin da ta Joyo Cikin Mamaki Maryam take duk da yarintarta a lokacin bai hana ta Fahimtar meye ma'anar sunan ifiritu yake Nufi Ba, jikinta a sanyaye ta dawo da nufi kwashe kayan, sai kuma ya caja shawara yace ke barshi ma nafasa Fice min daga daki duk randa nakara ganin kafarki cikin dakinan sai nasa su Rambo sun cakalkalamin Namanki yana Nufin karnikan su na gidan,


Simi Simi Maryam tafice daga dakin kamar tayi kuka


Binta yayi da kallo lokacin datake kokarin fita daga dakin a Filice yace haka kawai kisanya ni Mafarkai da Faduwar gaba babu gaira babu dalili ki cuceni


Abinda yasa ya hanata mayar da Abincin yasan dole ran Auntynsa ya 6aci shiyasa basa haka da Auntynsa ko bazaici Abu Ba in tabashi ya kan qar6a ne kawai domin yafaranta mata,






*gaskiya bana samun commet a wannan book ko in dai nayi muku*πŸ˜žπŸ€“








*MRS AHAMAD GWADABE*
[23/04, 14:59] +234 808 996 5176: πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—






*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)






*πŸ…Ώ18*




Jiki a sanyaye Maryam ta koma 6angaransu Aunty tace meye kika dade be,? Tun dazu haka, Cikin sanyin muryarta tace lokacin Dana fita ban ganshi Ba ,shine Baba ya nuna gurinshi,Aunty tace ai sai ki wuce ciki ke kinfiye Nawa da sanyi jiki shiyasa har kika kasa taddashi kin San a kwai isilamiyya ko?
Eh Aunty , to sai kuyi maza Ku kimtsa bana son makara,Aunty tafada tana shigewa kchin ita kuma Maryam din tashige cikin domin cire uniporm gami da yin Wanka domin shirin isilamiyya maryam yarinyace mai nutsuwa da hankali tana sanyin Hali Sosai Ana cewa duk mai suna Maryam tana da tsiwa banda wannan Maryam din ita ko Abu kayi mata da wuya kaga bacin ranta kuma a take a sannan zata manta batada riqo ko kadan,


Haka Abokan Nasir
Sukai tayin turoruwar zuwa jin cewa yazo hutu haka zasu shiga shashinsa su cika ai ta kallece kallecan finafinen batsa blue film gami da saka kide kide , Wani sa'in har mata ne suke zuwa irin "yan iskannan


Hankali Ya'u in yayi dubu ya tashi sabida ya lura tunda Nasir din yadawo baya fitowa sallah ckin jam'i kamar da ya lura yanzu Ba kasai fai yake tsayawa dasu Ba kamar da gaisuwace ka wai take hadasu ,domin yanzu Baban gida Ba kasafai yake zama a Bakin Get din Ba sabida girma Alhji Huseen ya ce ya huttashe dama rigima ce irin tashi tuntuni Alhaji Huseen din ya hanashi zama , yace Lailai sai ya zauna shikanshi Ya'u shi ya za6i zaman gurin ,Amma babu yadda Alhji Husen bai yi dashi Ba A kan yaje kasuwa ya bude masa shago ya zuba masa kaya ciki Amma yaqi yace zai zauna nan din , kawai sai Alhji Huseen din yasaka wani yaro ciki da sunan gurin na Ya'u ne duk cinikin da'ake a gurin nashi ne gaskya Alhji Huseen yacika mutumin kwarai,


A na ya gobe Nasir zai koma America ranar Asabar ne babu Aiki Mom' dinshi na gida tana zaune cikin kujera tasha kwalliyarta kamar ko da yaushe idonta sakaye da Farin tabarau irin na likitoci hannuta riqe da wani katon littafi irin nasu tana dubawa , Nasir yafito daga dakinshi dake cikin falon ,Cikin wata"yar iskar shiga wando iya gwiwa ya wani zazzago Dan har gajeran Wandonshi na ciki a nagani ke kyace wando zai sa6ulo yafadi ,Amma INA!a daure yake a qugunshi sosai da wani irin belt mai Masifar tsada ,Sai short' mai dogon Hannu cotton tana da kauri gaban rigar tambarin America ne As'ueal hannushi daure da wani tabkeken a gogo , Hakanan kafarshi sanye da boot Yayi bala'in haduwa,


Mom' ta dago kai tana kallonsa tace Ina zakaje haka My son, dubi time fa ya kamata ka zauna kayi shiryeshiryn Abinda bakayi Ba ko,


Kusa da'ita ya zauna yana kallon Agogo hannushi yace Mom' zanje ne muyi Sallama da Friends, dina Ai Ba wani dadewa zanyi Ba,




Murmushi tayi kadan tace A'a son nasan halinka fa yanzu kafita Kumar sai na ganka , wai kai Ba ka gajiya da yawace yawace ne? Kasan halin dady ko"?




✍🏻...................
*muje zuwa*
[23/04, 14:59] +234 808 996 5176: πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸ΅
*🐾YARO DA KUDI*🐾
πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—πŸ΅πŸŽ—




*✍🏻WRITTEN BY*
Binta Umar
(MAMAN ABDUL WAHABU)




*πŸ…Ώ19*






Momy' Manta da shi kawai kin San dole in fita muyi sallama da friends dina sai kawai in zauna nace miki bazan Dade Allah,




Momy tace dady naka za'a manta dashi Laila Nasir ka kanka kafi kowa sanin halinshi babu ruwana idan ta hadoku dashi,


Allah dady ne mom' yawa yake sai kace mace zan zauna a gida ai Ba zai yiwu Ba"




Ba nufinshi kai tazama a gida Ba duk inda zakaje kaje Amma ka daina dare a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login