Showing 21001 words to 24000 words out of 82745 words

Chapter 8 - Sakon So Book Complete by m Shakur ( By Ubeera ) .pdf

M Shakur   

11 Oct 2025

1657

sahu, kafanshi
na sanye da ankle sock dake cikin wani givency covershoe dake sheki sosai, juyawa yayi
yadauko wani bakin glasses dan idanunshi basason haske sosai yasaka sannan yakalli Arif
dakanshi ke kasa yace “muje ko”? Gyadamaikai Arif yayi yace “to bismillan mu Uncle” yay
maganan suna jerawa tunda yake baitabajin mutum dake kamshin turare kwatankwacin irin
turaren Uncle Imran ba, turaren Uncle Imran nada bala’in dadi gasu da sanyaya rai, tun kafin su
karasa cikin masallacin mawaka da maroka kemai wake wanda ko kadan bayaso hakan yasa
baice musu komiba koyabasu kudi ba yawuce suka shiga masallacin nan da nan abokin Arif
yace “waliyin Arif ya iso” karasawa sukayi cikin aka zazzauna nan da nan aka daura aure
tsakanin Arif da Salma akan sadaki 500k wanda Uncle Imran yabiya mishi akai addu’a ana
gamawa ko sec daya tal bai karaba yamike yajuya Arif yatashi dasauri yabishi abaya, abokin
Arif yataba wani abokinsu da duk sukabi Arif da Uncle Imran din dasuka fice daga masallacin da
kallo yace “dan Allah jibi Arif saikace yaga God” dayan abokin mai suna Muhammad yace “to ai
kusan hakane wannan Uncle din nashi shiyamai komi aduniya tundaga primary school konine
abinda yafi hakama zanmai wlh Aliyu tunda mahaifinshi ya gudu yabarsu bai kuladasu ba” tabe
baki wanda aka kirada Aliyun yayi yace “bakasan waye mutumin nan ba idan kasan irin kalan
bakin girmankan dayake dashi saikai mamaki bakaga yanda babu wanda yagaida a masallacin
nan ba sai uban dingile wando shi adole ustazu da ijiye gemu” wani kallo Muhammad kema
Aliyu yace “waikai Ali me mutumin nan yamaka ne danni wlh banga aibunshi ko daya ba”?
Mugun kallo Arif yama Muhammad yace “bazaka gane bane waini mutumin nan zai hana aiki
sabida wai inashan taba yay rejecting application dina a company shi, shi wayasan kalan
abubuwan dayayi lokacin dayake matashi yana soja kafin yay retire”? Kalan kallon da
Muhammad kemai yasa yace “me to ai gaskiya nafadi ni to even tell you the truth gwara dabai

daukeni ba dan ance mahaukaci ne tuburan tuburan saidai in alluran sojojinshi basu tashi ba
wlh bakaga saisa har yanzu babu wacce ta yarda ta aureshi ba sai tsufa yake agidan
tsohuwarshi” wani mugun harara Muhammad yamai yace “kainedai kaga tsufan dan ni bangani
ba wlh ko mahaifin Arif daya girma yafishi tsufa, haushin shi kawai kakeji sabida yahanaka aiki
dayayi, kuma aure dabaiyiba shine baiyi niyya ba tunda akazo har gida aka kashemai mata da
yara biyu” dasauri kaman jira Aliyu yake yace “kasan shekara nawa yanzu da mutuwansu? This
is the 13th year amman har yanzu bai kara aure ba, wlh basabida mutuwan matanshi bane ba,
matsalan haukanshi yasa babu wacce ta yarda ta aureshi” zai cigaba da magana ganin Arif na
tahowa wajensu yasa yay shiru yamike tsaye yana kakkabe rigan jikinshi.
EPISODE 1️⃣1️⃣




Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI



Hannunta Baba yakama cikeda damuwan dazaka iya gani kwance kan fuskanshi yace “Gwaggo
dan Allah ki zauna kiyi shiru maza suyi magana, haba mana Gwaggo” Abdulhadi shima cikeda
damuwan yace “dan Allah Gwaggo, dan Allah” cikeda bacinrai Gwaggo tace “aini banmasan
kamilin mutun bane haka ba babba kuma, nadauka irin yaran nanne dake tashen balaga masu
kudi da rawan kai amman wannan kalleshi nutsaste kamili dashi” hannunta da Baba keja
alamun ta zauna yasa ta zauna kan kujeran tace “nayi shiru yanzu amman wlh idan baku
karbanma jikata hakkinta ba wlh zan bude bakina ehe” ta zauna tana goge kwalla, dan
murmushi Musty yayi yataho wajensu anatse yace “dudda nasan kowa hankalinsa atashi yake
gaisuwan musulinci wajibi ne dan haka Assalamu Alaykum” atare dukansu su Baba suka amsa,
Musty yace “nasan meke tafe daku amman dan Allah alfarma nake nema inaso kafin ku yanke
hukunci kokuyi wani abu zan muku bayanin komi dakuma asalin nuna muku video CCTV
camera dake nan akowani lungu da saku na company mu” gyadamishi kai su Baba sukayi
alamun tom, yace “ni sunana Mustapha nine babban abokin Imran gashichan aboki nane tun
muna yara yan kanana” yanuna Abee daya maida kanshi kasa dukansu suka kalli Abee, Musty

yace “ga kannenshi chan Hamza da Ibrahim wayan nan kuma abokanenshi ne, Imrana nada
yara hudu, biyu sun rasu tareda matarshi da akazo har gida aka kashe” ahankali su Baffa
sukace “Allah musu rahama” Musty yace “sai biyu yanzu keraye, namijin nada shekaru 22,
macen 21, nasan kuna mamaki maisa nake fadamuku haka inaso kusan waye Imran ne, bawai
sabida Abokina bane, tunda nake bantaba ganin mutum mai kiyaye dokokin Allah kaman Imran
ba tun yana kankanin shi mutum ne kamili nutsastse mai amana, abinda kuma yafaru
tsakaninshi da yarku was nothing daya wuce kaddara kokuma nace samin akasi akayi wannan
shine kawai abinda zance bari na kunna muku CCTV camera footage na ranan dasukazo
makarantan kugani Ibrahim zokasa” zuwa Ibraheem yayi gaban babban tV dake office din
yamakala flash dinshi saiga video yafara daga inda sukazo makarantan tundaga waje har zuwa
ciki da lokacin datace zatai fitsari anajin maganan dudda bada kyau yake fitaba aka nuna inda
ta tsaya tana juye juye dan bata gane bayin ba saitabi corridor tahau gudu tana ciro su waya da
chocholate har zuwa inda ta bangaje Abee Musty yace “inaso kusaka idanunku akan wan nan
mutumin” bayan ta wuce tai kwana aka nuno Abee yayi hanyar office nashi ya murda akulle sai
kuma yay hanyar bayi saiga mutumin yafito, saikuma aka shiga lokacin da Lujain tashiga bayin
da gudu daganan babu komi kuma sabida babu camera a bayi, saiga Abee shima yazo
yashiga, Gwaggo ta gyara zama idanunta kaman zasu fito su sauka kasa, saiga mutumin yazo
ya soka waya yana video jin muryan mutane yatafi yabar wajen kusan 2min da shiganshi saiga
Lujain tabude kofa ta tsaya sai gashi anyo ball da jakanta da wayan ta tsugunna ta dauka ta
goya ta gyara riganta tana waige waige tawuce dahar yanda mutanen nan suka mata kwatace
saiga Ibrooo yazo har bayin yashiga rikeda key sannan aka nuna musu duka video Lujain a
factory da yanda tai Plate har lokacin databar company su sannan ya katse.



Anatse Musty yace “abu na farko danakeso kugane kuduba lokutan da abin yafaru idan
fasikanci ko wani abu sukayi dan wanan lokacin yayi yagama? Sanan akanme yana mai
kampanin nan gabaki daya bawai shida wani ba bazai kaita office nashi ba inda akwai daki, bayi
dakomi aciki sai nan bayin kowa bayin ma’aikatanshi Iyye? Koma bayin kowa ne zai iya sa
security idan wani abu zaiyi yace kar wanda yazo banda haka kuma bayin maza ne ita meya
kaita bayin maza dudda nasan yaran makaranta babu abinda waya baya sasu suyi tunda harta
bugeshi batama tsaya ta kalleshi ba balle bada hakuri, abu na karshe video dakuke gani idan
kunada wayanda sukasan computer zasu iya gayamuku cewa anyi editing dinshi da yanda
kofan ke jijjiga da muryan karan datakeyi duka kari ne, saikuma shi wanan mutum dakukaga
yay video yaturama abokina messege kan yanaso abashi miliyan dari da kampanin nan koyayi
releasing video shi yana tarayya da wata shi yasan baiyi abu hakaba yay blocking kaman yanda
kukaji abin nan kwatsam haka muma muka jishi kwatsam, dan Allah dudda dai babu abinda
kaddarace bayasawa amman babu amfanin cewa wannan keda laifi ko wanchan keda laifi,
munsan sunan diyarku yabaci haka shima nashi yabaci amman dan Allah kuyakuri, dan Allah
abu baiyi dadi ba ko kadan” binsu Baba Gwaggo tayi da idanu daya bayan daya kowa jikinshi
yay sanyi dan babu karya amaganan su bawai wanan ba dukansu sun kalli Abee baiyi kama da
wanda zai aikata hakaba dan zai iya haifan Lujain dinma kuma itama tafadi abinda yakaita
bayin tun kafinma suji bakin na mutanen nan, tsaf abinda tafadi shi suka gani a video, babu

atom of lie aciki, kumama idan akace za’ayi blame yarsu ce taje bayin maza ita takai kafanta,
this is just a common mistake da kowa can make ganin yanda sukai shiru babu wanda ya furta
abu yasa cikin kumfan baki Gwaggo tace “ohhh barakuce komi ba”? Dasauri Baba yace
“Gwaggo dan Allah kiyi shiru kitashi mutafi gida kawai”. ”mtswwwwww” Gwaggo taja wani
mugun tsaki ta mike tsaye batai wata wata ba ta jaye gyalenta data lullube Lujain dashi
idanunta sunyi jajir fuskanta yay jaaaa sabida kuka jikinta dabare da jirwajen drinks fuskanta har
kyallin dankon drinks yake tana kuka sosai tana wani kalan ajiyan zuciya tarike jikin kayanta
gam da hannayen ta data dunkule kowa yabita da kallo adakin banda Abee da kanshi ke kasa,
duk wani mai imani da zuciya yakalli Lujain saiyaji jikinshi yay sanyi, Gwaggo na rike da gyalen
ta taka zuwa gaban table din da Abee ke zaune cikin ihu tace “kawani sauke kai kasa kaman
sabon ango kalli jikana nace, dago kanta ta kalleta” ahankali Abee yadaga kanshi yadan kalli
Gwaggo sannan gently yakalli direction din datake nunamai gabanshi na faduwa sauke
idanunshi dasukai jaa yayi kan Lujain dake kuka sosai idanunta akasa yay shiru danji yayi
zuciyanshi tai wani iri, komawa Gwaggo tayi wajen Baba ganin yana kallon Lujain din datace ta
fizge paper da aka bama Lujain amakaranta tadawo ta ijiye gaban Abee tace “kaga yanda
akama jikata wanka da lemu tundaga ka har kafa banda haka makarantan suka bamu takarda
waisun koreta sabida fasika ce mugun iri zata bata musu sauran dalibai” fashewa Gwaggo tayi
da kuka sosai daidai nan ta durkushe awajen ahankali Abee yasauke kanshi ganin yanda
tsohuwar da akalla zata girmi Hajiyanshi da yan shekaru na kuka sosai agabanshi, Baba da
Abdulhadi ne sukazo wajen da saurinsu zasu dagata tace “wlh kuka tabani zan daga muku
nono awajen nan ku kayaleni kawai” tai maganan tana tashi takalli Abee da kanshi ke kasa
sannan takalli Musty tace “kaga yarinyar nan dakake gani haka marainiya ce uwarta na nakuda
kanta haifeta ta mutu agurguje akai operation aka cirota sabida wai tasha ruwan cikin wanda
yamutu yarinyan nan dakuke gani saida tai kusan shekaru biyu acikin kwalban asibiti ni ke biyan
komi ubanta wannan din nan dakuka gani” tanuna Baba dashima yasauke kanshi kasa tace “shi
baida kudin biyan kudin kwalba duba sha biyar duk ranan duniya acirota daga kwalban wai
mutafi gida, likita kuma yace ana cirota baifi tai awa ashirin da hudu ba zata mutu, mijina
babansu mai kudin kauye ne daya mutu inada gado kap na saida gidaje na manya manya a
binni guda hudu da shanaye na kauye haka na biya dubu sha biyar biyar na shekara biyu cur
kafin acirota, nine komi na diyar nan tundaga zama a asibiti, abincinta, kayan sawanta da
rainonta da komi ma, koda aka bani ita haka muka dawo gida yau lafiya gobe ciwo ko shigowa
bayayi yadubata dan yanada wasu yaran lafiyayyu marasa ciwo, nikuma na nunamai zan iyama
jikata mai ciwo gata tamafisu jin dadin duniya, saida yarinyar nan takai shekaru bakwai aduniya
tafara makaranta” Gwaggo tashare idanu dan hawayen sinki tsayawa tace “bakuga yanzu tana
shatara a SS2 ba bayan su Samira suna shekaru sha shidda sun zana jarabawan kare
sakadire, amman ita har yanzu bata gamaba sabida ciwo, ni nasan wahalan danayi akan jikata
nasan gumi rashin bacci rashin sukuni danasha akanta, har yau har gobe tunda tazo duniya
bantaba baccin dare bantashi ba saita tadani, yau awayi gari sunanta yabaci kuce nai shiru
koda akace zata mutu ban hakura akanta ba yanzu ne da lafiyanta kalau zan hakura nai shiru
akanta wlh wlh Billahillazi La’ilaha Illahuwa bazata yuba ko laifinta ne ko laifinshi ne nidai nasan
bakuyi fasikanci ba dan bangani alamu a jikinta ranan ina tareda ita data dawo daga
makarantan ai kaima bakai kama da Babba mai lalata yaraba dan haka idan kunason zaman
lpy abu dayan zan gayamaka shine ka auri jikata! Ka auri dan baran iya da raina da lafiya na

inaji ina gani sunan jikata yabaci ba, tun yanzu a makarantan su kadai an mata wanka haka da
koro uwa wacce aka kamata dumu dumu tana zina, ahanamini yarinya fita titi gudun kar adinga
nunata wlh baran yarda ba, hanya dayace shine ka auri jikata!”



Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


EPISODE 1️⃣2️⃣



Kowa na dakin hatta Lujain din dake kuka sosai dashi kanshi Abee saida yadago kanshi yakalli
Gwaggo jin abinda tafadi, cikin tsantsan nuna seriousness Gwaggo tace “eh haka nafadi, nace
saika auri jikata! Duk abinda babba ya hango karami bazai hango ba, wannan video dakuka
nunamin kokun watsashi aduniya mutane ba yarda zasuyi ba bazai wankemin jikata ba, hanya
daya zai wanke jikata tastas shine ace kaidin mijinta ne da aure tsakaninku, daga masu gulma
dashi usulin algugumi dan wutan jahannama daya yada video dana tabbata baku ganshi ba
haryau saisuji kunya kaga ko banza yay aikin banza, shi bazai sami miliyan darin ba shibai

samu kampanin ba” hannunta Baba yakama zaiyi magana Gwaggo ta fizge hannunta idanunta
sunyi jajir tace “wlh wlh duk wanda yace saija dani cikinku saina tsine mishi albarka ubanme
zaka gayamin lokacin dazata mutu ma baka tsaya mata ba yaune da aka kirata da fasika zaka
tsaya mata? Nine komin Lujain, nine uwarta, nine ubanta, nine kakanta, kamin shiru kawai, wlh
wlh saiya aureta akan wani dalili zaija sunan diyata ya baci kuma bazaiyi komi ya wanketa ba,
wlh saiya aureta inba hakaba wlh wlh sai hukuma tarabamu, marainiyan yarinya na eh ku jibeta
fa abin tausayi ubanta bai damu da ita ba sabida yaga batada mahaifiya, inda yau mahaifiyarta
na raye Kunsan kalan tashin hankalin dazata shiga kuwa? Bayan kunsan rayuwa yakoma
yanzu iskanci ado ne wajen namiji mace ce rayuwanta zai baci har abada, yanzu awannan
video banda bayanshi anga fuskanshi eh? Yar yarinyar nan dai akaga fuskanta har akaga tana
gyara riga, idanba aurenta yayi ba koya wanketa wazai auri Lujain iyye? Kufadamin wani namiji
ne zai aureta? Wasu iyayene zasu bar dansu ya auri yarinyan da video fasikancinta ke yawo a
yanar gizo? Shi yanzu bashi kwana biyu anmanta dashi itako fa? Namiji mutane barasu iya
taranka ma itako Yar yarinya mace halama saidai tadaina fita danta fita tareta za’ayi amata duka
a titi, yakukeso tayi? Matar ubanta kuma dama ba sonta takeba kaga gwara ka aureta naga
kanada hankali kanada yara dasunma girmeta zaka rikemin ita amana koyau na mutu banda
nadama dama kullum tunanina wazan aura mata da hankalina zai natsu dashi ashe kai Allah
zai kawo mata amman ta wannan kaddaran” Gwaggo tafashe da kuka muryanta kawai akeji a
duka office din ganin yanda take kuka kuma su Baba sun kasa mata magana gudun karta tsine
musu yasa ahankali Mustafa yaje inda take tsugunnawa yayi yakamota kaman yakamo
mahaifiyarshi hannu yasamata a fuska yana goge hawayen datake yace “dan Allah Gwaggo
kiyakuri kidena kukan nan dan Allah sabida ni” ahankali tahadiye kukan tana kallonshi cikeda
lallashi yace “Gwaggo kinga nan office neko wannan matsalan kuma matsala ce daya kamata
atattauna agida kibamu address din gidanku anjima da daddare namiki alkawari dukanmu
shima harda iyayenshi zamuzo sai ayi magana da kyau Gwaggo kinji Gwaggo amman yanzu
kutafi, itama ku kaita gida tacire kayan nan kar wani abun yasameta maganganun nan da ake
agabanta bai dace ba, kuma babu kyau yanda kike kuka agabanta, kece karfinta, kobaki hakura
kitafi dan kowaba kiyi dan ita naga yanda kike sonta” juyawa Gwaggo tayi takalli Lujain dake
kuka sosai har lokacin taji barata iya musuba tace “gidan mu na nan kwanan tipa a Gwarimpa
idan kun shigo gida na biyar mai gate mai ruwan goro” anatse Musty yace “zamuzo anjima da
daddare” tashi tayi tadauki gyalenta dake kasa taje wajen Lujain ta lullubeta dashi ta kama
hannunta tadagata tace “muje Allah natare dake, nima ina tareda ke” su Baffa duk suka tashi,
Musty yace “kaisu ta back door bata gaba ba sabida reporters” binsu su Ibro da Hamza sukayi
dan kaisu sannan ahankali Musty yazauna tareda sauke wani ajiyan zuciya yana kallon Abee,
Harun yace “wlh wlh idan aka kamo yaron nan I will make sure yay rotting at the worse Nigeria
prison” Abdul yace “the guy is evil” daidai nan wayan Musty yashiga ringing ganin Hajiya ne
yasa yakalli Abee da kanshi ke kasa yace “tashi muje gida Hajiya is calling” batare daya kalleshi
ba yana kokarin fara typing yace “ban tashi daga aiki ba sai 4, and this is just 12:54” shiru Musty
yayi yana kallonshi Allah kadai yasan yanda yake hurting right now amman bazai taba nunawa
ba, ganin bakinciki Abee zai cusamai yasa yajuya yakalli su Harun yace “kumuje” saikuma
yajuya afusace yadauki wayan Abee dake kan table yace “shima ka kwace idan ka isa” yawuce
yafita fuuu daidai Hajiya na kara kira dauka yayi kafinma tayi magana yace “Hajiya gani nan
zuwa komi yazo dasauki kada kidamu kanki hawan jininki yatashi” katse wayan yayi suna fita

suka shiga mota sai gidansu Abdallah da Kausar sun dawo daga makaranta dudda sunada
lectures ganin videos dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login