Showing 75001 words to 78000 words out of 82745 words

Chapter 26 - Sakon So Book Complete by m Shakur ( By Ubeera ) .pdf

M Shakur   

11 Oct 2025

1623


sai Kausar dan Lujain na sama tun safe data fito ta gaida Hajiya takoma waje Abee yasamu

yazauna anatse yasauke wani kalan babban ijiyan zuciya dayasa har Musty saida ya kalleshi,
Hajiya tace “Musty an wankesu? Yanzun nan Hamza da Ibraheem kebani labari” cikeda farin
ciki Musty yace “Alhamdulillah Hajiya komi yazo karshe Abdul suntafi da yaron police station ma
nasan anjima kadan zamuga broadcast” Hajiya takalli Abee dan murmushi kadan yasaki yakalli
Maman Aneesarh da Kausar yace “I need my breakfast” wani kalan dadi Kausar taji rabon
dataga Abee haka harta manta, zama Musty yayi kusadashi suna breakfast din tare sai kallon
Abee yake idan akwai wanda yasan Abee sama dashi aduniyan nan yana ganin saidai Hajiya
datake mahaifiyarshi dan tun suna yara tareda Abee suka taso kuma yasan menene azuciyan
Abee yanzu haka alkawari daya zaiyi shine bazai taba bari Abee yarabu da Lujain ba Allah
yamai kyautan taba sai inda karfinshi yakare yana cikin breakfast wayanshi yay kara hakan
yasa yadauki wayan yakalli screen din ya amsa wayan chan yace “alright gani nan zuwa” ijiye
wayan yayi Musty yace “ina zaka”? Ahankali yace “akwai some UK agent dazasu so daman
yau, wai sunzo zanje nagansu zaka” girgizamai kai Musty yayi yace “bazani ba, mikewa tsaye
Abee yayi yakalli Kausar yace “kawomin key motana adaki” gyadamai kai tayi tawuce sama
tadauko key tasauko tabashi karba yayi yajuya Musty yabishi yace “ahaka zaka kaman wani
black arab”? Gyadamai kai yayi yace “yes” haryakai mota zai shiga Musty yace “best friend”
tsayawa Abee yayi yakalleshi, Musty yace “tell me what’s on ur mind” wani kalan kallo Abee
yamai yace “kafi kowa sanin what’s on my mind” dasauri Musty yace “Imran menene aibun
yarinyar nan? Why do you wanna leave her? Batada any matsala rabon danaga mutum this
innocent kaman Lujain harna manta, Gatanan gradually she’s fitting into your family, batada
matsala da su Kausar yaranka ko mahaifiyar ka, maisa zaka rabu da ita please accept Lujain as
your wife” tunda yake maganan Abee ke kallonshi yace “ka isa kasani dolene”? Shiru Musty
yamai yana kallonshi Abee yace “do you expect me nai accepting wanchan jaririyan yarinyar
amatsayin mata for God sake Mustafa my last born ta girmeta what is that child abuse or
mene”? Baki Musty yabude zaiyi magana Abee yadagamai hannu yace “ko yanzu ma dan fitan
nan daya kamani ne Allah yakaimu anjima after isha’i dakaina zan kaita gidansu komi yakare”
yana maganan yabita gefen Musty yabude motanshi yashiga yaja motan yabar gidan Musty
yadade tsaye yana kallon gate din anatse yace “Imrana I am your best friend, kamin komi
aduniyan nan, I’ve watched you suffered for good 13yrs, bazan taba bari ka koma rayuwan nan
ba, bazan taba bari karabu da Lujain danasan she’s the best thing right now in your life ba dan
bazaka taba samin matan dazaka samu peace kaman da ita ba” yana tsaye wajen aka bude
gate Anty Binta ne tashigo da jeep dinta ganin mijinta tsaye yasa takarasa parking tafito tace
“Baby ya akayi” fuskanta yakalla yace “Wifey inaso kibani honest answer not because of me tell
me the truth kinason Auren Yayanki Imran da Lujain”? Wani kallon kallonshi tayi ganin how
serious he is yasa anatse tace “Husby inason Auren su sabida banjin Ya Imran zai iya samin
mata kaman Lujain ba, she’s fragile sweet and easy to handle gata yarinya kuma Lujain batada
matsala, her whole life is just she and her grandma, I love them together, maisa kamin
tambayan nan yace zai saketa ne sabida ankama yaron”? Gyadamata kai yayi anatse yace
“Wifey I have a plan, but kafin nai plan kune yan uwan Imrana zan biku gabaki dayan ku one by
one na tambayeku idan kuna sonshi da Lujain inhar dukanku kunaso I will do something today
and I will need your support” dasauri Anty Binta tace “count me in” daidai nan Ibraheem da
Hamza suka fito alamu yamusu dasuzo hakan yasa suka taho, Musty yakallesu yace “kunason
zaman Imran da Lujain”? Dasauri Hamza yace “sosai ma Uncle Musty, wlh I love Lujain she’s so

calm batada magana, ni kawai ina sonta sosai” Ibrahim yace “konima haka I wish Ya Imran zai
sota sosai danafi kowa jin dadi but har yanzu he’s not ready to accept any woman”, murmushi
Musty yamusu yace “kuwuce kutafi” wucewa sukayi shida Anty Binta ciki, a dinning yaga Kausar
na kokarin kwashe plate karasawa yayi yana tayata yace “muje nakai miki kitchen Auta na”
murmushi tayi tace “to second Dad” saida sukakai kitchen yana ijiye plates din batare daya
kalleta ba yace “kinason zaman Abee dinki da Lujain” dasauri tadago kanta takallai folding
hannunshi yayi akirji yana kallonta ahankali yace “Kausar kinason yanda Babanki baida peace
of mind, you are not a small girl Kausar kema yau ko gobe zaki iya aure at any given time, why
don’t you wanna understand your father that gives you everything? Inhar yaga kunason Lujain
he will accept her too bakisan cewa idanma kina tunanin sabida kin girmi Lujain ne yasa baki
sonta yarinya irinsu sune babanki zai iya ya tsawataar mawa kuma taji, yace tayi tayi tabari
tabari but babba bazai taba iya controlling nata ba, give me ur answer Last Born kinason
rayuwan Babanki da Lujain ko a’a”? Ahankali tace “da banaso Second Dad but yanzu inaso
banso Abee ya auri wacce zata wahalar dashi gwara Lujain kaga tsoronshima takeji” murmushi
yamata yace “Allah miki albarka” Abdallah da Maman Aneesarh duk ya tambaya ta siyasa suma
sukace sunaso dakin Hajiya yashiga yasameta zaune bakin gado tana waya zama yayi akas
saida takarasa wayan yakalleta yana murmushi yace “Hajiya kinason zaman Lujain da Imrana”?
Murmushi Hajiya tayi tace “inaso sosai Musty, sonake ma yadawo muyi magana nasan nace I
want to support him amman harga Allah banso yace zai rabu da yarinyar nan” murmushi Musty
yayi yace “in sha Allah bazai rabu da ita ba Hajiya bari naje anjima kadan zan dawo” to adawo
lpy, bude kofa yayi yafita afalo yaga Anty Binta zaune fita yayi hakan yasa tabiyoshi dasauri
tace “ina zaka?” Dan jim yayi yace “I have a plan but it involves Docton Imran bari naje
nasameshi baran dade ba” gyadamai kai tayi tareda murmushi motanshi yashige itakuma
takoma cikin gida sama tawuce direct dakin Lujain tayi kwance taganta akan gado daure da
towel tana rikeda hook nata na school alamun karantawa take ganinta yasa Lujain taji wani dadi
ta tashi zaune tace “ina kwana Anty” murmushi Anty Binta tamata tace “wai wannan kan naki da
santsi dukya warware Lujain tashi kisa kaya muje na kaiki saloon a tsefe awanke baraki kitso ba
sai a gyara miki kumba” dasauri ta sauka dagakan gado tana murmushi tace “dama nagaji Anty”
shiryawa tayi sharp sharp tasa dogon hijabinta sukama Hajiya sallama suka tafi saloon.
EPISODE 4️⃣2️⃣



Wuraren 2 suka fito daga saloon din an gyaramata gashinta anyi stretching anyi parking sai
kanshi yake an gyaramata kumbunanta, kallonta Anty Binta tayi tace “kin iyashan Popsicle”?
Gyadamata kai tayi dasauri tace “eh” murmushi Anty Binta tayi tace “sweet tooth, muje nasaya
miki” wani shago suka shiga tasaya mata sannan tasayama su Kausar sannan suka fito suka
shiga mota suka dawo gida kusan tare itada Musty suka iso gidan parking yayi yafito daidai
itama tafito haka Lujain murmushi yayi ganin Lujain yace “wifey ina kika kaima Imran mata”?
Dan dariya Anty Binta tayi tace “saloon nakaita kitsonta duksun warware shine mukaje aka
kawance kan gabadaya aka gyara” murmushi yayi ahankali Lujain da adan kunyace ta lallai
tana sunnar dakai tace “ina yini” murmushi yayi yana kallonta yace “lafiya lau Lujain je daki zan
magana da Anty taki gatanan zuwa” gyadamai kai tayi tawuce yakalli Anty Binta yamata alamu

data shigo cikin mota shigowa tayi shima yashiga tace “Husby wai ina kaje I mean mekaje yu da
Doctor Ya Imran”? Dan shiru yayi yace “Dr is the only person that can help us at this point
yadawo kaman family” yayi dan shiru saikuma yasa hannunshi acikin aljihun gaban riganshi
yaciro wani tablet kwaya daya rak yabama Anty Binta kallon kwayan maganin tayi tace “what is
this”? Dan shiru Musty yayi ahankali yace “ke kanwar Imran ne bai kamata ina fadamiki sirrin
yayanki ba but you are the only help danake dashi” shiru yakarayi ahankali yace “Wifey inaso
Imran ya sad…..” saikuma yadanyi shiru kafin ahankali yace “I want Imran yay consummating
aurenshi da Lujain!” Dawani kalan sauri Anty Binta ta kalleshi gyadamata kai yayi yace “that’s
the only way dazamu iya saving this marriage inhar abu ya shiga tsakaninsu nasan bazai taba
sakinta ba” yay dan shiru saikuma ahankali yace “after dogon explanation da magana Dr shi
yabani wannan kwayan maganin daya tal dakike gani shima yace aure will help Imran sosai he
needs a woman, he’s a full grown up middle age healthy man yana neman 14yrs ba mace
kenan karyazo ya haukace” cikeda dan tsoro Anty Binta tace “to mene maganin zai sashi”?
Ahankali Musty yace “I don’t know wlh exactly but nasan dai zai tadamai da sha’awa ne dabazai
iya bearing ba baya neman matan banza dan haka dole yaje wajen matanshi ta sunna this is
just my saying oo Dr bai fadamin takamaimen abinda maganin yake ba, but yace to avoid kar
Imrana ya zargi kowa abashi maganin around 7 dan 3hrs maganin yake dauka kafin yay taking
effects, kinga around magrib zaki samai a shayi dazai sha anan falo ko” gyadamai kai Anty
Binta tayi saikuma tace “yaya zamuyi da mutanen gidanmu Lujain is v……..” saikuma takasa
karasa maganan, dasauri Musty yace “shima is under my control duka yaran gidan nan kap
hatta Maman Aneesarh kwasansu zamuyi zance zan kaisu cinema, Hajiya kadai za’a bari
agidan akasa, around 9 zamu tafi idan yaso dagachan zan ce musu yau kowa agidana zai
kwana dama duk basu zo sabon gidanmu ba cus banson situation dazasusan something
happen tsakanin Imran da Lujain” dasauri Anty Binta ta gyadamai kai zuciyanta na bugawa
hannunta yarike yace “we got this babe, I am helping my best friend and you are helping your
brother, we are saving the most stubborn man dana sani aduniyan nan” atare dukansu sukai
murmushi, ahankali Anty Binta tace “I wish I can have a friend like you Husby” murmushi yayi
yace “I am nothing wlh wish to have a friend like your brother Imran not me” murmushi tayi
tashige jikinsu tace “Allah yabamu lada and May this plan be successful” murya chan kasa yace
“Ameen baby hold this magani well nasan anything 4 ko 5 zai dawo gida I will be with him har
dakinshi baran bari yay any rubutu ba balle yamata saki zamuje magrib bazan bari yazauna ba
zamu dawo da sumin cin abinci that’s when you will bring the tea a two cups kibashi mai magani
kibani empty mara magani” gyadamai kai tayi ahankali yace “sauka muje ciki namusu
announcing cinema thing din fa ticket din nan tayani kwasa agaba” kwashe ticket din tayi suka
fito suna shiga falo kowa na falo banda Lujain dataje sama Musty yace “tantadaaaaa yau
munada all family movie night, Ibro tell ur wife to get ready around 8:30 9 zamu tafi dukanmu
Hajiya ne kawai bazataje ba nasani” hannu Hajiya tadaga tace “aikam inani ina zuwa wani kallo
da idanun nan danake fama dasu” dariya akayi Kausar tace “Second Dad thank u wlh dama
mun dade ba’a fita damu ba” Anty Binta tace “theater gabaki daya ya karba mana sai ashirya”
sosai sukaji dadin zancen da rabon dasuyi having fun haka tun kafin kaddaran da yafada kan
babansu, zama Musty yayi yace “kubani abinci wlh yunwa nikeji Hajiya”, Hajiya tace “Binta
bama mijinki abinci”.

Wuraren 5 Abee yashigo gidan parking yayi yabude kofa yafito he’s so happy yau jinshi yake
sakat abinda ke kanshi ya sauka maida kofan yayi yarufe yawuce ciki, afalo yasami kowa yakalli
Abdallah ya wurgamai car key yace “jeka kawo abubuwan cikin mota is for you guys” gaidashi
kowa yayi da kai ya amsa ya gaida Hajiya sannan yawuce sama binshi Musty yayi dasauri yana
shiga cikin dakinshi shima Musty na binshi ciki yace “Ya Meeting din”? “Fine” ya amsa yana
shiga cikin closet saikuma yafito yawuce cikin bathroom kwanciya kan gadonshi Musty yayi
yana daddanna waya yadade cikin bathroom sannan yafito bayan yayi wanka daure da
bathrobe yawuce closet nashi nan ma yadade ciki shiryawa yayi cikin jean black dawata
maroon t-shirt sai kamshi yake zubawa yay wani kalan kyau dake shiga ido, Musty yanunamai
abincin da aka kawo a tray yatsine fuska yayi yace “I will eat later” Musty yace “waikai me abinci
yama I am sure tun safe bakaci komiba” hararanshi yayi yakalli agogon bango yace “tashi muje
mosque” tashi Musty yayi suka fice tare ana magrib Musty yatasashi agaba suka dawo gida
afalo suka zauna Anty Binta tawuce kitchen maida kofan kitchen din tayi tarufe tazuba musu
shayi a cup sannan ta balle maganin tajefa a cup na Abee nan da nan maganin ya narke cokali
tasa takara juyawa sannan tasa a tray tadauki tray tafito tana tafiya ahankali Gaban Abee taje
tadauki cup nashi tadauramai akaramin coffee table dake gefenshi tace “Ya Imran ga shayin ka”
murya chan kasa yace “thanks” sannan tawuce gaban Musty ta ijiyemai nashi cup din a coffee
table dake gabanshi sannan tawuce tace “bari muje mu shirya” gyadamata kai yayi, Hajiya tace
“kaji wai cinema zasuje Imrana, Mustafa da asaran kudi hall gabaki daya ya kama musu” dan
dariya Musty yayi yace “Hajiya inada wasu kannai ko yara sama dasu ne, ba asaran kudi bane
let them go out today and have fun” tabe baki Abee yayi yadauki tea shi yakai baki batare daya
sa bakinshi a zancen ba, tass ya shanye tea Kausar tasauko sanye dawata doguwan Riga na
abaya black tai kyau tazo gaban Abee tace “Abee kayan nan sunyi” kallonta Abee yayi ahankali
yace “yes” murmushi tayi tajuya takoma sama daidai ana kiran isha’i tashi Abee yayi lokacin
Ibraheem yashigo gidan shima ya shirya tsaf da matanshi da yaranshi biyu akunyace matanshi
ta gaida Abee da katon cikinta haihuwa yau ko gobe amsawa yayi batare daya kalleta ba
yamikama yaran hannu alamun sallama sakamai hannun sukayi sukace “Abeeeee” tareda
rungumeshi daukansu yayi tareda dan murmushi yace “how are you”? Dasauri Babban
Muhammad yace “Abee the coco pops u bought for us has finished” gyadamusu kai yayi yace
“okay” karamin yace “Abee second Dad is taking us to cinema will you go with us too”? Girgiza
musu kai yayi anatse yace “Abee has some work but I promise to go next time” murmushi yaran
sukayi sukace “okay” murmushi kowa na falon yayi harda Hajiya Musty aranshi yace “I can’t
wait Lujain ta haifomaka little baby Kausar tai kanwa ko kani” kaman Abee yaji abinda yace
kallonshi yayi suka hada ido ya sauke yaran kasa dan suje wajen Hajiya yace “let’s go” ficewa
sukayi dukansu harda su Abdallah da Hamza dasuka shirya suma duk sunyi kyau.
EPISODE 4️⃣3️⃣

LAST FREE PAGE
wa.me/+2347012181461

Chat me up anan

Toh jama’a anan nakawo karshen free pages na wannan littafin nawa mai suna SAKON SO.

Idan kinason cigaba da karantawa all you have to do is pay 1k into 3107021073 AISHA
MUHAMMAD FIRST BANK

Send evidence of payment to my telegram or WhatsApp via 07012181461.

Akwai groups guda biyu na yan 1k Episode guda biyu kullum.

Akwai group na 500 EPISODE guda daya kullum ake posting

SUNDAYS-WEDNESDAY ✍

Thank you❤️❤️❤️
Don’t miss this book for anything in this world



Karasa tajemata gashin Anty Binta tayi tamata parking dawani pink ribbon mai kyau yanada
butterfly ajiki na art, tace “yauwa gashinan gashin yadawo daidai harkin hargitse shi Lujain
abinda aka gyaramiki dazu dazun nan tashi kiyi wanka kizo” tashi Lujain tayi tana murmushi
sabida yanda Anty Binta ke magana, Anty Binta tafita daga dakin dawani cup tadawo nawani
magani tana murmushi ta ijiye tana juyawa sabida yahuce fitowa Lujain tayi daure da towel Anty
Binta tace “yi salla kizo” dadduma tahau tayi salla tana idarwa tazo wani red bubu irin masu
manyan gyalen nan Anty Binta tabude sabo fil a Leda tamika mata tace gashi ki feffesa turare
kisaka bari nadauko sugar nazo maganin nan ba sugar tana maganan tafice rigan Lujain
tadauka taje gaban madubi feffesa turare tayi ajikinta masu dadi sosai sannan tasaka rigan
batare data saka komi akasa ba daidai nan Anty Binta tashigo tsayawa tayi tana kallonta sabida
yanda jan bubu rigan yamata kyau tace “wow red abu namiki kyau Lujain zokisha” zuwa tayi
Anty Binta tabata magani a cup bayan tasa sugar shanyewa tayi tass tana tabe baki Anty Binta
tadan buge bakin tace “ni bantaba ganin yarinya shagwababbiya irinki ba Lujain duk zama da
Gwaggo ne yasa haka rainon Kaka kawai” dan dariya tayi kadan batace komiba Anty Binta tace
“rikemin wayan nan zauna kijirani ina zuwa you can play game idan kinaso” karban wayan tayi
tazauna bakin gado tana kokarin shiga game na candy crush.

Shigowa gidan sukayi around 8:30 Abee yakalli Musty yace “lemme go na kwanta nagaji” bai
jira amsanshi ya yakalli Hajiya yace “saida safe Hajiya” “Allah tashemu lafiya Imrana” dasauri
yawuce stairs dan tun a masallaci wani iri yakeji, kallon kallo Anty Binta da Musty sukayi, Musty
yace “kowa yakarasa shiryawa by 9 mufice” zama sukayi afalo mata duk suna sama da gangan
Anty Binta tabata lokaci sai wajajen 9:20 tafito tai kyau kowa na falo tace “sorry guys muje
muje” fita sukayi dukansu sukama Hajiya sallama suka fito, duk mota suka shishiga suka tafi.

Genesis sukaje wani private VIP hall daya kama musu shiga wajajen 11 Musty yamike tareda
kama hannun Anty Binta suka fito waje yace “time for the call nasan he’s suffering by now”
gyadamai kai tayi ta karbi wayanshi dayake bata tai dialing number ta…..
Lujain tayi nisa a game din datake bugawa ganin number Husby yasa tadan zaro idanu saikuma
tamike dasauri tabude kofa tafito tai dakin Anty Binta taga babu kowa tsit taji gidan kaman ba
nasu ba kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login