Showing 51001 words to 54000 words out of 82745 words

Chapter 18 - Sakon So Book Complete by m Shakur ( By Ubeera ) .pdf

M Shakur   

11 Oct 2025

1622

koshi saida shi yafaracin nashi shine zakimai batun assignment salon karyaci,
tunda aka haifeki Babanki yadainacin abinci yakoshi” kaman zatai kuka tace “ai nace sorry ko
Abee” ijiye coffee yayi ahankali yamika mata hannu alamun tabashi book din dawani kalan sauri
tabude jakanta tadauko book din takawomai maths ne kan probability ne, ahankali yace “come
here” kusadashi tazo cikin 2min yanunnuna mata yanda zatayi yamata solving daya yabata
second question din yace tayi yagani zama tayi tafara shikuma yacigaba da breakfsat nan da
nan tayi takawomai dubawa yayi yaga tayi daidai hakan yasa “now get ready, Hamza na jiranki
a car” hada jakan tayi tasa hijabi tafita dagudu, saida yagama breakfast dinshi sannan yatashi
yadan kalli Lujain data gama itama amman kanta akasa hakan yasa Anty Binta dake kallonsu
tace “tashi kutafi Lujain” tashi Lujain tayi tadan kalli Anty Binta saikuma takalli Abee dake tsaye,
juyawa Abee yayi yay kofa yace “Hajiya natafi” Hajiya tace “Allah bada sa’a bishi Lujain” binshi
Lujain tayi itama tabude kofa tafito waje duk su Hajiya suka bita da kallo, wajen wata mota

daban yayi bmw baka ba jeep din jiyaba budewa yayi yashiga gaba hakan yasa takarasa wajen
kirjinta bugawa yake kawai to ina zasuje baya tabude ahankali zata shiga suka hada ido wani
mugun kallo daya mata yasa tamaida kofan tarufe tadawo gaba tabude gently tashiga cikin
motan gabanta nawani kalan fadi, motan kamshi kaman ba mota ba, ganin credentials nata a
motan yasa tadan bude idanunta takalli file din datasan Gwaggo kadai ke boyemata dan awajen
Gwaggo suke acikin katon akwatin bununta taboyesu, ga birth certificate dinta, primary
certificate dana JSS Ce dakuma na indigen da Nin dinta duka awajen, dan juyawa tayi takalli
cikin gidan to Gwaggo tazone batasani ba, bude musu gate akayi suka fice dudda motan tinted
ne gani take kaman zaa ganta hakan yasa ta sauke kanta kasa, sun danyi tafiya mai nisa wani
hadadden school yakaita da baida wani nisa sosai da company shi yasan mai school din sosai
childhood friend nashi ne, kashe motanshi yayi a parking space yasa hannu yadauki file nata
yabude kofa yafito, kasa bude kofan tafita tayi sai kallon cikin school din take da student keciki
gabanta nafaduwa yanzu nan ma za’a faracemata Yar iska ne dan yanzu ko’ina ansanta
hawaye ne yacika mata idanu, juyowa Abee yayi ganin bata bude kofaba har lokacin yasa yazo
ta wajen bude mata kofan yayi dasauri takalleshi lips nata har rawa suke murya chan kasa tace
“ni……banason school, dan Allah kada kasani, wlh banaso” tai maganan hawaye na zubomata
daga idanu dasauri takai hannu tashare yana wani kalan kallonta yace “why?” Dan kallonshi tayi
saikuma tasauke kanta ahankali tace “nan ma zasuce ni yar iska ce maibin maza, everybody
will be looking at me ana nunani ana cewa nice a video nan” fashewa da kuka tayi yace “don’t
you dare cry for me anan” dasauri tahadiye kukan tana goge fuskanta da bayan hannunta, cikin
kakkausan murya yace “akwai wanda yadaukeki yakaiki sama ne when all the rest of the
students na reception akasa? Akwai wayanda yakaiki bayin maza ne?” Girgixamai kai tayi wani
abu na tokaremata zuciya, wani kalan dan tsaki yaja yace “kin zaci inason Auren nan da akamin
dakene kokuma I fancy you one bit?” Shiru tayi yace “the way I am dealing with you dudda I
don’t consider or regard you matata kema haka zaki shiga school din nan deal with anything
that comes ur way and study hard” gyadamai kai tayi ahankali tanaji kaman tafashe da kuka
danji tayi tabama kanta tausayi, anatse yace “futo” fitowa tayi daga motan ahankali ta matsa
gefe maida kofan motan yayi yarufe sannan yakalleta yace “ke” kallonshi tayi kaman yanda
shima ke kallonta, calmly yace “karki dauki Auren nan da akamin dake as anything, ke ba
matata bace and bazaki taba zama dayaba, as far as Imran is concern I don’t have a wife! Dan
haka do whatever you want, idan kinga wanda kikeso talk to him, mingle with your fellow
students, dazaran komi settle down zan rabu dakene u will be back to your parents house cus
babu abinda zanyi dake” yakarashe maganan yana tabe baki ahankali yace “kin gane”?
Gyadamai kai tayi ahankali sotake tayi kuka amman yahanata gaba yayi yace “let’s go” binshi
tayi tana tafiya ahankali, gaidasu masu gadi sukayi sannan suka shiga ciki ga mamakinta kusan
rabi da kwatan student na makarantan turawa ne kadan daga cikinsu ne yan nigeria, sama
sukaje wani babban office yabude yashiga wani babban mutum ne zaune yana ganin Abee
yatashi yana bashi hannu yace “welcome Soja, ga waje ku zauna” zama duk sukayi yakalli
Abee yace “itane student din”? Gyadamai kai Abee yayi yace “bani file nata” bashi Abee yayi
yadudduba sannan yakira secretary nashi yabata tamai photocopy documents nata duka
yabaama Abee original, agabanta tanaji Abee yabiya 5.7M school fees nata da kudin textbooks
nata da kudin Waec da neco dan yace yanaso tayi a SS2 din nan idan taci shikenan, secretary
aka kira ta tafi da ita changing room dan saka uniform shikuma mutumin yacigaba da magana

da Abee yace “I assure you this babu wanda zaiyi bullying nata a school dina, her image will be
well protected, sannan kaman yanda kamin bayani awaya last night zata dinga special lesson
din 4 idan ta tashi saikazo kawuce da ita gida, and lunch dinta will be given to her, kabata one
week zakaga tasake jikinta tashiga student da kyau without fear na being bullied ko kirata
names, Ya guy din ankamoshi kuwa?” Daidai lokacin secretary tashigo tareda Lujain data saka
kayan makaranta skirt ne dark blue da Riga sky blue long sleeve sai jacket dinshi dark blue,
dakaramin farin hijab sai farin safa da black shoes, uniform din sun mata wani kalan kyau she
looks chubby and sooo cute, tashi mai makarantan yayi yace “Soja muje mu kaita ajinsu tare”
raurau tayida idanu tana kallon Abee daya dauke kanshi daga kanta yamike shida mutumin
sukai gaba itakuma abaya wani class mai kyau SS2 suka tafi ajin duka turawa ne mutun 3 ne
Nigeria sai ita yanzu ta hudu ga teacher a ajin shiga mai makarantan yayi yasa aka mata warm
welcome sannan yakaita sit nata agaba tazauna ahankali tasake dagakai takalli Abee dashima
kallonta yake wani kalan lankwashe kai tayi ashagwabe hawaye yacika idanunta tam har kyalli
suke dawani kalan sauri Abee yabar wajen mai makarantan yasallami ajin yafito yasameshi
agaban office suka karasa magana sannan yawuce yafita daga school din yashiga motanshi
yawuce company shi that is just few blocks away.

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
EPISODE 2️⃣5️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/

Inner Sanctum
Zaune yake agaban wani drawer shi kadai acikin sanctum din sanye da jersey na riga green da
farin wando, an rubuta Mandawari abayan rigan, farin guy ne kal dashi siriri baida kiba ko
kadan, kanshi irin wannan askin nan na yan kwallo ne anyi murde murde ajikin tarin gashin da
abin yay kaman kitso dan twisting ne, wayanshi ne a hannunshi yana dubawa daidai an bude
kofan sanctum din an shigo wasu players ne kusan su 13 duk sun shigo ciki suna zufa kowa
yay wajen zamanshi goal keeper su yace “Man! What happen is like yau bakaine a field ba is
another different person, what’s happening Bro”? Wani guy ne kamanshi daya zaune kusa dashi
yana kokarin cire takalmin kwallon kafanshi mai suna Olusay yace “ai Man is going through a
heart break this is the second week his stalker batamai magana tamai dropping love messages
ba” wani mugun kallo Mandawari yama Olusay, yan dakin dukansu kowa barin abinda yakeyi
sukayi sukataho gaban Olusay dasauri sukace “yanzu Mandawari daman yanada budurwan
dayakeso”? Dan dukansu are finding it unbelievable, dan dariya yayi yace “yes” wani kalan
mikewa Mandawari yayi cikin fushi yace “ubanwa yace maka sonta nake” dariya Olusay yayi
sosai sannan yamike tsaye tareda cire riganshi yay hanging yajuyo yakalle team members
dinsu yace “wlh mugun sonta yake na rantse amman he feel mutum irinshi mai over 400M
followers can not love a girl like her shida har manyan top celebrities irinsu Kim ke sonshi
amman yarasa wanda zaiso sai yarinyar nan he’s even ashame to admit sonta yake barima na
nuna muku page dinta kugani kuyi following nata” yakai hannunshi zai dauki wayan Mandawari
wani kalan rikemai hannu yayi yana huci yace “how many time zan gayamaka kadainamin irin
abin nan Abdulaziz” cikin fushi Olusay yace “how many times zan gayamaka shi so babu two
ways about it idan kanason abu kanaso ne idan bakaso bakaso ne admit cewa bawata
Cinderella dream girl Allah yajarabeka da so ba, normal common girl Allah yajarabeka da so
Muhammad” wani kalan mugun kallo Mandawari yamai yace “and so”? Olusay yace “dan haka
kadena jan aji slide into her dm and respond to all her messages and confess your feelings Bro
koba hakaba guys” duka yan team nasu sukace “hakane” daya daga cikinsu mai suna Obi yace
“I can’t wait to see babe din da Man keso yanda yakema mata wulakancin nan I know she must
be the most beautiful girl on earth” dan tsaki Mandawari yayi yace “you guys should stay away
from me and my business” yay maganan yana cire nashi rigan ya chanza kayanshi zuwa
normal Riga da wando black yadauki wani big jacket yadaura akan kayan dan sanyi akeyi a
Greece thank God yau zasu koma nigeria, yana gama shiryawa aka shigo akace bus nasu is
ready fita duk sukayi koda sukakai bus din shida yasaba zama da Olusay yau bai zauna
wajenshi ba baya yawuce yazauna abinshi Olusay baicemai komiba.



Airport suka wuce business class aka biamusu dayake shida Olusay ne zasu Nigeria sauran
kowa yay garinsu, saida jirgin sannan ya kwanta wayanshi yabude yashiga chat dm din Lujain
yana dubawa tun 2019 tafara turamai messages har zuwa yanzu dasuke 2022 amman baitaba
amsata daidai dasau dayaba, fitowa yayi yashiga Fred dinta yana duba hotunan ta, 5 pictures
ne kawai tai posting, daga wanda tasaka scchool uniform sai wanda take itada Gwaggo, sai
wanda tayi ranan salla da Ya Samira, saikuma wanda tayi ita kadai tayi bala’in kyau a hotunan

duka pink lips dinta ya tsare da idanu kaman tasaka pink janbaki, fitowa yayi yawuce wani blog
a instagram yakara bude video ta na sex video nan da yanzu zai iya cewa yakalla yakai sau 20,
saikuma ahankali yafito yashiga video da blog din still sukai posting na debunking news din
cewa mutumin mijinta ne ga shaida daga wajen iyayensu, jazur idanunshi sukayi har jijiyoyin
kanshi suka fito kashe wayan yayi ya runtse idanu ahankali murya chan kasa yace “you are
mine Lujain! You love only me! You belong to me”…
*****


Har aka tashi daga makarantan tana aji, da kyar wuraren 1 ma tafita shima cafeteria officials
nasu ne sukazo suka kirata kan tazo ta amshi lunch haka taje lafiyayyen abinci aka bata da
drink harda kaza ga student awajen babu ma mai kallonta haka taci tadawo aji, malaman sai
nan nan da ita suke yan ajinma namata magana itane ma bata amsasu da kyau kawai duktabi
ta tsargu, 4 daidai aka gama musu special lesson din aka tashi kowa yashiga daukan jakanshi
banda ita dake zaune inda take saida kowa yagama fita yarage ita kadai a ajin yasa tashiga
hada books nata ajaka tamaida komi saikuma tai shiru tana kallon jakan yau kwana hudu kenan
bataji muryan yan gidansu ba, bata gansu ba, koda su Baba dasu Mama dasu Ya Abida basu
damu da ita ba Gwaggo fa? Yanzu Gwaggo barata nemeta ba, daman da gaske takosa
takadata daga gidansu shikenan batada kowa, wannan wani kalan rayuwa ne da rana daya
kawai tajefa kanta? Jitake kaman tadawo da hannun agogo baya ta chanza duka abinda yafaru
ranan, babu wani abu datakejin dadinshi arayuwanta, ita batada waya, ita gidan nan babu
wanda zai yarda yabata wayanshi balle takira Gwaggo ma, ita school dakomima baya mata
dadi yanzu sabida batada Mama ne saisa abu haka ke damunta? Inda Mamanta na raye tasan
barata wahala hakaba tunda gashi yanzu ma Gwaggo batasonta kaman Mama wasu kalan
hawaye masu zafine sukazo mata tundaga yatsun kafanta kawai kife kanta tayi akan kafafunta
tafashe da kuka sosai Abee yadade tsaye gaban ajin yana kallon yanda takife kanta kan
kafanta tana kuka sannan yadanyi gyaran murya da sauri tadago jajayen idanunta, ganin Abee
yasa dasauri tashare hawayen da bayan hannu ta mike tsaye ahankali tareda daukan jakanta
ahankali ta goya sannan tafara tafiya kanta akasa ta taho gaban kofan, baice mata komiba yayi
gaba hakan yasa tabishi abaya har zuwa waje, mota yashiga itama tabude gaba tashiga
tazauna har lokacin idanunta jazur, harzai tada mota saikuma yajuyo yakalleta bayabo ba
fallasa yace “why are you crying”? Dan juyowa tayi takalleshi yanda ya tsareta da idanu saitaji
takasa mai karya lips nata har rawa suke tace “kewan yan gidanmu nake…...” Wani kukan ne
yazo mata dasauri takife kanta kan jakan makarantan da akabata a school tafashe da kuka
sosai cikin kuka tace “babu wanda ya nemeni cikinsu da Baba da Mama, dasu Ya Samira
harma Gwaggo basu nemeni ba sun kawoni gidanku I am all alone babu wanda ke sona, kowa
haushina yakeji, I am so scared mutane su ganni kar adinga nunani babu abinda kemini dadi, I
just wish inama zan mutu maybe namaga Mamana achan naji dadi, babu wanda ke sona har
Gwaggo na” tunda tafara maganan kallonta yake tabashi tausayi sosai inda Kausar dinshi ne fa
in this situation, “wayace miki Gwaggon ki bata sonki” dago kanta tayi dasauri da rinannun
idanunta takalleshi dauke kanshi yayi yakunna key tareda tada motan yaja motan sukabar
wajen, saida suka shiga titi ahankali tace “inda tana sona dabatamin auren nan ba ni inada
wanda nakeso” dan kallonta yayi saikuma yadauke kai yakalli titi kusan 3min babu wanda yace

komi acikin motan kaman daga sama yace “shi kike kallo rannan abayi”? Gyadamai kai tayi
dasauri tana goge hawayen kan fuskanta da bayan hannu tace “eh sunanshi Muhammad
Mandawari, ni shinakeso na aura” yana kallon hanya yace “kinfadama Babanki” gyadamai kai
tayi tace “eh yasani” ahankali Abee yace “to mesa basu aura miki shi ba”? Dan rage murya tayi
looking so sad tace “ai baitaba amsa messages dina a instagram bane ba” batare da Abee
yakalleta ba yace “do you have phone”? Girgizamai kai tayi tace “a’a da wayan Ya Samira
nabude instagram nai following dinshi rannan dana fara ganinshi a tV dakin Gwaggo yana buga
kwallo” “kinason kwallo”? Abee yay maganan yana kallon titi, ahankali tace “eh inason kallon
kwallo kuma inason Mandawari sosai, nasan inda yau zan ganshi all my problems will be gone
zaije wajen Baba yace shine zai aureni bakaiba sai ka sakeni amini aure dashi natafi wajenshi
muyi zamanmu” daidainan sukakai gaban wani saloon yakashe motan yadan kalleta ganin tana
kallonshi kaman tasami tV da manyan idanunta masu kala dana mage yasa yadauke kai
wayanshi yadauka duk tana kallonshi komi nashi anatse yakeyi baitaba mata dogon magana
ba sai yau kuma kaman magic sai yan maganganun sukasa ta manta da bakin cikin datakeyi,
ijiye wayan yayi yajuyo yakalleta jin alamun ana kallonshi dasauri tadauke kai tana wasa da
yatsunta, dauke kai shima yayi daidai nan Anty Binta tafito daga saloon din tazo bangaren
Lujain tabude tace “Iyye yan makaranta oyoyo” murmushi Lujain tayi, Anty Binta tace “ke baki
gajiya da kuka ne look at your eyes fito muje to a gyara miki gashin nan dabaki iya tajewa da
kanki a kitsashi, kawo jakan nan nasa abaya Ya Imran yawuce miki dashi gida” fitowa tayi
tamaida jakan baya itakuma Anty binta tazagayo ta bangaren Ya Imran tace “Yaya bamu ATM
card dinka zandan yima Lujain siyayyan kaya dasauran yan kananun abubuwa na mata da
batadashi” wani dan iskan kallo yamata sannan yadauki ATM card nashi yabata yace “6701 is
the pin” murmushi Anty Binta tayi tace “thanks Big bro” jan motanshi yayi yawuce itakuma Anty
Binta yakama hannun Lujain databi motan nashi da kallo suka wuce ciki.EPISODE 2️⃣6️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/



Shuku Anty Binta tasa akamata mai bala’in kyau, mai style yan kanana nan da nan tayi kaman
ba itaba, tasa aka wanke mata kumbunan kafa da hannu Anty Binta sai kallon yatsunta take
both nakafa da hannu sunada bala’in kyau gasu so chubby sannan yatsun farare dogaye, mace

mai ni’ima kana iya ganewa daga yatsunta both na kafa da hannu, bakaramin addu’a take kan
Ya Imran yafara son yarinyar nan ba dan Lujain is a gift from Allah, kyautanta Allah yamai bayan
wahalan rayuwan dayayi, 13yrs ba mata sai zaman kadaici da bautan Allah saisa Allah yabashi
Lujain cus babu abinda Lujain batadashi gatada shiga rai, bala’in shiga rai, daga zuwanta
saloon din nan harsun fara sonta, mai saloon din harda cema Anty Binta tanason sister nan
nata tamata influencing saloon din nan adauki pictures nata zata biyata da kyau, saida tanuna
musu matan aure ne mijinta bazai yarda ba sukabar zancen.

Biyan kudi sukayi sannan suka fito wani babban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login