Showing 60001 words to 63000 words out of 82745 words

Chapter 21 - Sakon So Book Complete by m Shakur ( By Ubeera ) .pdf

M Shakur   

11 Oct 2025

1647

yace “Lujain Muhammad yayanki na waje come with me”
teacher dake koyarwa juyawa tayi takalleta tace “tashi kije” ahankali ta tashi gabanta hakanan
taji yafadi to me wannan Uncle din yazo yamata yanzu, ahankali take tafiya Security nagaba
tana bayanshi harsuka fita gate din ko kadan bata lurada Mandawari ba security ne yamata
pointing inda yake tsaye yace “ga yayanki chan jeki karbi sakon” juyawa tayi takalli inda aka
nuna mata ido da ido tayi da Mandawari wani kalan faduwa gabanta yayi ta tsaya chak tana
kallonshi, dan murmushi yasakin mata hakan yasa ahankali tasaki wani kalan cute smile batare
dataje wajenba dakai yamata alamu datazo gently tafara tafiya tana tahowa yabi cikinta da kallo
dayaga baiyi girman dayayi jiyaba harta karaso gabanshi ta tsaya tana murmushi akunyace,
tsareta yayi da idanunshi she’s breathtakingly beautiful, gawasu cat eyes manyan dayaji yana
neman yasashi ya shide daurewa yayi yahadiye murmushin dayakeyi yace “har yanzu kinacin
abinci dayawa ko cus you are still very fat” wani iri taji ahankali takalleshi batare datace komiba,
hannunshi yasa acikin aljihun wandonshi yaciro iPhone 12 Pro max yamika mata, kallon wayan
tayi dasauri saikuma takalleshi murya chan kasa tace “mezanyi dashi”? Tsareta yayi da idanu
yace “I want to talk to you today ko bazaki amsa bane”? Girgizamai kai tayi ahankali batare data
amsaba tace “mezance agida”? Dan daure fuska yayi yace “ke yarinya ne dakowa saiyasan
nabaki waya karba kada raina yabaci inba hakaba zance nafasa auren ki” dawani kalan sauri
takalli fuskanshi, gira daya yadaga mata yace “ko kindaina sona yanzu”? Wani kalan murmushi
tayi ahankali akuma dan kunyace tace “inayi” murmushi yamata yace “to karba” ahankali tasa
hannunta dake rawa sosai ta karba gabanta nafaduwa zuciyanta yaki natsuwa, kallon security
dake kallonsu yayi yace “hide the phone and go back to your class I will call you by 7 dot na
yamma bye” yajuya yashiga motanshi, gently ta tura wayan aljihun uniform nata tajuya takoma
aji tana tafiya ahankali she’s super happy to see him amman kuma wani bangaren zuciyanta sai
tsinkewa yake idan ta tuna she just collect phone from his hand wayama IPhone zuciyanta yaki
natsuwa harsuka tashi by one na rana.


Jakanta tadauka tareda goyawa abaya tafito ahankali take tafiya tundaga mota Hamza ke
kallonta, Lujain nada wani kalan kyau da idan ka daura idanunka akanta barakaso kadaina ba,
batada fada baiganta dawani damuwa ba, deep down he wish Ya Imran will settle down da
yarinyar yadaina kallon karantan ta zaiyi farin ciki hartazo tabude kofa baisani ba saida ahankali
tace “ina yini” sannan yayi murmushi yakalleta yace “ya school kinyi karatu da kyau dai ko”
murmushi tamai tareda gyadamai kai bata kara cewa komiba sundanyi nisa akan titi yace “do
you need anything nasaya miki” girgizamai kai tayi tace “a’a nagode” murmushi shima Hamza
yayi ganin bata sake dashi ba batare daya kara cemata komiba har sukakai gida sai kallon kofar

gidansu Mandawari take she just wish inama zata ganshi, parking yayi tasauko tawuce ciki
Hajiya kadaine a falo tanajan charbi ganin Lujain saida tai murmushi itama dan murmushi Lujain
tayi tazo wajenta tsugunnawa tayi ahankali tace “ina yini Hajiya” shafa addu’a Hajiya tayi tace
“sannu da zuwa Lujain, jeki chanza kaya kiyi wanka zansa mai aiki ta kawomiki abinci sama ya
makarantan” ahankali tace “Alhamdulillah Hajiya” “sannu kinji Allah miki Albarka” ahankali tace
“Ameen” tashi tayi ahankali tanadan yatsine fuska sabida yanda cikinta kemata ciwo tawuce
sama dakinta tashiga dayake a gyare tsaf kayan makaranta tacire tashiga bayi wanka tayi tafito
hijabi tasaka tai salla akan dadduman ta kwanta tana kallon jakan makarantan ta da wayan ke
ciki gently tasaka hannunta tajawo jakan budewa tayi taciro wayan tana juyawa tana kallon
daga ganin wayan sabo ne ba’a dade ana amfani dashi ba kunna wayan tayi ahankali hotonshi
ne a screensaver tadade tana kallon hoton dan murmushi tayi tarasa mesa take sonshi duk idan
taganshi wani kalan farinciki takeji bude wayan tayi ganin babu password tashiga gallery duka
hotunan shine wanda yake buga ball da sauransu fita tayi takoma dial calls number dayane
awajen da akai saving da Mandawari tadade tana kallon number kaman magic dailing number
tayi yana ringing dasauri ta katse gabanta na duka uku uku kirane yashigo wayan ganin shine
yasa ahankali tasa hannunta tai picking call din tareda kai wayan kunnenta tai shiru.



Daga dayan bangaren yace “baki iya gaisuwa ba”? Dan murmushi tayi ganin yanda yakeson
girma murya chan kasa tace “good afternoon” shiru yayi baice komiba hakan yasa tace “hello”
dan lunshe idanu yayi harcikin zuciyanshi yakejin muryanta ahankali yace “tell me everything
that happen, karkimin karya kikamin karya I will hate you Lujain, so what happen daga farko
zuwa karshe dahar yasa aka auramiki wannan tsohon” dan shiru tayi kaman mai tunani saita
shiga bashi labarin duka abinda yafaru har zuwa yau, dan ijiyan zuciya taji yasauke ahankali
yace “yataba rike miki hannu” girgixamai kai tayi tace “a’a” dasauri yace “kwana fa a ina kike
kwana” ahankali tace “awani daki ni bansan inda yake zama ba” shiru yayi saikuma chan yace
“kinason na aureki Lujain”? Dan lumshe idanu tayi tabude su ahankali sannan ta gyadamai kai
ahankali tace “eh” murmushi yayi yace “to kicemai yasakeki basai ankamo mutumin ba I am
here now kina fitowa zan aureki and make you mine mubar Nigeria” murmushi tayi sosai cute
fararen hakoranta suka bayyana lumshe idanu yayi yana sauraron sautin murmushinta dan
lunshe idanu yayi yabude yace “nabaki 1 week ki kashe Auren nan kifito lemme marry you,
sannan kirage cin abinci look good katon cikinki yakoma flat kinada shape mai kyau amman
katon cikinki yahana shape din nunawa dan haka work on yourself kinajina” gyadamai kai tayi
ahankali dan murmushi yayi yace “bakice kina sona ba kodai a chat kika iya fadi” dan murmushi
tayi zuciyanta namata wani kalan sanyi dan hararanta yayi kaman tana gabanshi yace “tell me
now” Murya chan kasa akunyace tace “ina sonka Mandawari” dan dariya yayi datakejin dariyan
daga cikin wayan yace “I am inviting you to my welcoming party gobe zan tura miki address din
awaya kizo da bolt zan biya kudin kika iso makesure you look good kada kici abinci sabida
cikinki yay flat” cikeda damuwa yace “please loose weight I hate mace mai kiba kinajina” yay
maganan authoritatively dasauri ta gyadamai kai tace “to naji” yace “don’t eat anything again sai
fruits da daddare and sleep only fruits fruits zaki dingaci yanzu kinji” gyadamai kai tayi tace
“tom” ahankali yace “bye saina kira anjima da daddare”.

EPISODE 3️⃣1️⃣



Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI



Bin wayan tayi da kallo sannan ahankali ta ijiye wayan akarkashin gado tareda kife cikinta dake
mata ciwo sosai sabida yunwa tunda take arayuwanta bata tabajin yunwa irin na yau ba
chocholate dinta takalla dake leda lips dinta talashe tareda lumshe idanunta bacci ne ya saceta
sai around 6 ta tashi kulan abinci tagani ankawo a injiyemata tashi tayi tawuce bayi alwala tayi
tazo tai sallan la’asar sannan ta tashi tareda cire hijabi tana gyara towel din jikinta gaban kulan
taje tabude su ahankali, biryani rice ne dayaji naman rago baja baja aciki wani kalan kugi cikinta
yayi batasan lokacin data fashe da kuka ahankali ba tana kallon abincin cikinta nawani kalan
murdawa dawani kalan sauri tarufe kulan tareda juyama abincin baya tadaura kanta saman
gado, bude kofan dakin akayi hakan yasa ahankali tadago kanta Anty Binta ne idanunta kadai
takalla tace “why did you cry Lujain menene”? Girgizamata kai tayi alamun babu komi sai kuma
hawaye yazubo mata sharrr binta Anty Binta tayi da kallo ganin yanda tai zuru zuru yasa Anty
Binta tace “kinyi lunch a school”? Girgixa mata kai Lujain tayi ahankali dan ita har yanzu bata
iya karya hakanan ba, hakan yasa Anty Binta tabude kulan datagani adakin na abinci ganin
bata tababa yasa ran Anty Binta abace tace “wai what is this behavior Lujain? Cikin gidan nan
akwai wanda yamiki complain angaji da abincin dakikeci ne koko muncemiki munaso kirage
kibane why will you be hurting yourself like this eh Lujain”? Wani kalan matsiyacin yunwa takeji
dayasa takasa hadiye kukan, Anty Binta tadauki kulan gabaki daya takawo gabanta tareda saka
mata spoon akai tace “dau abincin nan kici” girgixa mata kai tayi tana kauda kanta gefe tace “ni
baran ci abinci ba” shiru Anty Binta tayi tana kallonta tace “sokike nabata dake ko Lujain” girgixa
matakai Lujain tayi tana goge hawaye tace “kiyakuri Anty” tashi Anty Binta tayi tace “shikenan
nima yau zan tattara nakoma gidan mijina dama sabida ke nadan zauna agidan nan sabida
kisake amman tunda you are so stubborn kina neman yima kanki illa shikenan ke kadai kiyi
amman zanje yanzu nafadi ma Hajiya sannan nafadama Ya Imran shima” tana maganan tamike
dasauri Lujain tarike mata hannu tana kuka sosai tace “dan Allah kada kifada musu Anty” fizge

hannunta Anty Binta tayi tafita daga dakin dan sosai ranta yabaci kana ganinta kasan bala’in
yunwa takeji barinma ita da yawanci ita kebata abinci tasan yanda Lujain kedacin abinci all of a
sudden tana neman kashe kanta, fuuuu tawuce tasauka kasa Hajiya na zaune tareda Abee da
shigowanshi kenan ganinta kadai yasa Hajiya tace “lafiya ranki abace Binta” cikin fushi Anty
Binta takalli Abee daya zubamata shima yana jira yaji meke faruwa tace “Ya Imran ga matanka
chan na neman kashe kanta” wani kallo daya mata yasa tadan lumshe idanu tabude tace “I
mean Lujain tun safe bataci abincin kirki ba, smoothie tayi na celery wai na weight loss, yanzu
ma takicin abincin da aka kaimata sai kuka take, Ya Imran kamata magana please” wani kalan
kallo yamata Hajiya tace “Imrana jeka mata magana haka yara yanzu suke su kawai su gansu
sun dawo kaman tsinke Allah day ya kyauta jeka mata magana” wayanshi yaciro batare daya
dagokanshi ba yace “kubarta taji yunwa zataci abinci da kanta” baki Hajiya tabude zatai
magana yamike tsaye yace “I have to go Hajiya”.
EPISODE 3️⃣2️⃣



Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


Fita yayi daga dakin yawuce gym dinshi dake compound din dayake all kayanshi na workout na
wajen saisa baimaje sama dan chanza suit na jikinshi ba.


Kallon Binta datai zamanta anan kusada Hajiya tayi tace “tashi kije ki kiramini yarinyar nan
munaji muna gani barinta zamuyi ta kashe kanta” tashi Anty Binta tayi ahankali tawuce sama
tun kafin takai wajen dakinta taga kulan abincin agaban kofanta tsugunnawa Anty Binta tayi
tabude kulan ganin kotaba abincin batayi ba yasa ta murza kofan zata bude taji kofan arufe ita
abinma dariya yabata tace “ohhh sabida kada asakici abinci shine kika rufe kofan ko, to Hajiya
na kiranki” tashi Lujain tayi ahankali tana rike cikinta tawuce bayi dan batamaso tanajin
maganan Anty Binta, maida kofan bayin tayi tarufe ta tsugunna awajen ita kanta mamaki take
mahaukacin yunwa takeji bana wasaba tunda uwarta ta haifeta bata tabajin yunwa irin wanda
takeji yau din nan ba, amman ita wlh saita daina cin abinci sabida ta rame Mandawari yakara

sonta sosai.


Anty tadade tsaye awajen ganin taki bude kofan yasa tajuya takoma kasa Hajiya tace “ina
take”? Ganin yanda Hajiya ta damu yasa tace “Hajiya karki damu zataci abincin yanzun nan”
cikeda damuwa Hajiya tace “dan Allah Binta koma wajenta ki tabbata taci, hankalina bazai taba
kwanciya ba ace yarinya na wajena takicin abinci awani dalili ita ba azumi ba sai bama kai
yunwa, yooo ita kibar har guda nawa ke gareta bandama shirme irin na yarintar Lujain, kiba
kyau ne azamanin mu idan kinada kiba ba kowani kalan mutun nema zaizo neman aurenki ba
sai masu kudi sabida ansan Kinacin abinci mai kyau gidanku babu yunwa ke Yar gata ce,
azamaninmu da zaran an ganki mara kiba ramammiya cewa ake gidanku da yunwa baku
samun abinci kuci, ni wannan zamanin nema naga gayu ake da siranta kiga yarinya kaman
zaka hure da iskan bakinka tafadi wai shine gayu, to wlh bada niba, ni baran miki karyaba Binta
ranan da mahaifin Lujain yakawota nan gidan da daddare dana fara daura idanuna akanta
abinda nafara cewa shine Masha Allahu yarinya bulbul da ita son kowa kin wanda yarasa akan
mene takeson bata kanta, ita batasan rama bazai mata kyau ba, sotake iyayenta suganta ace
bamu bata abinci yarsu dukta tsotse jesama idan bataci abinci ba kizo kifadamin dan saina
saba mata daga ita har Imran da akacemai taki cin abinci yakama hanya yay gaba abinshi”
ganin yanda Hajiya tabata rai yasa Anty Binta tace “a’a Hajiya ai baimakai hakaba zataci ma
bari naje” Hajiya tace “kada mata shayi ki tafin mata dashi” kitchen Anty Binta tawuce tahada
mata tea a babban flask tadauko a tray da cup tawuce sama gaban dakinta taje ajiye tray tayi
akasa tai knocking tareda murza kofan amman har lokacin a kulle at this point Anty Binta jitayi
itama ta damu sosai, bubbuga kofan tayi hakan yasa Maman Aneesarh dake daki tafito tace “Ya
Binta lafiya” dan murmushi Anty Binta tayi da idanu tamata alamu data koma daki kar Hajiya taji
hakan yasa takoma daki itakuma Anty Binta tawuce dakinta dan dauko waya dauka tayi tafito
Hajiya dake kasa tace “taci kuwa”? Dasauri tace “eh Hajiya taci” gaban dakin Lujain taje takira
number Ya Imran dan shine spare keys ke hannunshi amman har wayan ya katse bai daga ba
kusan 3 miss calls tamai bai dagaba sake fitowa Maman Aneesarh tayi jin yanda Anty Binta ke
knocking kofarta tazo har wajen tace “Anty Binta wai menene”? Abincin dake gaban dakin
tanuna mata tace “Lujain refuse to eat she wants to loose weight kuma yunwa takeji kaman ba
gobe” kallon abincin Maman Aneesarh tayi tace “harwani kiban dazata rage takedashi tanadai
so tama kanta wani illan kin fadama Ya Imran” cikeda damuwa Anty Binta tace “kema kin sanshi
ko kulamu baiyiba danake gayamusu” Kausar da tun dazu tadawo daga school tana bacci bude
kofa tayi tafito daga bakin kofa ta tsaya tace “ni wlh dukkan hanani bacci, ku barta mana Anty
Binta maybe cikin nan nata yakoma flat kaman nawa” tai maganan tana dariya dakuwa daga
Anty Binta har Maman Aneesarh suka mata daidainan Abee yashigo saman kallo yabisu dashi
daki Kausar tawuce dasauri Dan babu hula akanta tace “welcome Abee” wani kallo yama
Maman Aneesarh da Anty Binta strictly yace “I don’t wanna see any one of you anan” sadaf
sadaf kowa yawuce Abee yace “it’s time for magrib” duk dakunan su suka shiga, yace
“Fateema” dasauri Anty Binta tafito tadawo har gabanshi anatse tace “na’am Yaya” strictly yace
“call your husband kiwuce kitafi gidanki” dan murmushi tayi tace “to Ya Imran” wucewa yayi
yashige dakinshi batare daya kalli kofar dakin Lujain ba, wanka yayi yafito ya shirya cikin wasu
fararen shadda riga da wando dayawani kalan haskashi yasaka, Wandon as usual iya idon sahu

rigan kuma jumper babu aiki ajiki hannun rigan yakamashi hakan yanuna murdaden hannunshi
irin full nan dinnan turare ya feffesa jin an tada salla yasa yasaka slippers yafito dasauri
yasauka kasa a compound yaga Hamza da Abdallah na alwala shigowansu kenan wucesu yayi
yawuce yafita suma suka biyoshi abaya, sai bayan isha’i yafito daga masallacin yana tafiya
ahankali Mandawari dake tsaye gaban gidanshi tunda Abee yafito daga masallaci yake
kallonshi tunda yake in his life baitaba ganin mutumin da he feels so insecure about ba kaman
Abee, tundaga kai har kafa yake binshi da kallo yakasa ganin makusa, gashin kanshi dana
gemunshi baki sidik shida yake yaro shine ma yakeda yan furfura akai, tundaga nan kofar
gidanshi yana iyajin hadadden kamshin da Abee keyi, hada idanu sukai da Abee daya kalleshi
sau daya ya daukekai dasauri shima yadauke kai yana tsaki yace zaiga kaman na damu
dashine, kaman daga sama yaji muryan Olusay yace “are you scared kar babe dinka tafara son
mijinta danni wlh mutumin nan yafi mini kai kyau sau dubu, just look at a matured classic cool
guy dan Allah ga naira, kai kaga shaddan jikinshi kakosan shaddan Oman ne wannan special
edition din nan just guda 10 ne aduniya gabaki daya nidakai ba munje siya ba but bamu
samuba thats what he is wearing, Mandawari a word of advice this guy no even send you so
back off” dawani kalan sauri Mandawari yajuyo azuciye chakumeshi yayi hakan yasa Olusay
yadaga hannuwanshi sama alamun yay surrender sannan yamai alamu da idanu kan ana
kallonsu masu fitowa daga mosque sakinshi yayi yawuce cikin gidanshi yashige fuuuuu.
EPISODE 3️⃣3️⃣




Afalo yasami Musty yana zaune kusada Hajiya rikeda radio nata da screw yana gyara wata Yar
waya data katse ciki, dago kanshi yayi jin kamshi dakuma sallaman Abee yace “shine zaka
koramin mata to ai gani nan nazo daukanta ko angaya maka nima so nake tana zama agidan
dakake zaune bayan kowa yasan you are bad energy” wani kalan mugun kallo Abee yamai
batare dayace komi ba, Musty yace “Hajiya kinga irin kallon dayakemini kuwa kimai magana”
juyowa Hajiya tayi takalli Abee hakan yasa ya gyara fuskanshi da sauri tareda dan sosa kai yayi
yasami waje ya zauna Musty yagama gyara radio tareda kunnawa radio yafara magana yace
“gashi Hajiya angama” cikeda jin dadi Hajiya tace “nagode Mustafa Allah ya shimaka albarka”
dariya yayi yatashi bayin falo yashiga tareda wanko hannunshi yafito kusada Abee yazauna
yana kallon fuskanshi yace “how far”? Kallonshi Abee

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login