Showing 54001 words to 57000 words out of 82745 words
super market sukaje jakunkuna Anty Binta
tasaya mata da takalma masu kyau da yankune da agogo, bracelets irin na yanmata dinnan, da
kayan sawa english wears masu kyau sosai su sexy gowns, shorts, shirts, jeans dan sotake
tadinga sawa Ya Imran yasoma dawowa hayyacinshi, takara mata abayoyi, da turaruka,
harzasu fito tace “Anty su Chocolate” wajen chocholate sukaje sai alokacin Lujain tafara deban
chocholates dasu biscuits dabama tasan dasu aduniya ba ita Anty abin dariya ma yabata tace
“ai saisa kike kiba sweet tooth ni mutafi” biyan kudi sukayi aka kaimusu kayan mota sannan
suka tafi bayan magrib suka shigo anguwan Anty Binta ke tuki gidan dake kusada nasu sukaga
an bude ana shiga da sababbin furnitures Anty Binta tace “kowaye yasai gidansu Maman Adam
oho” kallon gidan Lujain tayi dayake abude sai gyare gyare ake har fenti anyi, Anty Binta dake
tuki tana kallon gidan tace “Maman Adam makotan mune sunada kirki gidansu ne amman sun
saida sabida mijin zai koma US yasami aiki a chan” daidai anbude musu gate suka shiga cikin
gidan, parking tayi suka fito zare hijab din school Lujain tayi tadauki ledan chocholate dinta tayi
gaba mai gadi natayasu daukan sauran kayan sallama tayi tashigo falon ahankali daga Hajiya
sai Musty da Abee afalo Musty ne ma yadago shi daga masallaci dabai shigo gidan ba sai
bayan isha’i, kallo daya Abee yamata yadauke kai Hajiya tace “yan makaranta an dawo”
Gyadamata kai tayi batare data karasa wajen ba tace “ina wuni” sannan takalli Musty ahankali
tace “ina wuni” murmushi yamata yace “lpy lau” Hajiya tace “aiko kitson yay kyau mekika riko
mana a leda” ledan takalla for the first time dan murmushi tayi tace “chocholate dina ne” dan
dariya Hajiya tayi tace “sabida bakiso kibani ne kike cewa chocholate dinki ne ai shikenan
jekisha Lujain” akunyace tadan sunnar da kanta kasa kaman mai koyon magana tace “Allah ni
zan baki Hajiya” shi kanshi Musty dan murmushi yayi jin yanda tai maganan Hajiya tace “to
nagode Allah amfana jeki cire kayan makarantan saikizo kici abinci” Gyadamata kai tayi tawuce
sama, tana shiga dakinta taga jakan school nata an ajiyemata waje daya, bayi tawuce tacire
kayan school nata tareda jefawa a washing machine sanan tai wanka da ruwan zafi tafito daidai
Anty Binta na shigowa dakin rikeda manyan ledojin kayanta Maman Aneesarh ma natayata dan
kallon Lujain din Maman Aneesarh tayi yanda kitson yamata kyau tace “Ya school”? Ahankali
Lujain tace “lafiya lau ina wannan baby”? Murmushi Maman Aneesarh tayi tace “tayi bacci”
sannan tawuce tafita daga dakin, Anty Binta saida tajera mata kayan tass dan ita bata salla
sannan tawuce tafita itakuma tana idarwa zama tayi kan gado tabude ledan chocholate nata
tashiga sha saida tasha daban daban kusan guda 7 sannan ta tashi tasakeyo alwala tafito
tahau kan dadduma tana salla shigowa Anty Binta tayi ta ijiye mata abinci a kula tana idarwa
taci batawani ci dayawa ba sabida yanda tasha chocholate din nan hawa gado tayi ko 3min
batayiba sai bacci danta gaji.
Wuraren 2:30 tabude idanunta ahankali sabida shegen yunwan datakeji, dakin da hasken wuta
hakan yasa ahankali ta tashi zaune sauka tayi daga kan gado tabude kulan abincinta dabata ci
jiya da daddare ba, yatsine fuska tayi danji tayi batasoncin abincin tamaida tarufe ledan
chocholate nata ta dauka tabude ciro chocholate guda uku tayi sannan tabude jakan school
nata tafito da books dinta tana duba abinda aka musu tanaci saida tacinye tass sannan ta tashi
ahankali tasake hawa gadon nan da nan bacci yay awon gaba da ita.
4:30 Abee yafito saida yatada kowa sannan yakoma dakinta knocking yayi tareda bude kofan
ahankali ledojin chocholate daban daban kusan 10 dayagani akasa yasa yakalleta tana kwance
kan gado tadan rufa tana bacci ta peacefully, katon ledan chocholate din yakalla dahar ya rage
yawa sannan daganan inda ya tsaya yace “Ke! Kee!” Firgigit tabude idanunta ahankali tareda
dan turo baki saikuma chan kaman wacce ta tuna abu bude idanubta tayi tass ganin Abee ne
ba Gwaggo ba yasa dasauri tamike tsaye tawuce bayi Abee yajuya yafice.
Wuraren 7:00 tabude kofan dakinta ahankali tafito ta shirya tsaf cikin kayan makarantan dasuka
mata mugun kyau tagoya jakanta abaya hannunta rikeda farin hijab din dabata sakaba tanabin
saman da kallo daidai Abee ya hayo sama kallo daya yamata yadauke kai itakuma ta tsaya
chak inda take takasa koda motsi saida yakaraso daidai inda take yace “today should be the
last time dazan ganki a falo babu hula ko lullubi” yana maganan yawuce dan turobaki tayi
tasaka hijabin sannan tawuce tasauka kasa saida tafara gaida Hajiya sannan tai breakfast sosai
taci abincinta baruwanta tashi tayi Hajiya tace “ina zaki Imrana dazai saukeki baima fitoba”
ahankali tace “zan zauna awaje ne inga rana” murmushi Hajiya tayi tace “tom jeki” wucewa tayi
tabude kofa tafita waje Kausar tabita da harara ahankali take kallon ko’ina na tsakar gidan tana
kallon yanda gardener dinsu ke zubama flowes ruwa, juyawa tayi tayi wajen gate nasu tabude
karamin gate din kadan tana leken waje batasan mesaba hakanan taji kaman wani abu na janta
zuwa wajene ahankali tasa kafanta tafita waje wani sanyi taji yashigeta ahankali tadaga kanta
tana kalle kalle titin estate din shiru babu motoci dan duka duka yanzu is 7:15, jitayi kaman ana
kallonta ahankali yasa ahankali tajuyo da kanta takalli gidan dake kusada nasu chak taji
numfashinta ya tsaya.
Mandawari tagani yana tsaye gaban gate nasu sanye dawani rigan jersey na Liverpool dark
blue dawani farin short bathroom slippers ne a kafanshi hannunshi rikeda iPhone 14 dayakai
kunnenshi da alamu waya yake amman idanunshi kyar akan na Lujain dabai taba tunani zai
gani ba dan duka duka ko 20min baiyi da zuwa duba aikin da akeyi agidan ba.
Wani kalan sauke numfashinta Lujain tayi takai hannayenta dasauri ta goge idanunta dan
tanaso takara gasgata ba gizo idanunta kemata ba Mandawari take gani yanzu haka agabanta
jingine dawata mota black yana waya, ganin still shine yasa taji gabanta nawani irin mugun
gudu takasa koda motsi, kusan 2minutes sukayi tana kallonshi yana kallonta yana waya sannan
yazare wayan daga kunne awulakance yamata alamu da hannu datazo nan, nuna kanta tayi
tace “ni?” Gyadamata kai yayi batare dayace eh ba, gabanta nafaduwa sosai tafara tafiya
ahankali takarasa gabanshi ta tsaya tana kallonshi, cikin sigan yanga yace “why are you looking
at me like that kinsanni ne”? Wani kalan lumshe idanu tayi tabude ga muryanshi nan sak wanda
takeji idan yana live video batare daya kyafta ko idanu ba tana kallonshi tace “nasanka” tsareta
yayi da idanu hakan yasa tace “you are Mandawari, kana buga kwallo, kai player Liverpool ne,
sannan kana bugama Nigeria, ina following naka a IG, my name is Lujain and I am your biggest
fan” takarashe maganan tana gasping breath tana wani kalan kallonshi kaman zata hadiye shi
da idanu, dan yatsine fuska yayi yadau wayanshi yadan daddana batare daya kalleta ba yace
“my biggest fan can’t be this ugly” dasauri takalleshi looking confuse, janye wayan dayake
dannawa yayi daga fuskanshi sannan yakalleta awulakance yanunata da wayan dake
hannunshi daga sama har kasa yace “I mean look at you, you are so soo fat, I don’t think ko mai
cikin 5 months takaiki katon teba, so please excuse me go and loose weight saiki dawo kimin
magana” yay maganan tareda juyawa yabude kofan motanshi ya shige tareda jan motan da
gudu yawuce yabar anguwan daidai hawaye na zubomata sharrrr, “ana kiranki” taji muryan
Kausar hakan yasa tajuya da sauri hada idanu sukayi da Kausar, Kausar zata juya takoma ciki
dasauri Lujain tace “Kausar” hakan yasa Kausar ta tsaya tana kallonta karasawa wajenta Lujain
tayida sauri, bakin Lujain har rawa yake cikeda wani kalan damuwa tace “Kausar dan Allah
kifadamin gaskiya, please inada kiba”? Tsayawa Kusar tayi tana kallon fuskanta ganin yanda
idanunta sun cicciko da hawaye ga damuwa karara afuskanta yasa tace “ke baki sani bane kike
tambayana” juyawa Kausar tayi zata wuce dasauri Lujain tarike mata hannu tace “dan Allah
kifadamini gaskiya nasan you don’t like me so you will tell me the truth” dan shiru Kausar tayi
yanda taga she really wants to know yasa tace “eh kinada kiba Lujain” kaman jira Lujain take
hawayen idanunta ne suka zubo dan zaro idanu Kausar tayi tana kallonta tace “Waike lafiyanki
kalau kodai kinada aljanu ne” sakin hannun Kausar tayi daidai lokacin Abee yabude kofa yafito
Kausar tayi wajenshi tace “Abee waje taje tana kuka” dan kallonta yayi yanda take tsaye awajen
gate takai hannunta kan fuskanta tana sharewa kawai yawuce wajen motanshi hakan yasa
Lujain ta taho tashiga motan Abee yaja motan suka tafi harsuka kai school baice mata komiba
sauka tayi tashiga ciki yabita da kallo kafin yatada motan yawuce shima.
EPISODE 2️⃣7️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Ranan har aka tashi daga school tarasa abinda kemata dadi koda taje lunch takasa cin abinci
sosai, 4 suka tashi tadauki jakanta tafito daga ajinsu tundaga nesa tahango Abee tsaye jikin
motanshi yana sanye da suit nashi black yasaka wasu bakin glass a idanunshi wayanshi akan
kunne yana magana ahankali take tafiya harta karaso inda yake tasauke kanta kasa tana wasa
da yatsunta murya chan kasa tace “ina yini” wani kalan kallo yamata sannan yashiga cikin
motan itama zagawa tayi tashiga yatada motan suka tafi, tunda suka shiga estates nasu take
kallon gidan Mandawari dataga gate din arufe horn Abee yayi aka bude musu gate suka shiga
cikin gidan parking yayi tareda kashe motan dan juyowa tayi ta kalleshi daidai shima yadan
kalleta ganin bata bude kofa tafita ba, sauke kanta tayi kasa tashiga wasa da yatsunta kaman
yabude kofa yafice abinshi saikuma yace “me kike bukata”? Dan dago kanta tayi takalleshi
ganin ita yake kallo yasa ahankali tasauke kanta kasa tana wasa da cute white chubby fingers
dinta dakenan gyare tsaf murya chan kasa kaman batason abinda zata fadi tace
“dama….dama…..” saikuma tai shiru batasan tayaya zata tambayeshi kudiba, dan dago kanta
tayi ganin kallonta yake yasa tadauke kanta dasauri tace “I…..don’t have any money Uncle……”
taidan shiru realizing this is the first time take kiranshi kumama wai Uncle abin yamata wani
banbaran abaki, dan kallonshi tayi kadan suka hada idanu dan lankwashe kai tayi kaman wata
macijiya murya chan kasa tace “kuma…..kuma magani nakeson in saya” kallonta yake kyar
batare dayace komiba, dan dago kanta tayi suka hada ido murya chan kasa tace
“uhmmm….maganin rage ki…kiba” dan lumshe idanu yayi yakalleta sannan yace “a ina ake
saida maganin”? Dan kallonshi tayi kana ganin kwayan idanunta kasan batasani ba, ahankali
tace “nima bansani ba amman ai za’a samu a kasuwa” wani kalan kallo dayamata yasa tamaida
nata idanun kasa yace “kintaba ganin yaran gidanmu sunje kasuwa?” Girgixamai kai tayi,
ahankali yace “kin taba zuwa kasuwa?” Sake girgixamai kai tayi tace “amman Gwaggo na na
zuwa tana sayo magunguna da yawa nasan zan samu nima innaje” tunda take maganan yake
kallonta yace “did anybody told you kinada kiba a school ne”? Sake girgixamai kai tayi tace “a’a”
ahankali yace “maisa kikeson kisha maganin rage kiba”? Batasan mesaba hakanan taji takasa
fadamai karya ahankali tace “Mandawari bayason mace mai kiba” yadade yana kallonta
harsaida tadago kanta takalleshi dan gajeren tsaki yayi yace “yabaki maganin rage kiban to” yay
maganan yana yunkurin tashi dasauri tace “namishi magana”? Dan tsayawa yayi saikuma
yajuyo yakalleta yace “I told you zaki iya kome kikaga dama I don’t consider you my wife and
you are not my wife, dazaran this whole thing yalafa aka kamo yaron zan rabu dake” wani kalan
murmushi tayi daya lobar mata da dimples nata tace “thank you Uncle” tai maganan tana bude
kofa tafito tawuce ciki tana tafiya ahankali yadan bitada kallo.
Hajiya kadaine a falo da Maman Aneesarh ahankali tace “ina yinin ku” murmushi Hajiya tayi
tace “sannu da zuwa” Aneesarh data gani taduka tadauka tana murmushi tace “zomuje dakina”
murmushi Mamanta tayi tace “wanan saita batamiki daki wlh da barna” murmushi tayi tace “dan
Allah kibarni natafi da ita Allah ina sonta” Maman Aneesarh tace “shikenan kuje” wucewa sukayi
sama Abee yashigo shima gaida Hajiya yayi, Hajiya tace “sannu da zuwa Imrana” ahankali
Maman Aneesarh tace “sannu da zuwa Yaya” Gyadamata kai yayi yawuce sama, Maman
Aneesarh takalli Hajiya tace “Hajiya Ya Imrana is so nice towards this girl” Hajiya tace “Imrana
has always being nice to kowa, banbancin Babba mai hankali kenan da kananun yara samari,
Lujain is just like Kausar kozai wulakantata bazai iyaba dan kaman diyar cikinshi ne bazai iya
imagining wani ya wulakanta mai Kausar ba, nasan Imran dina dudda bayason Auren nan bazai
taba cutar da ita kokuma yaga abin cutarwa yabari ya cutarda ita ba” Maman Aneesa tace
“saisa yasata a makaranta mai tsada ko su Kausar ba makarantan turawan nan sukayi ba”
Hajiya tace “inba irin makarantan nan ba awanne za’a sata yarinyar da fuskanta ya zagaye
yanar gizo so kike kullum adinga dukanta ta tsani makaranta gabaki daya taki fita” ahankali
Maman Aneesarh tace “Hajiya ni tausayi yarinyar ke bani koda zamuso zamansu da Ya Imran
tayaya zata fara kula da Ya Imran? Babu abinda ta iya wannan saidai shi yakula da ita ai” Hajiya
tace “daga next week duk idan tadawo daga makaranta zan dinga sata tana shigowa kitchen
kuna koyamata abu daya biyu haka harta kware” kallonta Maman Aneesarh tayi tace “Mama
kinason auren su ne?” Hararanta Hajiya tayi tace “kin isheni da tambaya amman abu daya zan
fadamiki babu Babba dazai cemiki yanason mutuwan aure duk Auren da aka daura fatanmu
shine yadaure har abada, idan zamansu tare Alkhairi ne Allah yahada kansu kullum shine
addu’a na”.
***
Olusay ke tuki suka shigo estate din, horn yayi gaban gidan gateman yabude musu suka shiga
ciki Olusay yace “wow gidan yay kyau wlh Man” yadan kalleshi ganin yana cikin IG, karasa
parking yayi ganin Mandawari baima saniba yasa gently yakai hannunshi yadaura akan
shoulder nashi hakan yasa dasauri Mandawari yakalleshi yace “ohh harmun shigo”? Olusay
yace “kanachan kana kallon hoton stalker naka yaza’ayi kasani” kallonshi Mandawari yayi,
ahankali Olusay yace “can I talk to you Man I am serious”? Dan yatsine fuska yayi yana cire
sitbelt yace “what”? Dan jim Olusay yayi dan baisan how he’s going to take the magana ba
ahankali yace “first of all Muhammad I don’t know your reason na sayan gida right next to gidan
da stalker dinka ke aure, nabiyu you saw everything mezakayi da matan aure yarinyar data
Riga tayi aure? Thirdly kasan your Mom bazata taba bari ka auri yarinyar that went viral online
hakaba, and nahudu kariga kayi loosing chance dinka da bakin wulakanci for the past how
many years yarinyar nan namaka magana wulakancinka yahanaka kulata sai yanzu bayan an
mata aure ne zaka fara sonta what’s all this Man? Mezakayi da wannan yarinyan kanada
thousands of mata har yan film dake sonka sai wannan da aka mata unfortunate Marraige din
nan zaka wani fara so” shiru Mandawari yayi saikuma chan yace “you want an honest answer?”
Gyadamai kai Olusay yayi ahankali yace “I buy this house triple amount na gidan nan because
of the girl dan wasu harsun sayi gidan nakara kudade, sannan kai kanka you just call the
marriage unfortunate one kawai anyishine dan ayi blocking mutane from saying shit akan
honest mistake datayi well koma Iskancin tayi da mutumin I know he must be the one to force
her dan that girl love only me, and again what made you think Mom harta isa tagayamin ga
wanda zan aura ga wanda bazan aura ba bayan ita taje tayi aurenta da Dad dina yarasu? She
have no right over me, lastly kowa yarinyan nan ta aura I don’t bloody care she belongs to me!
Just me, watch and see how I win my girl and shape her to abinda nakeso that fat everything
she will loose it, idanma takasa dakaina zan kaita amata tummy tuck” dan murmushi yayi yace
“how is my welcoming party going”? Tabe baki Olusay yayi yace “I know how stubborn you are
just be careful, mijin yarinyan nan is not our mate that’s number one tsoho ne, nabiyu kuma he’s
a soldier, a retired old soja” dan dariya Mandawari yayi yace “that’s more of the reason why I
want to save her, mezatayi da tsoho dakeda yaran dasuka girmeta? She’s to young and fresh
for him, bata sonshi ni kadai takeso, just sit back and watch how I open her eyes and show her
the world” “hmmmm” Olusay yace da mamaki yabude mota yafito shima Mandawari yafito
Olusay yace “ni bantaba ganin mutum irinka ba yarinyar dabaka nuna mata so bamaka kulata”
dan tsaki yayi yace “leave me alone please, kaji da kanka” taba yaciro yakunna yanasha Olusay
yawuce ciki abinshi, saida yagama sha ya yarda karan ya shiga ciki.
EPISODE 2️⃣8️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Wuraren magrib tabude kofanta tafito tana daure dawani pink towel a kirji rikeda Aneesarh datai
bacci Kausar tagani dazata shiga dakinsu dasauri tace “inane dakinsu Aneesarh”? Kallonta
Kausar tayi saikuma tamata pointing dakinsu Aneesa wucewa tayi tashiga Maman Aneesarh
naciki tace “laaa tayi bacci” gyadamata kai tayi tana kallon wayan Maman Aneesarh dake kan
gado, karban Aneesarh tayi ta kwantar da ita sannan ta tashi takalli Lujain dake kallon wayan
tace “Ya akayi Lujain”? Ahankali tace “dan Allah na ari wayanki