Showing 36001 words to 39000 words out of 82745 words
a fighter! Yarona jarumi ne that can fight anything, inasonka sosai Imran” Mama
tai maganan duka ahankali takai bakinta saman sumanshi ta sumbaci kanshi jin kukan dayakeyi
na raguwa ahankali, murya chan kasa tace “zakasha ruwa”? Girgixamata kai yayi alamun a’a,
murya chan kasa tace “shayi fa Kausar ta dafamaka shi zakasha”? Shiru yayi kaman bazaice
komiba saikuma ya gyadamata kai ahankali wani kalan hamdala tayi azuciyanta tace “kwanta
anan in daukomaka” baiyi ko motsi ba daga jikinta hakan yasa gently ta kwantar dashi akan
gado da saurinta tai wajen kofa tana budewa taga tray shayin da kof an ijiye musu da magani
balli daya rak akai hakan yasa tadauko tashigo dagashi tazo tadinga bashi shayin tass ya
shanye yasha maganin sannan yakara maida kanshi kan cinyanta ahankali take shafa bayanshi
ahaka bacci yayi awon gaba da shi.
Kusan 2hrs Hajiya tayi adakin saida ta tabbatar da bacci yashigeshi sosai dan ayanda yake
baccin zaka gane yadade baiyi bacci ba yasa ta tashi tareda jan bargo tarufamai, tsugunnawa
tayi ta tofamai addu’o’i sannan tabude kofa ahankali tafita daga dakin tasauka kasa, duka yaran
tagani afalo Musty shima yana nan Kausar da Abdallah takalla dake kallonta ba kakkautawa
tace “In sha Allah komi yazo karshe now kowa yaje yacigaba da aikin dayake” tana maganan
kowa yamike yana hamdala Maman Aneesa da Kausar dasu Sajida da Zainab suna kitchen
Hajiya tawuce daki tama Musty da Anty Binta alamun su biyota daki, zama duk sukayi Anty
Binta tace “Hajiya menene”? Ahankali Hajiya tace “anya auren nan dana yarda akama Imrana
namai adalci kuwa? Nasan wannan matsalan na Imrana tun bayan rasuwan Maimuna amman
bantaba ganin yanda yake ciwon da idanuna ba sai yau kunsan har yayi yagama babu wanda
zai sashi a ido sai likitanshi yauda naganshi jikina yay sanyi” shiru duk sukayi saikuma chan
Musty yace “Hajiya aure rahama ne kuma mata garkuwan mijinta ne, saiki iyaganin sanadin
auren nan sanadin warakanshi kenan” shiru Hajiya tayi tana kara tuna condition dinshi tace
“anya kuwa Musty zancen auren ne yatada ciwon nan fa, nidai barance komiba dan lamarin nan
is complicated, abu daya dana nasani shine idan yaji bai iya zama da yarinyar nan zai sauwaka
mata bazan hanashi ba idan kuma ya zauna da ita still duk daya all abinda nake cewa shine I
will support Imrana dan Imrana is suffering fiyeda tunaninku, My son is suffering” cikeda kulewa
dakuma damuwa Anty Binta tace “koma wanene wannan mutumin dayama Ya Imran abin nan
wlh wlh bazamu yafemai ba zaisan yataba bawan Allah, tayaya ma Ya zai zauna da wacce ko
Kausar dinshi ta girmeta ni kawai sabida tashin hankalin nan yasa nai shiru amman idansu Ya
Abdul police suka kamo yaron dazaran yayi confessing agaban duniya ya wankesu Ya Imran
kawai ya saketa tunda baison Auren abarshi meyake nema? Yanada yara yanada sanaa
yanada family Hajiya, Muna kadai yakeso and he will love her har karshen rayuwanshi, mubar
Ya Imran yay kome yakeso Auren nan is nothing but a trash…….” wani kallon da Musty yamata
yasa tai shiru da maganan yakalli Hajiya yace “Hajiya kuyi taking komi easy nasan kun damu da
Imran, yanzu an gama saka furnitures adakin da yarinyar zata zauna?” Kallon Anty Binta Hajiya
tayi tace “angama aikin?” Tabe baki tayi tace “oho ni banduba ba kaima Husby saikace auren
soyayay ne dakawani bada kwangilan saka sabbin furnitures adakin kaman wanda suke dakin
basuyiba” hararanta yayi yatashi yace “bari naduba dakaina” sama yawuce wani daki wanda
dagashi sai kwanan lungun dakin Abee yaje bude dakin yayi dakin yay kyau anmishi wani
babypink fenti sannan ansaka wani farin gado mai bala’in kyau, ga carpet akasa ga komi da
komi, kusanshine yay komi da kudinshi dan Imran deserve more kome yamai bai biyashi ba
aduniyan nan maida kofan yayi yarufe sannan yakalli lungun dakin Abee saikawai yajuya, fita
yayi waje yadauki wayanshi yakira Anty Binta sannan yashiga bayan mota yazauna fitowa tayi
sanye da mayafi tazo wajen motan bude baya tayi tashiga tana kallon fuskanshi ganin bacinrai
karara akai, kai tsaye yace “are you trying kisa Hajiya ta tsani yarinyar da she’s not to be blame
for anything daya faru ko itama kinzaci tanason auren ne? Kinsan hakkokinta nawa aka tauye
Fatima? Explain your behavior to me?” Shiru tayi tana kallonshi saikuma ahankali hawaye
yazubo daga idanunta da sauri ta sharesu tace “kayakuri Husby nasan ban kyauta ba, wlh ko
nasan yarinyar is not to be blame for anything kawai I can’t help it ne some part of me nacemin
duk ita taja inda at the first place bataje bayin maza ba itada Ya Imran bazasuyi wannan clash
dinba, sannan inda badan aurenta ba PTSD Ya Imran bazai tashi yau 4days kenan ko 5 nema
dukanmu bamu sashi a ido ba baci basha ba fita,duk ciwon dazai hana Ya Imran fita masallaci
ai kasan babba ne, jibi yaranshi yanda sukai zuru zuru Abdallah yayi missing test a school
yaron dake medicine sabida all this things, look at Hajiya, look at us kanninshi kowa ya susuce
kaman bamuba kowa lost his happiness, I can’t help it but to blame her for everything dudda
nasan non of it is her fault I am sorry Husby” bakaramin tausayi tabashi ba ganin yanda take
kuka jawota jikinshi yayi ta kankameshi yana bubbuga mata abaya murya chan kasa yace “I
know non of this makes sense nasani, but I want you kizama kaman ni duk wani hard situation
dakika sami kanki arayuwa think of the positive things that could come out of it, yanzu idan aka
wayi gari Auren nan resulted to something meaningful fa mezamuce? Imran yazo yana sonta
morethan the way yaso Muna ma” dagokanta Anty Binta tayi daga jikinshi takalleshi kallon irin
anya, murmushi yamata yace “yes baby is very very possible, I am a man loneliness is not good
for anyman, kinzaci yanda Muna ta mutu feelings din Ya Imran sunbita sun mutu sun tafi ne? No
wife basu tafiba, Ya Imran is suffering nasan bai kamata ina gayamiki this ba danke kanwarshi
ce but I think you need to know dan kece elder idan su Sajida sukaga bakison yarinyar kina
kyaranta suma haka zasu dingayi, abinda yakamata muyi nidake is muzama team and help
Imran batare da yasani ba let’s make them come closer, let’s unite them batare dasu kansu
sunsan they’re getting closer ba, bakisan kirki da Imani dakuma kyautatawan Yayanki bane
yasa Allah yamishi kyautan fresh yarinya rana tsaka ba, is it easy mutum mai shekarunshi
yasami danyan yarinya jagab haka shekara 19 bakisan irinsu ne sukafi shiga zuciyan babba
tashi dayaba? Yanzu idan ya auri bazawara ko wata mai shekaru haka is not like I am saying
bazai sotaba no zai sota but time phase dazai dauka to fall in love with yarinya karama will be
faster than time phase dazai dauka to fall in love with Babba mai shekaru, budurwa of 19 are
sweet charming an shiga rai” turobaki tayi tace “wannan daka dage kanamin wannan bayanin
hope ba shiri kake kamin kishiya da yarinya Yar 19yrs ba” wani dariya maganan ta yabashi
baisan lokacin da yay Yar dariya ba yace “mata da kishi Allah dai ya yayemuku yanzu dai
kingane what I am saying, I want us to be team both not team your brother kadai” murmushi
tamai ta rungumeshi tace “thank you Husby for enlightening me, na amince and I am ready to
support you and make things work daga yanzu nadawo team both” murmushi yamata yace “da
this weekend zamu koma gidanmu an gama fentin but for this our mission nakara miki one
week” dariya tayi sosai tana murna yace “muje kiga gidan daganan ma nadanyi kin gane ai” Ya
kashe mata ido daya” dariya tayi tafito suka koma gaba suka bar gidan.
Asabar!
Karfe 4:30 yabude kofanshi yafito yana sanye dawata white jallabiya dayasha karin guga
yasaka hula fara sai wani kalan kamshi yake mai kwantarda hankali, bakaramin kyau yayi ba
saida kana kallon kwayar idanunshi zakaga yadan fada sosai yarame, direct dakin Hamza
yashiga bubbuga bakin gadonshi yayi Hamza yabude idanu ahankali ganin Ya Imran har sake
goge idanu yayi zaiyi ihu yatuna maganan Dr, “bazaka tashi bane” Abee yay maganan ahankali
murmushi yayi ranshi fess yatashi da sauri yace “natashi Yaya Imran” ficewa Abee yayi daga
dakin yashiga dakin Abdallah dake bacci Abdallah daya bude ido yaga mahaifinshi saura kadan
yafada jikinshi yadaure baiyiba yatashi yawuce bayi yana murmushi kaman anmai kyautan
dream car nashi c300, dakin Kausar yawuce ya kunna wuta yana kallon yanda ta kudundune
abargo dakinta kaman fridge AC yafara kashewa sannan yabubbuga gadon yana karbe bargon
hakan yasa tabude idanunta ganin Abee dawani kalan sauri ta mike tsaye daga gadon kawai
tafada jikinshi dan lumshe ido Abee yayi yabubbuga bayanta, sakinshi tayi tana murmushi tace
“Abee sorry na rungumeka banyi wanka ba mafarki nayi na rungumeka saisa ina ganinka nayi”
hancinta yaja yace “talkative” washe mai baki tayi yajuya yafice daga dakin kap yatada sister
nashi duk wanda yaganshi saikaga smile of happiness akanshi sauka kasa yayi zuwa dakin
Hajiya dayaga wutan a kunne ganinshi batasan lokacin data shafe addu’an datake ba tace
“zaku wuce masallacin”? Gyadamata kai yayi yace “eh Hajiya” murmushi tayi tace “incedai
wannan mayen baccin Hamza yatashi” dan murmushi yayi yace “yatashi” daidai nan daga waje
Hanza yace “to natashi Hajiya kuma naji abinda kikace” murmushi yayi yafito daga dakin
Hajiyan suka fice Hajiya tadaga hannu tareda godema Allah daya fito yau dakanshi.
Hi GGM, did you know just because you act different baya nufin kai mahaukaci ne, sometimes
is just PTSD! Now check on your family members and share ❤️
EPISODE 1️⃣6️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Wuraren 8 yashigo gidan na safe sabida yanda Baba Liman ya tsaidashi sunyi maganganu
masu tsawo, da sallama yabude kofan falo yashigo ganin Musty, Harun da Abdul police a tsakar
falon kan lallausan carpet suna breakfast da waina yaji man shanu da farfesu, ganinshi yasa da
hannu Musty yace “zo wlh saura kadan su Abdul su cinye maka wainar ka” dan murmushi yayi
ga mamakinsu tahowa yayi yazauna kusada Musty cikinsu yadauki spoon yafaracin wainar
dasu babu wanda hakan baimai dadi ba, sosai yaci abincin kodan baici abinci yau kwana nawa
bane oho saida yaji yakoshi sannan yatashi daga wajen dauke da mug na coffee Hajiya sai
farinciki take sabida yanda taga yaci sosai, laptop Abdul yaciro daga jaka yakunna yaduba wani
abu saikuma yarufe yatashi zuwa gaban TV yace “BBC sun fara sanarwan kuyi shiru muji” BBC
suna sanarwa cewa wani ma’aikaccen company shi yahadamai wannan shairin sabida bai
bashi miliyan dari ba dakuma takardun company tareda saka hotonshi a tashin kan cewa duk
wanda yaganshi hukuma na neman yaron, saikuma nabiyu Alhaji Imran mijin yarinya da ake
cewa yay fasikanci da itane ga shaidanan daga iyayensu nan aka fara nuno su Baba dasu
Hajiya suna cewa ma’aurata ne, sannan video edit ne su kansu tashar BBC sun tabbatar da
hakan sabida ma’aikatansu dasuka tabbatar dahakan, saikuma na karshe suna kirada Al
unmma sudaina yada karya idan kunne yaji gangan jiki ya tsira shikuma wannan gayen duk
inda yashiga hukuma zasu bishi har wajen akamoshi” adaidai nan news din yakare, yan dakin
kowa yashiga cewa Alhamdulillah Alhamdulillah, kurban shayin Abee yayi ahankali su Musty
suka shiga janshi da hira sai wajajen 11 yatashi dan yaje ya kwanta, sama yawuce ganin Anty
Binta nafitowa daga wani dakin da dagashi sai corridor shiga dakinshi rikeda kaskon turaren
wuta bamata lurada shi ba saida tajuyo ganinshi yasa tace “Yaya ina kwana” Gyadamata kai
yayi batare daya amsa ba hakan yasa tawuce ahankali yakarasa gaban dakin harzai wuce
saikuma yadawo kaman baiso yamika hannunshi yabude kofar dakin, gidansu nada bala’in
kyau bana wasaba but dudda haka dakin nan standout agidan gabaki daya yakai kusan 2min
tsaye gaban dakin yana kallon cikin dakin batare daya shiga ciki ba saikuma yajawo kofan
yamaida yarufe yawuce dakinshi.
*****
Yanda Lujain kejin jikinta ita kanta har mamaki take maganin shawaran kesata jin haka, gashi
Gwaggo kullum saita mata dilka ta gurgurza mata jiki hakan yasa fatarta yawani kalan kara
kyau dudda tanada fata mai kyau, jikinta yakara wani kalan lumu lumu dawani extra taushi
daman yawanci masu kiba nada taushin fata barin ita da fatarta is ultra soft yanzu saiyazama
wani extremely soft.
Yauma kaman kullum daga ita sai wani pink towel data daura akirji an tsife nata kalaban dake
kanta da alamu ma an wanke gashin sabida yanda bakin keta uban shinning gashinta is so silky
and coily ga tsayi an mata parking nashi dawani blue ribbon mai kyau anyi donut da bakin
gadhin, tana zaune a tsakar gida kan tabarma kusada Gwaggo dake tankade wani gari
hannunta manya manyan chocholate ne guda biyu tanaci tana kallon yanda Gwaggo ke
tankaden, dan juyowa Gwaggo tayi takalleta tace “mekike kallona nan nan dazan fita babu
yanda banyi dakeba muje tare kinki fita akanme zaki dinga tsoron fita, rabon dakimaje jikin gate
kibude ki leka waje harna manta, nace babu abinda mutane zasu miki dazun baki tashiba BBC
sun saka sanarwan an wanke ku tass to mezai faru, koma ba’a wanke kiba akwai wanda ya isa
yamiki kallon banza ne ina taredake eh”? Dan turobaki tayi tace “Ya Samira fa tanunamini
Gwaggo wlh muryana ne sarai ni bansan ya akayi yay tsawon nan ba” hawaye ne yacika
idanunta, murya chan kasa tace “kowa yanzu har yan islamiyyan mu kallon Yar iska sukemini
koni banmantaba tayaya wayanda suka kalla zasu manta wlh kaman in mut…..” buge mata baki
Gwaggo tayi tace “wlh kika karasa fadin kalman nan saina dokeki wawiyar yarinya kawai asalin
yan iskan duniya masu fasikancin na rayuwansu suke abinsu ba saike dabaki komiba duk kinbi
kin dami kanki duk jibi yanda kika fada kalli wuyanki har yau idanunki basu koma daidai ba
sabida kuka” tashi dagakan tabarman Lujain tayi da gudu tashige dakinsu tana kuka Gwaggo
tabita da harara tace “aisaiki tayi bakida damuwa ne yarinya tunda inasa kudina ina sayamiki
kayan kwalama ubanki nasaya miki ne” Gwaggo tai tsaki tacigaba da tankaden datakeyi
Gwaggo tacigaba da masifa tace “yarinya sabida ita yau kwana nawa kenan ban samu nahuta
ba amman ta isheni Alhamdulillah yau zanyi bacci nai munshari wahalar ki kuma saidai takoma
kan mijinki Imrana nahuta” Gwaggo takarashe maganan ahankali sabida tunda ta tasa rigiman
batason auren Gwaggo ta zuzxuba mata karya bata sake mata maganan ba ko anjima akazo
kaita da ubanta zata barta ai bata isa tama Babanta wannan haukan da shirmen ba tuni zai
karairayata yabama karnuka kashin itane dai data raina takema yan abubuwa, jin kukan yay
yawa yasa Gwaggo takasa daurewa dan jin kukan Lujain take har cikin jinin zuciyarta kakkabe
hannunta tayi tawuce dakin.
Anayin mangariba Gwaggo takirawo su Samira dukansu kuskus sukayi nadan tsawon lokaci
kafin su shiga falon Gwaggon inda Lujain take a zaune tana shan tea, ganin Samira rikeda
dawani babban jaka yasa Lujain ta tashi da sauri tace “Ya Samira baby yakawo miki wani abu
ne”? Daure fuska Samira tayi tace “banace kidaina kiramin saurayi da sunan danake kiranki ba”
dan murmushi tayi mai bala’in kyau tace “to yakuri menene amman ajakan” jakan tabata tace
“Baba yace mukawo miki ki shirya bayan isha’i yana nemanki” zaro idanu tayi takalli towel din
jikinta tace “Kodai yaganni da towel ne saida ya aikomin da kaya na shiga uku” tai maganan
tana fizge jakan dasauri tai uwardaka zata fara farke ledan Samira tashigo tace “Malama jeki
wanka” daga falo Gwaggo tai ihu tace “da ruwan maganin nan zaki wanka” wucewa bayi tayi
itakuma Samira ta zauna abakin gado tana bude jakan wani simple lafaya lace ne mai kyau red
and gold, sai Yar cikinta, sai set na dankunne da sarka na zirconia mai kyau shima sai flat shoe
na Zara kayan dai gabaki daya akalla Baba yakashe 35k fitowa tayi tana zaro idanu tana kallon
kayan tace “laaaa harda sarka da takalmi anya ni Baba yace akawo mawa kuwa saikace zanje
biki” tabe baki Samira tayi tace “idan kinje ki tambayeshi nidai Malama kidauko pant da bra
kisaka kizo kisa kayan” tsayawa tayi jimm kaman mai tunani Samira tace “kuma kima kanki fada
kidaina daura towel akirji kina zama koda yaushe nonon ki duk zasu zube ne” dan yatsine fuska
Lujain tayi tace “Ya Samira ni damuna suke wlh na tsani saka bra da pant, pant na cimini cinya”
tsakani ga Allah tai maganan, Ya Samira tace “kiba yasa suke cimiki jiki, ciye ciye yamiki yawa
babu namijin dazai soki idan kina haka cus yawan kiba is disgusting” tsayawa tayi tana kallon
Ya Samira saikuma tajuya mata baya tasauke towel din ta daura a waist zata fara saka bra,
saida tasaka bra din tajuyo tace “saisa su Ya Abida basa sona sabida inada kiba I am
disgusting” tsayawa kallonta Ya Samira tayi this is the first time take ganin jikin Lujain haka
dudda she’s putting on bra tanada very nice fat boobs gasu a tsaye, inda ace batada kiban nan
bakaraman Cinderella za’ayi ba anan gwarama da aka mata Auren nan dan nan gaba kar
samarinsu suzo suna ganinta sudinga cewa Lujain takeso, ganin yanda Ya Samira ke kallonta
yasa dawani kalan sauri takai hannunta takare kirjinta tace “mehaka Ya Samira”? Tsaki Samira
taja tace “Malama kizo kisa kayan nan angayamiki ke nake kallo ni I am lost in my thought ne
mezan gani anan da banda shi” karasa saka pant Lujain tayi tazo Ya Samira tashiga shiryata
bata mata kwalliya ko dayaba kawai lafayan tasaka da dankunne da sarkan ta tayafamata
lafayan akai sai Lujain tayi kaman ba itaba ita kanta Samira saida tace “dayake duk wanda
yasanki da towel yasanki inbadai kayan