Showing 9001 words to 12000 words out of 82745 words
sauko tana sanye da doguwan
rigan atampa mai kyau tasaka bakin safa akafanta da flat shoe sannan tarike milk hijabinta
ahannu, da dankwalinta a hannu, da jaka da ribbon a hannu tana shigowa ajiyesu tayi akan
kujera tazo wajen Abee da sauri tabashi ribbon din tace “Abee kamamini gashin” baki Hajiya
tasake tace “yanzu kiwuce duka matan dake dakin nan kitafi wajen ubanki yamiki parking gashi
dakecin abinci” turo baki tayi tawuce tabama Zainab tace “samin Anty” murmushi tayi takama
gashin da baida wani tsawo tace “kawo kallabin na daura miki shima kawowa tayi tadaura mata
sannan tazauna tana breakfsat dasauri sauri hada ido tayi da Abee dake kallonta, kallon daya
mata kadai yasa ta faracin abincin ahankali anatse dan yahanata cin abinci da sauri adolenta ta
natsu ta cinye tass sannan ta tashi tasaka hijabinta itada sauran yaran sukabi Ya Hamza dazai
kaisu sukabar gidan.
2 slice na waina yaci acikin hudun da aka sakamishi sannan yatashi yawuce sama dan
shiryawa, tsaf ya shirya cikin black suit dayasaka wata farar Riga aciki mai shegen kyau, baisa
boturin jacket na suit dinba hakan yasa kana iya ganin farin, yasa black Wandon suit din daya
tsayamai a idon sahu as usual yanda tsayin wandunanshi suke, covershoe yasaka na gucci
dake wani shining, wannan karan babu any hula akanshi hakan yasa gashin kanshi yay wani
kalan kyau ya kwanta lub sai kyalli suke, ahankali yake saukowa rikeda wata jakan laptop a
hannunshi daga Hajiya har duka matan ta duk suna falo da Matan Ibro itama yanzun nan
tashigo tanacin ragowan waina dan tsohon ciki ne da ita bata iyacin abincin data dafa, ganin
Abee yasa akunyace ta sauke kanta dan kowa nauyin Abee yakeji cikeda kunya tace “ina
kwana Abee” kallo daya yamata yadauke kai yace “Alhamdulillah” yakalli Hajiya yace “natafi
Hajiya” dan murmushi tasakin mai tace “ubangiji Allah yabada sa’a yakara daukaka” ahankali
yace “Ameen” su Anty Binta atare sukace “Allah bada sa’a Yaya” bai amsasu ba yafice suna
sonshi bana wasaba Ya Imran shine komi nasu, ci sha sutura, duka kanninshi dukansu duk
wata kowacce yana bata kyautan kudi hatta matan Ibro, banda Ibro da Hamza da suma tunda
sun gama makaranta duka yasasu a company shi duk suna aiki awajen, school fee na marayun
yaran Maman Aneesa na kanshi magani komi, sai su Abdallah da Kausar dake university
Kausar this year tafara tana 100level tana karantan Mass com, shikuma Abdallah na 300 level
medicine, Abdallah nada bala’in kokari da kwazo ga natsuwa da tausayi da kirki saisa Abee
yabashi motan kanshi dudda he’s 22yrs dan yawanci early morning lectures yake kuma bayida
gara gara, itama Kausar tana kokari ba laifi amman ba kaman Abdallah ba randa sukeda
lectures lokaci daya da Abdallah shi yake wucewa da ita idan kuma ya bambamta Hamza ke
kaita.
EPISODE 5️⃣
Exquisite world collections
Muna sai da jakakkuna da takalma masu kyau wanda idan kuka siya ba lallai ku sake ganinsu
wani wuri ba . I assured you. Ku siya ku godemin daga baya domin ingancin kayana. Ina turawa
ko ina kike ni kuma Ina Abuja.
Wannan shine instagram handle dina.
I'm on Instagram as shukhria. Install the app to follow my photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ithkqozo1zuq&utm_content=oeu4f73
08108517010 wannan shine number wayana kuma dashi zaku sameni a whatsapp.
Ahankali cikin muryan bacci wata kalan siririyan murya mai shegen dadi da zaki tace “Gwaggo
yunwa” shiruu kakeji banda sound na munshari dake tashi acikin duhun dakin, cikin wani irin
raw voice din nan dake nuna bacci mutum yake ko cikin bacci mutum yake maganan tace
“Gwaggooooo yunwaaaaaa!” Firgigit munsharin dake tashi daga dakin dakeda duhu nan ya
tsaya kaman anyi ruwa an dauke karan hannu kawai ketashi daga dakin dake nuna ana tattaba
gadon alamun abu ake nema sai chan aka kunna wani bright torchlight daya wani kalan haska
dakin bauuuu kaman wutan lantarki, wata tsohuwar mata ce da akalla zatai 70 kokuma 72 haka
kwance kan wani makeken gado mai kyau tana sanye cikin riga bubu da zani na atampa
gefenta kuma wata yarinya ce mai jiki sosai kwance ta kankame Yar tsohuwar kaman zata
koma cikinta idanunta akulle tana daure da wani pink towel, kallon fuskanta yar tsohuwan tayi
tace “Ohh ni Safara’u Allah ubangiji ka nunamin ranan dazanyi bacci tundaga farkon dare har
karshe batare da wannan fitinanniyan yarinyar ta tadani tanajin yunwa ba, Ya ubangijin sammai
da kassai Ya ubangijin dake busa numfashi rokonka nake Allah ka kawomin ranan nan da
gaggawa” cikeda takaici tace “aisai kitashi ga shayinki chan cike a flask, namanki da somasa
nacikin kula, buredi ma na wajen idan kuma harda shinkafa zakici to wlh dakanki zakije kitchen
kidebo dan kin ganni nan ban barin gadon nan Lulu” still cikin baccin batare data bude idanunta
har lokacin ba tace “Gwaggo wlh ki kawomini nan” tai maganan kaman mai shirin kuka dayasa
babu shiri Yar tsohuwan takai hannayenta ta kabarda hannunta dake kan jikinta tace “aisaiki
sakeni intashi yarinya kaman jikan mayu” tashi daga kan gado tayi tasauka tawuce wajen da
flask da wata katuwar kula da cup da duk suke kan faranta ta duka da kyar ta dauka tazo gaban
gadon ta ijiye sannan ta kalleta still idanunta arufe suke tace “tashi to kici” kaman jira take
ahankali ta tashi zaune idanunta still arufe tana rike da gaban towel dinta dake shirin zamewa
sannan ta gyara daurin zanin da kyau tana turo baki tashiga bude idanunta ahankali, wasu
hadaddun kitson kalaba ne kan yarinyar dasuka zubo mata har tsakiyan baya an jera beads a
bakin kitson kaman wata Yar yarinya, wani kalan kibane da yarinyar bana wasa ba, irin asalin
yaran nan ne da ake kira da chubby, idan kaga jikinta zaka dauka she’s about to burst ne
dankoni dazu dana ganta kwance kan gadon nadauka Babba ne sai yanzu dana kalli fuskanta
Nagane yarinya ce da duka duka bazata wuce 19-20yrs ba, wasu kalan cat sexy eyes gareta
dayasa idan ka kalli fuskanta saika kasa janye idanuwanka akanta for some seconds sabida
kyawun idanunta, tanada cikan gira kuma baki sidik hakama gashin idanunta da dan siririn
hancinta, tanada kumatu rubu rubu dasu that looks super cute on her dawasu kananun
succulent pink lips da kana kalllonta yana bada all this kananun jariran yaran nan dakeda kiba
din nan sosai, skin dinta is like butter ne ko milk banmasan yanda zan siffanta muku ba but
kaganta zaka dauka idan ka latsa jikinta jini zai fito ne, everything about her is chubby harta
yatsun hannuwanta dana kafafunta burbur dasu kaganta kaman zata fashe, sauka tayi ahankali
daga kan gadon tana kara gyara daurin towel dinta da kyau sannan akan soft carpet din tana
bude flask din ahankali duk cikin bacci itakuma Gwaggo tawuce tabude bandaki tashiga. Shayin
tazuba cikin wani babban cup dayaji madara da Milo yana tururi sannan tabude babban kulan
samosa ne kusan 20 aciki da naman kaza da akai pepper chicken dasu guda 5 da sauri
tashigaci tass ta shanye shayin kofin takara bude flask tadeba tacika tacigaba daci itakuma
Gwaggo tafito ta shimfida dadduma kawai tahau tass ta shanye shayin da samosan da duka
naman gyatsa tayi sannan ta tashi tahau gado ta gyara kwanciya ta kwanta murya chan kasa
cikin bacci tace “Gwaggo kizo mukoma bacci” hararanta Gwaggo tayi tace “nafila zanyi
gwarama kiyi baccin ki dan kinsan da asuba zan tadaki yau monday zakuje iskuko oho dai
amakaranta” dan gajeren tsaki yaja tanajan bargo ahankali akuma shagwabe tace “ni bazanje
ba Mandawari na zaiyi live broadcast karfe shadaya na safe yau” hararanta Gwaggo tayi tace
“asheko dake da shegen gantalallen Mandawarin daharyau baimasan ko akwai mai kamanki
aduniya ba babanku zai hada yaci ubanku” murguda baki tayi tareda lumshe ido kafi kacema
bacci yay awon gaba da ita ganin haka itama Gwaggo ta kishingida da bango danta dan runtsa
kadan tasan inhar batahau ba nan bada jimawa ba zata tashi da kanta dan Lulu bata iya bacci
bataji ta rike mutum ba tun tana yar kankanuwan ta take haka.
5 na asuba tabude ido ahankali takalli inda Gwaggo take kan dadduma sannan ta tashi zaune
ahankali tana jaye zanin gadon tana murmushi tasauka dagakan gadon da sauri tawuce
bathroom na cikin dakin da ruwan zafi tai wanka tai brush sannan tai alwala tafito daure dawani
towel din bayan ta wurga wanda tacire kan washing machine tazo dakin bataga Gwaggo
awajenba hakan yasa tadauki wani dogon hijabi tadaura akan towel na jikinta tahau kan
dadduma, tana sallame sallan ta tashi batare datayi azkar ba tawuce tafita daga dakin tashigo
falonsu wani chocolate dake kan center table na cabry diary milk tadauka da sauri tana budewa
tai wajen kofa daidai nan Gwaggo tafito daga kitchen tace “ina kuma zaki gari bai gama wayewa
ba Lulu”? Batare data kalli Gwaggo ba tace “wajen Ya Samira zani” baki Gwaggo tabude zatai
magana amman tuni tabude kofan tafice Gwaggo tabita tana kwalamata kira tace “bazakizo kisa
kaya ba da asuban nan kina yawo daga ke sai tawul babu dan kwali akanki Lujain” ko juyowa
batayi takalli kakartata ba saina kara sauri datakeyi zuwa babban flat din gidan tana tafiya
kaman Kazan agric dataci takoshin nan tana tafiya da kyar tana tafiya tana ballan chocolate din
hannunta tanaci, gidan dan Babba ne ba laifi kana ganin yanayin tsarin gidan kasan ba laifi
gidan masu rufin asiri ne daidai gwargwado, bude kofan flat din tayi tashiga dakin tsaf tsaf sai
kamshi yake babu kowa afalon direct tawuce wani daki dake corridor dataji hayaniya budewa
tayi tashiga da sauri tana murmushi, yammata uku ne acikin dakin dake dauke dawani babban
gado na daidai rufin asiri ga daddumai da hijabai akasa kana ganinsu hancinsu zaisa kagane
sudin duka sisters ne saidai su kaf dinsu black beauties ne kuma ko kadan basu da jiki kaman
ita su sirara ne yammata sosai, duk kallonta sukayi suka watsar amman ko ajikinta wani kalan
murmushi tayi tamaida kofan tarufe takaraso cikin dakin tana kallonsu daya bayan daya,
Babban cikinsu wacce akalla zatayi shekaru 23 ne da waya ke kunnenta tace “Baby ina zuwa
zan kiraka” sannan ta katse wayan takalli wacce ta shigon tace “Lujain ba jiyan nan da daddare
Baba yagama miki magana kan zama da towel dakuma rashin daura dankwali ba” dan yatsine
fuska tayi kaman zatai kuka ashagwabe tace “mancewa nayi ban daura dan kwallin bafa Ya
Samira” dasauri wacce takira da Ya Samira tace “to towel dinfa” dan turobaki tayi tace “wlh zafi
nakeji idan nasa kaya” daya daga cikin sauran biyun matan ne taja tsaki tace “yarinya gabaki
daya Gwaggo tamaidata mara saiti, ba dole kidingajin zafi idan kinsa kaya ba, jibeta kaman
buhu” da normally ne da yanzu tai kuka da aka kirata da buhu but yau she’s extremely happy
hakan yasa tace “wlh banda lokacin ki Ya Abida amman gobe ki tareni ki kirani buhu kiga abinda
zai faru” yunkurowa Abida tayi kaman zata daketa hakan yasa da sauri Lujain din takoma baya
Abida tace “maimaita abinda kikace”? Dauke kai tayi dayan sister da tundazu batai magana ba
tace “Ya Abida inba so kike yau duk mutafi school da bakin ciki ba kada kitaba yarinyan nan
yanzu dan wlh bamuba har Baba da Mama ransu yau saiya baci akanta kindaisan fitinan
Gwaggo sarai” kaman jira Lujain din take jin ankira Gwaggo kwafa tayi tace “barta ta tabani ma
tagani Ya Habiba” ganin rikici zasuyi yasa Samira tace “ni dan Allah ku kyaleta zonan kifadamin
meya kawoki wajena da asussuban nan keda nasan war haka baki tashi ba” murmushi tayi ta
harari Abida da Habiba tawuce wajen samira kaman maison gulma tace “ni akunnenki zan
gayamiki” kunnen Ya Samira tabata magana tayi mai tsawo sannan ta tashi wani mugun kallo
Samira tamata tace “chabdi wlh bazan baki ba hakanan” kaman zatai kuka tace “please Ya
Samira kome kikeso zan miki Allah” shiru Samira tayi tana kallonta hakan yasa tace “wlh kuwa”
murmushi Samira tayi tunawa da wani abu tace “inhar kin yarda zaki fasa asusun ki kibani duka
kudin ciki zan baki wlh dama banda kudin ankon Aisha kinga nasamu” kaman zatai kuka tace
“kai Ya Samiraaa duka fa kikace” hararanta Samira tayi tace “ashe baki cika crush din
Mandawari ba, ni wlh idan inason wani celebrity babu abinda bazan iyayi akanshi ba, kikasan
ma ko a live din dazaiyi yau yaraba ticket na zuwa kallonshi a stadium idan zai buga kwallo
basaikije ba, kuma yana ganinki zaice yana sonki kinga yanda kikeda kyau ne” wani kalan
mugun murmushi tayi dayasa kumatunta ya lotsa abin kaman wani machine ne awajen ya
bala’in haska fuskanta, Abida dakejin firansu ne ta tsoma baki tace “Ya Samira stop deceiving
this girl for your personal interest, international player irin Muhammad Mandawari kyakkyawan
footballer hadadde ga kudi bazai taba cewa yanason wannan buhun yarinyar ba ko itace last
woman on earth wlh” wani abune yatokarema Lujain wuya tajuya tana kallon Abida dake
kallonta hararanta Abida tayi tace “yarinya abincin dazataci dukanmu nan bamu iya cinshi,
tsakar dare kaman diyar aljanu dansu ke fatin abinci tsakar dare haka itama ketashi taci nata,
Gwaggo kawai tabude mata ciki, tayaya ma Mandawari zai dauketa? Wlh tafi karfinshi” daga
Abida har Habiba suka kwashe da dariya itakuma Samira tarike nata dariyan dan tana hango
samun da zatayi, Habiba dake dariya tace “Mama ma tace babu wanda zai taba cewa yana
sonta balle harma Ya aureta bakiga ba duka yan class nasu nada saurayi ita mazan ajin ko
kallonta ma basayi bata burgesu everybody gets irritated with cin abincin Lujain da kibanta”
juyawa Lujain tayi fuuu zata fice dasauri Samira tariketa tahararesu tace “don’t mind them yan
bakin cikine Mandawari will acknowledge you one day as his die hard fan sannan zai soki
harma ya aureki” sosai hawaye yacika mata idanu ahankali tace “are you sure Ya Samira
bazaice nacika kiba ba” murmushi Samira tamata tace “ai kiba halitta ce kuma shi so comes
from heart inhar na gaskiya ne ko kinfi kowa kiba aduniyan nan he will love you and cherish
you, now smile for me muje mukarasa deal din inhar zaki kawo kudin yanzu zan baki wayan ki
kalli live dinshi idan nadawo daga school na karbi wayata kin yarda” dasauri ta gyadakai
murmushi Samira tayi tace “to jeki kawo kudin kafin nan nagama waya da Baby” da sauri tajuya
tafita su Abida suka bita da harara sukace “wawiya kawai tama dawo ta dauke ledan chocolate
din nan data ijiye mana anan dan nan ba dakin kakarta bane data maida bola ba”.
EPISODE 6️⃣
Exquisite world collections
Muna sai da jakakkuna da takalma masu kyau wanda idan kuka siya ba lallai ku sake ganinsu
wani wuri ba . I assured you. Ku siya ku godemin daga baya domin ingancin kayana. Ina turawa
ko ina kike ni kuma Ina Abuja.
Wannan shine instagram handle dina.
I'm on Instagram as shukhria. Install the app to follow my photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ithkqozo1zuq&utm_content=oeu4f73
08108517010 wannan shine number wayana kuma dashi zaku sameni a whatsapp.
Tana fita daga dakin daidai wata mata wacce kana ganinta kasan itace mahaifiyar yammatan
datafito daga dakinsu sabida yanda sukai kama da mahaifiyar tasu, tsayawa tayi ahankali tace
“Mama ina kwana” kallonta Mama tayi daga sama har kasa taja tsaki tawuce hakan yasa itama
tawuce daidai tabude kofa zata fita daga falon taji Matar tace “duk randa aljanu zasu shigeki wlh
saina bada sadakan dubu ashirin” batace komiba bude kofan dakin tayi tafita daidai lokacin
wani magidancin mutum na karasowa gaban dakin sanye da jallabiya shima tareda wani
babban yaro wanda bazai wuce 25yrs ba, wani mugun kallo dayama yarinyar yasa kawai jikinta
yahau rawa kafinma yayi magana kaman zata fashe da kuka tace “Baba dan Allah dan Allah
Baba kayakuri karka doken dan Allah” juyawa tayi zata koma dakin tsabagen rudewa saikuma
tasake juyowa da sauri ta kwasa aguje tai side din kakarta mahaifinta yabita da kallo kaman zai
doketa da idanu, ahankali yaron dake taredashi yace “kamata hakuri Baba please” dan ijiyan
zuciya Baba yasauke saikawai yabude kofa suka shiga falon shida yaron.
Bata kara fitowa daga dakinsu ba sabida tsoron gamuwanta da Baba, saida tasake wanka dan
haka take kaman kifi arana zata iya wanka sau ashirin sannan ta shirya cikin kayan makaranta,
shima makarantan sabida Baba na nan ne da wlh bazataje ba, wani white long sleeve rigane
daya tsaya a cinya sai kuma wani dogon gown ash dazaka daura akan farin rigan sai abun yayi
kaman biri da wando dayay mata kyau sosai, zama tayi Gwaggo dakanta tashiga samata safa
akafa itakuma tana kirga kudin asusunta data bude Gwaggo tace “wai Mezaki da kudin ki
dakike tarawa ma salla iyye”? Turo baki tayi tace “wani abu zanyi” tabe baki Gwaggo tayi tana
karasa saka mata black cover shoes nata tace “kyadaiji da rigimanki baran biyemiki da safen
nan ba dan na lura neman abinda zaisa bazakije makaranta kike ba” Gwaggo tai maganan tana
kawo mata wani fine black bag pack tace “ga jakan ki” karban jakan tayi tabude da sauri
chocolate daban daban da aka zubamata ta kalla da biscuit da juices kala uku da goran ruwa
saikuma wani dan karamin flasks na snacks sannan tadago kai takalli Gwaggo kirji Gwaggo ta
dafa tace “menene kuma ni Safarau dazaki dallamin miyagun idanuwan nan naki” amugun
shagwabe tace “baki samin yoghurt ba Gwaggo” kaman Gwaggo zatai kuka cikeda lallashi tace
“wlh bansan yoghurt dinki sun kareba Lulu kiya kuri zansa Baban ku yasayo yau tashi muje
chan palour” makema Gwaggo kafada tayi idanunta sun cikada kwalla har kyalli suke amman
basu zuboba rudewa Gwaggo tayi tazauna kusada ita cikeda bala’in lallashi takai hannunta
tanajan kumatunta tace “haba mana Lulu na yarinyan datafi duka yaran duniya kyau so kike
ajimu, kema kinsan kome kikeso sai inda karfina yakare ko wannan ma bansan yakare bane
kiyakuri kina dawowa zaki tadda yogurt