Showing 45001 words to 48000 words out of 82745 words

Chapter 16 - Sakon So Book Complete by m Shakur ( By Ubeera ) .pdf

M Shakur   

11 Oct 2025

1621

yan WhatsApp
da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Breakfast aka fara kawowa cikin falon dan Hajiya tace ita barata dinning ba, Maman Aneesarh
tace “Aneesarh taho kisha cerelac dinki kibar Anty Lujain tayi breakfast†sauka daga jikin Lujain
Aneesarh tayi ahankali mikewa tayi kaman zataje wajen Mamanta saikuma da gudu tai wajen
Abee zatahau jikinshi takasa, daukanta yayi ahankali yana kallon fuskanta ahankali yace “you
don’t want to eat� Gyadamai kai tayi da sauri tana kallon Coffee dayake sha, dan murmushi
yayi yakai bakinta kurba tayi kadan jin daci yasa ta tabe baki tasauka daga jikinshi tawuce
wajen Mamanta.

Lujain na zaune inda take akasa atisha yazo mata hannunta takai kan fuskanta tayi tanajan
hancinta saiga nabiyu yazomata shima tayi tace “Alhamdulillah†na uku na zuwa, Hajiya tace
“sannu Lujain†na hudu ne yazomata shima tayi dayasa kowa ya kalleta banda Abee dake
kokarin kurban coffee shi, Hajiya tace “kin kwana da AC ne Lujain� Gyadamata kai Lujain tayi
ahankali, hakan yasa Hajiya tace “bata farfesu da shayi tasha Binta, sannu mura keson kamataâ€
shayi Anty Binta tahada mata mai kayan kamshi, bala’in yunwa takeji jikinta har rawa yasoma
ganin shayi, Anty Binta nagamawa dasauri tadauki cup nashayin takai bakinta ta kurba wani
kalan zafi dataji yasa batasan lokacin datasaki cup dinba shayin sai cinyanta wani kalan ihu ta
kurma dayasa har Abee saida ya kalleta. “Wayyoooo Allah na zafi, Gwaggo†tai maganan tana
kokarin kwaye doguwan rigan sama tana yarfe hannu tana kuka, Hajiya tace “daga gani bata
sabashan shayi mai zafin nan ba Subhanallahi sannu ya isa daina kuka†Anty Binta ganin shirin
dage rigan take yasa takai hannunta ta taba inda shayin yazuban mata tace “sannu sannu, jeki
cire kayan zan biyoki da breakfsat din sama†Gyadamata kai tayi tana share hawayen daya
zubomata tawuce sama da sauri tana tafiya ahankali su Sajida suka bita da harara, Anty Binta
tashiga hada mata breakfsat nata a tray tace “Kausar zo dauka ki kaimata†dan turobaki tayi
sannan ta tashi ahankali tazo tadauka tawuce sama daidai Abee ya mike yakalli Hajiya yace
“natafi Hajiya†ahankali tace “tom Allah bada sa’a Imran†wucewa yayi yafita daga dakin suma
su Hamza da Abdallah suka fice daga falon Sajida da kaman jira take su fice tace “tsakani ga
Allah wlh da auren wannan yarinyar kaman buhu gwara rashin aurenta, wanan shirmen za’a
bama Ya Imran a matsayin mata ai wlh ancuceshi haba mana†Zainab tace “mugun an cuceshi
ma bakiga ko kallo bata isheshi ba, yarinya banda haske babu abinda ya ceceta sai shegen
kiba, taga shayi jikinta har rawa yake sabida son abinci†Matar Ibro ne dake wajen tace “wlh irin
kibar yarintan nan ne, nima akwai kanwata Ummie haka tun tana karama takeda irin wannan
kiban kaman ana hurata tashi daya kuma ta zazzage kiban tass kaman ba itaba itama zata
rame ne, kwanan nan ma tunda duk damuwa yamata yawa†cikeda kulewa Sajida tace “ba
wannan ake magana ba kekuma Matar Ibro mu bama sonta amatsayin Matar Ya Imran ne,
mezaiyi da yarinyar da Kausar ta girma wannan ba cuta bane†daidai nan Kausar tasauko tace
“ni wlh na tsaneta Allah ya kyauta Abee dina yay rayuwa da wacce na girma amatsayin mat…..â€
wani mugun kallo da Hajiya tama Kausar yasa takarasa maganan tace â€zoki saka Hijabinki kibar
gidan nan kitafi makaranta nasan Hamza na mota yana jiranki†ba musu ta taho hijabi ta dauka
da jakanta tafice Hajiya takalli su Sajida tace “kuzo kubarmini gida babu ruwanku da yarinyar

nan, babu abinda ya shafeku da ita dan haka ku kiyayeta, bansonjin wani yakara maganan ta
agidan nan, ban yarda kuci zalinta ko zarafinta ba, babu ruwanku tsakaninta da mijinta Imrana
shine mai ita shine mai iko da ita, koni ba zamana takeba zaman mijinta take agidan nan, koba
komi I expect dukanku ku girmamata amatsayinta na Matar yayanku dan haka ku kiyaye†duk
shiru sukayi Hajiya tamike tawuce dakinta.
EPISODE 2ï¸âƒ£1ï¸âƒ£


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI



Abee na zaune a office nashi wuraren 2:30 aka tura kofan office dinshi batare da anyi knocking
ba aka shigo dago kanshi yayi kallo daya yama Musty dake sanye da manyan kaya yana
kalllonshi yana wani makirin murmushi yadauke kai yacigaba da abinda yakeyi, maida kofan
Musty yayi yarufe yakaraso gaban table yace “Ango Ango kai kaga wani glowing dakakeyi ne
irin na amarcin nan†dan dariya yayi ganin ko kallonshi Abee baiyiba Musty yace “no bama
wannan ba tell me everything about the first night†wani mugun kallo da Abee yamai yasa
yawani kalan kyalkyace da dariya yace “inda kallo na kisa da yanzu idanunka sun kasheni yafi
sau dari†dauke kanshi Abee yayi yacigaba da duba papers din dake hannunshi yace “idan
abinda yakawoka wajena kayi kenan kabarmin office please†hadiye dariyan Musty yayi yakalli
Abee yace “to ka ijiye takardun ka kallen mana muyi magana†dan ijiyan zuciya Abee ya sauke
ya ijiye takardun ahankali yakalleshi tareda folding hannunshi a kirji cikeda tsokana Musty yace
“yaushe zaka komarda Amarya gidanka? Kasan gidan Hajiya bazai barka kai amarci da kyau
bako� Akufule Abee yatashi pappers din yashiga tattarewa yabar wajen yakoma kan
lumtsetsen couch na office din yazauna ahankali yacigaba da abinda yakeyi anatse shikuma
Musty yana zaune inda yake yana kallonshi yakai kusan 10min sannan yatashi shima yazo
yazauna kusadashi batare da Abee yakalleshi ba yace “zan barmaka office din gabaki daya fa
Mustafa†murmushi Abee yayi yace “nasan zaka iya, all jokes apart magana nazo muyi Imran
look at me†yanda yay sounding serious yasa Abee yadago idanuwanshi ahankali yakalleshi
alamun ina jinka. Ahankali Musty yace “Nasanka to be someone da kana taimako kana tsayama
wayanda bama kasansu ba kabi musu hakkinsu ka kwace yancinsu, yaran dakai sponsoring

education nasu bansan iya adadinsu ba saisa yauma is still on that matter nakeso nida kai muyi
maganan fahimta best friend†shiru Abee yayi still yana kallonshi anatse Musty yace “I know
bakason auren nan and you don’t consider this girl your wife†daukekai Abee yayi hakan yasa
dasauri Musty yace “hear me out mana Imran bawai inaso nace you should consider her
matarka bane wlh ko daya I accept that take as long as u want kafin kai accepting nata
kokarkayi accepting nata ni duk dayane awurina but as your friend reminder na musulunci nazo
namaka†shiru Musty yakarayi sannan yakalli Abee yace “I know you better than anyone nasan
yanda kake idan bakason abu yanda kake wulakanta abin, banso kama dat small innocent girl
that kind of treatment Imran, bance kai accepting nataba as your wife but inaso ya zamto ka
kiyaye hakkokinta na musulunci, lafiya, ci, sha, sutura and respect, duk kabata kaga idan ka
wulakanta yarinyar nan and neglect her mutanen gidanku kap haka zasu mata suma, remember
bata tareda dan uwanta ko daya, remember kaman yanda su Kausar basuda mama itama
batadashi su Kausar sunma fita gata in the sense sunsan mahaifiyarsu banda haka kaga ga all
your sisters and family sun taso cikinsu itako has only her grandma! Just grandma, inaso kajata
ajiki be nice to her please Imran, saikuma second abu dazan fadamaka is school idan all this
issue yakara sanyi saika nemi wani good school kasata since school datake sun koreta saita
fara wani sabo mai kyau kaji Imran that’s the only abu da dama zan maka magana akai kaji�
Dan dauke kai Abee yayi kaman bazaiyi magana ba saikuma chan yace “naji†murmushi Musty
yayi yace “to hurry ka karasa abin nan gashichan ana kiran salla muje muyi saimu wuce gidaâ€.
**


Koda takoma daki kayan tacire tashiga bayi tana wanke kafanta wajen dan ja yayi dan bawani
konewan kirki bane towel ta daura tafito tana kallon kulan abinci da tray shayi dataga an kawo
mata dabatasan waya kawoba, zama tayi tahada shayin dakanta ta shanye tass sanan tacinye
duka chips da egg dake kulan ta shanye farfesun shima tass rabonta da abinci tun jiya hawa
gado tayi ahankali sai bacci koda Anty Binta tashigo ganinta kwance kan gado da towel yasa ta
murmushi ta kwashe kayan abincin tafita, wajajen azahar ta tashi tashiga bayi da ruwan sanyin
still takara wanka tafito tana atishawa hijabi tasa tai salla sannan tazauna kawai tai shiruu tana
kallon dakin, duniyan kawai yamata ba dadi, komi ya tsayamata chak, gidan yamata wani kala
kawai sai hawaye sosai tayi kuka jin ana taba kofanta ana magana yasa tashare hawayenta da
gudu, Anty Binta ne tashigo tareda wata mata kallo daya Anty Binta tamata tagane tai kuka
amman tai kaman bata saniba tace “anzo aunaki tashi to†tashi tayi ba musu matan ta aunata
tsaf sannan suka fice itada Anty Binta chan saiga abinci wata Yar aiki takawo mata dauke kai
tayi wasu hawayen sun sake zubomata that means bara’akaita gidansu ba kenan, tsanan
abincin taji tayi jin ana kiran la’asar yasa tawuce bayi tadauro alwala tazo tai salla, jin dakin
yamata wani kala sotake tama danga hasken rana babu yasa ahankali ta tashi tai wajen window
ta yaye labulen tareda bude window wani kalan iska ne yabuge fuskanta ahankali tasauke ijiyan
zuciya tadade tsaye wajen sannan tajuyo akwatin da aka kawo mata tai wajensu tabude duka,
robobin daddakkun magungunan ne daban daban da sauri ta maida tarufe dan barata shaba
magungunan nan da badadi dayan tabude ganin su chocholate minti biscuits da yogurt daya
cika akwatin yasa batasan lokacin datai murmushi ba tawani fashe da kukaba takifa kanta kan
kafa ahankali tace “Gwagooooooo†sosai take kuka da sunan Gwaggo, chocholate guda uku ta

dauka sannan tarufe akwatin tasaka wani white slippers pink dake dakin masu kyau daidai
kafanta tabude kofa ahankali tafito tana mamaki dataji gidan tsit babu ko muryan yara bin ko’ina
take da kallo hartakai stairs tafara sauka tana bude chocholate dinta wata Yar mata tagani afalo
tana shara matan jin tafiya yasa tadago kanta dan murmushi tayi ganin Lujain tace “ina yini
amarya� Dan turobaki Lujain tayi jin ankirata da amarya takarasa saukowa ahankali tace “ina
masu gidan� Murmushi matan tayi tace “duk sun fice nan makota yau ana sunan matan
Kamal†shiru Lujain tayi sokawai take tafita waje juyawa tayi tafara tafiya zuwa kofa itadai Yar
aikin tacigaba da sharanta tana mamaki ina Amaryan gidan nan zata daga ita sai towel akirji
babu ko hula, bude kofa ahankali Lujain tayi tana kallon babban tsakar gidansu dayaji flowers
ahankali tashiga sauka dagakan dakalin tana kallon gate dababu kowa awajen wani zuciyan
nacemata tawuce tabude tafice abinda ta tafi gida wani zuciyan kuma nacemata karta fita kotaje
gida daga Gwaggo har Baba zasu kara dawo da itane, tafita ma mutane su ganta ayita kallonta
ana kiranta Yar iska tunda yanzu duniya gabaki daya sun santa, hawaye taji sunzo mata tunawa
datayi abinda yasa tamazo gidan nan in first place, karasawa tayi wani wani plastic chair dake
wajen flowers na compound din ta zauna takai chocholate nata baki ta balla tana taunawa still
tana kallon gate din, kaganta kaman wata aljana fatarta fari kal kaman jini zai fito idan katabata
ga pink towel da slippers ajikinta she looks so adorable and very cute.



Tana nan tanacin chocholate din tana kallon gate aka bude karamin gate dasauri aka shigo mai
gadi ne baima lurada itaba key gate yacire da saurinshi sannan yashiga bude gate din sai zare
idanu take innocently tana kallo tanakai chocholate bakinta tana balla.
Ana bude gate din daga Abee har Musty dukansu hangota sukayi zaune kan plastic chair daga
ita sai towel babu dan kwali akanta hannunta rike da 3 different chocolate data bare tana
ballansu all at the same time, da sauri Musty yadauke kanshi yaciro wayanshi yana dannawa
kaman baiga komiba shikuma Abee kuri yayi yana kallonta yanda tadage tana kallon wajen gate
din har mikarda wuya take kaman wata jimina tanacin chocolate kaman akwai abinda ta ijiye
waje, jan motan yayi ciki tabi motan da kallo batare data gane waye aciki ba dan bata iya gani
mai gadi yashiga kulle gate din.
Ta glass Abee ke kallonta batare daya fito ba kozata tashi tashige ciki amman ko gezau sai
kallon gate din dama tacigaba da yi tanacin chocholate dinta, dan kallo Musty yayi ganin yana
danna wayanshi yasa batare daya kashe motanba yace “I need to get something for Hajiya bari
na karbo prescription din mutafi†“okay†Musty ya amsashi atakaice hakan yasa Abee yabude
kofa yafito tanacikin kallon gate taji karan bude kofan mota hakan yasa takalli wajen da sauri
hada idanu sukayi itada Abee dake mata wani kalan kallo wani kalan faduwa gabanta yayi
takasa cigaba da tauna chocholate din datakeyi takasa tashi takasa zaune takasa komi, sai
kirjinta dake bugawa dum! Dum! Dum! Daidai Abee yakai gabanta batare daya kalleta ba babu
alamun wasa a voice nashi yace “follow me†yay gaba tashi tayi hakanan kawai taji jikinta yafara
rawa falon itama tashiga amman taga haryay stairs hakan yasa tabishi abaya agaban dakinta
taga ya tsaya yay folding hannunshi akirji yajuyo yana kallonta, jitayi legs nata are shaking
amman haka tadaure kanta akasa takaraso ahankali gaban dakin ta tsaya tana watsa da
yatsunta cikin sanyin murya da yet zaka jishi a zafafe yace “bakida kayan sawa ne� Girgizamai

kai tayi batare data dago kanta sama ta kalleshi ba, cikeda dan zafi Abee yace “then why are
you sitting outside da towel� Dan tabe baki tayi irin na masu shirin yin kuka jin yanda yake
mata magana kaman zai daketa ahankali tace “ai kaya tsungulina sukeyi, haka nake zama
awajen Gwaggo naa†wani mugun kallo yamata yace “look up†ahankali gabanta na racing
tadago idanunta dahar sun cika da kwalla sosai takallai, babu wasa kan kwayar idanunshi yace
“this house yamiki kama da gidanku?†Girgixamai kai tayi daidai hawayen na zubowa sharrr
yace “then this should be the last time dazaki daura this thing kifito waje understood�
Gyadamai kai tayi ahankali saikuma tajuya da sauri tabude kofan dakinta tashige tareda
fashewa da kuka sosai tafada kan gado, yakai kusan 1min tsaye wajen yanajin karan kukanta
yadanja tsaki yawuce dakinshi yarasa mesa yakemata magana with anger he’s so pissed of ne
wlh.
Wanka yayi ya shirya tsaf cikin jeans da Riga yadauki wasu jersey yahada awani karamin
workout bag dan yanaso yabuga kwallo bayan magrib yafito batare daya kalli kofan ba yawuce
yasauka kasa.
EPISODE 2ï¸âƒ£2ï¸âƒ£


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms 💃 idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu💃💃

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


Wajen motanshi yayi yabude yashiga ciki yana jefa jakan daya dauko baya yatada motan Musty
na kallonshi baicemai komiba saidan murmushi dayayi tareda gyara zamanshi, ganin ba hanyar
pharmacy sukayi ba sai barrack dasukayi zuwa filin kwallo yasa Musty kawai murmushi yace
“maganin Hajiya fa†changing room Abee yawuce batare daya amsashiba Musty yabishi abaya
suka shiga shidayake Musty nada kayan chanzawa a locker shi na changing room shiryawa
sukayi suka fito suka shiga field sosai suke buga kwallo team na Abee daban nasu Musty
daban Abee saicin kwallon yake kana gani kasan ya iya kwallo sosai ya kware, saida aka fara
kiran sallan magrib sannan suka tashi wanka sukayi suka maida kayansu sannan suka wuce
mosque.

Saida akayi isha’i sannan yadawo gidan kashe mota yayi yafito yana magana da waya akan
kunnenshi, yashiga falo anan ma yake gani suma basu dade da shigowa ba, samin waje yayi
yazauna yakarashe wayan dayakeyi sannan ya amsa gaisuwan kannenshi daidai nan Hajiya
tafito daga dakinta da charbi a hannunta tace “waini tunda nashigo banga Lujain ba, ke Kausar
tashi kije ki kiramini ita nasata a idanu†tashi Kausar tayi ahankali tawuce sama, Hajiya takalli
Abee tace “dazu fa kaman nace itama ta shirya tabimu sunan saikuma dai na bari dan bangaya
maka ba†shiru Abee yayi baice komiba dan baimaso anamai magananta daidai nan Kausar na
saukowa tace “tana wanka Hajiya†amman nafada mata daidainan Anty Binta takawoma Abee
shayi zubamai tayi a mug tabashi karba yayi ahankali tace “Yaya nakawo maka dinner� Girgixa
mata kai yayi yace “no†saida ya shanye shayin tass sannan yatashi yace “Hajiya bari naje dakiâ€
“to Imrana Allah bamu alkhairi†wucewa yayi yahau stairs yayi sama yana gab da karasawa
gaban dakin Lujain Lujain tabude kofan tadakinta tafito tana sanye dawani doguwan riga black
tana rawa rawan sanyi dan bala’in sanyi takeji gashin kanta ya dan hargitse ga lema leman
ruwa tagaban gashin, juyowa tayi bayan ta maida kofan tarufe karaf suka hada idanu da Abee
dake tahowa yana tafiya one one kaman wani sarkin kasa, wani kalan mugun faduwa gabanta
yayi dawani kalan sauri har hannunta na rawa tabude kofan dakin takoma cikin dakin dasauri
tareda maida kofan tarufe daidai wani atishawa na zuwan mata tayishi, bin kofar dakin nata
Abee yayi da kallo yawuce yashiga corridor yabude dakinshi yashiga.


Ahankali tazauna kan gado tai shiru tadade zaune ahaka saikuma ta tashi tacire rigan tadauko
towel tadaura tasake dawowa ta zauna bakin gado tasakeyin shiru tanajin wani kalan yunwa,
wani kalan kwanciya tayi kaman marainiya tana kallon kofa bude kofan nata akayi aka shigo
saida tadan firgita ganin Anty Binta ne yasa dasauri ta tashi Anty Binta tace “kince ma Baba
baki kara zama da towel amman kinata zaman ko†sauke kanta tayi ahankali kasa tana wasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login