Showing 48001 words to 51000 words out of 82745 words

Chapter 17 - Sakon So Book Complete by m Shakur ( By Ubeera ) .pdf

M Shakur   

11 Oct 2025

1650

da
yatsanta batare datace komi ba, Anty Binta takaraso gaban gadon tace “Hajiya na kiranki mesa
bakizo”? Dago kanta tayi ahankali takalli Anty Binta saikuma takalli kofan dakin takasa cewa
komi, kallon kofan Anty Binta tayi itama ganin kofan take kallo saikuma ta kalleta tace “Ya Imran
yahanaki fitowa”? Gyadamata kai tayi ahankali hawaye na gangarowa daga idanunta wani
kalan mugun tausayi Anty Binta taji tabata hakan yasa gently tazauna bakin gadon bama tasan
mezata ce ba tace “ki yakuri kinji Lujain” kaman jira Lujain take fadawa jikin Anty Binta tayi ta
kankameta sai kuka, dan lunshe idanu Anty Binta tayi tabudesu zatama Hajiya magana
tagayama Ya Imran yanemi makaranta yasata tun wuri kan wani abu yasami yarinyar mutane
gashi babu mai kulata daga ita sai Hajiya ke kulata yanzu idan ta tafi next week yazatayi,
tadade tana kuka sannan Anty Binta tace “Ya isa to” Anty Binta takai hannunta kan fuskanta
tana sharemata hawayen tana mamakin taushin fuskanta da kumatunta kaman fuskan Yar
jaririya, ahankali Anty Binta tace “kinajin yunwa ko”? Gyadamata kai tayi cikin kuka, murmushi
Anty Binta tayi tace “to bari naje nakawo miki abinci da shayi, stop crying now konai fushi”
hadiye kukan tayi tana kallon Anty Binta, murmushi Anty Binta tayi tajuya tafita daga dakin bata
wani jimawa suka dawo itada Kausar daketa kumbure kumbure tadauki tray na kayan shayi
itakuma Anty Binta tadauki flask guda biyu Kausar na ijiyewa ko kallonta batayiba tajuya tafita
itakuma Anty Binta ta ijiye tace “to sauko kici” ahankali tasauko tana dake goge hawaye.

Zaune yake gaban desktop nashi yana wani aiki dagashi sai singlet dawani dan gajeren wando
wayanshi ne yay kara hakan yasa yadauka ganin Hajiya ne yasa yakai wayan kunnenshi yana
mamakin meyafaru take kiranshi.
“Ka sameni adakina Imrana” ta katse wayan, ijiye wayan yayi yatashi tareda daukan jallabiya
yasaka sannan yasa slippers yafito batare daya kalli kofan dakin Lujain dayake iyajin maganan
Anty Binta aciki ba tana mata fira wucewa yayi yasauka kasa Hamza da Abdallah yagani a falo
suna buga video game suna ganinshi duk suka natsu dakin Hajiya yawuce da sallama yabude
kofan yashiga Hajiya na zaune bakin gadonta tana kallonshi hakan yasa yakarasa ciki yazauna
kan lallausan carpet na tsakar dakin ahankali yace “gani Hajiya” karasa jan charbi datakeyi tayi
ta ijiye sannan takalleshi tace “Imrana” dan dago kanshi yayi yakalleta yace “na’am Hajiya”
ahankali tace “I promise not to meddle with affairs naka dana matarka but I think akwai
somethings that I can overlook a matsayina na babba” Hajiya tadanyi shiru saikuma tace
“banson damuwa yama Yar karaman yarinyar nan yawa Imran, kaiba kulata kake ba kannenka
ma haka, Binta ne kawai ke kula da yarinyan nan agidan nan nikuma baran iyaba dan kafafuna
ba barina zasuyi ina hawa saman nan ina saukowa kullum ba” Hajiya takarayin shiru sannan
tace “inaso gobe kafin katafi aiki ka dauki yarinyar nan ka kaita makaranta mai kyau kasata,
islamiyya kuma zaka sata wanda su Kausar ke zuwa asabar da lahadi, amman dai gobe
yarinyar nan tafara makaranta kaga karatu nata wuce ta, tunda bawai wani abu take agidan ba
banda zaman kadaici da kuka dan haka ka kaita kasata a makaranta mai kyau kaji ko Imrana”
gyadama Hajiya kai yayi yace “to” Hajiya tabishi da kallo tace “tashi katafi to Allah bamu
alkhairi” ahankali yace “Ameen” yatashi yafita daga dakin tareda maida mata da kofan yarufe,
sama yakoma daidai lokacin Anty Binta tafito tareda Lujain din da hijab ke jikinta black
dayawani kalan haskata, ganinshi yasa tasauke kanta akasa tashige bayan Anty Binta ahankali
tana wasa da yatsunta, Anty Binta ma sauke kanta kasa tayi ganin yanda yake kallonsu da
wannan idanun nashi dabaka jurewa, kallonsu yayi ba yabo ba fallasa yace “where to”?
Ahankali Binta tace “dakina zamu ta kwana awajen Ya Imran wai bata iya kwana ita kada…….”
wani mugun kallo yama Anty Binta yace “bacemin daga nan” dawani kalan sauri Anty Binta
tawuce tayi hanyar dakinta, wani kalan kuka Lujain taji yazomata batare data kalleshi ba tajuya
ahankali takoma cikin dakinta ko tsayawa kulle kofan ma batayiba da gudu tafada gado sai
kuka, yadade awajen tsaye sannan yakarasa gaban dakin nata batare daya kallo ciki ba yasa
hannu yajawo kofan yarufe yawuce dakinshi.
EPISODE 2️⃣3️⃣



Wanka yashiga yafito ya shirya cikin wasu milk pajamas masu bala’in kyau yazauna kan gado,
drawer jikin gadon yajawo yadauko wani babban english novel na UK mai suna the soulless
love, wani akwati yabude na glasses yabude yaciro wani white glass yasaka sannan ya jingina
da gadon tareda kashe wutan dakin yakunna wutan side lamp kadai ya jingina da gado tareda
jan bargo ya lullube kafanshi yabude book din yafara karantawa yanajin kukanta sama sama
dan daga nan dakinshi yakanji abinda ke faruwa acikin dakinta, almost 2hrs yayi yana karanta

book din sannan ya maida yarufe ya ijiye saman drawer ya kwanta ahankali yanaso yay bacci
amman baya iyawa kuma bayaso yanashan magungunan shi, dan lumshe idanu yayi yabudesu
jin ko’ina tsit that means tayi bacci kenan, wayanshi yadauka ahankali yabude wani locked
folder hotunane aciki na wata black beauty mata maidan jiki kaman yanayin girman Anty Binta,
kaganta kamanninta da Kausar daya sak kaman tayi kakin Kausar ta tofar, lumshe idanunshi
yayi ahankali yabudesu yasake daurawa akanta yatsanshi yakai kan fuskanta yana shafawa
murya chan ciki yace “I’ve missed you Muna, why did you have to go and leave me alone at this
stage of life” shiru yayi tareda lumshe idanunshi again yaja wayan yakaishi kirjinshi ya rungume
tsamtsam.


Karfe uku daidai kaman wata mayya tabude idanunta sabida azababben yunwan datakeji
kaman wacce ta kwanta bataci abinci ba tsabagen yanda tasaba cin abinci tsakar dare, ga
kanta dake wani kalan sarawa hancinta taji yatoshe da majina hakan yasa dabaki take numfashi
ma, ahankali tabi dakin da kallo dan wutan dakin a kunne yake, saukowa tayi daga gadon
dasauri zuwa wajen kulolin dake dakin tashiga budewa amman babu komi cikinsu dan tas
tacinye komi jiya da daddare, mikewa tayi tsaye tana kallon kofan dakin gabanta na faduwa
saikuma ahankali tai wajen kofan gabanta nawani kalan mugun faduwa bude kofan dakin tayi
kadan ta leka wutan corridor a kunne hakan yasa tafito da sauri tana gyara daurin towel din
kirjinta kanta ba dan kwali, waigawa tayi takalli falon saman gabaki daya babu kowa ko’ina tsit,
tafiya tafara ahankali tana taba cikinta da har wani ciwo ciwo yake mata yanadan kugi sabida
yunwa stairs tayi tafara sauka tana kallon falon da wutanshi akashe yake gabanta nawani kalan
fadi har hadiye yawu take tana sauke ijiyan zuciya takarasa sauka tana tafiya sadaf sadaf
kaman wacce zatai sata tayi dining area dayake akwai dan haske dake haskowa daga wutan
falon sama, ahankali kaman mai sata tashiga bubbude warmers na abinci dake kan dinning
table din tana dubawa ganin akwai naman kaza soyayye dayawa dakuma rice a warmers din
yasa tajuyo ahankali zata dauki plate daka cikin dankin wankakkun plate din dake kan dinning
table din, mutum tagani tsaye abayanta yay folding hannunshi akirji kaman gunki, wani kalan
zaro idanu tayi tawani kalan bude baki zata kwala ihu danta bala’in tsorata cikin zafin nama
Abee yawani kalan fizgota tawani fado jikinshi taredakai hannunshi kan bakinta yarufe gam dan
yasan tana ihu Hajiya zata farka dan batada nauyin bacci ko kadan tafito tagansu anan and
that’s the last thing he needs now, cikin wani kalan low voice kaman mai whispering yace “don’t
you dare scream” wani kalan zaro manyan cat eyes dinta take tana kallon fuskanshi dadan
haske kadan din dake wajen wanda yazo daga falon sama jikinta ko’ina rawa yake jin gabaki
dayan jikinta na manne danashi banda fuskanta dake facing nashi takasa kwace kanta gashi
yataushe mata baki kamshin dayake narawa ni ratsa mata hanci, wani kalan kallon kwayan
idanunta data zaro yake dudda the place is dark amman harwani kyalli suke, yanda yake
kallonta batare daya zare hannunshi daga bakinta ba yasa taji wani kalan natsuwa nashiganta
ahankali jikinta yadaina rawa hakan yasa tasaukar da idanunta kasa ahankali danta kasa jure
idanunshi akanta, kaman wanda yatuna wani abu zare hannunshi yayi dagakan bakinta dasauri
tareda tureta daga jikinshi tangal tangal tayi zata fadi tabuge da table kaman wacce batada
stamina dasauri yakama hannunta yarike hakan yasa bata bugeba adan kufule yace “what are
you doing here”? Dan kallonshi tayi adan tsorace akuma hankali cikeda sigan shagwaba tace “I

am hungryyyy” tai maganan tana kokarin kwace hannunta daya kama dayasa taji hannun
yamata wani iri, sakin hannun yayi shima dasauri strictly yace “go back to ur room” kwabe
kwabe tayi da fuska kaman zatai kuka saikuma tawuce dasauri batare datace komiba takoma
sama kanta na bugawa sosai, shiga dakin tayi batare data kulle kofanba dan tsoro takeji takoma
gado tazauna tana dafe kanta dakemata ciwo sosai tana numfashi da baki, kugin da cikinta yayi
na yunwa yasa ta kwanta ahankali kan gadon tareda kife cikinta tajuyayar da fuskanta tana
kallon mirror ta hakan yasa tajuyama kofan baya ahankali tana lumshe idanu wasu zafafan
hawaye na sauko mata daga idanu sabida shegen yunwan datakeji gashi yakorota ciki, almost
5min tana kwance ahaka kaman daga sama taji kamshin turaren mai dadi nashiga hancinta
dudda muran datake hakan bai hanata jin dadin turaren ba, ahankali tajuyo da kanta batare
data tashi zaune ba dantaga waye yashigo dan ko kadan bataji alamun tafiya ba, Abee tagani
tsaye bakin kofanta dauke da tray a hannunshi yana kallonta ba yawo ba fallasa, dawani kalan
sauri takai hannunta tashare hawayen dasuke kwance kan fuskanta sannan ta yunkuro ta tashi
zaune dan dafe kanta tayi tareda yatsine fuska sabida ciwonkan dataji kaman kanta zai tsinke
yafadi, daukekai yayi daga kallonta batare daya shigo dakin ba yace “tashi kisa kaya” babu
musu ta tashi gaban wardrobe taje tabude wani dogon rigan bacci tadauka sannan tajuya tadan
saci kallonshi ganin yana tsaye inda yake har lokacin yasa ahankali tazo tawuce bathroom
tamaida kofan tarufe, towel din jikinta ta cire tayi hanging sannan tasaka rigan baccin peach ne
very decent ya tsaya mata iya knees dinta rigan yamata kyau sosai gadan katon tebanta daya
fito daga rigan, gashin kanta dukya kara hargitsewa sabida yanda tasaka rigan dagaka, bude
kofan tayi ahankali taleko cikin dakin, baya dakin amman ya ijiye mata tray abincin akan carpet,
jellof rice ne da naman kaza kusan 5 akai sai tururi suke alamun yamata microwaving sai goran
ruwa akan tray mara sanyi da spoon, da wani kalan sauri tafito har murmushi take ganin abincin
zama tayi tadauki spoon dasaurinta zata fara ci daidainan aka sake bude kofan dakin dasauri
tadaga kanta daidai tanakai rice bakinta hada ido sukayi da Abee dake rikeda kwalin magani
guda biyu a hannunshi, ahankali tasauke kanta kasa tana ijiye spoon na abincin dazata kai baki
tarasa mesa dazaran taganshi she use to become restless yatsunta tashiga wasa dashi batare
dako motsin kirki takarayiba, karasowa cikin dakin Abee yayi har zuwa gabanta ya tsaya tareda
ballo paracetamol biyu da actifed guda daya murya chan kasa kaman wanda bayason yay
magana yace “take” dan kallonshi tayi ganin kallonta yake ba wasa kan fuskanshi yasa kaman
wata yar yarinya tabashi hannunta, palm dinta yafara kallo sannan yasamata pills din aciki
raurau tayida idanu tana kallon magungunan babu abinda ta tsana arayuwanta kaman magani,
bottle water daya kawomata mara sanyi yadauka yabude yabata hannu tasa takarba shima
sannan tadan kalli fuskanshi kaman mara gaskiya awani irin hankali akuma tsorace tace “in
sha?” Wani mugun kallo yamata yace “no kishafa” raurau tasakeyi da idanu, sannan ahankali ta
daura pills din kan cinyanta tadauki guda daya rak acikin guda ukun tana kallo sannan takalli
fuskan Abee adan tsorace ganin ita yake kallo yasa dasauri ta dauke kanta takai maganin ta
wurga baki taredakai ruwa ta kurba wani kalan kakarin amai tahau yi Abee dake kallonta yace
“kikamin amai anan saikin lasheshi tass” yay maganan yana fizge ruwan daga hannunta ganin
tana shirin zubarwa, sauran pills din yadauka daga kan cinyanta yarike a hannunshi sannan
yakai ruwan bakinta ahankali yace “open your mouth” babu musu tabude bakin zuba mata
ruwan yayi aciki sannan yace “raise your head” daga kanta sama tayi sannan yadan matso
kusada ita faduwa gabanta yashigayi sosai amman tadaure, watsa mata pills din acikin bakin

yayi dasauri tahadiye tana wani kalan tabe fuska da baki kaman taci kashi tadauki spoon tadebi
rice dasauri takai bakinta tanaci hawaye yayi fall acikin idanunta, AC dakin yakalla ganin akashe
yasa yakalleta har lokacin tabe fuska take irin na wanda yasha magani yace “da ruwan sanyi
kike wanka”? Kaman daga sama taji tambayan, dan kallon fuskanshi tayi saikuma ta gyadamai
kai ahankali kafin tadauke kanta tace “ban iya kunna ruwan zafi ba” dan shiru yayi yana kallon
yanda take magana, jin baice komiba yasa tadago kanta hada ido sukayi dasauri tadauke kai,
mikewa tsaye yayi yawuce bathroom nata yabude ya tsaya daganan bakin bayin yana kallon
ciki bayin is very clean towels ne kusan guda 5 ta shaya ajikin hanger juyawa yayi yakalleta
ganin tana zaune inda take bata tashiba yace “sainace kizo zakizo” dago kanta tayi tadan
kalleshi saikuma ta taso ahankali dauke kai yayi yashiga bayin tabiyoshi ta tsaya daga nan
bakin kofa nuna mata yanda zata kunna hot water yayi sannan yajuyo yace “kingane”?
Gyadamai kai tayi ahankali kanta akasa ganin yana tahowa yasa tafice daga bayin dasauri
takoma wajen abincinta tazauna tafaraci shikuma yafito daga bathroom din yawuce yafita daga
dakin.


Tass tacinye abincin da naman tasha ruwa sannan tahau gado sai bacci.
4:30 Abee yafito cikin jallabiya yatada mutanen gidan batare daya shiga dakin Lujain ba,
yawuce masallaci.
Wuraren 7 nasafe Hajiya tafito falo taxauna kan kujera daidai Kausar dake cikin kitchen tafito da
kula zata ijiye kan dinning Hajiya tace “Kausar jeki cema Auntyn ki Lujain tashirya tsaf ta sauko
Babanku zai kaita yasata a makaranta yau” Gyadamata kai Kausar tayi tawuce sama.
EPISODE 2️⃣4️⃣




Knocking kofarta Kausar tayi jin shiru yasa tabude kofan dakin akan dadduma taganta dan
yanzun nan ta tashi ganin tana salla yasa tace “Hajiya tace ki shirya kizo kasa” tana maganan
tajuya tafita daga dakin.
Saida ta idar da salla tai azkar sannan ta tashi bathroom takara shiga tai wanka da ruwan zafi
sosai ciwon kan datakeyi yatafi batajinshi kuma saidan hancinta dayay blocking shima kuma
yaragu sosai dan tana iya numfashi da hancin yanzu bakaman jiyaba, fitowa tayi daure da towel
tazo gaban wardrobe tabude tana kallon kayan wajen, wani abaya tajawo black ne gabaki
dayanshi mai kyau kana ganinshi kaga saudi abaya, yauma bata saka bra ba singlet tasa da
pant sannan tadaura abayan akai bayan tashafa mai, tadau gyalen abayan tadaura akan
yamutsassen gashinta tabude kofa tafito ahankali tafara tafiya chak ta tsaya ganin Abee na
hayowa sama idanunshi akanta hakanan jitayi gabanta na faduwa sosai, saida yazo daidai dap
da ita bakinta yadan fara rawa takasa ma magana, wani kalan kallo yamata daga sama zuwa
kasa sannan yace “go back inside kidauki hijab kisa” yana maganan yawuce yabarta awajen,
saida taji karan ya maida kofan dakinshi yarufe sannan tajuya ahankali takoma dakinta,
wardobe taje tabude tana kallon hijaban wajen wani maroon hijab tadauka tasaka yamata wani
kalan kyau kaman balarabiya ne tasaka hijabin sannan tadauki takalmin da Baba yasaya mata

tasaka dan babu wani takalmi adakin shima hala dan ba’asan size nata bane tafito ahankali
take tafiya tazo stairs sauke kanta kasa tayi sabida yanda suka cika falon duk ana shirin yin
breakfsat tunda tafara saukowa idanun Hajiya kyam akanta maroon hijabin datasaka ba
karamin kyau yamata ba deep down tana addu’a Allah yasa suzo juna itada Imrana dan
tanamai mugun kwadayin Yar yarinyar nan, murmushi tayi tace “Lujain an sakko” dago kanta
Lujain tayi tadan kalli Hajiya wani kalan kunyan matan taji hakan yasa tamaida kanta kasa
takarasa wajenta saida tazauna akasa kusada ita murya chan kasa tace “ina kwana Hajiya”
murmushi tamata tace “har yanzu muran bai sakeki ba? Duk muryanki ta chanza kinsha magani
kuwa”? Gyadama Hajiya kai tayi ahankali, Hajiya tace “waya baki maganin”? Dan shiru tayi dan
batasan yaya zata kira sunan Abee ba hakan da Hajiya ta lura yasa tace “Imrana yabaki”?
Gyadamata kai tayi ahankali, Abdallah dake saukowa kasa gaban Hajiya yazo yace “Hajiya
natafi yau ina azumi bazanyi breakfast ba” yakalli Lujain da kanta ke kasa yace “good morning
Anty Lujain” dago kanta Lujain tayi ahankali tadan kalli Abdallah dake kallonta yana murmushi
sauke kanta kasa tayi tama rasa mezatace itane wannan babban yakira da Anty, Haiiya dake
murmushi tace “Antynku Lujain badai kunya ba” murmushi yayi yace “natafi” “Allah bada sa’a
Abdallah” Hajiya tafadi tana hararan Kausar datazo ta zauna gefen kujeran da Babanta ke
zama rikeda plate na chips itama ta shirya makaranta hijabi kawai zata saka tafita, fitowa daga
kitchen Anty Binta tayi itada Maman Aneesarh ganin Lujain yasa tai wani kalan murmushi tazo
wajen suka ajiye kuloli tashafa kumatun Lujain hakan yasa tadago kanta dan murmushi tama
Anty Binta tace “good morning Anty” morning Lujain bari nahada miki tea” tea tahada mata a big
cup this time sannan tazuba mata chips a plate da fried egg da pepper soup, ahankali tafaracin
chips din tanashan tea ahankali dan yanada zafi ba kaman wanda Gwaggo kemata ba, kamshin
turaren Abee da yacika falon yasa tasan yasauko ne dan ko kadan bakajin footsteps nashi,
zama yayi Anty Binta tace “Ya Imran coffee ko shayi Wanne kakeso”? “Coffee” yafadi ahankali
yana duba agogon hannunshi, Hajiya dake kallonshi tace “zubamai da chips da farfesu Binta ni
bantaba ganin makiyin abinci irin Imrana ba saisa gashinan Abdallah kaiya dauko” Baice
komiba kawo mishi Anty Binta tayi a tray tadaura kan table dake gabanshi coffee yadauka
yafara sha daidai nan Kausar tagama tamike takalli Abee shima kallonta yayi yanashan Coffee,
kaman zatai kuka tace “Abee ban iya assignment dina ba” wani mugun kallo yamata yace “and
u are telling me now” sauke kanta kasa tayi sabida mugun kallon dayamata ahankali tace “Abee
kayakuri baran karaba” Hajiya dake jinsu tace “ke wlh fitinanniyan yarinya ce Kausar, ke kinci
abincinki kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login