Showing 30001 words to 33000 words out of 82745 words
to,
Hajiya share hawayen fuskanta tayi tass sannan tawuce sama, Dr yabi kowa na dakin dasukai
jugum da kallo yace “he is fine nan da 24hrs that’s idan yamakai kenan ya warware” yay
maganan yana bama Ibraheem prescription sheet yace “he needs this drugs now kuje kusayo”
tashi Musty yayi yakarbi takardan a hannun Ibro yace “bari naje nasayo kai Ibro drop Dr at
home tunda ba mota a hannunshi” suka fita tare.
EPISODE 1️⃣3️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Parking yayi awajen parking nacikin gidan, yakai kusan 5min zaune acikin motan ya jinginar da
kanshi tareda lumshe idanu sannan yatashi yabude kofan motan yafito ahankali da Maigadin
yafaracin karo da shima idanunshi yay ja sai kallon Abee yake kaman yauya fara ganinshi,
dauke kanshi Abee yayi, laptop dinshi ya dauka yamaida kofan motan yarufe sannan yay cikin
gidan da sallama chan kasa yabude kofan Babban falonsu yashiga kowa na zaune falon harda
Zainab dayasan takoma gidanta kaman gidan da akai mutuwa duk suna kallonshi ga Hajiya ita
tabuga tagumi itama kallonshi take, ahankali yace “ina wuni Hajiya” batare daya jira amsanta ba
yawuce stairs dasaurinshi dan baimason wani magana yana zuwa yabude dakinshi yashiga ciki,
zama yayi ahankali bakin kujeranshi yacire takalminshi da safan kafanshi kafin yatashi yamike
tsaye ahankali yake tafiya zuwa bakin gado gently ya kwanta akan gadon tareda fuzar da ajiyan
zuciya ya lumshe ido ahankali yanajin kaman zazzabi na neman kamashi, knocking kofarshi da
akayi yasa ya runtse idanunshi da karfi yabudesu ahankali batare dayay magana ba, muryan
Kausar yaji ahankali tace “Abee” tashi zaune yayi da sauri yakalli kofan anatse yace “come in”
bude kofan dakin akayi Kausar yagani tareda Abdallah idanunsu sunyi jaa suna tsaye gaban
dakin duk suna kallonshi dawasu kalan disturbing eyes, wani abu yaji ya tsayamai azuciya
amman yadaure batare da wani abu yanuna akan fuskanshi yace “kushigo” Kausar tafara
shigowa da gudu tana zuwa batai wata wata ba kneeling tayi akasan gaban gadon gabanshi
kawai tafada jikinshi tasa kanta akirjin ta rungumeshi ta kulle hannayenta ta bayanshi ta
kankameshi sosai tawani kalan fashe da kuka duk duniyan nan batada abinda takeso kaman
babanta, ahankali Abdallah da Abee ke kallo yanajin yanda Kausar ke kuka ajikinshi yakaraso
wajen shima zama yayi akusa da mahaifin nashi agefen gado gently yadaura kanshi kan
kafadan Babanshi batare dayace komiba, saukan dumin hawayenshi Abee yaji kan kafadarshi
tunda abin nan yafaru sai yanzu ne Abee yaji kawai he’s completely heartbroken sabida yanda
yaranshi suke kuka ajikinshi, Kausar ita wannan daman ta iya kuka but Abdallah rabon dayaga
kukan Abdallah tunda mahaifiyarshi da yayyinshi suka rasu, shiru yayi jikinshi yayi wani kalan
sanyi baimasan wane zai lallasa cikinsu ba, baisan mezai gayamusu ba, all he knows is yau
shine reason behind his children tears, kusan 10min kuka suke ajikinshi hakan yasa yasauke
ijiyan zuciya Abdallah yafara dago kanshi da hannunshi yace “mehaka kakeyi Abdallah Men
don’t cry” dago fuskan Kausar yayi daga jikinshi dake kuka sosai hannunshi yakai yasharemata
hawaye yadanyi murmushi tareda jan mata hanci yace “kinsan bansan kuka ko” girgizamai kai
tayi cikin wani kalan sheshekan kuka tace “mekamusu akeson abata maka suna Abee, me
Babana yamusu? Why you Abee”? Kifa kanta tayi akan kafanshi tahau kuka sosai gwanin ban
tausayi, dagota Abee yayi idanunshi sunyi ja yakalleta dan murmushi yakakalo yakalli Abdallah
dake kallonshi yama rasa abinda zaice musu kawai rungumesu duka yayi akirjinshi duk suka
kankameshi kaman yanda he was holding them so tight, bayansu ya bubbuga anatse calmly
trying to soothe them yace “everything is going to be fine I promise” yay shiru jin haryanzu
hawayen su na zuba ajikinsu yace “if you two wants to break me kucigaba da kukan nan”
kaman yabasu pills din tsayarda kukan sukayi hakan yasa yadago kansu murmushi yamusu
yahada hannayensu biyu yakai bakinshi yamusu peck ahankali yace “you two are Abee’s
strength if you break I break, so I want you to be my strength not my weakness kunji, everything
is going to be fine I promise” gyadamai kai sukayi ahankali, murmushi yayi yaciro handkerchief
a aljihunshi fuskan Abdallah yafara gogewa tass sannan yashare na Kausar shima tass
ahankali yace “jeki kawomin abinci I am hungry” dasauri ta tashi tana gyadamai kai tafice daga
dakin hakan yasa Abee yakalli Abdallah yace “mesa zaka biyema Kausar kuyita kuka idan
tanayi bakasan kaine zaka lallasheta ba”? Gydama Abee kai yayi, Abee yay shiru yana
kallonshi saikuma chan yace “how many lectures kai missing yau?” Ahankali yace “all” cikeda
rashin nuna jin dadi Abee yace “kar hakan yasake faruwa” gyadamai kai Abdallah yayi daidai
Kausar takawo abinci fried rice a tray da flask na shayin shi zama yayi ahankali akasa sannan
yakalli Abdallah dake kan gado yace “sauko” debo abincin yayi yakai bakin Abdallah yace “haa”
dan yasan dukansu biyun basuci abinci ba tsaf yay feeding nasu yasha shayi sannan yasa suka
tafi shikuma yashiga bayi dan yay wanka yayi shirin zuwa masallaci magrib.
Shiryawa yayi cikin wani sky blue soft yadi mai kyau dinkin jumper da wandonshi iya idon sahu,
hula yasaka sai uban kanshi yake yazura takalmi yafito daga daki afalo yaga su Hajiya da
sauran yaran Hamza Abdallah da Ibro na ganinshi suka mike dan zuwa masallaci yakalli su
Binta yace “salat” ahankali tace “eh duk yanzu zamu tashi Yaya” suka wuce suka fita, saida
akayi isha’i yazauna yakarasa addu’o’in shi mikewa yayi zai tashi Baba Liman yace “Imrana
biyoni” ahankali Abee yabi bayan Baba Liman daya daukeshi amatsayin uba har zuwa waje
gaban wata Babban jeep da kallo daya yamata yasan motan Musty ne, bayan motan
yabudemai yajuya yana kallonshi yace “shiga” dan jimm yayi ganin Musty da Harun ne agaban
, Baba Liman yace “koban isa bane Imrana” babu musu yataho ahankali yashiga bayan motan
Liman yashiga sannan yarufo kofan motan Musty yaja motan.
Suna kaiwa kofar gidan da Gwaggo tamusu kwatance ga mamakinshi motan Ibro da Abdul
yagani akofar gidan, Hajiya, Anty Binta, sai Hamza da Ibro duk suna tsaitsaye da alamu su
kawai ake jira, kofa Baba Liman yabude yafito yakalli Abee dake zaune yace “fito” ahankali
Abee yafito daidai Baba yabude gate yafito sabida sallama da akace anayi dashi daman suna
expecting nasu hakan yasa yagaisa da kowa yace “bismillan ku”.
Falon Baba aka kaisu duk aka zazzauna kujerun ciki basu dauki kowa ba hakan yasa duk suka
zazzauna akasa daga Hajiya sai Baba Liman ne akan kujera da Gwaggo datake zaune har
yanzu kayan dazu ne ajikinta sai Mama da Baba, su Samira na dakinsu duk sun zauna jingine
da kofa dan suji ne za’ace, yanda Gwaggo kebin kowa da kallo kasan daidai take da kowa Baba
na shirin magana tadagamai hannu tace “dakata Malam ai ba kai kabasu adreshin gidan nan
bako dan haka wajena sukazo” Takalli Musty tace “kun yarda da sharadin nawa”? kafin Musty
yay magana Baba Liman yay gyaran murya hakan yasa akai shiru adakin taron yabude da
addu’a sannan yace “na farko dai nine ke matsayin mahaifi ga dukan yaran nan, marigayi
mahaifinsu babban abokinane, dukanmu munzo nan ne mukara jajantawa sannan mubaku
hakuri kan abinda yafaru wanan abin kaddaran, sannan na tunatar damu cewa mu musulmaine
hakkine akanmu na murufawa juna asiri, sannan kusani cewa abin nan dayafaru tun kafin
dukanmu nan muzo duniya aka rubuta hakan zai faru a Lawhun Mahfuz dan haka” yakalli
Hajiya da ahankali tace “nine mahaifiyar Imrana, amatsayina na mahaifiyarshi na yarda da
zancen Auren nan!” Wani kalan dagokai Abee yayi yakalli Hajiya dan baitaba sanin abinda suka
yankeba kenan shifa yadauka sunzo ayi sulhu sunada hakuri ne but what is it yake fadi haka
wani kalan rawa hannuwanshi suka fara gently Musty yadaura hannunshi saman hannayenshi
dake rawa yarike hakan yasa yadago ifanunshi yakalli Musty da idanu yamai alamu da karyay
magana ya kunyata iyayenshi, ahankali Hajiya tace “Imrana soja ne, yanadaga cikin manyan
sojojin da Nigeria ta tura su yaki yan kungiyan bamaiyi dasuka addabi Nigeria dasaka
bamabamai shekaru 13 kenan dasuka wuce, shine sojan dayaci nasaran kashe asalin Ogansu
gabaki daya hakan yajawo mishi makiya har akazo har gidanshi aka kashemai mata da yara
biyu sauran yara biyun ma da baa kasheba dan yaranshi hudu Allah ya tsirar dasu ne sabida
sunzo gidana su kwana, tun lokacin bai kara aure ba, d’ana kamili ne adali kuma yarone da
amana dayarike addininshi da gaskiya, ni nasan Imrana bazai tabayin abinda aka ce yayi ba
amman tunda haka kaddaran tajuyo wayemu dazamuja da ikon Allah mun yarda adaura Auren
Allah yasa hakane mafi alkhairi” washe baki Gwaggo tayi tace “Alhamdulillah Alhamdulillah”
takalli Baba dake kallonta tace “ka tsareni da idanu waye zai rikemana diya amana inba mutum
haka daya samu kyakkyawan shaida ba takanas takano wannan tsohon limamun yabiyoshi
harnan shima yamishi shaidan kirki, dazu nan nan su Abdulhadi damuka bincike suka dawo
suka ce duka yan anguwansu sun bada shaidan kirki idan baka aurama jikata mutum hakaba
kamili Babba mai hankali wazaka auramawa Iyyee” Ahankali Baba yakalli Baba Liman yace
“bismillah Liman adaura” wani kalan mugun ciwon kai Abee yaji yanaji idanunshi namai wasu
kalan duhu Misty yarikeshi gam batare da kowa yay noticing ba, agabanshi yana zaune yana
kallon kowa aka daura aure tsakaninshi da Lujain akan sadaki dubu dari biyu da friends dinshi
Musty Harun da Abdul suka biya take yanke in cash, Gwaggo tace “jedakina Hadi ka kwaso
goro” dasauri Hajiya tace “Muma muntaho dashi tashi ku kwaso Hamza da Ibro” tashi sukayi
nan da nan suka fara shigo da carton carton na goro da sweet ana kawowa falon Abee na
mamakin lokacin da duk aka sayo abubuwa haka but yasan aikin Hajiya dasu Musty ne shiru
kowa na dakin yayi banda Gwaggo data tashi tana bare kwalin sweet da Goro tana kakkasawa
kana ganinta kasan ita kadaine ke farinciki da wannan auren.
Dan gyaran murya Abdul yayi yakalli Gwaggo yace “Kaka mu bangaren police muna bukatan
video da statement naku dazaku bayar amatsayin shaida cewa sudin mata da miji ne sabida
duniya tagani hakan zai siliencing kowa kafin ayi tracking yaron shima muna kan hakan” dasauri
Gwaggo ta ijiye kwalin tace “to fara dani” kunna video yayi yace “Kaka waye Imarana” washe
baki tace “mijin jikata ne, jikata matarshi ce” yama su Baba dasu Baffa sannan yama Hajiya tace
“Lujain Matar d’ana ne” saida yagama sannan yay murmushi yamaida wayan aljihu yazauna
dakin aka karayin shiru anatse Liman yace “Alhamdulillah yanzu an daura aure Imrana Lujain
matarka ce yanzu sai magana tagaba aahhh yaushe zata tare”? Gamgam Musty yarike hannun
Abee dayaji na rawa sosai, Baba na shirin magana Gwaggo tace “zakudan bamu kwanaki
mudan shirya, tunda yau litinin ranan asabar idan Allah yakaimu mahaifinta dakanshi zai kaita
dakinta ko”? Gyadamata kai Baba yayi yace “in sha Allah” Gwaggo tai murmushi tace “yanzu
ma dan tai bacci ne dana turota ta gaisheku tunda nake bantaba ganin Lulu tai irin kukan datayi
yauba har muka dawo gida har magrib kuka yarinyar nan take Allah dai yasaka muku dagakai
Imrana har Matar taka Lujain, kutashi kutafi gida shima yaje yahuta Allah kadai yasan yanda
zuciyanshi ke tafarfasa Dan mutum kamili dashi wani gantalalle chan Ya batamaka suna ana
kiranka da fasiki, Allah ubangiji ya saka muku yakuma bimuku hakkin ku, yanzu fa anxama daya
zamu hadu mu kare mutunci yaranmu ne murufa musu asiri, kai dan nan idan akwai wani video
dakakeso nayi kuma kazo zan maka In har hakan zai kawo saukin lamarin nan” dan murmushi
Abdul yayi, Baba Liman yatashi hakan yasa Gwaggo da kowa na dakin suka tashi gaggaisawa
akayi Gwaggo da Hajiya sukai sallama sannnan har waje suka rakasu suka tafi.
EPISODE 1️⃣4️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Gwaggo kotakan su Baba batabi ba bangarenta takoma tana shiga tamaida kofan dakinta tarufe
tasaka sakata ta ijiye kwalin sweet da goron data shigo dashi akasa sannan tawuce uwardakan
tana kallon fuskan Lujain dake kwance kan gado daure dawani farin towel kanta babu dankwali
idanunta sun kumbura sosai da fuskanta ma, karasawa gaban gadon Gwaggo tayi tazauna
ahankali tana kallon fuskanta murya chan kasa tace “bantaba sanin kankanin abu na faruwa ba
dazai kawo wani rayuwanka wanda hakan yake kaman aya agareka ne sai akanki Lulu, ninafi
kowa sanin yanda kikeson wannan gantalallen dan kwallon Mandawari, yau agabana kika fasa
zunzurutun asusunki kika kaima wanan kuran kudin Samira dan kawai ta aramiki waya ki kalli
dan daudun mesaka hakorin makka, ni tsabagen yanda nama tsani yaron da kullum kike
nunamini awaya idan yana magana zan ma iya zanashi da pencil naganshi, ranan sabida shi
bokon ma bakiso zuwa ba dan kada yazo baki kalli video ba amman Allah bless yasa kikaje
makarantan, jibidai yanda nida idona da muna kallon video naga bayin dakiketa nema akasa ki
shiga baki ganiba domin Allah ya daukemiki idanun awajen so yake kije sama kihadu da
Imrana, kikaje saman kika bangajeshi kika bata mishi kaya da fanta amman fuskanki nakan
waya shaidanin nan kike kallo kika wuce bayi nafi kowa sanin yanda kike neman waje shiru ki
natsu duk sanda zaki kalli Mandawari dan ko ni nan idan zaki kalla uwardaka kike shigewa ko
nazo ina kwalamiki kira shiru kike ki kyaleni” shiru Gwaggo tayi sannan ahankali tace “Allah ne
ya aiko miki Imrana diyata, shima kuma Allah ne ya aikamishi ke rayuwanshi saikuma Allah
yakaddara cewa ba kaddara mai dadi bace zata fara hadakuba hasalima na batanci ne, na kalli
fuskan yaron nan nakara kallo babu abinda nagani kan kwayan idanunshi Sal dumbin alkhairai,
nasan baki sonshi shima bayi sonki, baki sanshi ba bai sanki ba amman kuma Allah yahadaku!
Allahandaya hadaku shinake roka ya dawwamar daku awanan rayuwan Auren har abada Allah
yasamishi sonki da kaunar ki dakuma tausayinki kema Allah yasamiki haka, koyau nafadi
namutu Alhamdulillah, kullum banda zullumin daya wuce wazaki aura wazai auri Lulu na,
amman kinga wannan mutumin yanada yara da sunma girma miki Dan haka ina mai kyautata
zato zai iya tafiyar dake da kyau” hannu tadaga ta tottafa addu’a sannan tashafama Lujain a
fuska kafin takashe wuta ta kwanta kaman jira Lujain take kankame Gwaggo tayi Gwaggo tace
“ahap aini nasani duk yanda takai ga bacci inhar taji dumin mutum saita kwakumeshi” kafin
kaceme Gwaggo tafara jan minshari.
Suna kaiwa gida Abee bai kula kowaba fita yayi daga motan dasauri yay flat dinsu Hajiya zata
kirashi Liman yace “kul Hajiya kubarshi, kubar yaron nan shi kadai yasan meyakeji” yajuya
yakalli su Ibro yace “ku kira likitanshi kuji” gyadamai kai yayi sannan Baba Liman yace “saida
safen ku” godiya duka sukamai yawuce, Musty da Harun ma sukama Hajiya sallama dan tun
ahanya suka sauke Abdul ya sauka a police station dinsu sukuma sauran suka shige gida.
Wuraren 2:30 wani kalan bakin yunwa ne yatadata daga bacci muryanta ya dishashe sosai
sabida kuka ahankali tace “yunwaaa” firgigit Gwaggo tafarka tocula tajawo ta haska dakin yay
haske sannan ta tashi zaune tana kunna wutan dakin tace “mussamman nasan yau dole kitashi
da wuri dan babu abinda kikaci kikai wannan wahalallen baccin, sauko ga abincin ki nan a tray”
Gwaggo tai maganan tana jawowani katon tray gaban gadon ta zauna tana bubbude mata
kulolin, sannan tadau wani babban kofi tana juye mata tea dayaji madara da Milo dake tiriri
akan a cup din, daidai nan ta sauko tana gyara kullin towel din kirjinta, Gwaggo tadauki cup din
shayin tabata ahankali takarba takai bakinta tana karban buredin da Gwaggo kebata data
yagomata kato ahannu, Gwaggo takai hannunta saman goshinta tace “kinga har jikinki yay zafi,
nida har sadaka saida nayi na murnan daina zuwa asibiti yanzu kuma zaki maidamu ne” shiru
tayi kawai shan shayin take da buredin da sauri da sauri tass ta shanye shayin tana mikama
Gwaggo kofi tace “karamin” karasa juyemata ragowan tea tayi shima yacika cup din takai
bakinta tanasha maganan su princess ne yadawo mata sabo aranta jitayi shayin da abincin
gabaki daya yafita aranta, ahankali tasauke cup din daga bakinta ta ijiye akasa dasauri Gwaggo
tace “menene kika ijiye shayin kuma keda ke shanye shayinki tass” ahankali takai hannunta kan
katon kumatunta tabuga tagumi dasauri Gwaggo tasa hannunta tacire tagumin tace “bana
gayamiki babu kyau tagumi ba” kaman jira take wani kalan rushewa da kuka tayi sosai tanuna
kanta tace “Gwaggo su princess sunce wai ni Yar iskace, ni karuwa Gwaggo ai kintuna lokacin
dana fara period kince min ko hannun namiji yarike zanyi ciki ko” Gwaggo ta gyadamata kai
itama kaman zatai kuka ganin yanda Lujain ke kuka bitterly, cikin mugun kuka tace “wlh
Gwaggo, wlh wlh ko yatsana bai tababa, baimazo kusadani ba, Gwaggo bantaba ganinshi ba
sai ranan, Gwaggo nida banda saurayi babu wanda kesona sabida ni katuwa ce inada kiba,
dawane zanyi iskanci? Gwaggo ni yanzu konaga mutumin ma bansanshi ba baranma ganeshi
ba, Gwaggo nayi ihu daga ganshi bisa ka na abayi sabida nasaka earpiece banmaji karan
tafiyan da ba, ganinshi akaina yasa nai ihun nan ba wannan ihun wanda wanda….. wanda naji
aaaa……..” tawani kalan fashe da kuka sabida yanda abin kemata ciwo, hannunta Gwaggo
takai zata share mata hawayen cikin kuka kaman wanda ta tuna wani abue tace “shine suke
kirana fasika, karuwa da Yar iska, Gwaggo ni, ni ni Lujain ce karuwa” tanuna kanta tana wani
kalan kuka mai tsuma rai dayasa Gwaggo tafara