Showing 69001 words to 72000 words out of 82745 words

Chapter 24 - Sakon So Book Complete by m Shakur ( By Ubeera ) .pdf

M Shakur   

11 Oct 2025

1618

filoli da bargo tana neme neme yasa Gwaggo tace
“nashige su mehaka kika juyamin daki wai mekike nema haka kinbar mijinki shi kadai adakinshi
ke kina nan tun dazu yatafi ya kwanta” turo baki tayi tazauna ganin bakin gadon tai tagumi
ganin bataga wayan ba, karasowa dasauri Gwaggo tayi gabanta takama hannunta tareda
mikarda ita tsaye tace “yo wai ke wace kalan yarinya ne Lulu iyye? Oya wuce kitafi dakin mijinki”
turobaki tayi tace “ni anan nake kwana” baki Gwaggo tasaki saikuma tamata dakuwa kaman
zata tsokale mata idanu da sauri ta kulle idanunta Gwaggo tace “aida kin barshi bude kiga
yanda zan tsiyaye miki wayan nan idanuwan magen naki tunda bakida hankali, wuce kitafi dakin
mijinki” akufule Lujain tace “ni bansan dakinshi ba Gwaggo kumani ki kyaleni” hararanta

Gwaggo tayi kawai ta finciki hannunta tayi waje da ita tana masifa tace “da girmana billahillazi
barakisa nayi abun kunya ba nazo gidanku inaji ina gani kizonan ki kwana dani barakije ki
kwana da mijinki ba” duk yanda Lujain ke turjewa kin sakinta Gwaggo tayi har gaban dakin
Abee kai tsaye Gwaggo tabude dakin tareda wurgata ciki itama tana shigowa Abee dake zaune
gaban study yadago kanshi yakallesu yanda Lujain ke makema Gwaggo kafada alamun barata
zauna anan ba Gwaggo ta washe baki tana kallon Abee tace “Imrana zan lallasa matar nan
naka akanme sabida taganni barata kwana dakin mijinta ba sai wajena, kibiyoni kiga abinda zan
miki” Gwaggo tawuce tafita tareda rufomusu kofan tsayawa wajen tayi chak kanta akasa
hawaye ya gangaro daga idanunta takai hannayenta tanajan riganta kasa she’s so
uncomfortable, Abee cigaba da abinda yakeyi yayi batare daya kara bata second look ba, gajiya
tayi da tsayuwa ganin kafafunta na neman rikewa ta tsugunna ahankali akasa saikuma tazauna
awajen kaman marainiya tarasa abinda kemata dadi, wuraren 11 tafara gyangyadi awajen.


12 daidai Abee yagama aikin dayakeyi tass yakashe computer sannan yajuyo ahankali yadaura
idanunshi akanta gabaki daya atakure take tana gyangyadi kanta na lilo awahale. “Kee!” Wani
kalan mugun firgita tayi tabude idanunta dasauri tareda mikewa tsaye tana kallon Abee awani
kalan tsorace, mikewa tsaye yayi ahankali tareda zuba hannayenshi acikin aljihun wandon dake
jikinshi yafara tafiya yana tahowa inda take, batasan mesaba wani kalan faduwa gabanta
yashigayi yawani kalan cika mata idanu yamata mugun kwarjini kasa jure kallon dayake mata
tayi dawani kalan sauri tasauke kanta kasa, karasowa yayi gabanta ya tsaya chak hannunshi
zube a aljihu yana wani kalan kallonta, tunda take bata tabaganin mutumin dayamata rumfa
kaman yanda Abee yamata ba ganin yanda ya tsaya daf da ita ko Baba baya mata rumfa haka,
hakanan jikawai tayi kafafunta sun kasa daukanta, dukewa tayi awajen dasauri tana wasa da
yatsunta, kallonta yayi cikin kakkausar murya yace “stand up!” Babu musu ta mike tsaye kirjinta
nawani kalan bugawa babu kakkautawa bata tabajin kalan faduwan gaba datakeji ayanzu ba
wani kalan zati da kwarjini Abee yakedashi da ita kanta bazata iya bayani ba, ganin yanda
takasa dago idanunta takalleshi yasa strictly yace “look into my eyes!” Dago idanunta tayi
tadaura akan nashi kasa cikakkun 3secs tayi ganin kalan kallon dayake mata zata sauke
idanubta kasa azafafe yace “don’t you dare!” kafeta yayi da idanu yana tura hannunshi cikin
aljihu yaciro wayan Mandawari tareda nunamata wani kalan ijiyan zuciya tasauke saida yaji
saukan numfashin akan fuskanshi gashi ya tsareta da idanu bayako kyaftawa daburcewa tayi
daburcewan dabata tabayiba tunda tazo duniya kawai fashewa tayi da kuka, yatsanshi yakai
kan lips nashi hakan yasa tawani kalan hadiye kukan tass, anatse yace “kuka nace kimini”?
Girgixamai kai tayi tanawani kalan sauke ijiyan zuciya gwanin ban tausayi, ganin yanda take
numfashi kaman zata shide yasa ya sassauta murya ahankali Yace “what did I say?” Adaburce
tace “kace wayan waye wannan?” Tsareta da idanu yayi alamun yana jiran amsa, lips dinta har
rawa suke kaman an jonamata electric shock tace “Maa…….Man…….d…..wari
yab……b……bani” tafada dukta burkice, wani irin kallo dayamata yasa taji cikinta ya murda
batasan lokacin datace “a school din nan yakawomini” wani irin kallo Abee yamata yace “ina
jinki” kuka ne a muryanta sosai amman yahanata yi in that crying tone tace “ina aji security guy
yazo yace Yayana nakirana I thought kaine naje naga shine, he asked me yanda akai auren mu,
saiya bani wayan yace zai kirani and he’s inviting me to his welcoming party, da……daz….zu

ma yaaaaa…..kir……rani” Abee jiyayi kaman ta watsamai garwashin wuta azuciyanshi, nunata
yayi da yatsa yace “listen here girl babu abinda zanyi dake, I don’t consider you my wife one bit,
ko anjima aka kama yaron nan I will be sending you back to your father’s house batare dana
bari kin kara koda kwana daya agidan nan ba, but listen here dagayau don’t ever bring wani abu
that belongs to wani namiji into my house kinajina” gyadamai kai tayi dasauri tana tagwayen
ijiyan zuciya idanunta na mugun kyalli sabida yanda suka cikada hawaye, cikin zazzafan murya
Abee yace “nine nace you can live anyhow and talk to duk wanda kikaga dama and that same
me yau na janye! Inhar kina gidan nan kina zama karkashina karki kara kula wani, idan kika
kara koda kallon that small boy saina baki mamaki kinajina” gyadamaikai tayi dasauri tace “eh
naji” cikin fushi sosai Abee yace “just sit and be praying akamo mutumin nan so that you will get
out of my life forever nagaji dake! I am tired of you! Pray akamoshi sabida narabu dake only
then you can do duk abinda kikaga dama and talk to duk wanda kikaga dama Imran doesn’t
care! Understood” gyadamai kai tayi dasauri, hakan yasa yawuce fuuuuu yafada bathroom
nashi, wanka yayi yafito sanye da kayan dayashiga dasu bayin yana fitowa yabude kofa
yashiga dakin closet nashi yadan jima aciki sannan yafito dawasu pj dark blue ajikinshi yana
wani kalan kamshi hannunshi rikeda wani babban bargo batare daya kalleta ba yace “jeki
kwanta akan gado” dan dago kanta tayi takalleshi ganin yay kan dogon couch din wajen yana
shirin kwanciya yasa ta tashi ahankali tai kan gadon har wani tsoron hawa gadon take, gadon
fes fes bedsheet din fari kal amike kaman ba’a kwana akai, kaman wacce bata bata ganin gado
ba tahaukai ta kwanta gadon nawani kalan kamshin turarenshi, bargo taja ta lullube sabida
yanda dakin keda sanyi, kashe wutan dakin akayi hakan yasa ahankali tasauke ijiyan zuciya
tareda lumshe ido.
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI



EPISODE 3️⃣8️⃣




Hakanan jitayi baccin yaki zuwan mata tarasa sukuni bakaramin damuwa ne aranta ba, yace zai

saketa dazaran gaskiya ya bayyana amman kuma yahanata magana da saurayinta mai sonta
wanda zai aureta dazaran sun rabu, duka maganganunshi dawomata suke, wani kalan kukane
yazo mata taushe bakinta tayi da bargon data lulluba dashi tadinga kuka, tarasa farincikin ta
rana daya kawai sabida wani mugun shairi dawani mutum yahada mata, dudda Babanta baida
kudi Babanta atampopi yake saidawa akasuwa gidansu babu Ac kaman wannan, gidansu is not
mansion kaman wannan, babu motoci agidansu kaman irin manyan motocin gidan nan but she
has always been a happy person, kometakeso takeci, Baba nadadewa kafin ya yanka musu kaji
but Gwaggo koda yaushe tana cikin yanka mata kaji tana soyamata, dudda lokacin Mandawari
baitaba kulata ba ko amsa messages nata still she’s always happy, she’s always at each she
sleeps peacefully clinging to Gwaggo so tight, but rana daya she lost everything she lost her
sweet life, kunya da tsoron fita take, zaman aure take dabama tagane kan Auren ba, zama take
a inda batasan kowaba, Mandawari da sunan shine kullum acikin sallolinta biyar finally Allah
yahadata dashi he loves her so much har yana bata iPhone IPhone dabata taba rikewa a hannu
ba, but Mandawari yabata yay yay inviting nata but she couldn’t show up duk sabida wannan
kaddararren auren duk dan sabida wannan shairin da aka mata, Allah kadai yasan yanda
Mandawarinta yake fushi da ita yanzu ina zatasa kanta taji dadi, babu abinda kemata dadi
aduniya, cikinta ne taji yadaurenata kanta na sarawa, lallashin kanta tasomayi juye juye
tadingayi akan gadon tarasa abinda kemata dadi aduniya, daga baya tashi zaune tayi gashi
wutan dakin akashe abinda yakara kara mata damuwa kenan, yaye bargon tayi ahankali
tasauke kafafunta sama dudda dakin ba duhu mikewa tayi ahankali tana shafa bango kaman
mayya tana kokarin locating bayin dataga yashiga dazu, jin ta taba kofa yasa ahankali ta murda
kofan tabude wani kalan farin bayine tsaftaccen gaske ita har tsoron shigama tafara dan karta
mai datti da bayin ganin yanda hasken bayin ke shigowa cikin dakin yasa tadan juya atsorace
takalli kujeran dayake kai ya lullube fuskanshi kadaine ke waje dasauri tashige cikin bayin
tareda maida kofan ahankali tarufe, tana kalle kalle, wanke fuskanta tayi da ruwan sanyi takalli
fuskan nata a madubi idanubta sunyi jajir sun kumbura sabida kuka, bayin tabida kallo ganin
bataga towel ba wani drawer mai bala’in kyau datagani takai hannunta har rawa yake tabude
towels tagani kusan guda 10 farare tass anmusu wani kalan rolling ninki sotake tadauka tadaura
amman yanda taga an gyarasu awajen yasa tsoro ma yahanata tabawa, bayin tashiga kallo
tana kallon sabulan wankanshi kadai kusan 13, different shower gel na maza, da scrubs
dakuma set na bubble bath, abubuwan dayake dashi ko ita batadasu bayin sai kanshi yake
bude kofan tayi ahankali tafito ta maida tarufe tana daddafa bango tawuce takoma gadon ta
kwanta ahankali tacigaba da rolling still takasa bacci sai wajajen 2:30 bacci yay awon gaba da
ita.


Tashi Abee yayi ahankali ya zauna dan all this while ba bacci yakeba yan addu’a yayi 3 dot as
usual yatashi yawuce bayi alwala yayi yafito yahau kan dadduma yafara salla har zuwa 4:00
yanakan dadduma sannan yatashi bayi yashiga wanka yayi yafito da pj dinajikinshi yawuce
closet nashi shiryawa yayi cikin wani jallabiya fara kal da hula sai kamshi yake zubawa yafito ko
kallon gadon baiyiba dan yasan ba salla takeba yabude kofa yafito tada mutanen gidan yayi
suka wuce masallaci.

Wuraren 6 tabude idanunta ahankali tanabin dakin da kallo daya kunna wutan ciki, gently ta
tashi zaune kaman wacce ta tuna wani abu saikuma ta yaye bargo tasauka daga gadon dasauri
tana kallon zanin gadon ganin bata batamishi ba yasa harwani ijiyan zuciya ta sauke, agurguje
tashiga gyara gadon dan amike taga bedsgeet din kaman ba’a kwana akai, maida bargon shima
tayi ta shimfida yanda tasameshi sannan tajuya tana bin dakin da kallo dakin komi white kar kar
sai kamshi kaman kada kafita shi karan kanshi dakin nauyin kallo yake mata kaman mai dakin
naciki, kaman yana kallonta daga wani waje wucewa tayi tafita daga dakin dasauri tawuce
dakinta tabude kofa tashiga babu Gwaggo adakin ko ba’a fadamata ba tasan tasauka kasa ne
bayi direct tawuce brush tayi tai wanka tafito tasake shiryawa tsaf wani gown tasaka very simple
mai ruwan ganye daya tsayamata a guiwa sannan ta feffeshe jikinta da turare tasake kwanciya
agado tanajin wani sabon ciwon ciki dan rabonta da magani tun wanda tasha jiya, bude kofan
dakin akayi Anty Binta ne murmushi tayi ganinta sanye da gown idan tasaka kaya saitayi daban
saita kara kyau, karasa shigowa dakin tayi da katon tray tace “sauko kiyi breakfast kisha magani
bari nakawo miki atampopinki da aka gama dinkawa jiya daman sabida bakida lafiya ne nan
baki ba” tana ijiye tray akasa tawuce tafita, saukowa tayi ahankali tazuba shayin a cup tana
kallo, bude kofa Anty Binta tayi tashigo dawani katon ghanamasgo dan anan telan ta lodo kayan
bin Anty Binta tayida kallo data wuce gaban wardrobe nata tashiga jera kayan itakuma ahankali
tadauki tea ta shanye tasss, takasa cin daidai da kwai kawai babu abinda kemata dadi ko kadan
dawowa wajen Anty Binta tayi tadauki magungunan ta tashiga ballo mata tace “ga maganin
kisha tundadai yauma baraku hadda ba sai kuma next week ke ba lafiya Kausar kuma wai
bazata ita kadaiba saikace da chan ba ita kadai ke zuwa ba” tabe fuska tayi ganin maganin da
Anty Binta ke bata, Anty Binta tace “wlh ko kisha kona fita nakira miki Yaya Imran daman
yadawo” hannu tamika mata dasauri kaman zatai kuka tace “ai zansha” runtse idanu tayi tasha
kaman zatai amai da sauri Anty Binta tabata tea tasha sannan ta tashi zatahau gado Anty Binta
tace “sauka kizauna bakisan babu kyau dazaran mutum yaci abinci Ya kwanta ba, baida kyau
sannan yanasa kiba, yanasaka katon ciki, medically kuma yanasa abinci yadawo maka har
hanci tashi muje falo ki gaida su Hajiya saiki dawo ki kwanta tunda bakida lafiya” Gyadamata
kai Lujain tayi tamike tsaye ahankali tareda saka slippers zata fita Anty Binta tabita da kallo
yanda manyan hips nata ke shaking a rigan are way too sexy, wani kalan crazy sexy shape ne
da Lujain babu abinda batadashi all this chubby orobo fine yaran nan she’s just one, gashi su
Harun da Musty duka abokanen Ya Imran na falo idan akwai one thing datasani kan Ya Imran
lokacin tun Mamansu Kausar na raye shine yanada bakin kishi dudda dai Lujain bawai sonta
yake ba kokuma yadauketa matsayin mata bane still bazaiji dadi tafito falo haka gaban
abokanenshi ba babu ko dan kwali gatada gashi duk wanda zai kalli kitson shukun kanta saiya
kara sabida yanda yay kyau bakin kiston duksun warware ma tsabagen santsi sunyi coils,
“Lujain” Anty Binta takirata dasauri ganin harta bude kofa, juyowa tayi Anty Binta takalleta tace
“zoje dauki hijabi kisaka” Gyadamata kai Lujain tayi takoma tashiga cikin dakin tana tafiya
ahankali Anty Binta na kallonta dan bata saka bra ba yau ko singlet dinma bata saba rigan
kawai tadaura ajikinta Anty Binta tace “maisa baki son saka bra Lujain batun yau na lura ba
bakison nonon ki zasu zube ba” karasa saka hijabin tayi tareda lankwaye kanta murya chan
kasa dan yau ko magana ma bason yinshi takeba tace “ni damuna yake” yanda tai maganan

Anty Binta takalla saikuma tai murmushi tace “muje” mamaki kawai take da har yanzu Abee bai
farason Lujain ba she’s damn adorable, yanda yake abubuwa ashagwabe, her expression, dan
karamin pink lips nata, kumatunta are just so sweet and too cute to watch, she just wish inama
Allah zai bata diya Yar chubby haka kaman Lujain daba karamin dadi zataji ba.

Tunkan takarasa saukowa Gwaggo dake falo suna hira dukansu Maman Aneesa, Ibro da
matanshi, Hamza, Musty, Harun da matarshi Amina dakuma Hajiya, Gwaggo ta dama musu
fura mai dan karan dadi har Hajiya saida tasa aka zubamata tanasha shima Abee na rikeda cup
a hannunshi yanasha yanadan danna wayan dake hannunshi baya amsa hiran dasuke, ganin
Lujain da Anty Binta yasa Gwaggo takafe Lujain da idanu saikuma tajuya takalli Abee da
hankalinshi kekan waya tace “Imrana wai wani mai kasiyama Lujain ne haka kaga yanda takara
uban haske kuwa wannan ai zabiya take neman zama Innalillahi” Anty Binta dahar sun karaso
cikin falon da Lujain da kanta ke kasa sabida yanda Gwaggo tasa duk ake kallonta tace
“Gwaggo man datake shafawa bayasa haske ko daya nima shinake shafawa kawai gyara jikine
dashi yasa asalin kalan fatarka tafito bagashi ni ina shafawa ba amman ni baka ce” baki
Gwaggo takama tace “ba shakka ai haka mahaifiyarta take nan fara tal usulin bafulatana,
Maman mahaifiyarta takoya mini yanda ake fura da nono, toke rashin lafiyan har bakinki
yakama ne Lulu kinzo kinga tulin jama’a baraki gaisuwa ba” sauke kanta kasa tayi ahankali tana
wasa da fararen yatsunta tace “ina Kwanan ku”.
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


EPISODE 3️⃣9️⃣




Murmushi kowa na dakin yayi mata duk suka amsa suna mata yajiki ahankali ta amsa feeling so
uncomfortable tarasa maisa kowa ke kallonta, zuwa Gwaggo tayi kusada ita tazauna tana mika
mata cup dake cike da fura tace “ga huran ki to” makema Gwaggo kafada tayi tana turobaki dan
haushin ta takeji sosai datasata taje ta kwana dakin Abee murya chan kasan makoshi kaman

munafuka dan batason wani yajisu tace “bara’a shaba din” ta harareta tareda juyarda idanunta
karaf suka hada idanu da Abee da idanunshi ke kanta hannunshi rikeda cup na furan, wani
kalan kunya taji dasauri tasauke kanta kasa, Gwaggo tace “to mekikeso nafa miki har farfesu
iyyee Lulu wai mesa aduniyan nan da tsufa na idan baki bani wahala ba bakijin dadi ni kadai ne
me jika aduniyan nan jibi Hajiya dan Allah bulbul da ita bata komi saidai amata amman nida
nama fita tsufa nine kema jikata aiki, Allah ma zuciyata yagani yabani karfi izuwa yau ban
gurgunce ba” kowa na falon danne dariyanshi yake Musty ne yace “Lujain mezakici to”? Dan
dagokanta tayi tadan kalleshi saikuma takalli Gwaggo dukdan ta kule Gwaggo tace “tuwoo” baki
Gwaggo takama tace “wlh karya take babu abinda Lula ta tsana kaman tuwo wahalar dani
kawai takeson yi” for the first time dan murmushin mugunta Lujain tasaki murya chan kasa irin
ta marasa gaskiya tace “ni kitashi kimin” tai maganan tana juyarda kanta gefe still tana
murmushin muguntan karaf tasake hada idanu da Abee dake mata wani mugun kallo dasauri
tadauke kanta Hajiya tace “Lujain zakici tuwo da gaske idan zakici saikuje kitchen dake da
Kausar dakuma Maman Aneesarh ta nunnuna muku komi kuyi kidaina wahalar da kakanki babu
kyau kinji” ahankali ta gyadama Hajiya kai, murmushi Hajiya tayi tace “zakici tuwon ne da
gaske”? Girgiza mata kai tayi tace “a’a tea zansha” yanda tai maganan kaman ka cinyeta it was
so

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login