Showing 63001 words to 66000 words out of 82745 words
yayi shima yace “what”? Dan kallon
Hajiya yayi ganin hankalinta nakan radio ta yace “about that small boy”? Dan yatsine fuska
Abee yayi yace “ohh I can’t even recall his name” dan murmushi Musty yayi yafi kowa sanin
halin Imran aduniyan nan this answer kadai na nufin baikarabi takan yaron ba yaron kuma bai
karamai magana ba, abinci Kausar takawo musu bayan ta gaida Second Dad dan haka suke
kiran Musty tawuce sama.
Wuraren 11 shida Anty Binta sukabar gidan Hajiya tuni ta shige dakinta, tashi Abee yayi yarufe
kofa tareda kashe wutan falon yawuce sama abincin dake gaban dakin Lujain yabida kallo
dahar lokacin ba’a tababa yawuce dakinshi wanka yasakeyi ya chanza kayanshi zuwa pajamas
dark blue, coffee da aka ijiyemai adaki yabude flask din yazuba a mug yadauka ya jingina da
gado tareda kaiwa baki yay sipping, drawer shi yabude yaciro novel din dayake karantawa
yacigaba da karantawa yanashan coffee.
Wuraren 1 tabude idanunta daga wahalallen baccin datayi dudda wutan dakin a kunne amma
wani kalan jiri jiri take gani cikinta namata wani kalan ciwo dabazata iya misiltawa ba sabida
yunwa, rabonta da abinci tun chips da Anty Binta tasa taci dan kadan dasafen nan sai ruwa
kawai data dingasha, kokarin tashi tayi zaune amman jitayi takasa cikinta yamata kaman
gyambo takasa mikewa wani kalan fashewa tayi da kuka ahaka, kofan dakin take kallo da
idanunta da key kofan data ijiye gaban madubi tana tunani yanda zata tashi taje tadauki key
tabude kofa tadauko abincin bakin kofan taci, da duka dan energy daya rage mata tayi yunkurin
tashi wani kalan ciwo da cikinta yamata batasan lokacin data saki wani karaba tafado kasa akife
tafashe da kuka sosai…..
Gently Abee yamaida novel din hannun nashi yarufe yay dan jim yana sauraron yanda take
kuka wanda kaman akunnenshi takeyi, ijiye novel din yayi akan side drawer ahankali ya yaye
bargon daya rufe kafanshi dashi yasauko da kafafun kasa yasaka bedroom slippers sannan
yamike tsaye yana kulle boturan gaban riganshi da kyau ahankali yayi wajen kofa, bude
kofanshi yayi yafita yana tafiya a natse yafito daga corridor ya tsaya gaban dakinta taredakai
hannunshi ya murza handle na kofan jin har lokacin a kulle yasa yay dan jim saikuma yajuya
yakoma dakinshi wani drawer yaja da keys daban daban keciki yadauki wani key yatashi yafito
gaban dakin yazo yasaka key aciki ya murza sannan yabude kofan ya tsaya chak inda yake
batare daya shiga cikin dakin ba, daga ita sai wani dan pink towel data daura kanta babu dan
kwali tana kwance akasa ta kife cikinta da hannunta kekai tana kuka sosai dabaima fita da kyau
tsabagen yanda ta galabaita idanunta akulle, sai hawayen dake fitowa daga cikinsu kana
ganinta kaga wanda yunwa ya mugun galabaitar, juyawa yayi yakoma dakinshi karamin fridge
dake cikin dakinshi yabude wani goran almond milk yadauko yamaida fridge din yarufe yafito
dan tsayawa yayi agaban dakinta kaman wanda ke tunanin shiga ciki saikuma yashiga ciki
ahankali tareda maida kofan dakin yarufe yakarasa zuwa gabanta, gently ya tsugunna tareda
ijiye goran Almond milk din agefe, hannunshi yakai ahankali zai daura akan shoulder dinta
saikuma ya tsaya tareda maida hannunshi yarufe ahankali yana kallon fuskanta yace “Ke”
ahankali take bude idanunta kafin tagama budesu tass tadaurasu kan Abee, jiri take gani sosai
amman dudda haka tagane fuskanshi, kwayan idanunta kadai yakalla da yanda sukeyi yagane
jiri take gani, with a very calm and light tone yace “sit up” girgizama mai kai tayi dawani kalan
sigan shagwaba tana turo pink lips nata, cikin wata kalan murya yar karama tace “carry me” dan
kallonta Abee yayi dasauri kaman wanda baisan abinda taceba, ahankali take kuka tana kara
kama cikinta dake yakushinta sosai tana kallonshi da idanunta dasuka kankance sosai suke
juyawa, gently yazaro hannunshi yamika mata hannun guda daya batare daya tabata ba
alamun tarikeshi ta tashi zaune, hannunshi takalla that is so clean ahankali kaman wata yar
karaman yarinya tadaga dayan free hannunta dabata kama cikinta dashi ba, gently takai
hannun saitin hannunshi dayake bata idanunta na ganin jiri takai hannun awani kalan hankali
tasaka hannunta cikin hannunshi hakan yasa soft tafin hannunta yasauka akan tafin hannunshi
har cikin brain dinshi Abee yaji wani iri hakan yasa ya lumshe idanunshi kafin yabudesu
ahankali yadaura kan cute chubby hand nata dake cikin nashi farcenta farare fat dogaye kaman
tana wankesu da farin fenti, ahankali yadan kama hannun da kyau sannan yajawota tashi zaune
tayi tawani kalan fashe da matsanancin kuka tayi tace “wayyoo cikina ciwo, Uncle zan mutu”
wani kalan mugun kallo yamata baice komiba hannunshi dayan that’s free yamika yabude goran
almond milk din sannan yadauka yajuyo tareda mikamata yace “karba kis……” wani kalan kawo
fuskanta tayi da sauri takama hannunshi hade da goran takai bakinta tanasha dawani kalan
sauri kaman irin yaran dasuka dade basuci abinci ba sunajin extreme yunwa, ahankali yabi
hannunshi data rike gam da kallo tanashan milk din zuwa fuskanta gently yadaura idanunshi
kan goshinta da gashin kanta suka kwanta lub lub wasu kuma sunyi coiling ga kitson da
akamata kanana dasukai bala’in kyau bakin jelan gashin sun soma warwarewa da kansu sosai
sabida santsi, idanunta duka biyun a lumshe sai dogayen gashin idanunta dasuka jike sharkar
da ruwan hawaye, dauke idanunshi yayi daga kallonta saida ta shanye milk din tass sannan
ahankali tasaki hannunshi tana komawa baya ta jinginar da bayanta da gado tana kama cikinta
dataji yawani kalan daure mata fiyedana da tana lashe lips dinta dan almond milk din yamata
dadi bata tabashan irin madaran ba, hannunshi Abee yakalla sannan ya ijiye goran akasa
yakalleta kana ganin yanda take kasan ciwon yakaru ne yace “gobe ma you should starve
yourself” hannayenta duka biyun takai kan fuskanta tafashe da kuka sosai dayasa Abee kawai
ya tsaya yana kallonta yarinyar nan badai shagwaban banza ba, yunkurawa yayi zai mike tsaye
dawani kalan sauri tazo gabanshi kaman zata shige cikin jikinshi dan komawa baya yayi dasauri
kaman wani matsoraci yace “Ke what”? Cikin wani kalan kuka tone tace “har yanzu yunwaaaaa”
dan hararanta yayi yatashi yajuya yafita daga dakin yamaida kofa yarufe tsugunnawa yayi
abakin kofan ya kwashe kulan abincin da flask yawuce yasauka kasa yana tafiya ahankali, bude
kulolin dinning yayi babu wani abinci daya rage hakan yasa gently yajuya yakalli kofan kitchen
dinsu ahankali yabude kitchen din, rabon daya shiga kitchen dinan harya manta ko ranan a
microwave na dinning yadumama abincin yakai mata, dan tsaki kadan yayi yashiga kitchen din
ruwa yasa a kettle sannan yay shiru yana tunanin meya iya dafawa mezai kaimata? Idanunshi
ne suka sauka akan egg, guda two yadauka yafasa saikuma kaman wanda yay tunanin wani
abu yakara two again yafasa yasa pan a wuta da oil juye kwan yayi dayadan soyu yajuya
sannan yakwashe a plate yakashe gas din yataho yahada mata tea mai kauri yasa a tray yadau
bread yafito yawuce sama yana tafiya ahankali, bude kofan dakinta yayi ahankali tana kwance
inda yabarta ganin yashigo da tray da sauri tamike tana zaro idanunta dasuka kankance tana
kallon tray daya shigo dashi, karasowa gabanta yayi ya ijiye tray akasa dawani kalan sauri
tadauki tea zatakai baki dasauri yace “Ke is hot” fashewa tayi da kuka sosai da abin yaso yama
bashi dariya dan girgizakai kawai yayi danbaimasan mezaice ba yace “give it to me” karban
mug din yayi yajuya tea tareda daukan bottle water mai sanyi dayasa akan tray yakara ruwa
kadan aciki sanan yasake juyawa yadauka yabata dasauri takarba takai bakinta tafarasha,
bread yabude yaciro one slice yabata sauke tea tayi daga bakinta da sauri ta ijiye akasa takarbi
bread din, da spoon yadebo fried egg din yadaura mata akan bread din dasauri tai folding nasu
takai bakinta ta gutsura gadai kwan da zafi amman ko gishiri babu a kwan bare Maggi, dan
dago idanunta ahankali tayi takalleshi hada idanu sukayi dasauri ta maida kanta kasa tacigaba
dacin bread din da kwan ahaka sannan tadau tea tasha, bread yakara daukowa yabata zai
samata kwan ta girgixamai kai alamun a’a bari yayi ta karbi bread din taci, kusan 9 slice of
bread ta cin ta shanye tea tass sai alokacin taji ciwon cikin yadaina sosai, half fried egg dake
plate din takalla saikuma tadan kalleshi hada idanu sukayi karaf kai tsaye yace “what” dan zaro
idanu tayi tareda dan turo baki kadan kaman mai tsoron fadin abinda zata fadi murya chan
kasan makoshi tace “you can’t…..cook Uncle” takarashe maganan wani short smile na kubuce
mata abaki dayasa dimples dinta suka wani kalan lotsa duka biyun dawani kalan sauri Abee
yadauke kanshi yashiga hade komi a tray sanan yamike tsaye batare daya kalleta ba yace “is
that your thank you”? Wani kalan sunnar da kanta kasa tayi akunyace tace “thank you” dan
dago kanta tayi jin bataji any motsi ba hada ido sukayi wani mugun kallo yamata dayasa ta
sauke kanta kasa dasauri yajuya yafice daga dakin, sauka yayi yana maimaita abinda tacemai
wai you can’t cook uncle, children of now adays ba basu da at all, kitchen yashiga ya ijiye tray
din harya juya saikuma yajuyo hannunshi yakai ahankali ya gutsuri fried egg din kadan yakai
bakinshi dawani kalan sauri ya tofar sai yanzu yatuna baisa komi a kwanba kawai ya fasa ne ya
soya, wani kalan kunya yaji girgiza kai kawai yayi yawuce yafita daga kitchen din yahayo sama
kallon kofar dakin nata yayi yawuce yashiga dakinshi bayi yashiga dan dauro alwala dan yanzu
lokacin sallan daren shine.
https://chat.whatsapp.com/DinmgBAo43r4mDZSIUvrBb
Exquisite world collections
Muna sai da jakakkuna da takalma masu kyau wanda idan kuka siya ba lallai ku sake ganinsu
wani wuri ba . I assured you. Ku siya ku godemin daga baya domin ingancin kayana. Ina turawa
ko ina kike ni kuma Ina Abuja.
Wannan shine instagram handle dina.
I'm on Instagram as shukhria. Install the app to follow my photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ithkqozo1zuq&utm_content=oeu4f73
08108517010 wannan shine number wayana kuma dashi zaku sameni a whatsapp.
EPISODE 3️⃣4️⃣
Wuraren 6 tabude idanunta ahankali sosai tayi mamakin yanda babu wanda yatasheta yau tashi
zaune tayi ahankali tana taba cikinta dataji baya mata ciwo kuma tamike tsaye ahankali tawuce
bathroom dan dauro alwala ganin small blood yasa tai brush tareda wanka tafito daure dawani
towel daban zama tayi abakin gado tai shiru tana tunani tunawa datayi da wayan Mandawari
yasa tasauka kasa dagudu tana leka karkashin gadon jawo wayan tayi tana dannawa ganin 6
miss calls dinshi dakuma 2 messages from him dasauri tabude messages din.
“Ke kinsan waye ni? Dan kinma samu ina kiranki shine baraki dagamin wayaba dan kina tareda
wannan Baban mijin naki don’t ever call me again”
Wani kalan faduwa gabanta yayi gently tashiga second messege din.
“Wlh idan kika bari yamiki wani abu kokuma kika yaudareni Lujain saina wulakanta miki rayuwa!
You belong to me Muhammad me only!”
Wani kalan faduwa gabanta yayi duk zuciyanta yamata badadi dialing number shi tashigayi
daidai lokacin taji ana shirin bude kofanta dawani kalan sauri ta tura wayan karkashin cinyanta
ta gyara zama tana kallon kofan daidai lokacin Kausar tashigo takalleta tace “Hajiya tace ki
sauko muyi breakfast ki shirya daganan zamuje hadda” juyawa Kausar tayi zata fice dasauri
Lujain tace “Kausar” juyowa Kausar tayi takalleta batare datace komiba, ahankali Lujain tace
“please kibani pad bandashi da maganin ciwon ciki anjima kadan cikina zai fara ciwo” dan
hararanta Kausar tayi saikuma tace “ni banda maganin ciwon ciki dan banayi” tana maganan
tawuce tafita bata wani jimaba tadawo dakin dauke da pad guda biyu masu kyau dan ita kanta
Lujain bata taba ganin irinsu ba bata tayi hannu tasa takarba tana murmushi tace “thank you”
juyawa Kausar tayi zata fice tace “kuma kiyi sauri” tana fita tamike tsaye tareda daukan wayan
taduba gani tayi yama dauki call din but ya katse sake kiranshi tayi tawuce tana shiga bayi
tareda maida kofan tarufe, saida wayan yayi kaman zai katse yadauka kafin tamace wani abu
yace “who do you think you are Lujain sabida kin samu mutum kaman ni na kulaki bakisan I am
doing you a favor bane? Tell me what is good about you? Kene yarinya a sex tape that went
viral online, kene gaki nan kaman zaki fashe, yarinya babu shape babu kyau, anhadaki da tsoho
yanzu still na tsaya akanki nace zan aureki amman harkin kai matsayin ni Mandawari the
biggest footballer in Nigeria na kiranki baki dagamini ba, where were you danake kiranki”? Wasu
kalan hawaye ne sukazo mata sabida yanda yake mata ihu yana masifa sosai kaman zai
daketa daga wayan, jin yanda tai shiru yasa abin yakara tunzurashi yace “Lujain nike miki
magana ni Mandawari kikama shiru kika share? Fine dagayau bani bak……” cikin wani kalan
sauri bakinta har rawa yake tace “da……..dan Allah kayakuri” wani kalan lumshe idanu yayi
yanajin yanda harshenta ke rawa alamun kuka take yarasa what’s so special about this local girl
da Allah yajarabeshi da sonta, idan yatuna yakirata last night bata daukaba saiyaji wani mugun
kishi ya turnikeshi, dan calming muryanshi yayi kadan dan baiso yamata ihu jin tana kuka yace
“kina ina jiya da daddare bayan nagayamiki zan kiraki wajen mijinki kikaje? Meya miki did he
hold your hand? Touch you did he kiss you koko yanzu finally kunyi sex din da akayi accusing
naku dashi ne” dasauri tashiga girgizamai kai kaman yana gabanta tace “a’a” cikin ihu k aman
yasamu yarshi yace “to me yamiki! Tell me” Yanda ya daka mata tsawa saida ta janye wayan
daga kunnenta dan kaman zai fasa mata kunne, maida wayan kunnenta tayi ahankali tace “wlh
babu abinda yamini jiya banida lafiya ne” ahankali yace “are you sure”? Gyadamai kai tayi tace
“eh” dan sassauta muryanshi yayi yace “meya sami baby na what’s wrong with you”? Dan
murmushi tayi jin yanda yakirata da baby ahankali tace “cikina ke ciwo I was so hungry” dan
shiru yayi saikuma chan yace “waike akwai abinda kika sani sama da abinci kuwa aduniyan
nan? Sabida nahana ki kada kici abinci shine zaki bingile da ciwon ciki, hope bakici abincin ba
haka kika kwana”? Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh” dan murmushi yayi yace “good baby,
that’s why I love you” wani kalan murmushi tayi mai dan sauti yace “tom yanzu kije ki nika fruits
kisha idan akwai salad zaki iya ci, daga yanzu salad su yayan ganye da yayan bishiya ne
abincin ki kinji” gyadamai kai tayi tace “tom” ahankali yace “I want to see you today, 4 ne za’a
fara event dina a city conference center zan turamiki address din, makesure you look peng
okay” gyadamai kai tayi saikuma kaman mai tsoron magana tace “mutane zasu ganni suganene
nice ta video” murmushi yamata yace “babu wanda zai ganki you are coming to see me akwai
wanda zaizo yadaukeki yakawoki har private room danake ciki okay” gyadamai kai tayi tace “to”
murmushi yayi yace “now go and have breakfast Mandawari’s baby, I love you Lujain” wani
kalan sanyi taji azuciyanta tadade tana mafarkin rannan da Mandawari zaice mata he loves
jitayi kaman zata zauce, wani kalan murmushi tayi zatai magana taji ya katse wayan fitowa tayi
daga bayin tawuce tadauki wani handbag cikin wayanda Anty Binta tasaya mata tasa wayan
aciki sannan ta shirya tsaf cikin wani Riga da skirt na kanti milk skirt din yawani kalan fito da
katon hips nata, inba kasan Lujain ba kaganta zaka dauka all this yaran nan dasuka kai 24/25
ne sabida yanda takeda girman jiki da gabobi saidai idan tayi magana kokuma ka kalli kwayan
idanunta dan akwaita da zakin murya ga muryan Yar siriruwa, wani milk hijab sabo fil dake
wardobe din tadauko tasaka takoma gaban madubi tana kallon fuskanta wayan hijabin yadan
mata yawa kadan hakan yasa yadan zame baya kana ganin gaban gishinta da farko farkon
kitsonta da hakan yasa tai bala’in kyau, babu abinda tashafa a fuskanta amman tai wani kalan
kyau tai haske sai naman idanunta dasuka danyi ja sabida kukan datayi jiya da daddare
dakuma yanzun nan, turarukanta ta dauka ta feffesa tana murmushi bakaramin dadi sukedashi
ba, wani black flat takalmi ta zura kafafunta aciki dan yatsun kafanta sukai wani kalan kyau aciki
sosai sannan tadauki jakan tafito tana kallon dakin dabata gyaraba dudda bawani datti sauka
tayi kasa Hajiya ne kawai a falo sai Kausar dasu Aneesarh da yaran Ibro da Baban su
yakawosu yanzun nan yafice, ganin Lujain yasa Hajiya tace “zonan Lujain karna karajin kince
barakici abincin agidan nan ba kina jina, ke bakisan kiba rahama bace jibeki kaman asace
agudu kina nema ki lalata kanki dawani rama, Allah shiya hallito sirara shikuma ya hallito masu
kiba to akanme kikeso kice ke ga wanda kikeso? Kada nakarajin kinyi irin abinda kikayi jiya
kinji” gyadama Hajiya kai tayi ahankali kanta akasa tace “baran karaba Hajiya kiyakuri” wani
kalan murmushi Hajiya tayi tace “nayi yanzu jeki debo abincin ki kizo nan kici Hamza zai kaiku
hadda mijin naki yafita ni banmasan inda yaje yau asabar da sassafen nan ba Imran dabai cika
fita weekends ana kiranshi awaya yafice, tafi hado breakfast naki kizo” tashi tayi ahankali
tawuce kitchen babu kowa a kitchen din, blending fruits tayi kaman jiya ta shanye a kitchen din
tana bata fuska sannan tahada tea batasa madara ba ta debi kwai tafito kin zuwa falon tayi
tazauna a dinning ta cinye tass sannan ta tashi takai komi kitchen saida ta wanke sannan tafito
Hajiya tace “tashi Kausar kutafi Hamza na tsakar gida” tashi Kausar da itama ke sanye da hijabi
tayi tadauki jakanta tai gaba Lujain tabita abaya tace “muntafi Hajiya” murmushi Hajiya tayi tace
“adawo lpy” bude kofan tayi ahankali tafita daidai lokacin wani jeep na benz na shigowa cikin
gidan motan tabi da kallo daga ita har Kausar suna sauka daga dakali, parking motan yayi bude
gaba akayi aka fito Abee ne yana sanye da jean da wani t-shirt fari mai v neck daya kamashi
sosai chest dinshi yafito broadly, kafanshi sanye da crocs black, kofan baya yabude ahankali
Gwaggo tasauko daga motan