Showing 42001 words to 45000 words out of 82745 words
shower ne, kasa amfani da
shower tayi, da kyar ta iya bude pampon shikuma ruwan sanyi ne aciki duk yanda zatai tayi
takasa hakan yasa tabude wani sabon towel fari kal data gani abayin tadaura tafito tana tafiya
ahankali tana kalle kalle dakin, bakin gadon taje tazauna ahankali dudda sunce zasu kaita gida
gobe but hakanan taji wani sabon kuka yazomata data tuna auren da aka mata yasa take awan
nan gidan dabatasan kowa ba, babu wani abu dake mata dadi aduniya, bata taba tunanin zatai
aure yanzu ba ita dake ganin zabga zabgan yayunta agida basuyi aure ba, wai itane matan
aure matan wani tayi kukan jin kanta na sarawa yasa ta tsagaita da kukan hakanan tareda
jingina kanta da bangon gado wani kalan gyangyadi ne yafara dibanta har baccin yay nasaran
kwasheta ahaka wuyanta ya bankare.
Ganin Shadaya har darabi yasa Anty Binta takashe kallon tace “zomuje mu duba Amarya saimu
je mu kwanta” kashe wutan falon sukayi sukai sama, sallama sukayi jin shiru yasa Anty Binta
tabude kofan ahankali zaune suka ganta daga ita sai towel babu dan kwali akanta wuyanta Ya
karkace tana bacci awahale Amina tace “laaaaaa” gaban gadon Anty Amina tayi takira sunanta.
“Lujain, Lujain” amman shiru dan ita tanada nauyin bacci idanba itane ta tashi ba saikai da
gaske zaka iya tadata, Anty Binta tace “ko kayan bacci bata sakaba baccin ya kwasheta” Amina
tace “gajiya ne da uban kukan datashi gyaramata kwanciyan kawai” gyaramata kwanciya Anty
Binta tayi hakan yasa tasake sauke ijiyan zuciyan kuka Anty Binta tadan kalleta sanan taja
bargo tarufa mata tareda rage gudun AC dakin sannan takashe wutan dakin sukaja mata kofa
sannan suka wuce dakinka.
“Don’t forget cinta, shanta, lafiyanta, suturanta her well-being is now on you, not any of your
family members ko Hajiya, I know you saisa nake fadin hakan, it doesn’t matter ko kanason
auren ko bakaso anriga an daura, make sure ka kiyaye hakkokin that girl Imran, she’s in that
house because of you, so kaji tsoron Allah and remember Allah na yafe kowani laifi banda
hakkin wani bazanzo kafara this phase at the wrong foot her” dan gajeren tsaki yayi gama
karanta messege din da Musty yatura mai ijiye wayan yayi yana kallon magungunan shi dake
gabanshi kwashesu yayi yaja drawer yazuba su all this while baya sha yanzu ma bazai faraba
duk maganin sa bacci hakan zai taimakamai da migraine but no kusan 12 yakai yana aiki a
desktop nashi komi anatse yakeyi sannan ya kashe komi yamike yawuce gado kwanciya yayi
tareda addu’a yaja bargo dudda bayajin bacci but he’s trying to fall asleep.
Wuraren 3:00 cikin bacci tace “Yunwaa” ahankali tasake cewa “yunwaaaa” jin shiru yasa dakarfi
tace “Gwaggo yunwaaaaaa” jin yanda dakinta ya amsa maganan sabida yanda tai dakarfi yasa
tabude idanunta rasss ganin duhu still adakin babu hasken torchlight na Gwaggo yasa ta tuna
bata gidansu yau, gadon datake kai tashiga tattabawa hartakai karshen gadon bataji alamun
mutum akaiba wani kalan mugun tsorone yasauka akan zuciyanta tunda ta taso tai wayau
yaune rana na farko datake ganinta adaki ita kadai bata kwana da kowaba she’s always with
Gwaggo ga ko’ina tsit babu ko minshari irin na Gwaggo dake fadi wani kalan tsinkewa zuciyanta
yashigayi ko za’a kasheta batasan ina switch yakeba dazata danna taga haske ba balle kuma
waya, tashi tayi lips dinta har rawa suke ta jingina da bangon gado tana kwalalo idanu tana bin
ko’ina da kallo gani tayi kaman akwai wasu abubuwa da yawa kan carpet na dakin hakan yasa
ta kara Gwalalo idanu ganin abubuwan na motsi suna kusada ita yasa tawani kwala uban ihu
tsakar daren nan. “Wayyooo Gwaggooo, Gwaggo kizo akwai aljanu agidan nan wlh gasunan
Gwaggo suna tahowa kusadani, wayyooo Allah na nashiga uku na bani, Aljanuuuu” tai
maganan takai hannunta tadaura akan idanunta ganin kaman kwara daya yahayo kan gadon
nan daidai nan aka bude kofar dakinta tareda kunna wutan dakin hakan yasa haske ya gauraye
dakin, Abee ne tsaye gaban dakin sanye dawata faran jallabiya batare daya rufe boturan
wuyanba da alamu da sauri yafito dan mana iya hango kwantaccen gashin kirjinshi, ganin
yanda take ihu tana kiramusu Gwaggo kaman zata tadamusu da gida sama sabida ihu yasa
yace “Ke!”
EPISODE 1️⃣9️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Har tsakiyan kanta taji tsawan da aka daka mata dayasa lips dinta nawani irin bari tashiga bude
idanunta kadan kadan tana kallon direction din da Abee yake tsaye kafin takarasa bude idanun
rass sai alokacin wani kamshin turare mai bala’in dadi yadaki hancinta, dawani kalan sauri
hartana neman faduwa akasa tai tsalle ta duro daga gadon tai wajen Abee daya dauke kai daga
kallonta dasauri ganin abinda ke jikinta, dan nesa dashi ta tsaya tasaki kuka ahankali takai
hannuwanta duka biyun kan idanunta tace “dan Allah ka kaini gida wajen Gwaggo na nan gidan
akwai Aljanu gasuchan a tsakar dakin yan gajejjeru” tai maganan tana mai pointing da hannu
tsakar dakin sannan tajuya jakunkunan ta guda biyu da Gwaggo ta bada akawomata tagani da
kuloli guda uku na abincin da aka kawomata jiya dan zaro idanu tayi sannan gently tajuyo da
kanta kaman mara gaskiya tadan kalli Abee daidai shima yazubamata nashi idanun wani kalan
cika mata idanu yayi ahankali tasauke kanta kasa dasauri takai hannunta tana goge hawayen
dasuka zubomata babu alamun wasa akan voice nashi yace “those things looks like Aljanu to
you”? Girgizamai kai tayi ahankali tanajin muryanshi har cikin heart dinta, dan tsaki Abee yayi
yajuya zai fita wani kalan fashewa da kuka tayi kaman jira take tabiyoshi da gudunta da sauri
yajuyo jin tabiyoshi da gudu hakan yasa chak ta tsaya chak tasauke kanta akasa tana kuka,
kallo yamata daga sama har kasa kaga idanunshi kaman zai daketa dasu yace “where do you
think you are going”? Kasa magana tayi sai kukan datakeyi strictly yace “wuce ki koma cikin
dakinki” ahankali kaman wacce idan tai magana da kyau zai make tace “I can’t sleep alone”
watsa mata harara yayi yace “amman kin iya zuwa bayin maza alone” dago jajayen rinanun
idanunta tayi takalleshi hada idanu sukayi dasauri daga ita har shi kowa ya kauda kanshi shi
kanshi baisan yama akayi yayi maganan ba he’s just angry so many things acikin zuciyanshi,
cikin dan murya azafafe yace “go back inside” shiga cikin dakin tayi dabaya dabaya takoma ciki
tana kallonshi batare data kulle kofan ba, dan gajeren tsaki yakarayi yakai hannunshi yakama
handle na kofan yajawo zai rufe karaf yaji tarike taleko da kanta ta ragowan space din dayarage
ta kwawkwabe baki takalleshi idanunta sun cika da hawaye tam kaman ana ciremata rai tace
“dan Allah dan Allah karka rufeni wlh tsoro nakeji, idan ka rufe ni zan mutu kaji I can’t sleep
alone pleaseeeee” dan kallon idanubta yayi kadan cikin wani kalan fushi Abee yabude kofan
yashiga dakin da sauri takoma baya ganin yanda yashigo kaman zai daketa, azafafe yace “inda
kinsan you can’t sleep alone dabaki abinda kikayi ba, dabakije bayin maza kin rufe kanki kina
kallon only God knows what ba with phone, ke bakison kwana ke kadai ni do you think I love
this kaddararren auren nan da akamin dake? Do you think I want someone like you as my wife?
Do you think I will ever consider you my wife? Listen and listen well? Dagayau you will sleep
alone and learn how to live and survive anan you did that to yourself not me understood? Kome
kika sami kanki aciki ayau ke kikama kanki, I never wanted you, I didn’t initiate this marraige,
your family did, su suka miki so deal with it understood?” Gyadamai kai tayi dasauri tana hawa
gado dukta daburce ta manne jikin gadon sosai ko’ina najikinta rawa yake sai gyadamai kai take
kaman lizard alamun taji arayuwan nan bayan Baba sai wannan mutumin ne suka taba mata ihu
da tsawa kuma sutafi tsoro yanzuma saitaji kaman tafi tsoron wannan kan Baba dan Baba
kome zaiyi Gwaggo is always there to save her wannan ko babu wanda zaizo, shi kanshi Abee
yanda yaga tanayi kawai saiyaji zuciyanshi ya tsinke tabashi tausayi baimasan mesa he vent
his anger on her is just a mistake dako Kausar dinshi can make so why is he this bitter towards
her? Did she even understand him? Why will he even waste anger nashi akan Yar yarinyar nan
saikace yana fada da babba sa’anshi. Juyawa yayi yafice daga dakin dasauri tareda bangin
kofan dakin kaman jira take sauka tayi daga gadon dasauri ahankali ta zauna akasa kusada
kofan jitayi yunwan ma yabace dataga bala’i, sosai take kuka tanabin dakin da kallo kaman
wani abu zai bayyana tagani haka takeji, maganganun dayamata sai yawo yake mata akai, for
the first time bayan yay maganan sai itama taji mema yakaita tashiga bayin maza? Look abinda
tama kanta yanzu? Wannan wani kalan rayuwa ne tashigo rana daya, idanunta kur har aka kira
sallan farko na asuba tana matsar hawaye tananan awajen ta zauna ta kudundune kanta dan
tiles ne wajen ba carpet ba ga sanyin kasa ga sanyin AC gashi daga ita sai towel wani kalan
wahalallen bacci yay awon gaba da ita.
As usual 4:30 dot Abee yafito, wani ash color jallabiyane yanzu ajikinshi fuskanshi har wani
haske yake na musamman sabida yawan sallan dare yana kamshi mai dadi dakin Hamza
yashiga yatada shi, yashiga na Abdallah, sannan yafito yashiga yatada Kausar kafin yatada
kannenshi su Anty Binta harzaiyi stairs Lujain tafadomai arai yanzu dai da gaske responsibility
yakaru akanshi he can’t believe it abin namai kaman he’s dreaming, juyawa yayi kaman baiso
yataka yawuce zuwa bakin kofanta hannunshi yadaga kaman baiso yayi yakai hannun kan kofa
yay knocking kofar ahankali batare dayay magana ba jin shiru yasa yabude kofan kadan da
fuskanta yafaracin karo dake lilo sabida yanda tai baccin awahale anan kusada kofa bayanta
jingine da bango, idanunshi ne suka sauka kan hannunwanta data kankame jikinta dasu duk
cikin bacci, tsigan jikinta sun tashi yirrr dazai nuna mugun sanyi takeji, almost 30sec yayi yana
kallonta sannan yadaukekai shibaimasan ta yanda zai tasheta ba. “Ke” yafadi ahankali amman
ko gezau batayiba kana ganin baccin kasan bata dade dayinshi ba. “Kee!” Yafadi da karfi dudda
tanada nauyin bacci amman har cikin zuciyanta taji yanda yakirata agigice tafarka tamike tsaye
towel dinta na neman kwancewa dawani kalan mugun sauri Abee yadauke kai tareda juyawa
yace “go and pray” yaja kofan yawuce da sauri dudda uban baccin datakeji but she’s so use to
salla da asuba bayi tashiga tanaso tai wanka still tarasa yanda zatayi jikinta har danko yake
mata gatanan kaman kifi sabida son wanka, brush tayi kawai tayo alwala tafito tana tafiya
ahankali gaban babban wardrobe na bango dake dakin taje tabude ahankali kaya tagani acike
sababbi babu atampa ko daya saidai abayoyi da kayan bacci da kananun kaya sai hijabai wani
milk hijab taciro tasaka tana tunanin to inane gabas aka turo kofan Kausar ce sanye da kayan
bacci na riga da wando batare data shigo ba ta tsaya nan gaban kofan, gaban mirror tanuna
mata tace “nan ne gabas Abee yace nazo na nuna miki” tajuya zata wuce dasauri Lujain tace
“ya ake kunna shower ruwan zafi yazo”? Batare da Kausar tajuyo ta kalleta ba tace “ki murza
wajen zuwa kasa” tana maganan taja kofa tawuce dan hararan kofan Lujain tayi tace “angaya
miki nima inason gidan naku ne dan nama tambayeki shine zaki amsani kaman na rokeki kudi?
Mai halin Ya Abida kawai” tasake hararan kofan Dadduman ta shimfida tahau kai tai salla
saikuma tai shiru bazama ta iya kwatanta abinda takeji ba kaman taita ihu tana kuka takeji
sabida kunci daura kanta tayi akan gadon tana tunani ga yunwa datakeji bana wasa ba yanzu
shikenan barata dinga ganin Gwaggo ba da Gwaggo na nan da yanzu taci abinci, da yanzu
tana mata hira, she’s missing Gwaggo kaman takira sunanta taganta anan wani sabon kuka
yazo mata kawai tahau kuka anan saida tayi takoshi sannan bacci yay awon gaba da ita.
7 daidai Abee ya shigo gidan saida ya gaida Hajiya sannan yataho sama dakinshi yawuce
batare daya kalli daidai da kofar dakinta ba sake wanka yayi yashirya cikin wani black suit na
italian yasa black takalmi sai kamshi yake yafito rikeda wayanshi a hannu harya wuce kofan
dakinta kaman wanda yatuna wani abu yadawo wannan karan bai knocking ba yabude dakin
zaune yaganta kan dadduma sanye da milk hijab tadaura kanta akan gado tana bacci, daganan
kofa yakirata. “Kee!” Firgigit tabude idanunta kaman taji muryan mala’ika mikewa tayi zumbur
hakan yasa towel dinta yay kasa hijabin yawani kama jikinta dayasa zaka iya ganin komi dauke
kai Abee yayi saikawai yajuya yafita batare dayace mata komiba.
Kokarin hawa gado tayi ta kwanta but jin fatar jikinta kaman ma danko danko yake mata yasa
tacire hijabin tawuce bayi, da ruwan sanyin hakanan tai wanka dawani sabon soso da shower
gel datagani abayin mai kamshin dadi sai ihu take tana sauke ajiyan zuciya sabida sanyin
ruwan, daura towel tayi tafito har rawan sanyi takeyi sosai tawuce takashe AC sannan taje
gaban madubi wani cream datagani awajen na QEI tadauka tabude dan shima sabone tashiga
shafawa sabida sanyin ya barta gama shafa man tayi ganin taki daina jin sanyi yasa takoma
bayin tacire towel din ta wurga washing machine datagani abayin tadauko wani towel din
tadaura tafito, zama tayi jin sosai takejin sanyi yasa tasake mikewa tai wajen gadon tashiga
gyarawa sabida tadainajin sanyin daidai tana gama gyaran ana sallama tareda bude kofan
dakin hakan yasa da sauri takalli kofan da kodaddun idanunta dasunsha kuka Anty Samira ne
tace “gyaran gado kikeyi Lujain”? Gyadamata kai Lujain tayi ahankali tace “ina kwana”?
Murmushi sosai Anty Binta tayi tace “muntashi lafiya ya Kwanan sabon waje”? Shiru Lujain
tamata batare dabata amsaba karban bargon hannunta Anty Binta tayi tace “kawo natayaki
ninkewa naga yamiki nauyi kaman ma kin wanka ko”? Gyadamata kai Lujain tayi ahankali, Anty
Binta tace “to je saka kaya duk suna cikin wardobe atampopinki ma yau tela zatazo ta aunaki, yi
maza sa kayan musauka kasa”? Gyadamata kai tayi hankalinta na kara kwantawa wannan
datace su sauka kasa that means zata kaita gida kenan, wardrobe din tabude dogon rigan da
hannunta yafara tabawa tadauka wani nakine amman yanada gold stone dake sparkling, dan
juyawa tayi tadan kalli Anty Sam ganin hankalinta gabaki daya nakan bargon datake gyarawa
akan gado yasa ta dauki cotton pant data gani awajen Babba aka sayo da kananu babban
tadauka tasaka yamata cip tasaka underskirt, sannan tazare towel din ta ijiye tajuyama Anty
Samira baya tadau wani white singlet tasaka daya kamata bam dan ko kadan batason tasaka
bra tadauki rigan tasaka dayawani haskata da kaman dan ita akayi, dan kwalin abayan tadauka
zata yafa dasauri Anty Sam data gama tana kallonta tace “noo kifara gyara gashinki” dan zaro
idanu tayi ahankali tace “ban iyayi ba Gwaggo ke mini” yanda tai maganan saida Anty Binta tai
murmushi ganin yarinyar nada shagwaba komi nata ashagwabe takeyi dan yamabi jikinta tace
“zauna kiga” zama tayi akujeran gaban dressing Anty Binta tacire ribbon din tana kallon tsayin
gashinta sannan tadauki man kitso tashafa mata tareda tsage gaban kan sannan ta tajemata
ahankali tai parking gashin dayawani kwanta tai parking tsaf tana kallon fuskanta tagaban
madubi tace “idanunki sun kode da yawa sa kwalli saimu sauka muyi breakfsat ana jiranmu”
kwallin tadauka tasaka ahankali sai idanun sukai kaman na aljanna gyalen Anty Binta ta karba
tayafa mata aka sannan tace “tashi mujeto” tashi tayi Anty Binta tai gaba tana biyeda ita abaya
suka fice daga dakin sukai stairs kanta akasa, kowa na nan, Hajiya na zaune tasanya wata
atampa blue mai kyau, sai Abee dake zaune kan one sitter dake facing stairs din, sai Kausar na
zaune akasa wajen kafanshi rikeda littafi da byro a hannunta tana rubutu, sai Abdallah yana
zaune kusada Hamza da Ibro duk suna kallon stairs din sai Sajida da Zainab da Maman
Aneesarh duk suna zaune suma tareda matan Ibro ga yara akasa suna zazzaune, kallo daya
tama falon da mutanen ciki tasauke kanta kasa hakanan kawai gabanta nafadi dum dum dum,
ko Anty Binta ta lurada hakan ne kamo hannunta tayi suka karasa sauka kasa har zuwa gaban
Hajiya tace “ga Maman mu nan gabadaya dudda jiya dakika ganta kinata kuka but itane Maman
Mu Hajiya Babba dakanta” dakuwa Hajiya tama Binta tace “kinci gidanku Binta” sannan takalli
Lujain da kanta ke kasa tace “Mun tashi lpy Lujain” Gyadamata kai Lujain tayi ahankali murya
chan kasa tareda dan dukawa kaman yanda take gaida Baba tace “ina kwana Hajiya” murmushi
Hajiya tayi tace “lafiya lau, to har yanzu boyemana fuskan akeyi ne” kara noke fuskanta tayi
kasa, kusada ita Hajiya ta nuna mata tace “zoki zauna to” kasa zama tayi kusada Hajiya
ahankali ta zauna akasa kaman zata fashe da kuka daidai nan Aneesarh dake wasa akasa
tawani rarrafo dagudu zuwa jikinta tana kokarin magana na yara tana kallon fuskan Lujain din
kaman yanda yara keyi irin taga bakuwan fuskan nan sai kowa na dakin ya tsaya yana kallonsu,
ware idanu Lujain tayi for the first time dawani kalan sauri tasa hannunta tadauki Aneesarh
ahankali tace “Fine babyyy” washe baki Aneesarh tayi tana dariya tanajan gyalenta ahankali
gyalen abayan ya zame kasa gashinta da Anty Binta ta gyara mata yawani bayyana for the first
time Lujain tawani saki murmushin dayasa dimples nata duka biyun suka lotsa ganin yanda
Aneesarh keja mata gyale daidai lokacin Abee yadan kallesu.
EPISODE 2️⃣0️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce