Showing 66001 words to 69000 words out of 82745 words

Chapter 23 - Sakon So Book Complete by m Shakur ( By Ubeera ) .pdf

M Shakur   

11 Oct 2025

1624

tana wani kalan washe baki tana gyara dankwalin kanta dake
neman zamiyewa hannunta rike dawata Yar purse da akayita da yadin atampan jikinta takalli
Lujain dake kallonta saikuma ta taba Abee tace “jibin mini sha sha shan yarinyar chan taganni

kuma ta tsaya sangangan kaman gunki tana kallona uwa bata sanni ba” wani kalan murmushi
Lujain tayi jin muryan Gwaggo batasan lokacin data wani kalan kwasa da gudu ba tana zuwa
wajen wani kalan mugun tsalle tayi ta rungume Gwaggo tana wani kalan dariya da bala’in
murna. “Oyoyoooo Gwaggooo na”. EPISODE 3️⃣5️⃣


Exquisite world collections

Muna sai da jakakkuna da takalma masu kyau wanda idan kuka siya ba lallai ku sake ganinsu
wani wuri ba . I assured you. Ku siya ku godemin daga baya domin ingancin kayana. Ina turawa
ko ina kike ni kuma Ina Abuja.

Wannan shine instagram handle dina.

I'm on Instagram as shukhria. Install the app to follow my photos and videos.
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=ithkqozo1zuq&utm_content=oeu4f73

wa.me/+2348108517010 wannan shine number wayana kuma dashi zaku sameni a whatsapp.

Ciro wata Yar katuwan jakan Gwaggo Abee yayi daga motan tareda maida kofan yarufe yadan
saci kallon fuskan Lujain, today is the first time daya fara ganin all set na cute white short teeth
nata duka sabida how happy she is ga dimples dinta dake wani kalan lotsawa kaman ana
operating nasu da remote, ta kankame Gwaggo gamgam tareda lumshe idanu kaman wani zai
kwace mata ita, dan dauke kai yayi tareda gyaran murya hakan yasa Gwaggo dake murna
sosai ta tureta tace “cikani Lulu mun tarema mijinki hanya” sakinta tayi ahankali tana komawa
gefenta batare data kalli Abee ba daidai lokacin Hamza da Kausar sun karaso wajen cikeda
girmamawa Hamza yace “ina kwana Gwaggo” washe baki Gwaggo tayi tace “kaga yaro mai
tarbiya ba irin nawa jikokin ba basu rusunawa idan zasu gaidani” ahankali itama Kausar tadan
rusuna tace “ina kwana Gwaggo” wani kalan washe baki Gwaggo tayi tace “ana ganin kwayar
idanunki anga na Babanki yaya sunanki yammata” ahankali Kausar tace “Kausar sunana”
Gwaggo tace “Masha Allah Kausar ina zaku haka keda Lulu kukaci hijabia kaman matan
limamai” murmushi tadanyi ganin Gwaggo is so lively tace “Hadda zamu” dasauri Lujain
amugun shagwabe tana kara kama hannun Gwaggo tace “Gwaggo ni barani ba” ba Hamza da
Kausar kadai ba har Abee saida yadan kalleta jin yanda tai magana yadauke kai dasauri, irin
Gwaggonta tazo din nan mai taremata, itama Kausar dasauri tadan kalli Abee dasauri taje
wajenshi hannunshi takama kaman zatai kuka tace “Abee dan Allah muhuta gobe saimuje eh
Abee tunda Gwaggo tazo” dasauri Gwaggo tace “da sunana zakuyi amfani kuyi sabon Allah
badaniba” saikuma tadan kalli Abee tace “adan barsu suhuta yau ko Imrana” adan kunyace
yace “to Gwaggo” yana maganan yawuce rikeda jakan Gwaggo a hannunshi Kausar da Lujain
sukahau tsallen dadi Hamza yace “Allah shiryeku” Gwaggo ta tabe baki tace “tayani fadi dan
nan yara kiri kiri suki karatu wanda yafi na yahudun dasuke zuwa amfani, nidai ku kaini cikin
gida” tai maganan tana mikama Kausar Yar purse dinta tace “rikamin naira dubu uku da dari

biyu da hamsin ne aciki dake na yarda nasan baraki cimin ba amman kinga wannan” tanuna
Lujain tace “kuran kudi ce” dariya daga Hamza har Kausar sukayi Lujain ta daure fuska sukai
cikin gida, daga Kausar har Hamza wani kalan dadin ganin Gwaggo sukaji, wani kalan uban
sallama Gwaggo ta rangada afalo Hajiya dake zaune tareda Abee ta amsa tana murmushi tace
“barka da zuwa Gwaggo” cikeda farinciki Gwaggo tace “nasameku lafiya ya Lula incedai bata
tadaku da yunwan dare” wani kalan daure fuska Lujain tayi tasaki Gwaggo tawuce tasami waje
akasa tazauna Gwahho ta kalleta tareda tabe baki tace “too danna fadi gaskiya shine zakiyi
fushi dani aisai kiyi tayi” Gwaggo tai maganan tana zama akan 3 sitter daga Kausar da Hamza
suka zazzauna kusada ita suna kallonta kaman sunga tV, Gwaggo tace “Hajiya kinga wannan
jikan tawa fitinanniyan yarinya ce ga taurin kai da kafiya ina chan gidan dana amman ina
tunanin halin dazata sakamini ku ciki” dan murmushi Hajiya tayi takalli Lujain dake kumbure
kumbure tace “Lujain batada matsala bata taba daminmu ba gaskiya” dan dariya Gwaggo tayi
tace “ai shine nan, bani jakata kagani Hamza” tashi yayi yadauko jakan yakawo gaban Gwaggo
sauka tayi kasan carpet tashiga bude jakan dasauri Lujain dake fushi tazo wajen tace “mekika
kawomini Gwaggo”? Hararanta Gwaggo tayi tace “yanzu kinga daman kulani” Gwaggo tai
maganan tana ciro wani katon kwano data daka lafiyayyen yaji da bushashen nama da kayan
kamshi tace “Hajiya ga yaji dakaina na dakashi kinga wayan nan gantalallun yara su Samira
dazaran sunga zan fara aiki guduwa suke su labe hope ke baki kiwuya” tai maganan tana kallon
Kausar dake kallonta dasauri Kausar ta girgiza mata kai tace “a’a banda kiwuya” baki Hajiya
takama tace “Kausarrrr sannu da aiki” kwashewa da dariya Hamza yayi da Lujain harda
kyalkyacewa Abee yadan saci kallonta yanda take kallon Kausar tana dariyan kasan tsokana
ce, dan girgizakai kawai yayi yakai coffee shi baki yay sipping, Gwaggo cikeda lallashi tace
“karki biyemusu ni ina ganinki nasan baki da kiwuya kin iya shan aduwa da goruba da
magarya”? Dasauri Kausar ta gyada mata kai tace “eh” fito da ledojinsu Gwaggo tayi ga
goruban duk an kankare jiki sunyi kyau tace “zoki debi naki kafin su wayan nan dake miki
dariya” kaman Lujain zatai kuka tace “Gwaggo nifa” daga Abee har Hajiya dawowa yan kallo
sukayi Gwaggo entertaining nasu kawai take agidan ana haka saiga Musty da Harun da Ibro da
Anty Binta sun kawoma Lujain atampopinta da aka gama dinkawa haba dakin kachamewa yayi
wawan goruba ake Musty da Harun harda Yar rige rigen dauka, sosai Musty ke lura da Abee
yanda any magana da Lujain zatayi saiya kalleta kodan sabida bata taba magana da dariya irin
na wanda takeyi yau ba ganin Gwaggo ta oho shi kanshi Musty kallonta kawai yake she’s so
adorable and a very sweet and beautiful girl, he just wish abokinshi zaizo yarinyar nan and open
up his heart da yanzun ne xaisan soyayya.


Dan yatsine fuskanta tayi jin maranta ya murda, tashi tayi ahankali Ibro yace “ina zaki ana hira
mai dadi dake babu wanda yataba jin muryanki agidan nan haka” Musty yace “sai yau da
Gwaggon ta kenan ba” Anty Binta tace “to kishi kuke yarinya da Gwaggonta” Gwaggo tace “ai
tunda aka kawota nan gidan ku nahuta jibi yanda tai haske takara kyau ashe haka kikayi sa’an
zuri’a dan Allah jibi yanda kansu yake ahade kowa nada kirki, babu yanda banyi da ubanta
yakawoni nan nadubata ba yaki kunsan idan yafita sallan asuba baya kara dawowa sainai bacci
sabida karnace yakaini, shinefa na kira Hadi dole nasashi yasaka mini number Imrana awaya ta
nakira Samira tamini saving nasa kiramini shi, kira daya nama dan albarkan nan jiya da

daddaren nan yace shikenan zaizo da safen nan ya daukoni, saiko gashi yazo aike Lulu kinyi
miji” wani kalan kunya taji juyawa tayi tawuce stairs abinta tana tafiya ahankali Gwaggo kuma
takara gyara zama tabude sabon chapter babu wanda baya dariya adakin nan sai Abee da
kawai jinsu yake babu Uhm babu um um, Gwaggo sai zuba take ana dariya a falon harda
hawaye.



Tashi ahankali Abee yayi Gwaggo tace “ina zaka Imrana” anatse yace “abu zan dauko a sama”
dasauri tace “ayyooo tafi to abinka” stairs yayi Gwaggo tabishi da kallo saikuma takalli su Musty
tareda rige murya kaman wacce zatai gulma tace “surukin nawa baida hayaniya kaman ku”
haba mezasuyi banda dariya shi kanshi Abee dake stairs yana jinsu dan murmushi yayi yawuce
abinshi Musty yace “ai Imrana Gwaggo tun muna yara haka yakeda miskilanci akwai shariya da
rashin son magana” Gwaggo dake kallonsu tace “uhmmmm ba shakka” yanda tai maganan
yasa suka kara kwashewa da dariya.



Karasawa sama yayi yana tafiya ahankali harya wuce kofan dakin Lujain saikuma yadawo baya
ahankali ya tsaya chak gaban kofan yana sauraron sautin kukanta dayaji yakai kusan 1min
tsaye awajen saikuma yasaka hannunshi ahankali yatura kofan batare daya shiga cikin dakin
ba, tana tsugunne agaban bathroom na dakin da ledan pad da Kausar tabata a hannunta, dan
dago kanta tayi tadan kalleshi shigowa cikin dakin yayi yana tafiya one one yakarasa inda take
a tsaya akanta ahankali yace “what’s wrong with you”? Gently ta janye hannunta taboye pad din
hannunta abayanta sannan takife kanta akan kafafunta murya chan kasa tace “cikina ke ciwo
sosai” yana kallonta ahankali yace “stand up” girgixamai kai tayi batare data dago kanta ba,
kana ganin yanda take kasan cikin bakaramin ciwo yake mata ba, juyawa yayi yafita daga dakin
yanajin yanda kukanta ke karuwa yafito da wayanshi Anty Binta na zaune a falo suna dariyan
Gwaggo wayanta yashiga ruri ganin Ya Imran ke kiranta yasa dasauri ta mike tsaye tareda daga
wayan takai kunnen tace “Hello Yaya” anatse yace “go and check on that girl” yana maganan
yana katse wayan, dasauri Anty Binta takarasa sama dakin Lujain tawuce datagani abude
ganinta a tsugunne har yanzu takasa tashi tana kuka sosai yasa tai wajenta dasauri tace “Lujain
menene what’s wrong” ganin pad a hannunta yasa tace “Subhanallahi maranki ciwo yakene”?
Gyadamata kai tayi Anty Binta tace “tashi to ki kwanta kafin asayo miki magani” cikin wani kalan
murya tace “kafana yarike ki kiramini Gwaggo na” dasauri Anty Binta tace “haka kafanki ke
rikewa” Gyadamata kai tayi tana kuka, tashi Anty Binta tayi tafita dakin Abee tayi tai knocking
tareda sallama, daga taciki yace “shigo” bude kofan tayi tashiga ahankali yana zaune gaban
desktop dinshi, kusadashi tayi tace “Yaya she’s having MP cramps ne sosai yana rike mata kafa
Ya Imran zaka kaita asibiti ne ko zaka kira Dr yamata prescribing magani asayo?” Batare daya
kalleta ba yace “you can go” juyawa tayi tafita daga dakin batare data kara cewa komiba.
EPISODE 3️⃣6️⃣

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

Fita tayi daidai Gwaggo da Kausar data rike mata hannu na hayowa sama Gwaggo na salati
tana sallallami tace “bani zaku maida kuturwa agidan nan ba, wannan bene haka haba”
karasawa dakin Lujain din tayi atare dukansu ukun suka shiga dakin Gwaggo na ganin Lujain
duke tace “ke kinfara ciwon cikin ne ohhh ni wannan ciwon ciki yaushe zaibar Yar nan, ina
kukasa akwatinan nan nasaka miki maganin aciki, Binta da Kausar kutayani dagota ahankali
kafanta yarike” da Anty Binta da Kausar ne suka dagota da kyar kwantar da ita sukai akan gado
sannan Anty Binta takawo mata akwatinan Lujain din Gwaggo ta aika Kausar takawo ruwa, nan
da nan Gwaggo tajika mata wasu magunguna saida sukai da gaske sannan tasha kadan
Gwaggo tace “kunganta nan banga wanda yakaita laulayin ciwoba tun tana yar yarinyan ta
amman tafi kowa tsanan magani” bacci ne ya kwasheta Gwaggo tamike takalli Kausar dake
kallonta tace “zomuje ki kaini bayi” daga Kausar har Anty Binta dariya sukayi Kausar tanuna
mata kofan bayi tace “ga bayi nan” ahankali Gwaggo takarasa tabude bayin tana kallon komi
naciki saikuma tajuyo takalli Kausar tace “yoo ta ina na iya amfani da kalan wanga bayi kaman
a film” kaman abinda Kausar da Anty Binta ke jira kenan dariya sukayi Kausar tashiga bayi ta
gwadama Gwaggo komi sannan tafito suna duk suka fice yin salla.


Bayan anyi azahar Abee yashigo gidan sama yayi daidai Anty Binta nafitowa daga dakin Lujain
dake bacci kaima Gwaggo abinci ledan magunguna yabata dasauri takarba taredayin murmushi
tace “thank you Ya Imran” wucewa yayi abinshi itakuma tajuya takoma dakin Gwaggo tabama
ledan tace “gashi Gwaggo mijinta yasayo mata magani” wani kalan murmushi Gwaggo tayi tasa
hannu takarba tace “yayanku na kulan mini da jika da kyau Allah dai ya sakamai da alheri, idan
ta tashi dakaina zan kiraki kizo kibata danni ba gane rubutun maganin asibiti nikeba” murmushi
Anty Binta tayi tace “to shikenan” wucewa Anty Binta tayi tafita itakuma Gwaggo tabude kuka ta
debi shinkafa da stew da soyayyun kaji dayawa tana murmushi tace “abinda ba’aci agidan
ubanki kenan sai salla salla inbadai nina soyamiki” sosai taci tai kat tasha ruwa da lemu anan
kasa bacci yay awon gaba da ita.


Vibration yatadata a bacci datakeji kaman a kunnenta bude idanunta tayi ahankali tana dube

dube saikuma chan ta hango waya akarkashin gado nakawo haske yana vibration hannu
Gwaggo tasa tace “waya manta da wayanshi adakin nan gashi sai kira ake” tashi tayi tafice
rikeda wayan dake vibrating bude kofa tayi daidai Abee da dawowanshi kenan daga sallan
la’asar a masallaci yahayo saman ganin Gwaggo yasa ya sunnar da kai kasa ahankali yace “ina
yini Gwaggo” murmushi Gwaggo tamai itadai bakaramin kima da mutuncin shi take ganiba tace
“kaga Imrana bansan ko Binta ko Kausar bane sukabar wayansu ba bacci fa nake naji giririrriii
natashi shine naga waya akarkashin gado anata kira itakuma tana bacci balle nabata takawo
musu gashi katayani basu bari naje nai salla tunda wayan yatadani” ahankali Abee yakarbi
wayan daidai number da akai saving da Mandawari na kira Gwaggo kuma tajuya takoma daki
tareda maida kofa tarufe Abee yadade yana kallon wayan harta katse daidai nan kuma yaga
hoton Mandawari ajikin screensaver, yakai kusan 2min yana tsaye awajen kallon wayan yake
yaji zuciyanshi nawani kalan tafarfasa dayarasa dalilli kafin ahankali yafara tafiya yawuce
dakinshi, Binta IPhone 14 take amfani dashi, kannenshi da yaranahi dukan su 13 pro max
garesu har Kausar Wanan ne kawai 12 agidan nan, yana shiga dakinshi ijiye wayan yayi kan
desk yawuce yafada bayi.



Wuraren 5 tafarka ita kadaine adakin amman tana iyajin muryan Gwaggo anan falon sama tana
zuba sai waka takema jikokin gidan su Aneesarh, gently ta tashi zaune tanajin ciwon cikin
nadawo mata sabo fresh, sauka tayi dagakan gadon ahankali tawuce bayi wanka tayi da ruwa
mai zafi sosai tafito daure da towel shiryawa tayi tsaf tadauki wani simple gown mai spaghetti
hand anytime take period she don’t use to feel comfortable at all takurama rayuwanta yake ba
kadan ba dan batason saka pant naturally, kuma batason zama da kaya, feffesa turaruka tayi
tana kallon kulolin abincin dake dakin amman bakinta baya mata dadi daga kanta tayi tabi dakin
da kallo idanunta ne suka sauka kan agogo 15min after 5, wani kalan zaro idanu tayi tamike
tsaye dasauri tai wajen gado taleka zata ciro wayan da dazu tacire daga jaka ta tura karkashin
gado amman bata gani ba, tashi tayi dasauri taje ta dayan side din gadon tana leka karkashin
gadon amman bata ganiba jin anbudo kofa yasa dasauri ta dago Gwaggo ne, zaro idanu
Gwaggo tayi tace “ke ciwon cikin keneman sakaki shigewa karkashin gado, zokisha magani
mijinki yasayo miki kici abinci” shigowa Anty Binta tayi tace “sannu Lujain kinji Zokisha magani”
girgixakai Lujain tayi tafashe da kuka tace “ni naji sauki basainasha magani ba” Gwaggo tace
“hakafa take sainai da gaske yarinyar nan keshan magani, ballo maganin kigani Binta” ballo
magungunan Anty Binta tayi guda hudu ne tana gani Lujain tawani kalan fashewa da kuka
mikewa tsaye tayi dawani kalan gudu tabude kofan tafita daidai Abee dake waya yazo zai wuce
wani kalan fadawa jikinshi tayi one two three Abee yay tangal tangal, baya Abee yayi kaman zai
fadi saikuma yay sauri yay standing on his feet waya na kunnenshi still yabita da kallo yanda ta
rirrikeshi ta kulle idanunta gam danta dauka fadi zatayi ana hello hello awayan da Abee yake
yakasa cewa komi hakan yasa gently tadago kanta jin hello da akeyi hada idanu sukai da Abee
dake mata wani mugun kallo dawani kalan sauri tafita daga jikinshi takoma baya, Anty Binta da
Gwaggo dasuka fito dasauri Gwaggo tace “yauwa Imrana kaga magani take guduwan mawa
haka hartanacin karo dakai gashi mugun ciwon ciki take” kallon Anty Binta dake rikeda maganin
da ruwa a hannunta yayi babu alamun wasa a muryanshi yace “bata tasha” mikamata Anty

Binta tayi tace “gashi” karba tayi ahankali tana wani kalan shagwababben kuka daga Abee har
Gwaggo da Anty Binta kallonta suke, Anty Binta sai murmushi take dan gown din datasaka
yamata wani kalan kyau shape nata yafito sosai, ruwa tasaka abaki sanan tadau daya zata
saka Abee yace “drink all” gyadamai kai tayi ahankali takara sautin kukan datake Gwagho tace
“aisai kiyi nagode ma Allah da yanzu inada maganin ki” watsa maganin tayi abakinta tana
yunkurin amai Abee yace “don’t you dare” hadiyewa tayi tana batarai tawuce tashige dakin
dasauri Abee yawuce yasauka kasa abinshi, abinci taci badawani yawaba dan bakinta badadi
gabanta sai faduwa yake tarasa ta yanda zata tambayi Gwaggo wayan haka taja bakinta tayi
shiru tun cikin namata ciwo harya daina.
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI


EPISODE 3️⃣7️⃣




Bayan salla isha’i ta tashi daga kan gado tanajin dariyan Gwaggo dan turobaki tayi tarasa
ganekan wajenta Gwaggo tazo ko wajen yan gidan nan tana gama bata tea yanzun nan takara
fita, wanka tawuce tashiga tadade abayin tafito shiryawa tayi tsaf bayan ta shafa mai ta feffesa
body spray tasaka wani rigan bacci orange yana nan kaman t-shirt a iya knees dinta kanta babu
dankwali saitayi kaman wata Cinderella, sake tsugunnawa tayi taleka karkashin gadon tana
kara duba wayan Mandawari but still bata ganiba, wuraren 10:30 Gwaggo tabude kofa tashigo
dakin ganin yanda Lujain take daddaga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login