Showing 57001 words to 60000 words out of 82745 words
nakira Gwaggo na”? Dan
murmushi tayi tace “to dauka kije ki kirata” wani kalan tsalle tayi cikeda farinciki tace “nagode
Mom Aneesarh” daukan wayan tayi da gudu tafita tana saka number Gwaggo data haddace
aciki tai dialing tabude kofan dakinta tashiga daidai wayan na ringing Gwaggo tadauka cikeda
ihu yanda take waya tace “hello” dan murmushi Lujain tayi dayasa hawaye yataru akan
idanunta murya chan kasa tace “Gwaggo” cikeda ihu Gwaggo tace “jama’a muryan Lulu
nakeji”? Gyadamata kai Lujain tayi kaman jira take tawani kalan fashe da kuka itama Gwaggo
fashewa tayi da kuka tace “wlh inda badan Babanki nina haifeshi ba da tuni na tsine mishi, tun
Washegarin ranan da aka kaiki gidan miji naji ina baran iya rayuwa bakiba, ranan kasa bacci
nayi nayi nayi da Babanki yakawoni gidanki yaki da asussuba kafin natashi yake fita baya kara
dawowa sai dare bayan nai bacci, keto ya isa daina kukan hakanan kinji” gyadama Gwaggo kai
tayi ahankali, murya chan kasa tace “Gwaggo dan Allah kizo kitafi dani gida” Gwaggo tace
“namiki alkawari ko ana ha maza ha mata sainazo kafin satin nan yakare nadubaki kinji daina
kukan kinashan maganin dana daddaka miki nasa miki a akwati”? Turobaki tayi ashagwabe
tace “ni baram sha…..” daidai lokacin aka bude kofan dakin Abee ne yana tsaye sanye da
kananun kaya riga da jean sun mishi wani kalan kyau sai kamshi yake ganinshi yasa dasauri
tace “Gwaggo bye bye” takatse wayan dasauri tana zaro idanu, wani kalan kallo yamata tareda
mikamata hannu alamun tabashi wayan, tashi tayi ahankali tazohar gabanshi sannan tabashi
wayan yajuya yafita.
Koda akai magrib Abee zamanshi yayi a masallacin danjin ta’aleem da akeyi kan zamanta kewa
da hakkoki mutane, saida aka gama tass malam yabada daman tambaya daga baya wani
yadaga hannu hakan yasa Malam yace “yi tambayanka” dan sosa gemunshi yayi sannan yakalli
Malam yace “Malam ni sonake nasan hukuncin tsofaffin dake auremana yammatan mu” duka
jama’an masallacin juyowa sukayi suna kallonshi yahade rai banda Abee dake duba littafin
hannunshi, Malam dake kallonshi yace “ban gane tambayanka ba yan samari” dan yatsine
fuska Mandawari yayi yace “yanzu saikaga tsofaffi misali irinku malam na auren mata dakun
haifesu kusan sau biyar mukuma yara mekukeso mu aura me atambayata dabaka ganeba”?
Sai alokacin Abee yadago kanshi dan tambayan sounds so disrespectful to Malam dan Malam
ba karamin mutum bane, shima Mandawari kyar idanunshi akan Abee, yanda yake kallon Abee
yasa Abee ya gyara idanunshi akanshi, gyaran murya da Malam yayi a speaker yasa
Mandawari ya janye idanunshi dagakan Abee dake kallonshi kyar yakalli Malam, Malam yace
“shidai aure na farko Halas ne yan samari, dudda dai bansan mesa kayi irin wannan tambayan
ba dan ba darasin mukeba amman dai abinda nasani shine wacce baraka iya aura ba aduniyan
nan shine wacce take muharamman ka, idan kuma ana maganan Auren yara ne annabin mu
Annabin Tsira Muhammad tsarki yatabba agareshi ya auri Yar yarinya Aisha kuma mu koyi
mukedashi, jama’a atashi sahu” tashi sukayi akai salla ana idarwa Abee yafito dan yanada
business meeting dazaiyi a zoom by 9, harya zo zaishige gida yaji ance “Yallabai” chak Abee ya
tsaya saikuma yajuyo ahankali, Mandawari ne yataho tareda Olusay dayay hanyar gate nasu,
jallabiya ce ajikinshi yakaraso gaban Abee hannu yamikamai yace “kasanni”? Wani kalan kallo
Abee yamai tsaf yaganeshi from the first glance dayamai a mosque, hannu Abee yakawo zai
bashi kaman jira Mandawari yake with so much disrespect and humiliation yajanye hannunshi
yarugume hannunshi a kirji, hannunshi Abee yakalla daya kaimai su gaisa dake nan acikin thing
air ahankali yaja hannunshi ya maida jikinshi yazubama Mandawari idanu, baisan mesaba jiyayi
gabanshi yafadi amman daurewa yayi with so much courage yace “you took something that
belongs to me Mr Imran, kuma na tabbata fada da kananun yara irinmu dazaka iya yara damu
is not ur thing dan haka I come to tell you in peace ka saki babe dina daka daura lokacin da
abin nan yasameku I wasn’t in Nigeria yanzu nadawo I want my woman back I want to marry
her” wani kalan kallo Abee yamai saikuma yay folding hannunshi akirji yana kallonshi,
Mandawari yace “yanzu ma nasameka ne namaka magana out of respect inba hakaba” anatse
Abee yace “mezakayi”? Kallonshi Mandawari yayi yace “I will defame you! I will scatter
everything you’ve ever stood for” dan murmushi Abee yayi iya lips nashi sannan yajuya yawuce
anatse wani abu Mandawari yaji ya tsayamai awuya kaman yabishi ya chakamai wuka sai
yanzu daya tsaya gaban Abee face to face kawai yaji yawani tsaneshi wani kalan mugun kishi
nacinshi dan ko kadan mutumin doesn’t look old gashi he’s so handsome gashi so neat kayan
dayake jikinshi tundaga kan slippers na kafanshi are designers, kamshin dayake koshi dayake
takama yafi kowa using turare baikai Abee kamshi ba, wani kalan dunkule hannu yayi yadaki
iska sannan yajuya yawuce gida, akan benci mai gadi yasami Olusay zaune Olusay na ganinshi
yamike tsaye yace “Man nasanka to be stubborn tun muna yara, but idan kasan kazo anguwan
nan ne to make trouble ni zan tattara nabarmaka gidanka, this man baida any business to do
with you and yet you want to make trouble dashi akan mene ubanme yamaka eh” cikeda ihu
Mandawari na tafarfasa yace “he stole my woman from me abinda Yamin kenan” cikin sauri
Olusay yace “woman din dabaka taba cema kanaso ba or respond to her messages, this is not
good Man, trust me this is not good at all” hannu Olusay yakai zai tabashi wani kalan bugemai
hannu yayi yawuce ciki yana tafarfasa tsayawa Olusay yayi so worried Kodai yakira Mom
yafada mata abinda ke faruwa ne amman yay haka Man will never forgive him, shi yasan Man
always view her message dan shinema yafadamai about Lujain amman baitaba fadamai yana
sonta ba saima wulakanci dakin kula yarinyar, saida wannan sex tape da news na aurenta ya
yada social media shine fa tundaga ranan Mandawari yafara having sleepless night.
***
Falonsu yashiga da sallama chan kasa Musty yagani da Harun sunacin tuwo, Hajiya kadai
yagaida yamusu mugun kallo yawuce sama, Hajiya tace “kudai kuna kokari da wannan abokin
naku” tashi Musty yayi yace “cigaba daci Harun bari najawoshi ya sauko kasa” daidai Abee na
zama gaban desk nashi Musty nashigowa ciki yace “waikai tunda kayi auren nan nakasa gane
kanka” wani mugun kallo Abee yamai yace “I told you Musty, kasanni Musty banson aure let’s
not even go there idan wata ne maybe I can even manage Auren na zauna not Auren little girl
like this da dan karamin yaron saurayinta zai tareni this night yana threatening dina, what is all
this rubbish what kind of mess kuka sani ciki haaa? At this stage some stupid small boy da aka
haifa jiya jiya zaizo yatareni yanamin maganan banza can you imagine”? Yanda Abee ke
magana zakasan he’s really pissed hakan yasa Musty yace “wait Imran I don’t understand me
kake cewa? Waya tareka wani boyfriend kake magana”? Cikin dan ihu kadan Abee yace “her
boyfriend dashine the reason behind abinda yasa taje toilet na maza mana taxauna tana kallon
live video nashi Muhammad Mandawari” shiru Musty yayi yana kallon Abee dan shi dama
dayashigo anguwan dazu Hamza ke fadamai sunyi neighbor wani footballer baima tsaya jin
waye ba sabida Hajiya daketa kwalamai kira, one thing da Abee ya tsana to the core
arayuwanshi is raini ya tsani raini da rashin kunya, dafe kanshi yayi saikuma yadago yace “how
far about the tracking dasu Abdul keyi idan bazamu iyaba zan turama contact dina number a
USA cus I can’t wait for all of this shit to be over narabu da yarinyar nan data shigo rayuwana
tahanani kwanciyan hankali I am tired Musty I am tireddd” yay maganan yana kabar da keys na
motanshi da wayanshi dake kan desk din kasa, dasauri Musty yazo yadafashi trying to calm him
down yace “calm down Imran, fushinka is not good for you and kowa dake tareda kai, calm
down please” dan ajiyan zuciya Abee yasauke ahankali Musty yace “what happen tell me”
kaman Abee bazaiyi magana ba saikuma yafadamai komi shima Musty baci ranshi yayi yace “I
don’t care koshi waye what gave him the gut dazai tare soja yanamai magana anyhow, lemme
go and lock him up wlh sainai uselessing kafafuwan nan nashi na kwallo ” Musty yazo zai wuce
dasauri Abee yarikeshi yace “common mu yarane dazamu biye musu, he’s just a child let him
be please, is not easy karasa abinda kake so cikin dare daya to some extend I understand how
bittered he’s” dasauri Musty yace “her grandmother told me baitaba kulata ba all this childish
crush Lujain kemai” yatsine fuska Abee yayi yace “that’s non of my business, I’ve taken care of
her, nasata a school da babu wanda zai bully nata, nayi securing waec nata and neco I am just
waiting waiting for the whole thing to be over nagaji” yay maganan ahankali, murmushi Musty
yamai yace “ya isa tashi muje falo muci tuwo tare” yatsine fuska Abee yayi yace “baran ci ba”
Musty yace “Allah saikaci” badan yasoba yatashi yabishi suka fita falo tare, sai wajajen 11
sukabar gidan hakan yasa yarufe ko’ina yawuce sama ko dakin da Lujain keciki bai kalla ba.
EPISODE 2️⃣9️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Around 1 tafarka daga bacci sabida mugun yunwan datakeji rabonta dacin abinci tun lunch
dataci a school shima ba sosai ba taci, yanda Mandawari yagaya mata tacika kiba taje tarage
kiba kafin takulashi yadameta tayi alkawarin zata rage kiba, barata dingacin abinci sosai ba,
kulolin abincin da aka kawomata jiya da daddare takalla amman taki zuwa wajen, kife cikinta
tayi ahankali tanajin yanda cikin ke sokanta amman tadaure tana lumshe idanu, ganin yaki
denawa yasa ta tashi tadauki bottle water tabude tasha sosai sannan takara kwanciya tana
shafa cikinta da hannunta dake cizonta cikin wani kalan murya tace “wayyooo cikina wauyooo”
juyi kawai take akan gado sai wajajen 3:00 bacci yay awon gaba da ita, 4:30 Abee yafito, tada
kowa yayi saida yatada Kausar yace “jeki tashi yarinyar nan” gyadamai kai Kausar tayi tawuce
tafita shima Abee yafita yasauka kasa.
Bude kofan dakinta Kausar tayi takarasa gaban gadon tana mamakin yanda koda yaushe tana
daure da towel bubbuga gadon tayi hakan yasa tabude idanunta ahankali Kausar dake kallonta
tace “Abee yace kitashi kiyi salla” tashi tayi ahankali ta zauna itakuma Kausar tawuce tafita
daga dakin, mikewa tayi ahankali tashiga bayi wanka tayo tafito tai salla sannan ta tashi tashiga
saka kaya tana tunanin yau jumma’a zata huta, kayan makarantan ta tasaka batare datasa safa
ko hulaba tafito sai kamshin turarukan data fesa take masu bala’in dadi, gaban dakin Kausar
taje tadade tsaye sannan tabude kofan ahankali tashiga ciki Kausar dake saka dogon Riga
tajuyo dasauri takalleta ta tace “mehaka kika shigo mini daki” girgiza matakai Lujain tayi
saikuma ta taho cikin dakin zuwa gabanta ahankali tace “mesa kika tsaneni baki sona”? Tai
maganan tana kallon fuskan Kausar hararanta Kausar tayi takarasa saka riganta tajuya tadauki
dan kunne tasa ahankali Lujain tace “eh mesa” juyowa Kausar tayi dasauri tace “kinason ki
sani, to sabida ke sunan Babana Abee yabaci aduniya, because of you mahaifina is suffering,
bayan komi laifinki ne, kene kikazo kampanin shi amman ba’a duba hakaba sannan aka kuma
kakabamai Auren ki akanshi sabida mugunta irin naku da yan gidan ku” hawaye ne yazubo
daga idanun Lujain dasauri tasa hannunta ta goge takalli Kausar tace “kinsan mesa naketa son
miki magana sabida ke kadai nagani agidan nan datake nan kaman matsayin yayyuna su Ya
Samira, kin dauka I am happy with all this ne, kaman zan mutu nakeji, nima nagaji nagaji
dakomi” saikuma tafashe da kuka wani iri Kausar taji dan tanada bala’in tausayi dauke kanta
tayi tace “nidai me kikazo mini adaki mekikeso” hannunta Lujain tasa tashare hawayen fuskanta
tass tace “sonake kiduba min recipes na rage kiba awayanki kibani narubuta inaso narage kiba
ne” dan kallonta Kausar tayi ganin yanda take kallonta yasa Kausar tace “kiba halitta ce, haka
Allah ya yiki maisa kikeson wahalar da kanki”? Girgiza kai tayi tace “nidai dan Allah kidubamini
inda inada waya bazanma zo wajenki ba” bala’in tausayi tabama Kausar wayanta tadauka
tashiga google tamata browsing sannan tabata wayan da memo da byro tace “write it down”
zama tayi abakin gadonta tashiga kwafewa da saurinta Kausar duk tana shiryawa tana kallonta
komesa takeson rage kiba oho kuma kiban yamata kyau sosai da chubby kumatunta yanzu idan
tarage kiba tai muni fa oho itadai baruwanta, gama rubutawa tayi tamike tsaye tana ijiyemata
wayan akan gado tai murmushi sosai dayasa Kausar ta tsareta da idanu sabida yanda dimples
dinta ke lotsawa tace “thank you Kausar” sannan tawuce tafita, dakinta takoma tadauko jakanta
da hijab tashiga saukowa lokacin babu kowa a falo jakan ta ijiye akan kujera sannan takalli
kitchen dinsu datagani abude tawuce tashiga ciki Anty Binta datagani tsaye tana aiki yasa tai
murmushi tabi kitchen din da kallo ganin yanda tahadu tace “good morning” murmushi Arty
Binta tayi tace “kin tashi lpy Lujain mekikazo yi a kitchen”? Dasauri tai wajen Anty Binta paper
tanuna mata tace “weight loss smoothie zan hada” kallonta Anty Binta tayi tace “kewayace miki
kirage kiba so kike Gwaggon ki taganki tace bamu baki abinci” murmushi tayi batace komiba
Anty Binta tace “ai shikenan fruits duka na fridge ga blender anan” dasauri tai fridge, celery
tadauko, da green apple, cucumber dakuma ginger tahada tai blending Anty Binta sai kallonta
take one thing datagani is tanada tsafta kaganta zaka dauka bata iya komiba amman ta iya
danta yayyanka abinta tasa a blender ta blending Anty Binta dakanta tabata bottle mai kyau da
straw tajuye aciki tace “Allah bada sa’a nidai banga me zaki rage ba” dan turo baki tayi tace “flat
tummy da fats” dan hararanta Anty Binta tayi tai murmushi takai bittle na baki tazuko tasha taba
tabe baki ko kadan baimata dadi ba amman sabida yanda takeso ta burge Mandawari rufe ido
tayi ta shanye tass sannan tawanke giran da blender dasauran kwanukan wajen Anty Binta tace
“debi chips naki kije dinning kici” girgiza mata kai tayi tace “a’a ni nakoshi” wani kalan kallo Anty
Binta tamata tace “Lujain what’s all this kaman wacce tai wani mafarkin abu yunwa kikeso kifara
hora kanki dashi sokike naje nafadama Ya Imran abinda kikeyi”? Dasauri Lujain ta girgiza kai
tace “to zanci Anty please karki fadama kowa” tai maganan tana daukan plate chips kadan
tadeba tasa kwai ma kadan kaman ba Lujain ba Anty Binta tace “tea fa” girgizamata kai tayi
tace “idan nadawo shi zan sha” a kitchen din tazauna kan kujera taci abincin tass sannan
tawanke plate ta taya Anty Binta kwaso kula tafito dasu falo Hajiya sai murmushi take tana
samata albarka afalo duk akaci abinci banda Abee dabai dawobama yana gym dinshi ita tana
kitchen wajen Anty Binta, Kausar ne tashigo kitchen din tace “Uncle Hamza yace kizo mutafi
yau shizai kaiki school” wanke hannunta tayi tace “Bye Anty” bye Anty Binta tamata tana
murmushi sanan tawuce tafita zama afalo tayi tasa safa da takalmin makaranta sannan tasaka
hijab tagoya jakanta tafita itada Kausar dake daddanna wayanta motan Uncle Hamza suka
shiga, motar mai kyau benz amman ba tinted bace, murmushi yama Lujain yace “Amaryan Ya
Imran” sauke kanta tayi kasa bata sake cewa komiba suka fito, tsaye taga Mandawari a kofar
gidanshi yauma yana sanye da wani rigan jearsay da gajeren wando, hada idanu sukayi ga
mamakinta wani dan karamin murmushi yasakin mata batasan lokacin dataji wani farin ciki ya
lullubeta ba, hannu yadaga mata alamun bye bakaramin mamaki tayi ba noke kanta tayi batare
datamai bye ba, ita suka fara ijiyewa a school sannan yawuce yatafi da Kausar school.
EPISODE 3️⃣0️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Wuraren 11 yay parking motanshi wata crazy Brabus jeep agaban school din, yadan dade aciki
sannan yabude kofa ahankali yafito sanye yake da kayan kwallo farare sun mishi kyau sosai
kitson kanshi ya gyara ya shafa mai sai kyalli suke, zare glasses na idanunshi yayi yakarasa
zuwa wajen security dake gaban gate din suna kallonshi daya daga cikinsu zaro idanu yayi
yace “ohhh my God Mandawari look guys” dasauri sauran securities din suka kara kallonshi
dukansu bashi hannu sukayi dan murmushi yayi daya bayyana hakorin makkan bakinshi daya
daga cikin security yace “Selfie please Mandawari” murmushi yayi yace “yeah sure” daukan
hotuna biyu sukayi yace “it’s okay sauri nake” dasauri sukace “mekazo yi makarantan mu”? Dan
murmushi yayi yace “wajen sister na nazo sako zan bata it’s urgent” security yace “laaa kanada
sister a school din nan wacece what’s her name”? “Lujain Muhammad” daya daga cikinsu yace
“wani class Kodai sabon zuwan nan da aka kawo” dudda baisani ba gyadamusu kai yayi, dayan
yace “let’s go kashiga office kazauna akira maka ita” girgiza musu kai yayi yace “naah zan jirata
anan jikin motana sako kawai zan bata” Babban su yace “jeka kira mishi ita yisauri” murmushi
Mandawari yayi yaciro bandir na yan 1k sababbi fil yabama babban cikinsu sai murna suke
suna godiya yawuce yakoma jikin motanshi ya tsaya tareda folding hannunshi akirji yana kallon
gate din.
Tana zaune a aji cikinta ciwo yake sosai sabida yunwa amman takicin abinci har awurin lunch,
daga bakin aji security ya tsaya