Showing 33001 words to 36000 words out of 82745 words
matse hawaye tana kallonta takasa lallashinta
tace “Kola harda cewa wai zaiyi Iskanci dani ya siyamini shawarma guda biyar da Fanta goma
sabida nine mayyan abinci dazan iya iskanci idan zaa bani abinda zanci, wlh banyi komiba
Gwaggo ni danasani da banmaje excursion dinba dan dama banso zuwaba” yanda take kuka
yasa Gwaggo tahau matsar kwalla tace “Allah kaimu gobe wlh wlh har ajinku zanje sainayi
dambe da gantalallun yaran nan masu tallan bushahhsen gero, shegun yara wayanda ba’a
haifesu ranan juma’a ba, ai gasunan sune zasusha kunya tunda Imrana ai yanzu mijinki ne” duk
wani kuka da Lujain keyi tsayawa yayi ta kalli Gwaggo da rinannun idanunta tana zarosu tama
kasa tambayan komi wani kalan washe baki Gwaggo tayi ganin tana kallonta tace “ai wlh kinyi
goshi Lujain dakika sami miji irinshi ga kudi, ga kyau gakuma hankali jibi girman kampaninshi
barima kiga” Gwaggo ta tashi da sauri tayi falo ta kwaso mata kwalin giro dana sweet din tace
“kinga goro da sweet na daurin aure, jiya da daddare kina bacci aka daura gaban kawunanki da
duka dangin su Imranan anan falon babanki bakiga idanun Maman su Samira ba kaman zasu
fado kasa sabida bakin ciki taga Allah yabaki mai kudi daga sama ita dake cewa barama kisami
mai aurenki ba balle mai kudi yanzu ai gashinan ke kinyi miji nata zankadaddun yaran dabata
basu abinci suci su koshi sabida karsuyi kiba na nan agabanta” Gwaggo takara washe baki tace
“dazaran kin tare da yan kwana biyu nima zan tattaro yinawa inawane nadawo gidan naku ina
zan iya zama gidan talaucin nan ubanki na fama da saida atampopi akasuwa too wlh badani ba”
wani kalan mugun kuka Lujain tasaki tace “Gwaggo ninace muku ina sonshi ne dazan aureshi
dazu nadauka tsoratasu kawai kikayi akanme zaki auramin mutumin dabanma san kamannin
shiba? Mandawari na fa”? Wani mugun harara Gwaggo tamata tana tabe baki tace “kina ganin
yanzu da wannan video naku ya zagaye yanar gizo mandawari zai yarda ya aureki idan ma ya
kulankin kenan? Yau shekara nawa kina bibiyan yaron dabaimasan da zaman ki adoron kasan
nan ba” cikin kuka tace “eh nidai shinake so, ai dama celebrity basa amsa messages da wuri,
kinsan followers nashi nawa ne almost 400million global followers, baruwanki da ni da
Mandawari, wlh wlh banason Auren nan nibaran aureshi ba” dan dariya Gwaggo tayi tace “aure
kuma tuni ya dauru yarinya naki wasane, bakida hankali yanzu lamarin nan na manya ne
kimana shiru kawai ki kalli ikon Allah” wani kalan kukan datake yasa taji cikinta na hantsinewa
ta tashi da gudu tana kukan sai bayi Gwaggo tabita duka shayin datasha amayo dashi tayi
tadasa uban kuka tun Gwaggo na lallashi ta tana bata baki harta shareta ta kwanta akan gado
abinta tai bacci itama daga baya anan kasa baccin yay awon gaba da ita.
Koda Gwaggo ta idar da sallan asuba da jan charbinta tashi tayi tafito falo tareda bude kofa ta
taho bangaren su Mama bude kofa tayi uwa an biyota tazauna akan kujera daidai Mama tafito
daga dakinta ganin Gwaggo taso tafirgita saikuma tace “lafiya Gwaggo da asuban nan” kallon
banza tamata tace “lafiyan ce takawo haka” tabe baki Mama tayi tawuce tashiga kitchen abinta
bata wani jima afalon ba saiga Babatareda Yayansu kafinma ya gaisheta hannu tamikamai tace
“bani kudin sadakinta” dan kallonta yayi da mamaki yace “Gwaggo dama zan cika kudi ne
namata kayan daki” cikeda daga murya tace “bakaji ance yanzu anan gidansu zasu zauna ba
baa gama gidanshi ba lokacin daya gama gidanshi anemo wani kudin amata kayan daki” zama
kawai Baba yayi yana kallon mahaifiyar tashi ganin haka yasa tace “ko baraka bani bane”?
Ahankali yace “zan baki mana Gwaggo amman mezakiyi dahar dubu dari biyu gabadaya”
cikeda ihu tace “yoo gyaran Amarya mana dudda ma babu wani lokaci mai tsawo yau kwana
hudu yarage atafi da ita gidan mijinta amman dai abinda zanyi kenan” Mama dake tsaye cikin
kitchen tanajinsu ahankali tace “fitinanniyan tsohuwa inama tamutu ahuta” kallon Yayan su
Samira Baba yayi yace “jeka kawo kudaden nan adakina Auwal” tashi Auwal yayi yawuce dakin
Baba baijimaba yafito da bandir na yan 1k guda biyu yakawoma Gwaggo yage takardan guda
tayi sannan takalli Auwal din tace “kaine Babban jikana kaito ga dubu biyu sadaka kasama
Auren kanwarka albarka” gudun fitina yasa yasa hannu yakarba yace “Allah basu zaman lpy”
kwalama su Samira kira tayi tace “nasan kuna jina to kuzo nan” kaman munafukai suka fito
suka gaida Baba da Gwaggo dake kallonsu tace “nasan kunsan kaddaran daya fada kan
kanwarku Lujain, koma baku sani nasan farfesan uwar ku tariga ta fesa muku labarin daga
tushe zuwa iri to yanzu dai Alhamdulillah Allah yabata miji nagari son kowa kin wanda yarasa
da ake cewa bazata taba samin wanda zai sotaba da wannan kiban babu kalan gorin da baku
mata ba to yanzu dai ga sa’an datayi dan haka nan sadakin tane zan muku sadakan dubu dai
dai duk ku sanya mata albarka” dubu dai dai tazaro tabasu amsa sukayi kowannensu yace
“Allah sanya alheri” tace Ameen, sannan takalli Baba tace “kake kallona kokaima nabaka ne”
girgixamata kai yayi tace “bari naje namata abincin kari zan fita anjima, da daddare tarinka amai
inhar naji jikinta da zafi zaka kaita asibiti” Gwaggo na maganan tana daga zaninta tana tura
kudaden a cikin lalita tawuce tafita tana kaiwa dakin akan dadduma taga Lujain din tai salla
takifa kanta akafa tana kuka hararanta Gwaggo tayi tace “aisaikiyi” kitchen tashiga tahau
dumamata shinkafan jin kukan kuma taji takasa daurewa fitowa yayi tashiga uwardakan zama
tayi agabanta tabuga tagumi tana kallonta tace “wai Lujain saikin kasheni tatas kinga bana
numfashi zakiji dadi iyye? Yanzu mikikeso fadamin”? Ahankali batare data da go kanta daga
kafanta ba tace “ni banason Auren nan ban isa aure ba kumani Mandawari nikeso” shiru
Gwaggo tayi tana kallonta saikuma tace “kikace baki isa aure ba inace nannan Aisha har ajinku
ta Islamiyya dake shekaru sha shidda tai aure har anko saida kika tasani agaba namata, su
Zainab ma dake sha bakwai ba suna zana jarabawan gama sakandire aka musu aure ba kema
inda rashin lafiya yabarki kinfara makaranta da wuri da yanzu kin tsufa da gama sakandire,
kawayenki kadai yan layin nan dasukai aure sunkai hudu yanzu da akazo kanki ne zakice baki
isa aureba, shikuma Mandawarin yasan ki? Yasan dake? Yamasan sunanki? Ke yarnan ki kiyayi
kanki da auran calamburuti ina gayamiki barinma Mandawarin nan mai kamada shaidanu har
kitso yakema gashin kanshi” sosai take kuka still bata dago kanta ba tace “wlh shiba shaidani
bane Gwaggo yanada kirki, yana bada taimako har gidan marayu yake zuwa, yarabama
guraguma keke” Haba Gwaggo takama tace “to akace miki shi kadaine mai kirkin duniya” tai
maganan tanajan hanci jin kauri natashi tace “nashigesu wannan yarinya tasa na babbaka
abinci” tai maganan tana fita daga kitchen da sauri kashe rishon tayi dan arisho take girki
tadawo zama tayi kusada Lujain din ahankali tadagota tace “haba Yar jikata Yar lukutata Yar
bulbul Yar kyakkyawa yimin murmushi ingani” ashagwabe hawaye na gangarowa daga idanubta
tamakema Gwaggo kafada irin baratayiba, washe baki Gwaggo tayi tace “naji to zan miki
abinda kikeso” dasauri tace “zaki raba Auren ki nema mini Mandawari”? Gyadamata kai
Gwaggo tayi wani kalan murmushi tayi dayasa dimples dinta suka lotsa tai bala’in kyau tawani
rungume Gwaggo Gwaggo na dariya tace “to jekiyi wanka nima fita zanyi amman bari nafara
hada abincin ki” tashi tayi tawuce bayi tsaf Gwaggo tahada mata abincin kari da shayi wani
green towel ta daura tazo ta zauna tafaraci Gwaggo tadauki mayafi tace “tonatafi kiyi zamanki
adaki kada kije konan da chan kinji” gyadama Gwaggo kai tayi.
Tun safen nan sai wuraren 4 na yamma Gwaggo ta dawo da buhu buhu na itace da saiwowi
saikuma zabi kaji da tantabaru da aka hadesu aka kullemusu kafafu, wasu yara takira tasa suka
yanka mata aka gyara tafito dasu karfi da yaji sukazo suna aiki Gwaggo tun tana yarinya tayi
gadon iya hada magunguna lafiyayyun tsumi tayi anan tsakar gida akan ittace daya hada da
zuma da mazankwaila babu suga ko digi, sai farfesun su zabin datayi na magungunan hada su
Samira tayi da Lujain din duk sukaci sannan tashiga hada farfesun jijjibi wasu magunguna kuma
ta shanyasu, sai wajajen shadaya suka gama komi su Samira suka koma dakinsu itada Lujain
suka koma dakinsu tsumi tazuba cikin kofi tabama Lujain tasha sannan tahada mata wani
ruwan zafin wasu itace data dafa, Lujain dake zaune tana kallon cartoon a falo tanashan tsumin
kadan kadan tace “Gwaggo wai magungunan menene” batare da Gwaggo takalleta ba tana
saka farfesun daban daban datayi dasuka jera a robobi a dankareren freezer ta tace “shawara
tamiki yawa baki gankiba Saura kadan kizama zabiya tsabagen haskenki” yatsine fuska tayi
tana gyara daurin towel dake jikinta tun Gwaggo namata mitan tawul harta barta dan bata taba
ganin mutumin daya tsani kayaba irin Lujain.
Gwaggo bata kara mata maganan auren ba sai uban magungunan datake loda mata na safe
daban na rana daban na dare daban, ita dakeson yogurt saida Gwaggo tasa tasani yogurt
sabida yanda take zubamata garin magana a yogurt din daban daban.
****
Yau Friday tun ranan Monday bayan an daura auren nan dasuna shigowa gidan Abee yawuce
dakinshi dagudu rabon kowa dayaganshi ko masallaci baya fita, Ya kulle dakinshi baya karban
abinci yanda za’a kawo abinci a ijiye gaban dakin haka zaa dawo adauka, shigowa gidan Musty
yayi afalo ya zauna yana kallon yanda Hajiya dakowa yay jugum ahankali yace “har yanzu bai
fitoba Hajiya”? Wani kalan ijiyan zuciya Hajiya ta sauke tace “ai inhar ciwon nan yatashi
saikuma yanda tayu, har yanzu likitan nashi”? Ahankali Musty yace “gashinan zuwa Ibraheem
yadaukoshi daga airport” shiru dakin yasakeyi babu wanda keda walwala Kausar da Abdallah
yakalla sun bashi tausayi yauma basuje makaranta ba, jin karan gate yasa Musty yaleka yace
“Alhamdulillah gasunan” Dr na shigowa falon baima tsaya gaidasu ba yace “give me his room
key” ciro key Hajiya tayi daga Yar purse na hannunta yawuce sama kowa na zaune akasa,
kusan 30min yayi aciki sannan yasauko kowa tashi tsaye yayi yana jiran abinda zaice dan
murmushi Dr yayi yace “ku kwantar da hankalinku he is fine” ajiyan zuciya kowa yayi, Mustafa
dake kallonshi yace “Dr maisa yake kulle kanshi yaki fitowa duk yanda Imran yakaiga son
bautan Allah jam’i baya wuceshi zakaga hatta masallacin baya fita yaje, yaranshi dayakeso
baya yarda yagansu baya ganin kowa, why is it like that”? Ahankali Dr yace “kasan patient
nawa aka rasa to PTSD post traumatic stress disorder? I applaud Imran bakaramin jarumi bane
mai kwazoba he’s fighting it with all of his strength, PTSD nakama mutum ne Idan mutum yay
experiencing a shocking event, mutuwan matarshi, yanda akai hanging nata sun harbeta a
goshi, aka kashe yaranshi in cold blood shine abinda yasa PTSD yakamashi, symptoms nashi
shine magrine, da mutum ya tsani kanshi yayita bama kanshi laifi akan abinda yafaru, mutum
yay isolating kanshi daga mutane kaman yanda yake yanzu dasauransu irinsu rashin yawanyin
magana, gashinan gashinan ne, for 13yrs I’ve been managing him da little medication su Anti
depression dakuma psychotherapy, yana zuwa har office dina he talks to me I talk him out of all
the guilt the experience dakomi dayake feeling, for a long time now kusan shekara daya kenan
baitasomai ba sai ranan Monday din nan shima sabida wannan dan he’s traumatized sabida
kazafin da akamai aka kuma yada aduniya yanar gizo, saikuma this sudden Marraige, Auren
nan dan gani yake he’s betraying his late wife, yanzu dai I assure you komi yazo karahe, Hajiya
inason kije kiyi magana dashi but before then dukku zazzauna inason magana daku gabaki
daya” zama dukansu sukayi shima Doctor yazauna yace “all abinda patient na PTSD ke bukata
is love and support from close family nasu and friend, ku nunamai kuna sonshi he means a lot
to you, sannan kununamai ku bama kusan yana ciwo ba koyanada wani ciwoba duk randa
yabude kofan nan dakanshi yafito kuyi mu’amala dashi kaman bakumasan yashiga daki ya kulle
kanshi na kusan kwana biyarba baci basha kungane”? Dasauri kowa yace “eh” Dr yace “sannan
karkumai kuka, don’t show him pity rather show them love, idan yaga kuna nunamai pity
kunamai kuka zaiyi worsen condition nashine dan he will feel yana causing muku pain, karku
nunamai kowani abu instaed ma zai iya idan yafito kuce mai babu kaza kaza kaza agida, Abee
inada assignment kaza kaza kungane engage him in something life moves on” yakalli Hajiya
yace “idan kinje dakin nan ba danki mai lafiya ke magana ba, ba Imran dinki zakigani ba, this
one is Imran mara lafiya, PTSD mess with brain Hajiya, so no matter mezaiyi don’t show
weakness kokuma kiyi kuka agabanshi, as his mother handle him kaman jariri tell me
kinasonshi he’s your everything, sannan idan kin shiga dakin daidai da hasken screen na
wayanki kada kisake ki kunna bayason haske bayason hayaniya bayason kuka at this time cus
all of that nakara tunamai da traumatic experience na lokacin memory nadawo mishi fresh, idan
tadade adakin ku aikamata da abinci kar wanda yashiga dakin abakin kofa zaku ajiye kutafi,
babu abinci acikinshi sannan he’s dehydrated, ga weakness kungane” atare duk sukace to,
Hajiya share hawayen fuskanta tayi tass sannan tawuce sama, Dr yabi kowa na dakin dasukai
jugum da kallo yace “he is fine nan da 24hrs that’s idan yamakai kenan ya warware” yay
maganan yana bama Ibraheem prescription sheet yace “he needs this drugs now kuje kusayo”
tashi Musty yayi yakarbi takardan a hannun Ibro yace “bari naje nasayo kai Ibro drop Dr at
home tunda ba mota a hannunshi” suka fita tare.
EPISODE 1️⃣5️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Ahankali Hajiya tabude kofan dakin tashiga ciki tareda maida kofan dakin tarufe dakin duhu
kaman tsakiyan dare bata ganin komi amman haka ta lallaba takarasa da tattaba bango
harzuwa wajen gadon tazauna abakin gadon ahakali, dan ijiyan zuciya tasauke tana gyara
numfashinta ahankali tana saita kanta, murya chan tace “Imrana Hajiya ce, your Mom” dan
murmushi tayi, tace “natuna ranan da aka faracewa ina dauke dakai acikin cikina I was so so
soo happy, tun aciki ka kasance yaro mai hakuri wanda baida damuwa ko kadan, cikin duka
yaran dana haifa aduniya dudda kaine dan fari kai kadaine banma mugun laulayi ba sannan
nakudan kama haka kasan me mahaifinka ke yawan kiranka dashi”? Tadanyi murmushi tace
“dan baiwa” dan dariya tace “kuma bantaba karyata sunan ba sabida hakika kai dan baiwa ne,
you are a God gift, muna tsananin talauci amman muna haihuwanka Allah yafara budama
Babanka kofofin samu, tun kana dan yaro kankani 10yrs ka sauke Al Qur’ani mai girma, kana
zana JSSCE kaci, WAEC da Jamb duka sau daya kayi kaci, kana applying zama soja sau daya
kasamu, bayan kai quitting kanasa hannunka a sana’a Allah yadafa maka kalli company daka
gina ayau in just how many years, kampanin ka shine number one a Nigeria dana Africa gabaki
daya, kuma kampanin yay suna aduka duniya gabaki daya, imagine kampanin ka nacikin top
ceramic company da Forbes sukai publishing, idan kai ba dan baiwa bane kai menene Imran?
You are my son Imrana, abin alfaharina, sanyin idaniyata, yarona mai kyakkyawan zuciya,
yarona mai taimako, yarona mai jama’a, yaron na yaron Hajiya Sadiy…….” Ahankali taji saukan
kanshi akan kafafunta yakama duka hannayenta biyu hannunshi narawa sosai yakaisu zuwa
fuskanshi ya kankame muryachanchan kasakasa dan itama Hajiya dabadan ta natsu ba da
barataji ba yace “Hajiya” ahankali itama kaman yanda yay magana tace “Imrana” bakinshi da
lips dinshi da duka jikinshi bari suke duka cikin wani kalan murya yace “Hajiya I am scared hold
me” wani kalan kankameshi tayi yakifa fuskanshi akan cikinta kaman dan yaro jikinshi nawani
kalan bari, ahankali tace “shi shiiii I am here now don’t be scared yarona, Mamanka na nan”
wani kalan jiniya taji yafara daya tahoda kuka sosai tunda Hajiya take tana ganin tun bayan da
Inrana yay girma yaune nabiyu datake ganin kukanshi da rasuwan Muna shima hawaye ne
kawai sai yau yaukuma kukane jitayi zuciyanta na breaking babban mutum ke kuka haka
Innalillahi wa innailaihi raji’un, cikin kuka yace “Hajiya they killed her sannan suka dauketa sukai
hanging nata da igiya a fanka kirjinta na fitarda jini from harbin bindiga, kalli hannuwa Hajiya
gabaki daya duk jini Muna da nasu Abdul ne kingani” cikin kukan yadaga hannayenshi yana
nuna mata acikin duhun dakin, gyadamai kai tayi ahankali tace “nagani Imrana Allah zai saka
maka kaji, daina kuka kada su rainamin kai, kanuna musu kai jarumine jarumina kaji” wani kalan
ajiyan zuciya yake saukewa yana shesheka, ilimi education ma yayi ne arayuwa dan idan wasu
sukaga irin abin nan da Abee yake cewa zasuyi kodai Ya haukace kokuma aljanu ne nanko is a
medical condition call PTSD, zaro hannunta Hajiya tayi tasaka cikin suman kanshi tana shafa
kanshi ahankali tace “ya isa hakan nan duk wanda ke neman ganin bayanka Allah bazai barsu
ba kuma kasan mene duk wanda aka kashe dan aljanna ne so be happy, I love you so much
Imran, nasan cewa bansha gayamaka hakaba sabida bakada magana sosai bakada hira dani,
kuma I use to feel ka girma kai babba ne ga manyan yara what’s the point of telling you ina
sonka, but I love you deeply Imrana, ina bala’in kaunar ka dako sauro banson yatabamini kai,
kome zai sameka gwara yasameni burina kullum inganka lafiyanka kalau, I want you to fight
Imran, fight this thing for me ni mahaifiyar ka, for kannenka, for yaranka Abdallah da Kausar,
fight for your family, fight for your friends and love ones, tell yourself I am fine! I am okay lafiyata
kalau, you are