Showing 15001 words to 18000 words out of 82745 words
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
Baki gayen dake video yakama daga waje yana kallon yanda kofan ke jijjiga kaman ana wani
abu jin muryan yarinyan na nishi, jin mutane na zuwa wajen dasauri yaciro wayanshi daga cikin
bayin yawuce abinshi yana maida wayan aljihu yama ma’aikatan dazasu wuce maganan yace
“sannun ku” yawuce suka wuce corridor abinsu yalabe wani lungu dan yaga fitowarsu.
Ganin yanda take ihu ta kulle idanunta gam da bakinta gashi takare kofan gabaki dayanta da
kibanta balle yama fice abinshi yasa cikeda daka tsawa yace “Ke!” Har cikin kwakwalwanta taji
tsawan daya daka mata hakan yasa tarufe bakinta gum sannan tafara bude idanunta kadan
kadan ta makale jikin kofan kaman zata manne awajen zuciyanta na bugu ba kakkautawa
tasauke idanunta ahankali kan fuskan Abee, ganin yanda tayi kaman tana shirin sakin fitsari
yasa yace “open the door kifita” bakinta har rawa yake sosai danta bala’in tsorace tace
“ban…….ban…..iy……iyaba” ganin dukta tsorace kawai ta manne kyam akofan yasa anatse
yace “step away” gyadamai kai tayi sannan tamatsa ahankali bude kofan yayi fuska adaure
batare daya kalli fuskanta ba yace “out” da bala’in sauri tafice daga bayin jakanta da chocholate
da wayanta dake kife akasan bayin yakalla hartasa hannu zata bude kofan bayin tafita yasake
dakamata tsawa yace “kee!” Juyowa tayi azabure suna hada ido tasauke idanunta kasa jikinta
yadauki bari takasa koda daga kafa tai tafiya ball yayi da jakanta daga cikin bayin tareda wayan
duka ko ajikinshi dasauri ta tsugunna tadauki jakan tadauki wayan ta jefa cikin jakan ta mike
batamasan halin da wayan keciki ba kawai jikinta bari yake fitowa tayi tana waige waige bama
tasan ta ina tabiyo tazo wajen ba sai gyara riganta take tafara tafiya tafita daga corridor hanyan
bayin wasu ma’aikata ne su biyu mace da namiji suka ganta sukace “what are you doing here
student”? Tsuri tayi bamatasan mezatace ba macen dake kallonta tai dariya tace “hala ta bace
ne, come” kaman jira take dasauri tai wajen macen murmushi tamata ganin duk ta tsorace tace
“don’t be scared kowa da kikagani awajen nan ranan farkon zuwanshi saiya bace acikin
company nan, just take that stairs zai kaiki direct kasa though naga Mr Hamza na shirin tafiya
daku Factory” Gyadamata kai tayi zata wuce matan tace “what’s your name”? Juyowa Lujain
tayi takalleta saikuma tanuna kanta ahankali tace “ni”? Gyadamata kai tayi ahankali tace
“Lujain” murmushi matan tace “you have a very very beautiful eyes” Gyadamata kai tayi tajuya
da sauri sauri tai stairs mutumin yace “kedai Kiyawa kinada son mutane” murmushi tayi tace
“she just reminded me of myself danake yarinya haka nataso inada kiba sosai but kasan
banbancin mu?” Da sauri ya girgiza mata kai suka cigaba da tafiya tace “she’s so beautiful
nikuma I was fat and ugly” dariya sukayi yace “common don’t say that wlh kinada kyau sosai ke
kinganki ne” murmushi tayi tace “yanzu danai girma ne nakuma dakaina nai kyau, amman this
girl nada kyau kam sosai Masha Allah kaman ka saceta” murmushi yayi yace “ni duk idanunta
sukafi burgeni” dariya dukansu sukayi suka shige office nasu.
Tana kaiwa Anty su tace “ina kikaje? Anje bayi ba’a ganki ba”? Kaman zatai kuka tana haki tace
“I got lost dazani bayin sainaje na sama” mugun kallo teacher su tamata ba’a kara cemata
komiba suka wuce factory din, sun zagaya factory tass bata taba sanin haka ake kera plate din
tangaran dasukecin abinci ba sai yau, aka nuna musu tana daga cikin wayanda ma aka zaba tai
practicing tayi plate aka bata kyautanshi daganan suka tafi show room kaman ta kwashe komi
takaima Gwaggo takeji sai wajajen 1 sukabar wajen saida taga sun fita sannan hankalinta ya
kwanta, abakin layinsu school bus yasauketa.
*****
Tsayawa yayi abayin yabi kasan bayin da kallo yanda chocolate suke akasan wait ma what in
the first place takeyi a Gent’s restroom?? Dan tsaki yayi daidai Ibro dayasake kira kan yazo bayi
direct yakawomai key yashigo ganin Yayanshi dayayi acikin bayi tsaye ga chocolate akasa yana
kallo yasa yakarasa gaban bayin da sauri yace “lpy Yaya Imran” juyowa yayi yakalleshi dasauri
Ibro yazaro ido yace “what happen to kayanka Ya Imran”? Hannunshi kawai Abee yasa ya
karbe key office nashi dake kan hannun Ibro batare daya amsashi ba yawuce yafita daga bayin
yay kofa harya bude batare daya juyoba yace “call Hamza tell him I will not be able to see those
school people” yana maganan yawuce office nashi yabude yashiga wani kalan lafiyayyen office
ne babban gaske gaban wani daki yaje direct yabude lafiyayyen bedroom ne ciki da gado
dakomi bayin dake dakin yashiga wanka yayi da ruwa kai zafi yana fitowa yadauki wani sabon
suit ash yasaka sannan yadauki makullin motanshi yawuce yafita.
Stairs yayi daidai mutumin nan yafito daga office girgizakai yayi ganin Abee ya chanza kaya
saikuma ahankali yakoma cikin office ya zauna yana jinjina lamarin nan azuciyanshi.
Koda aka sauketa da kafa takarasa gidansu bude gate tayi tashiga Mama ne a tsakar gida da
Abida suna gyaran shinkafa duk suka bita da kallo ahankali tace “sannu da aiki Mama” fitowa
Gwaggo tayi daga bangarenta tace “makiran matan nan ina zata amsa gaisuwanki taho diyata
tun dazu nake zuwa kofar gida na leka ko kin fara dawowa amman baki dawoba zonan diyar
Gwaggo” Gwaggo tabude mata hannu dasauri tana murmushi tawani fada jikin Gwaggo
ahankali tace “Gwaggo yunwa” sakinta Gwaggo tayi tace “tuni namiki abinci dakaina dakuma na
wanchan Matar ubanki data kawo saida na dandana dan intabbatar ba guba tunda gashi har
yanzu ina raye ba guba muje daki” daki suka shiga saikuma tafito ta kalli Abida tace “kin fasa
shan furan dakikacemin zakisha ne tijararriya”? Dasauri Abida ta tashi Mama ta tabe baki
batace komiba dan yasan dazaran tace wani abu Gwaggo zata hada karya da gaskiya yau yau
din nan ta tara yaranta kaf takai karanta.
Tana shiga dakin taga Lujain zaune akasa ko takalmin makaranta bata cireba Gwaggo tacika
mata abinci agaba kusan kala takwas, Mama dama fried rice tayi da salad da chicked, Gwaggo
takara soyamata wani Kazan daban cikin kula, ta dafamata kwai guda hudu, sai katon flask din
tea, ga buredi saikuma taliya ga fanta da coke gakuma fura datake rabawa bama Abida tayi
cikin kofi tace “ungo” karba tayi tana kallon cikin kazan dake cikin kula gaban Laujain data
faracin abincin ga Kazan Gwaggo badai dadi da zaki ba tanajin kafizabo ahankali tace “Gwaggo
nima kaza” dan zaro idanu Gwaggo tayi takalli Lujain data batarai Gwaggo tace “fisabilillahi
Abida ni dai bansan kokin maida Lulu kishiyarki bane amman tsakani ga Allah kemafa dazu kin
shigo nabaki Kazan nan sannan kinci na wajen uwarki yanzu na jikata ne baraki bari taci ba”
turo baki Abida tayi tace “ai nima jikankice” ihu Gwaggo tayi tace “daman nace ke ba jikata bace
ni Safara’u amman ai wannan bata da uwa keko ga uwarki chan awaje tana aiki sai shegen
bakin zuciya” daure fuska Abida tayi tamike zata fita Lujain tadauki katon cinya tace “uhm”
juyowa Abida tayi ganin Lujain nabata tazo ta amsa tajuya bako godiya Gwaggo tace “kobaki
gode ba Allah dai yabata lada kinga banbancin rainona da rainon uwarki ko, diyata akwai kirki
da farar zuciya kuko zukatanku uwa an shafa bakin fenti irin na gyatumarku” daidai nan Lujain
ta tashi tana gaytsa ahankali Gwaggo takalli abincin dudda bata cinye komi ba amman tarage
sosai tawuce tashiga bedroom nasu kayan makarantan tacire tashiga bayi wanka tayi tafito
daure da towel tasa hijabi tai salla sannan tafito falo ganin bataga Gwaggo ba yasa tadauko
jakanta taciro wayan Ya Samira ta kunna wayan batai komiba amman screen din ya tsage
faduwa gabanta yayi ahankali ta tashi tana rike da wayan tafito da towel din nan tawuce side
dinsu bataga Mama awaje ba hakan yasa yasan tana kitchen dakinsu Ya Samira tashiga tana
zuwa ta ijiye mata wayan akan kayanta sannan tafito tadawo daki Gwagho da fitowa ta daga
nan daki kenan tace “barakizo kihuta ba kinsan anjima kadan zaku islamiya ko
EPISODE 9️⃣
Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu
Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;
https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/
Bayan one week!
Yau Saturday kasancewa jiya Zainab ta tafi dan mijinta yadawo yasa jama’an gidan suka ragu,
kowa na gidan nanan Abdallah ne kawai bayanan danshi both asabar da lahadi duka yanada
lectures.
Zaune yake a falo yana sanye da jallabiya fara mai kyau hannunshi rikeda wani cup na shayi
mai kyau yana kallon Hajiya da Mustapa dawani abokinshi Haruna shima soja ne yau kuma
yashigo Abuja sai hira suke da Hajiya suna dariya shi iyakanshi yay murmushi aka tambayeshi
eh ko a’a idan dasabo harsun saba da halin nan nashi, idan baka sansu bama zaka dauka
shine bako su Musty sune yaran Hajiya, shayin yakai bakinshi ya kurma daidai wayanshi kiran
IPhone 14 pro max dake aljihun gaban farin jallabiyan shi na kara ahankali ya ijiye mug din kan
coffee table dake gabanshi yaciro wayan ganin messege ne from an unknown number yasa
gently yabude.
“You have 24hrs to pay sum of 100 million in cash dakuma papers na company na Imran
ceramic inba hakaba we will release your sex tape ma duniya, in 24hrs time zamuyi contacting
naka ta hanyar fadamaka inda zakakai komi ka ijiye”.
Abee kyar ya tsaida idanunshi kan messege din daya karanta kusan sau hudu. “Hey hey
Imran!” Firgigit dayago kanshi ganin Mustafa akanshi da Haruna sai Hajiya duk suna kallonshi,
ganin idanunshi yasa Mustapa yace “lafiya dai ko me kake dubawa haka”? Mustapa yay
maganan yana kokarin karanta abinda ke screen nashi da sauri yay locking wayan yana
mikewa tsaye yace “time for asir ko let’s go” atare dukansu suka fice suna hira Haruna yakalli
wani babban gym dayaga ana fito da tsofaffin kayan workout din ciki ana saka sabo yace “anya
kuwa Musty komu sojoji zamu nunama Imran training kuwa”? Dasauri Mustafa yace “inafa
bakaga saisa baya tsufa ba look at him please kaman Yayan Abdallah” wani mugun kallo Abee
yamai yace “kadaina maidani yaro I don’t appreciate that” Musty shima mugun kallo yamai yace
“kayi zuciya kai tsufa to” daidai sun kawo masallaci.
Har suka idar da salla sex tape na ranshi to kodai bashi za’a turama sakon ba sukai mistake
amman kuma sun kira sunan company shi, gida suka koma daidai an gama lafiyayyen tuwon
shinkafa da miyan kubewa da kifi yana zaune akan kujera wayanshi yakara kara ahankali
yabude wayan video yaga an turamai babu wani rubutu tareda video, 5 secs video ne hakan
yasa yabude tareda maida karan to mute shiya gani a video abayi yana tafiya yana kokarin
kwance belt zaije bayin nan just 5secs yakare shiru yayi bayan video yakare he don’t really
know what to think wannan ranan dahar yay using that general restroom was ranan da yan
makarantan nan sukazo to where is the sex yan second dayayi abayin nan ne sex? waye a
company shi yamai wannan video? Blocking number yayi sannan yay deleting message din
gabadaya dan baiga amfanin abin ba though abin ya tsayamai arai dan shi yasan baiyi wani
abu mara kyau ba.
“Are you eating ko mu cinye mubarka”? Musty yay maganan yana kallon Abee, Hajiya tace
“ahap wannan aishi da abinci makiya ne baci zaiba kuci abunku ku manta dashi” mikewa yayi
dagakan kujera yace “kuci I will eat later ina zuwa” yana maganan yay stairs duk suka bishi da
kallo, dakinshi yawuce zama yayi akan gado yay shiru sai chan yay dialing number chief head
of security na company shi ringing daya yadauka yace “Sir” anatse yace “Mr James I need you
to email me the CCTV footage of on 23rd right away” cikeda girmamawa yace “yes sir” tashi
yayi yawuce wajen desktop nashi ya zauna tareda kunna desktop din ya bude email nashi
daidai video yashigo budewa yayi sunada yawa danna kowani department daban department
da office nashi yake yabude yay fast forwarding zuwa daidai lokacin dayaje bayi saikuma
yadawo baya daga lokacin daya fito daga office nashi yana waya har zuwa yazo corridor nan
saiga yarinyar tazo da gudu ta bangaje shi alokacin yaga wani ma’aikacin shi da bazai ma iya
tuna sunanshi ba but yasan yana cikin Human Resources team nashi, zama yayi yana kallon
komi harzuwa sanda mutumin yaje wajen bayi a corridor bayi akwai cctv but babu acikin bayi
daidai inda mutumin yafito da wayanshi yasa acikin bayi yay lumshe idanunshi yayi yay shiru
meyama yaron nan da yakeso yabatamai suna daidai nan aka turo kofan dakinshi aka shigo
dasauri ya kashe desktop din ganin Mustapha da Haruna, Musty dake kallonshi trying to read
something from his face yace “are you okay kuwa Imran” key dinshi na mota dake kan desk din
yadauka yace “I need to go to office now something came up” ta gefensu yabi yafice yabarsu
nan tsaye Haruna yace “what is this saying ma?….Hali zanen dutse ko” tabe baki Musty yayi
yace “ai murdadden halin Imran bazai taba chanzawaba tun yana yaro” zama sukayi, Haruna
yace “Musty yafijin maganan ka wai har yanzu bazai aureba Kodai yanada matsala ne irin I
mean medical one din nan” dan dariya Musty yayi yace “lafiyanshi kalau wlh” Haruna yace “to
tayaya yay surviving 13yrs ba mata ni gashi yanzu inada mata biyu na uku ma nake neman yi
yanzu dan sunmin kadan, nakasa gane yaya yake surviving” tabe baki Musty yayi yace “ohon
mishi idan yazo katambaye shi, ni tashi muje mu buga ball jikina yamin nauyi sabida yan kwana
biyun nan damukai ban motsa jiki ba” Haruna yace “yaushe za’a gama aikin gidan naku ne
kadau matanka kutafi” murmushi yayi yace “cikin this week yau suke fenti ma dazu nida Imran
munje gidan” suna hira suka fice daga gidan bayan sun gayama Hajiya zasu dawo suyi dinner
tace to su kawo mata inibi.
Zama yayi acikin office nashi bayan yaciro file din Human Recourse team nashi kowanne ga
sunanshi da passport da information nashi awajen akan yaron ya tsaya sunanshi Abdulganiyu
Olaniyi Asiwaju Razak bayerabe ne from Osun state aikin nan ne yadawo dashi Abuja this is his
second year a company shi, shiru yayi yana kallon hoton yaron, saikuma ahankali yashiga
daukan number shi yay dialing yaji akashe ajiyan zuciya yasauke ya maida paper ya ijiye yay
shiru kana ganinshi kasan tunani yake yana nan cikin office shi kadai har magrib jin ana kiran
salla yasa yatashi yakulle office yafito tareda masu gadinshi sukai salla yajasu jam’i suna idarwa
kyautan kudi yamusu har mota suka rakashi suna godiya yawuce yatafi tsayawa yayi wajen
masu saida fruits siyan dayawa yayi aka samai a boot harzai wuce saiga mai saida ribbon Muna
yatuna batada wani gashi but yanason ribbon most time yakan tsokaneta da aukin siyan ribbon
amman babu gashin dazata kama dashi kiran mai ribbon din yayi yace “kawo” dasauri mutumin
yazo kafinma mutumin yay magana Abee yace “nawane duka”? Washe baki yayi yace “duka
nan kayan 4,500 ne” 5k yaciro ya kirga yabashi godiya mutumin yashiga yi yaciro komi yahada
yabashi karba yayi yaja motanshi yawuce.
Saida yafara tsayawa yay isha’i a masallacin anguwansu sannan yafito yawuce gida bayan ya
dauki su Hamza da Abdallah daya gani amadallacin yana parking ribbon din kadai yadauka
yaba Hamza key yace “ku kwashe fruits kukai ciki” yawuce babu kowa a falo hakan yasa
yawuce sama ahankali yay sallama tareda bude kofan dakin Kausar tana zaune sanye da
dogon rigan atampan ta mai kyau rubutu takeyi tadage ganin Abee yasa ta yarda biron ta tashi
da sauri tace “Abee dana dawo daga kitso bakanan” tai maganan tana tafiya wajenshi dan yana
tsaye gaban dakin, ganin yana kallon kitson da aka mata yasa tawashe baki tace “kitson yay
kyau Abee” gyadamata kai yayi yace “sosai” ledan hannunshi yabata dasauri ta karba tace
“meka siyamin Abee” ganin ribbons dayawa daban daban wani kalan ihu tayi ta rungumeshi
tana tsalle tace “Abee thank you” dan murmushi yayi yace “saken kije kicigaba da assignment
dinki, kinci abinci”? Gyadamai kai tayi tana kallon ribbons dinta hankalinta yay nisa awajen, fita
yayi daga dakin zuwa nashi.
Wanka yayi shayi kawai Hajiya ta aikamai dan tasan yanda dare tayi bazaici abinci ba, zama
yayi yanashan shayin yana tunani na farko babu anything like sex dayayi so wanan ma is off
list, nabiyu this so called guy dake blackmailing nashi employee nashi ne and when something
happen that has to do with employee naka you need to handle it with lots of precaution, he will
try his number again tommorow yaga how things goes.
Washegari yay dialing number still akashe ganin har yamma still babu komi yasa ya tattara komi
ya watsar dan in the first place yasan babu wani sex video ballema har ayi leaking nashi a
online.
Yau monday as usual bayan breakfast kowa yakama gabanshi Abdallah tareda Kausar suka tafi
school dan lecturer su nasafe yace baida lpy bazai zoba, Hamza ya sauke yara yawuce shima
Abee yashirya cikin wani Italian suit black dayamai kyau bana wasaba hannunshi daure da
rolex, yana kaiwa company abinda yafarayi was yashiga office na HR amman seat na guy din
empty bai zuwa wucewa office nashi yayi dan yanada ayyuka dayawa dazaiyi.
Wuraren 10 aka fita break kowa na ajinsu SS2A yafita banda ita dake zaune tafito da duka
abubuwan da Gwaggo tazuba mata a jaka tanaci one by one, tana cikin cin egg and chips
princess tashigo class din da ita da Lily dawasu maza guda biyu rike da goran drinks a
hannunsu kallo daya tamusu tadauke kai ganin sun