Showing 12001 words to 15000 words out of 82745 words

Chapter 5 - Sakon So Book Complete by m Shakur ( By Ubeera ) .pdf

M Shakur   

11 Oct 2025

1668

naki” makema Gwaggo kafada tayi still ita bata yarda ba
Gwaggo tace “to yanzu mekikeso? Ni wlh kin fitineni Lujain kin hanani sakat aduniya, zanfa
tattara nakoma kauye nabarki” kaman jira take fashewa tayi da kuka sosai kaman ana yankata
ta tashi fuuu tafice ko jakan bata daukaba da sauri Gwaggo tadau jakan tabita abaya tana
kwalamata kira tace “Lujain zoga dubu daya saiki saya wlh wasa nake babu kauyen dazani
nabarki, nima ina zan iya rayuwa babu ke kinmini nisa” kojuyowa Lujain batayiba sai kukan
datake daya cika gidan gabaki daya yana eco daidai Baba yafito daga falo chak ta tsaya anan
tsakar gidan kukan yamakale awuya Gwaggo takaraso dasauri tana hararan Baba tace
“kaikuma meya fito dakai ina ruwanka damu ai magananmu mukeko Lulu” da sauri Lujain ta
gyadama Gwaggo kai tana goge fuskanta da bayan hannu, strictly Baba na kallonta yace
“collect your bag muwuce school” ahankali tamika ma Gwaggo hannu, Gwaggo tace “yauwa
diyar albarka zan sayamiki kafin kidawo kinji ga jakan” karban jakan tayi ta goya Baba yafito zai
gaida Gwaggo tace “jeka kaisu kadawo ai ina nan babu inda zani” girgiza kai kawai yayi yawuce
Lujain tabishi haka su Samira ma dasuka fito duk sun shirya su sun fara university, suna shiga
bayan motan murya kasa kasa Samira tace “ina kudin”? Mikamata kudin Lujain tayi aboye itama
taja jakan Lujain tasamata wayanta da earpiece aciki tace “ai kinsan password dina”
Gyadamata kai Lujain tayi tana murmushi kaman ba ita tagama kuka ba, a school dinta Baba
yafara parking school ne mai kyau ba laifi ga buses awaje an jerasu sabida excursion din daza
ayi sauka tayi Baba yakalleta yace “zagayo tanan” zagayowa tayida sauri ta tsaya wajen glass
din motar daya sauke yana kallon fuskanta dukta tsure dan tana tsoron Baba sosai, dan jim yayi
yana kallonta kaman mai tunanin wani abu saikuma yace “menene bakida shi dakike kuka?”
Adan tsorace kaman mai tsoron fadi tace “yooo………ghurt Baba” murya chan kasa still yana
kallonta yace “ana saidawa acikin school din naku?” Gyadamai kai tayi ahankali, yace
“nawane”? Ahankali tace “500 ne Baba” dubu daya yadauka yabata yace “gashi to kisaya” wani
kalan murmushi tayi daya bayyana fararen hakoranta tass irin na yara din nan tace “thank you
Baba” murmushi yamata yace “excursion zaku yau ko”? Gyadamai kai tayi tana rikeda 1k din
yace “ina”? Hannu tanunamai alamun batasani ba tace “amma ance wajen ceramic ne, zamuje
muga yanda ake yin su flower verse, broken plate, bowl, tiles da sauransu” gyadamata kai Baba
yayi yace “is a good thing makesure kinyi paying attention and learn everything kinji” gyadamai
kai tayi tace “too” juyawa tayi tubur tubur zata wuce Baba yace “Lujain” dasauri tajuyo takalleshi
tace “na’am Baba” ahankali yace “be careful okay” gyadamai kai tayi tajuya tawuce saida Baba
Yaga shiganta school sannan yasauke ajiyan zuciya yatada motar duk cikin yaranshi yafijin
tausayinta bawai sabida ita marainiya bace kadai ba sabida many things, she gets bullied a lot a
school, a islamiyya, har agidama, wani zubin yanaso yarabata da Gwaggo but idan yakalla abin
deep down badadan Gwaggo ba da yanzu she’s depress Gwaggo nakoya mata komi ba komi
bane karta sake tai taking maganan mutane to heart and she should be confident kiba is beauty
kuma haka takeyi Koka cemata me kiba da sauransu wani zubin zata iya kuka but give her one

hour ta kakkabe jikinta tayi moving on gashi ko kadan batada riko her heart is as pure as white
paper.
EPISODE 7️⃣

Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Ku danna link dinnan dan following dina a Instagram;
https://www.instagram.com/p/CnmsOO8I0XL/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Ku danna wannan link din dan following dina a TIKTOK;

https://vm.tiktok.com/ZMYekGsQV/





Tana shiga school ana cewa sufito afara shigan bus dan 9:30 zasu bar school yan class nasu
yan SS2 akace sufara tafiya bus nasu ita hartama saba batada friend shiga tayi itane sit 1 dan
ita tafara biyan kudi tana zama tabude jakanta tadauko ledan biscuit tafaraci yan ajin saikaga
wannan yataba wanchan anunata sai akwashe da dariya ko kallonsu batayiba dake bude jakan
tayi ta leka wayan Ya Samira tareda dannawa taduba time dan 11 Mandawari zaizo live a IG,
murmushi tayi maida jakan tarufe tana cigaba da cin katon biscuit dinta wata Yar class dinsu
tamike tsaye a bus din bayan an gama shiryasu an koma wani bus ana shirya wasu yan ajin
base on payment tace “Hey Class mate I have a story to tell u tantadaaaaa” duk kallonta akayi
wasu yan mata da samari click dinsu sukace “we are listening princess” dariya tayi tace “I want
to call some part of the body kugayamin uses dinsu” duk akace okay, tace “the eyes is for
whattt?” Yan ajin sukai ihun “seeing” tace “the ears is for what”? Suka kara ihun “hearing” cikeda
zolaya from her tone tace “and the mouth is for whatttttttt?” Yan ajin sukai ihu atare “eating” tace
“for what” sukace “eatingggggg” Haba sai dariya duk Lujain najinsu hakan bai hanata cigaba da
cin abinta ba, komawa princess tayi tazauna tana dariya saiga wata ta tashi da ake cema Lily
tace “aga aga” dayake dudda akwai Christian a ajin but duk sunajin hausa universal language
sukace “aga” tace “aga chop chop din aji” atare duka suka nuna Lujain sukace
“aaaagannntaaaaaa” sai dariya tace “aga mara kawa” suka nunata sukace “aaaaagannnntaaaa”
tace “aga mara aboki” sukace “aaaaagannnntaaaa” sanan tai wani ihu irin na final one din nan
tace “aga mara boyfrienddddddd” duk aka nuna Lujain akace “aagannnnnnntaaaaa” kwarema
Lujain tayi ba kakkautawa dasauri tashiga bude jakanta taduko ruwa da sauri tashiga sha saida
tasha sosai sannan click din su princess din sukazo inda take tsabagen son ta kulasu Princess
tace “ke miss chubby bakijimu bane Fatty bom bom” wani mugun kallo Lujain tamata batai wata
wataba tamike tsaye tareda ajiye jakanta kan sir din dasauri Princess suka koma baya dan sun

zaci dukansu zatayi ko zaunesu cikin kunanrai Lujain tace “Ohhkayyy you want me to say
something ko” boldly takalli yan cikin bus din tace “aga aga” Yan makaranta fa akwai son bala’i
da fitina, they live for it shine the joy and the fun that comes with being in school da sauri
sukace “aga” Lujain tace “aga masu satan amsa during test and exam masuyin chokes olodon
aji amman sunfi kowa iya makeup” habawa sai dariya kyakyalya bakaramin kunya princess da
Lily sukaji ba, Lujain tanunata da hannu tace “idan kika kara kirana Chubby kowani stupid name
saina fasa miki ciki, my name is Lujain but I prefer idan ankirani da LJ, and I am pretty, prettier
than this bullies, and I am brilliant cus banayin choke, and I am beautiful I don’t need makeup
kuma I have boyfriend a celebrity for that matter” tanunasu habawa sai ihu ajin ana bubbuga
kujeru da kasan motan da kafa ana dariya yan class din suka fara matching ana tafi “LJ! LJ!!
LJ!!! LJ!!!!” juyawa tayi takoma sit dinta dasauri ta bala’in danne kukan datakeji Gwaggo tasha
gayamata kada tasake tayima yan ajinsu kuka idan sun kirata da sunaye dan zasu cigaba saisa
bata sake tai kuka and bata taba nunawa wani dan ajinsu she needed them ba tana homework
dinta tai karatunta da kanta dan Allah yamata brain.


Teacher dake incharge na class nasu ne tashigo tareda zama akan kujera tace “let’s settle down
student remember not to touch without being permitted and not to go anyway da abace muje ba
understood” duk suka amsa, juyawa tayi ta kalli Lujain da already ta tara ledojin biscuit uku
agabanta tanacin na hudu zatamata magana saikuma kawai tai shiru ta gyara zamanta bus
dinsu yafara tafiya.
Bini bini Lujain ke bude jakanta tana duba time awayan Ya Samira ganin har lokacin eleven
baiyiba yasa tai murmushi ta juyarda kanta tana kallon hanya, sunyi tafiyan kusan 30min
sannan sukakai wani dankareren babban building ita duk zamanta a Abuja bata taba zuwa
wajenma bama tasan wajenba to inama take zuwa daga boko sai islamiyya da yamma sai
hadda weekend, building na company yayi kyau an rubuta “IMRAN CERAMICS” security gate
ne sukai directing nasu to inda zasuyi parking dan musamman aka basu special parking space
dan student dole adauki caution saukowa akayi sannan one by one aka fara basu wani sticker
dake dauke da rubutun visitor ajiki agaban riguna nan school nasu dake matsayin access card
nasu, tanaji wasu yan ajinsu na “wow babban company na wannan, just look at how beautiful
visitor’s access card namu” sai alokacin tama kalla dan ana bata mannawa kawai tayi saida
teachers dinsu aka kara maimaitamusu yanda zasu behaving da banda tabe tabe sanan akace
zasu iya shiga wani ajiyan zuciya tasauke dan surutun yasa bata iya duba wayanta ba kafin
teacher sugani a kwace ahankali take tafiya kafin ahankali tasaka kafanta tashiga cikin katon
hall don dayake nan reception wani kalan sanyi taji dayasa ta yatsine fuska ahankali tace “AC
yay yawa” ihu principal nasu tayi da shigowanta kenan cikin personal car tazo tace “Assemble
yourself student” assembly duk sukayi gwanin ban sha’awa murmushi principal din tayi daidai
lokacin Hamza yakaraso yana sanye da suit cikeda girmamawa ya gaisa da ita sannan yace
“sudan jira kadan CMD na attending ma wasu baki ne” murmushi tamai sannan takalli daliban
tace “I am sure all my students here wants to meet the owner, the brain behind this company,
this art, this ceramic work dakenan number one a Nigeria keji dashi, the only ceramic company
dake exporting kayayyakin su su plate, verse, mugs, tiles dasauransu zuwa kasan waje, let’s
know little about him and his success story right, what’s the best way to know inda daga

bakinshi ba” student akace yes Ma tace “tom gashinan zuwa” sauke jakanta Lujain tayi tana
yatsine fuska kawai anzo an ajiyesu waje daya su haryanzu baa nuna musu komiba ko mene
zasuyi damai company oho, danna wayan tayi tacikin jaka ganin 11:05 yasa ahankali tace
“Innalillahi na shiga uku” tashi tayi tashiga waige waige ganin teacher su anan baya tsaye yasa
tai wajenta dasauri teacher tamata alamu da hannu menene? kaman zatai kuka tace “I want to
pee zai zubo” binta da kallo teacher tayi kaman tamaketa tace “Ya za’ayi bazakiji fitsari ba babu
kalan abinda bakici ba amota kaman danke kadai akai abubuwan ci aduniya” tai maganan tana
cewa follow me binta tayi dasauri zuwa wajen wani security guard tace “excuse me rest room
please my student wants to excuse herself” wani waje yanuna musu hakan yasa tace “Oya go”
Gyadamata kai tayi ita bama tagane ina ake nunawa ba kawai tawuce abinta da sauri daga
malaman har daliban aka bita da kallo wasu na danne dariya ganin yanda hankalin kowa yayi
kanta yasa principal tace “attention” duk juyowa sukayi suna kallonta tacigaba da jawabi, ko
kadan ita bataga bayin da akacemata ba amman ba wannan ne matsalanta ba waje take nema
inda zata labe ta zauna takalli live na Mandawari wani babban corridor data gani yasa tai wajen
da saurinta tashiga tafiya harta fita daga corridor taga wani bene da gudu gudu tana haki
tashiga hawa benen at the same time tana cire jakanta daga baya duk tana gudu, kaga yanda
take tafiya zaka dauka all this kafin agric ne da ake shirin yankawa sunason su gudu, wayan
taciro da sauri tana kunna data tana makala earpiece akunne ta sannan tasa hannun tadauko
ledan chocolate guda biyu atare tabare ledan ta yarda ledan akasa, jakan batare data rufeba ta
sagale a hannunta tana finciko goran fanta da Gwaggo tasamata agefen dan ragaragan aljihun
nan na wajen jaka, daidai tana shiga instagram tai logging into her account tana kokarin takai
duka chocholate biyu dake hannunta baki ta balla tana kalle kalle ko kadan batasan inda takeba
bama tasan tayaya tazo wajenba tadaisan dazu tahau staircase cigaba da sauri tayi ganin duka
offices ne awajen kuma duka akulle yasa tacigaba da tafiya zuwa wani corridor data hango
daidai tana shiga live din daidai tana yankan kwanan corridor din kawai karo taci da mutum
fantan data bude dake hannunta ya kware ajikin mutumin zuwa kasa chocolate din hannunta
yawani karye ajikin mutumin yafadi akasa tasan tafadi tasan taci karo da mutum amman still
gabaki daya da fuskanta da hankalinta nakan wayan da shi kadaine abinda bai fadi daga
hannunta ba sabida yanda tarike gamgam dan shiyafi mata komi mahimmaci ayanzu, ko kallan
wanda tabuge batayiba kawai tabi ta gefenshi da bala’in gudu tacigaba da tafiya takara shan
wani kwana data gani kawai taga wani kofa abude batai wata wataba tafada ciki ganin bayine
ga bayuka kusan biyar kowanne da kofanshi inda take tsaye kuma wajajen wash hand basin ne
da mirror yasa da gudunta tayi bayin farkon wajen tana budewa ta sauke marfin masan
dakennan karkal ta zauna akai tareda yarda jakanta akasa tawani sauke ijiyan zuciya ta tura
kofan dabaigama rufuwa har karshe ba balle tamasaka sakata tana kara tura earpiece din
kunnenta da kyau tana kallon wani bakin gaye mai irin askin yan kwalo dinnan da aka kitsa
yana sanye da rigan kwallo na magana yana murmushi wani farin hakorin makka na shunning
abakinshi wani kalan murmushi tasaki takai wayan ta rungume kirjinta tareda lumshe ido
zuciyanta na bugawa tace “I love you Mandawari” na kusan 30sec sannan tacire wayan daga
kirjinta tafara replying to live dinshi I love you Mandawari from LJ, My heart beat for you, please
check your DM kullum saina maka magana, emojis babu na kalan soyaya dabata dinga turawa
ba tana. Cewa please if you see my comments ko sunana ne ka kira a live din nan kana ganin
yanda takeyi kasan gabaki dayan brain nata na live din nan.

***
Waiwaye baya kadan….
Daidai taci karo dashi aka bude kofan wani office wani zai fito but ganin Oga tareda wata
katuwan yarinya dake sanye da uniform ajikinshi dukansu a tsaye yarinyar na kallon waya
kaman abu take nunamai shikuma Oga na kallon fuskanta yasa yakoma cikin office da sauri
batare daya gama rufewa ba yana leke, wucewa tayi batare data dauki goran fanta daya fadi da
gutsurorin chocolate nataba ta fanfala da uban gudu.


Chak Abee ya tsaya yanabin jikinshi da kallo gabaki dayan suit din dayasa yabaci har zuwa
farin rigan ciki dan bai kulle boturin jacket dinba afarin rigan fanta ya zube ga chocolate din
some sun manmanne a rigan kaman kashi, sai alokacin ma ya iya juyawa amman hartai kwana
sai farin safan kafanta da sandals daya hango azuciyanshi dudda baisan kalan uniform na
makarantan dazasu excursion ba but yasan babu any of his employee dazasu dressing like that
dan haka that must be a student what on earth student keyi in this floor, kwata kwata nothing
yahadasu da this floor dan dazaran yay welcoming nasu factory za’a wuce dasu dake ciki cikin
building din suga yanda ake production, jikinshi yakara kallo tayaya zai sauka kasa ahaka yay
addressing student, juyawa yayi ahankali cikeda takaici yabude kofan wani office daban
ma’aikatan wajen duk suka mike batare daya shigaba yace “call cleaners agoge nan” atare
sukace yes sir sannan yawuce yana tafiya anatse zuwa wani special corridor dakenan dawani
hadadden office da aka rubuta CMD ajiki murda kofan yayi yaji akulle sai yanzu yama tuna
yabar Ibro a office yacemai idan yagama yarufe kofa yakai mishi wasu files mota dan yana
gama magana da student fita zaiyi yanada wani meeting dawasu Chinese dasuke son yamusu
toiletries, wani mugun tsaki yayi yanzu dole saiyaje General rest room na this floor fitowa yayi
yajuya yashiga wani corridor yafara tafiya daidai nan shima wannan employee dayaga lokacin
dasukai karo yafito daga office ahankali ganin Oga yay hanyar da yarinyan tayi yasa ahankali
yace “Oga yasanta ne”? Saikuma yahau tafiya da sauri yace “interesting I thought ustazun
mutumin nan baison mata so apparently he’s deceiving kowa” ahankali Abee yabude kofan
bayin yashiga ya tsaya gaban wash hands basin yana kallon kanshi ta madubi dan gajeren tsaki
yayi ganin yanda kayanshi suka baci sosai bude tap yayi yatara ruwa a hannunshi ya yarfe
hannunshi yakai yana goge chocolate din wani kalan mugun tsaki yayi ganin chocolate din kara
spreading ma yake kawai kayan bazasuyi ba dole ya chanza su yasa yaciro wayanshi yakira
number Ibro kai tsaye yace “where are you now”? Yadanyi shiru yace “leave the factory ka
koma mota ka kawomin office key” yana maganan ya katse waya ji yayi ma he’s a bit press
hakan yasa yajuya ahankali direct first bayin dake wajen dayaga kofan adan bude yanufa kai
tsaye yana tafiyan yana kokarin bude belt din wandonshi daidai lokacin mutumin nan yaturo
kofan bayin batare daya shigo ba yakawo wayanshi taciki yana video don baison aji mutum
awajen afasa abinda za’ayi saisa yaturo waya yana video ganin Abee na kokarin cire belt yasa
yaware idanu yakai hannunshi kan bakinshi aranshi yace “badai yarinyar ke jiranshi anan ba, ai
Oga baya using this restroom saina office nashi” kai tsaye Abee yabude bayin tareda shiga ciki
atare wani irin ware idanu yayi ganin yarinya zaune akan masan data rufe ga jakanta akasa
waya a hannunta tana kallo earpiece akan kunnenta ga chocolate a hannunta tanaci tana
murmushi sosai tana kallon waya, alamun kaman da mutum akanta dataji yasa tadago manyan

cat eyes dinta ahankali dan ko kadan bataji shigowanshi ba dan ta taushe kunnenta da earpiece
maganganun Mandawari kawai takeji, wani kalan mugun ihu ta kurma tareda zabura ta mike
tsaye tana maida kofan tarufe su, takai hannayenta tadaura kan idanunta tace “wayyooo
uhmmmmm” tashiga bubbuga kofan da bayanta tana kokarin bude kofan tana kuma kokarin
kama bakinta ganin mutum babba kaman aljani akanta.
EPISODE 8️⃣


Jama’a I am back! Wannan littafin nawa zaku sameshi a all my social media platforms idan
kuma kuna bina a Instagram ko Tiktok su akodayaushe zai kasance sun wuce yan WhatsApp
da page biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login