Showing 1 words to 3000 words out of 82745 words
EPISODE 1️⃣
DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI
~Masjid Ibn Taymiyah~
Aka rubuta ajikin babban masallacin dake cike makil da jama’a kowa yaci manyan kaya
manyan shaddoji da kanagani kasan daurin aure ake shirinyi, wani matashin saurayine ke
sanye da manyan kaya dakuma babban Riga na shadda datasha aiki yana tsaye daga ta wajen
masallacin yana kallon agogon hannunshi da alamu lokaci yake dubawa chan kuma yadago
kanshi yana leken kan titin da masallacin ke kai, tabashi akayi daga baya dayasa dasauri ya
waigo wani matashin saurayine yatabashi shima yana sanye da manyan kaya yasha hula kube,
cikeda damuwa yace “he’s 20minutes late Arif kazo mutafi koda na’ibin limamum masallacin
nanne ya karba maka Auren, duk an taru mutum daya ake jira haba mana is not cool”
girgizamai kai wanda aka kirada Arif yayi yace “I know he will come let’s just give him some
time, Uncle Hamma is just…..” dasauri abokin yace “sociopath” wani mugun kallo Arif yamai
zaiyi magana daidai wata Babban jeep na parking abangaren masallacin dayadan sami space
na parking, wani kalan walwala ne ya bayyana akan fuskan Arif baisan lokacin dayabar abokin
nashi yafice daga cikin premises na masallacin dasauri ba dudda jama’a na kwalamai kira ta
ko’ina suna ango ango baibi takansu ba yay wajen motan dayake nan bamaka ganin kowa na
ciki sabida tinted glass ne duka kuma arufe, ahankali yasa hannunshi batare daya jiraba yabude
gaban motan bangaren mazaunin direba tareda tsugunnawa har kasa cikeda girmamawa
batare dayama kalli fuskan mutumin dake cikin motanba yace “barka da zuwa Uncle Imran”
wani magidancin mutum ne zaune cikin motan da akalla zaiyi 48/49yrs yana sanye dawani soft
milk yadi daya haska bakar fatanshi dake bala’in sheki tsabagen hutu.
Yanada cikan gashin gemu sosai gasunan baki sidik masu tsayi kadan dawasu sirarren saje
dakenan a kwance suma lublub, ga cikan gashin gira dakuma suman kai dudda lafiyayyan
hulan minister na kanshi hakan bazaisa kagane cewa yanada cikan sumaba, yanada wasu
kalan kananun yet manyan idanu idan ya zubamaka su idanba ka natsu ka kalleshi ba zaka
dauka idanun nashi a lumshe suke amman abude suke ras kwayan idanun farare fat, hancinshi
dogone sosai kuma siriri sai lips dinshi dakenan jazur, kallo daya yama Arif dake tsugunne
kanshi akasa babu wani murmushi ko fara’a akan fuskanshi sannan kuma babu wani bacinrai
ko wani yanayi akan fuskanshi saima fuskanshi dake nan adake dake lullube dawani kalan
warm rahama akai, kaman baiso yay magana yace “Arif” wani kalan murmushi Arif din yasaki
cike da mugun girmamawa yace “na’am Uncle Imran” tareda dago kanshi yadan kalleshi
saikuma yasake sauke kan nashi kasa dasauri baitaba ganin mutumin dake tattare dawani
kalan mugun kwarjini dakuma haiba irin na Uncle Imran ba, duk yanda kakai ga bushewar
idanunka baka iya kallon tsabaragen idanun Uncle Imran kamai, Ahankali kaman baiso yay
magana cikeda wannan natsuwan yace “get up kayanka will get dirty” tashi Arif yayi babu
gardama still kanshi na kasa hakan yasa anatse ya sauko daga cikin motan yafito ya tsaya
kusada Arif duk tsayin Arif akafadar Uncle Imran yake dan Uncle Imran giant ne sosai, dudda
babba ne shi ya manyanta amman jikinshi da gabobinshi gabaki daya atsaye suke tsaf kana
ganinshi kaga wanda yake gyara jikinshi ta hanyar cin lafiyayen abinci dakuma excercise, yana
sanye da babban riga dake kyalli da wandonshi daya tsayamai a daidai idanun sahu, kafanshi
na sanye da ankle sock dake cikin wani givency covershoe dake sheki sosai, juyawa yayi
yadauko wani bakin glasses dan idanunshi basason haske sosai yasaka sannan yakalli Arif
dakanshi ke kasa yace “muje ko”? Gyadamaikai Arif yayi yace “to bismillan mu Uncle” yay
maganan suna jerawa tunda yake baitabajin mutum dake kamshin turare kwatankwacin irin
turaren Uncle Imran ba, turaren Uncle Imran nada bala’in dadi gasu da sanyaya rai, tun kafin su
karasa cikin masallacin mawaka da maroka kemai wake wanda ko kadan bayaso hakan yasa
baice musu komiba koyabasu kudi ba yawuce suka shiga masallacin nan da nan abokin Arif
yace “waliyin Arif ya iso” karasawa sukayi cikin aka zazzauna nan da nan aka daura aure
tsakanin Arif da Salma akan sadaki 500k wanda Uncle Imran yabiya mishi akai addu’a ana
gamawa ko sec daya tal bai karaba yamike yajuya Arif yatashi dasauri yabishi abaya, abokin
Arif yataba wani abokinsu da duk sukabi Arif da Uncle Imran din dasuka fice daga masallacin da
kallo yace “dan Allah jibi Arif saikace yaga God” dayan abokin mai suna Muhammad yace “to ai
kusan hakane wannan Uncle din nashi shiyamai komi aduniya tundaga primary school konine
abinda yafi hakama zanmai wlh Aliyu tunda mahaifinshi ya gudu yabarsu bai kuladasu ba” tabe
baki wanda aka kirada Aliyun yayi yace “bakasan waye mutumin nan ba idan kasan irin kalan
bakin girmankan dayake dashi saikai mamaki bakaga yanda babu wanda yagaida a masallacin
nan ba sai uban dingile wando shi adole ustazu da ijiye gemu” wani kallo Muhammad kema
Aliyu yace “waikai Ali me mutumin nan yamaka ne danni wlh banga aibunshi ko daya ba”?
Mugun kallo Arif yama Muhammad yace “bazaka gane bane waini mutumin nan zai hana aiki
sabida wai inashan taba yay rejecting application dina a company shi, shi wayasan kalan
abubuwan dayayi lokacin dayake matashi yana soja kafin yay retire”? Kalan kallon da
Muhammad kemai yasa yace “me to ai gaskiya nafadi ni to even tell you the truth gwara dabai
daukeni ba dan ance mahaukaci ne tuburan tuburan saidai in alluran sojojinshi basu tashi ba
wlh bakaga saisa har yanzu babu wacce ta yarda ta aureshi ba sai tsufa yake agidan
tsohuwarshi” wani mugun harara Muhammad yamai yace “kainedai kaga tsufan dan ni bangani
ba wlh ko mahaifin Arif daya girma yafishi tsufa, haushin shi kawai kakeji sabida yahanaka aiki
dayayi, kuma aure dabaiyiba shine baiyi niyya ba tunda akazo har gida aka kashemai mata da
yara biyu” dasauri kaman jira Aliyu yake yace “kasan shekara nawa yanzu da mutuwansu? This
is the 13th year amman har yanzu bai kara aure ba, wlh basabida mutuwan matanshi bane ba,
matsalan haukanshi yasa babu wacce ta yarda ta aureshi” zai cigaba da magana ganin Arif na
tahowa wajensu yasa yay shiru yamike tsaye yana kakkabe rigan jikinshi.
EPISODE 2️⃣
Tunda yashigo cikin estate dinsu yahango wani magidancin mutum tsaye agaban wani
dankareren gida da sojoji guda uku ke tsaye wajen taredashi, kana ganin mutumin kasan zasuyi
age mate saidai shi mutumin yafishi tsufa sosai dan ga furfura ko’ina akan fuskanshi, dan ijiyan
zuciya yasauke sannan yakarasa gaban gidan batare daya kashe motan ba yasaukar da glass
din motan kasa hakan yasa sojojin wajen suka sassaramai Sir! Gyadamusu kai yayi a natse
batare daya amsasu ba sannan yasauke idanuwanshi kan mutumin daya taho wajen motan
dasauri fuskanshi babu alamun rahama akai baiyi wata wataba babu gaisuwa ko sannu cikeda
masifa yace “Alhaji Imrana nagaya maka karabun mini da d’ana kaki I agree cewa lokacin nan
nagudu na barsu Kaika sashi a makaranta da sauransu yanzu I am back yarona don’t want
anything to do with me, imagine ni mahaifin Arif ina masallacin nan amman ko kallo ban isheshi
ba sabida kai sai rawan jiki yake yana binka kaman yaga sarki, karabun mini da dana allow me
to be his father” tunda yake maganan kallonshi yake saida batare da yanayi kokuma wani abu
na fuskanshi ya chanza ba yagama tsaf sannan yace “nabarka lafiya Baban Arif” tareda maida
glass din motan sama aka bude mishi gate yawuce yashiga cikin katafaren gidanshi yabar
mutumin awaje yana nuna kanshi yace “ni zaka gwadama miskilanci”? Duk maganganun
dayake sojojin kallonshi suke so suke suje su bubbugeshi amman kallon da Oga kadai yamusu
is kallon kar wanda ya kula bakona cikinku yagama duk abinda zaiyi yatafi.
Wajen jerin motocin dasunkai kusan 12 acikin gidan yayi karasawa yayi da motan yana tafiya
very slow yay parking sannan yakashe motan yakai kusan 5min zaune a motan kaman bayaso
yafito sannan yabude kofan ahankali yafito sannan yamaida kofan yarufe yajuya yafara tafiya
yana dumfaran cikin gidan ma’aikatan cikin gidan dake aikace aikacen su na gaidashi da kai
kawai yake amsa musu yakarasa gaban babban durmemen flat daya rak dake cikin gidan
dakeda girman gaske yabude kofan ahankali yashiga wasu yan kananun yarana su biyar da
dukansu bazasu wuce shekaru 3, 4, 5 hakaba suna tsalle tsalle suna ganinshi duk kowa ya
natsu duk suka zauna akasa atare cikeda gwaranci irin na yara sukace “Abee Assalamu
Alaykum” maida kofan yayi sanan yajuyo yabi yaran da kallo dayar karaman murmushi daya
bayyana akan fuskanshi a natse yace “wa’alaykumus salam Children” sannan yashigo cikin
katafaren falon dawani katon family picture frame ke bangon dake dauke dawata tsohuwa da
akalla zatakai 70yrs sai shi yana tsaye agefenta daga yanayin yanda fuskanshi yake ahade
zaka gane ko kadan bayason hoton sai wasu manyan mata dasuma sun manyanta masu kama
dashi su uku, saikuma wasu maza su biyu dakana gani zakasan kanninsu ne saikuma yara
dayawa a frame din, zama yayi kan kujeran sannan yabi yaran da kallo daduk suke kallonshi sai
yanzu yama tuna baitaho musu da komi ba this is so not like him saurin dayake yasa yamanta,
wannan karan dan murmushi kadan yayi sannan yamike musu hannu yace “kuzo nan” kaman
jira suke dawani kalan gudu suka taho murmushi yayi anatse yace “zan dauki kowa one after
the other okay” gyadamai kai duka sukayi babban cikinsu dake 5 yafara dauka yace
“Muhammad” yaron ya kyalkyace da dariya sannan yadauki na biyun yace “Faisal” yadauki
macen yace “Nana” sanan ya ijiyeta yadauki dayan macen yace “Miemie” sannan yadauki
karaman dake 2yrs yace “Anees…….” Shiru yayi sabida zafi dayaji ajikin yarinyar hakan yasa
yakai hannunshi dasauri yataba goshinta jin dumi yasa yakalli Muhammad yace “call Aneesarh
Mom” dasauri yaron yajuya yay kitchen, ko 1sec Muhammad baiyi da shiga kitchen ba wata Yar
Babban mace tana kamadashi tafito da apron ajikinta dasaurinta tace “Yaya Imran kadawo”
kafin yay magana wata yarinya Yar budurwa fara da akalla zatai 21yrs tafito daga kitchen din da
gudunta tana wani kalan mugun murna dudda akwai Aneesarh ajikinshi saida tazo ta gefenshi
tawani kalan rungumeshi tace “Abee Assalamu Alaykum” dan murmushi kadan yamata tareda
daga kanshi yakalli fuskanta yace “wa’alaikumus salam Kausar, ina dan kwalinki”? Yay
maganan yana kallon kanta dababu dan kwali tayi tsifa rabi tabar rabi, dan zaro idanu tayi
sannan tajuya da gudu tai sama binta yayi da kallo sannan yadawo da hankalinshi kan
kanwarshi yace “why is Aneesarh body hot”? Kaman Maman zatai kuka tace “wlh babu yanda
banyi da itaba takishan maganin Ya Imran” kallon fuskan Aneesarh yayi dake kan jikinshi daketa
kallon fuskanshi sannan yakalleta yace “kawomin maganin” dasauri tai sama tana murmushi
sosai bata taba ganin mutumin da yara ke bala’in so kuma suke tsoro kaman Ya Imran ba
dazaran yashigo kowa zai natsu sannan kowa yayta murna suna kallonshi saukowa tayi da
ibuprofen na yara a hannunta tazo har gabanshi ta tsaya ta bude maganin ta debamai a marfi
5ml tabashi tace “Allah sa tasha ni karma ta amayo makashi Ya Imran tabata maka jiki” karba
yayi sannan yakalli Aneesarh dake kallonshi yadan mata murmushi ahankali yace
“haaaaaammmm” yabude bakinshi kadan hakan yasa dasauri yarinyar tabude bakinta tace
“haaaaa” samata maganin yayi abaki ahankali with so much care and love kaman yana
handling Yar kwai dasauri yarinyar ta shanye murmushi yamata yace “good job Aneesarh” yay
maganan tareda sakata ajikinshi tai lamo yana caressing nata sannan yadago kanshi yakalli
mahaifiyarta dake kallonsu tana murmushi sosai yace “su Hajiya basu dawo daga gidan bikin
ba”? Gyadamai kai tayi tace “eh amman yanzun nan mukai waya suna hanya, harda Anty Binta
itama dazu ta iso da mijinta” gyadamata kai yayi batare dayace komiba hakan yasa tace
“nakawo maka tea ko coffee Yaya” girgiza mata kai yayi yace “no anjima” gyadamai kai tayi
sannan tajuya tawuce kitchen dan karasa girkin daidai nan itama Kausar ta sauko tana sanye
da hula tana kallon mahaifin nata tace “Abee nasaka” kallonta yayi sannan ya Gyadamata kai
tawuce kitchen tana murna Maman Aneesarh dake sauke tukunya daga kan wuta tace
“mehaka”? Dariya tayi takaraso kusada ita tace “murna nake Abee yadawo kinga zai tayani
karasa tsifan” hararanta Maman Aneesarh tayi tace “ke wai bakisan kin girma bako Kausar
kullum Babanki zai fita yaje aiki yadawo inhar yashigo gidan nan saikin sakashi yamiki naki aikin
bakiji abinda Hajiya tagaya miki bako kina wahalar mata da dand’a” turobaki tayi ashagwabe
tace “nikuma ai Babanane” yanda tayi abinma dariya yabama Maman Aneesarh tace “Allah ya
shiryeki ina Abdallah baitashi daga lectures din bane”? Dasauri Kausar tace “4-6 yakedashi aini
bazan iya Medicine ba ko kadan wlh wahalallen course” ahaka suka cigaba da hiransu suna
girkin gwanin ban sha’awa.
Yana rikeda Aneesarh a hannunshi yana caressing nata ahaka bacci yay awon gaba da ita,
haka yake inhar zai dauki yara su dan jima awajenshi duk rigiman yaro saiyayi bacci, tashi yayi
yana rungume da ita a kirjinshi har gaban kitchen din yaje batare daya shiga cikiba yace
“Kausar” dasauri Kausar dake kwashe shinkafa a flask tace “Na’am Abee” tasaki spoon din
tajuya tafice daga kitchen din dagudu ganin Abee agaban kitchen din rungume da Aneesarh
datai bacci yasa tace “Abee gani” ahankali yace “jeki kawo zani ki goyata” gyadamai kai tayi
dasauri tace “to” tabi tagefenshi tai bene tafara hawa dagudu anatse yace “what did Abee said
about running”? Daina gudun tayi dasauri tai piki piki da ido tace “no running” tana tafiya tai
sama bata jimaba tadauko zani tazo har gaban kitchen din ta duka gabanshi tace “Abee samin
ita” ahankali yazare ta daga kirjinshi sannan yasamata ita abaya ahankali tareda karban zanin
yadaura mata akai itakuma tamike tana gyara zanin tace “Abee goyon yayi”? Ahankali yana
kallonsu yace “eh” sannan yajuya yayi stairs yawuce sama itakuma Kausar tawuce tashiga
kitchen din suka cigaba da aiki.
Babban sama ne gidan akalla akwai dakuna dakuna sunkai kusan ashirin ko da biyar dan irin
babban family house din nan ne, asaman ma wani kebentaccen bangare yawuce da kofanshi
ke cikin lungu sannan yabude kofan dakin ahankali yashiga da sallama ko kadan dakin babu
wani hayaniya ko tarkace aciki lafiyayyen gadone aciki dake shimfide da white sheet ga white
bargo akai an gyarashi tsaf saikuma study da akayi agefe daya da shelf’s na bango dake cike
da littatafi sai desktop akan table da kujera saikuma wasu dakuna biyu wanda day bathroom ne
daya kuma closet, bathroom nashi yashiga wanka yayi sannan yafito yashiga closet ta shirya
cikin wata faran jallabiya mai haske agoge kar yana wani kalan kamshi yasaka wani farin hula
kwankwasa kaji hadisi din nan gemunshi na kyalli fuskanshi na annuri ga tabon salla ijiye
wayanshi yayi akan gado sannan tazura wasu flat takalma na gida yafito tun kafin yakai wajen
stairs yakejin hayaniyan su muryan Hajiya haryakai stairs yafara sauka yanabin kowa na falon
da kallo.
Wata har tsohuwar mata ce kan doguwan kujera tana sanye dawata atampa mai kyau anmata
dinkin bubu da zani irin dinki tsofaffi dai kana ganin matan kasan ta kwan biyu aduniya dan
akalla zatai 70yrs, saikuma wata mata dake zaune akan lallausan carpet akasa tana sanye da
lace na alfarma tana kasa su dibla da alkaki da nakiya a babban tray yaran duk sun zagayeta
kowa na Mama bani nawa, ga Maman Aneesar dakuma da Kausar suma kowa na jiran nashi,
ga wasu manyan mata biyu suma kana ganinsu kasan da mai rabon dasu duka yan uwa ne
Zainab da Sajida saikuma wasu maza dasuka zazzauna kan kujera suna danne dannen waya
kowannensu na sanye da shadda, yanda yake tafiya ko kadan bazakaji karan sahun tafiyanshi
ba amman kamshin turarenshi daya fara isowa falon yasa jikake falon yay tsit kowa yadago
kanshi yakalli stairs Anty Binta dake kasan su alkakin ne tai wani kalan murmushi tace “Yaya
Imran” dan murmushi kadan yayi anatse yace “Fatima ina mijinki”? Murmushi tamai tace “yaje
gidansu anjima zaizo” gayadamata kai yayi yakalli maza biyun dasuke azaune dazu daduk sun
tashi tsaye kowa kanshi akasa anatse sukace “Ya Imran ina wuni” gyadamusu kai yayi yace
“mutafi masallaci” sannan yajuyo da kanshi yakalli mahaifiyarshi da tunda yafito shi take kallo
ahankali yace “Hajiya barka da dawowa” ahankali tace “Imrana aiko su Umman Arif sunce
amaka godiya sosai sunyi murna” Anty Binta tace “eh wlh, musamman aka bamu Leda cike
dasu cincin da alkaki da nakiya da nama akace mu kawo maka, Sajida ina yake nashi”? Dasauri
Sajida tashiga kokarin bude wani jakan hannunta dan yatsine fuska yayi yace “baranci ba”
Hajiya tace “batun dazu nagaya muku Imrana bayacin duk ire iren shirmen nan ba saidai su Ibro
da Hamza kubama su Ibro wannan kusai kuraba wannan” tai maganan tana nuna kannenshi
dasukai gaba sannan tace “wai haryanzu jama’a jikana Abdallah bai dawo daga boko ba” Anty
Binta dake bama yara kasonsu tace “Hajiya nakirashi yana hanya” wucewa yayi yafice abinshi
hakan yasa Hajiya itama tamike ahankali tace “kuwuce kowa yaje yay salla” karasa bama yaran
nasu tayi itama Kausar ta karbi nata tawuce daki ta ijiyema su Abdallah da Ibro da Hamza nasu.
EPISODE 3️⃣
Koda aka idar da Magrib gyara zama yayi dan yaji ta’aleem wanda dama shi haka yake sai
bayan yay isha’i yake komawa gida, yana zaune inda yake wani yaro dan matashi haka dabazai
wuce 22yrs ba yay kamadashi kaman yay kaki yatofar yazo kusadashi ahankali ya zauna tareda
daura hannunshi kan nashi warmly yace “Abee” dagoda fuskanshi yayi yadaura akan fuskan
yaron asanyaye yace “Ya school”? Murmushi yaron yamai yace “fine Abee yanzun nan nadawo
nashigo masallaci dannai salla bari naje gida nai wanka naci abinci Abee I am hungry”
gyadamai kai Abee yayi hakan yasa yatashi tareda wucewa yafita daga masallaci mahaifin
nashi nabinshi da kallo ganin yanda gajiya ya nuna afuskanshi karara.
Sai bayan sallan isha’i sannan suka fito daga masallacin dashi da kannenshi biyun maza
Hamza da Ibro sai Abdallah, magana yayi da Ibro dazai wuce gidanshi dan