Showing 24001 words to 27000 words out of 108975 words

Chapter 9 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf

M Shakur   

09 Oct 2025

2820

tace “meke damunka eh Hydar? Duk wanda yasanka yana ganin Wanan
idanun naka yasan bakada lafiya, meke maka ciwo” tashi daga kan kujeran yayi yace “tunda
bazaki barni nai bacci ba bari na barmiki dakinki” yay maganan yay hanyar fita tana kwalamai
kira kaman badashi takeba, cikeda damuwa tace “ai idan bakaji nawa ba zakaji na ubanka, yaro
sai bakin zurfin ciki da shegen share mutane sabida yaga nadamu dashi” duk yanajin ta tana
surutunta bai amsata ba flat dinshi yawuce bude kofa yayi yashiga cikin dakin da babu abinda
yakeyi sai kamshi ko’ina a gyare kaman babu wanda ke zama adakin, bedroom nashi yawuce
yana shiga adaddafe yacire rigan yan sandan ya Yar anan kasan dakin sanan yazauna takalmin
kafanshi yacire yazaro wayanshi yadaura saman side drawer sanan ahankali ya kwanta
yanadan yatsine fuska bala’in ciwon kai yakeyi daya rasa na menene amman sai uban dauriya,
har bacci yasoma daukanshi yaji wayanshi na ringing da kyar yadaga hannunshi yakai wajen
wayan dauka yayi batare dayama kalli screen dinba yakai wayan kunne ahankali yace “Hello”
daga tachan bangaren muryan wani magidanci ne yace “Aliyu meke damunka?” Dan yatsine
fuska yayi yanaji kaman ya rufe Gwaggo da duka akan me zata fadiwa Abba dan gyara
muryanshi yayi yace “Abba I am fine” cikin rashin gamsuwa Abba yace “Aliyuuu” dagashi sai
Abba sukasan meaning din anytime yakirashi da Aliyuuu hakan yasa gently ya fuzar da dan
iska ahankali yace “Abba kaina hurts so bad” anatse Abba yace “is that all”? Ahankali yace “yes
Abba” “okay I am coming yanzun nan nadubaka” dasauri yace “no Abba I am fine kazauna
please zansha magani” dan jim Abba yayi yace “Aliyu haryau banga wanda yakaika tsanan
magani ba” sanin tsaf Abba zaibar hospital yazo yasa yace “Allah Abba zansha I promise”
cikeda gamsuwa dan yasan Aliyu baya promise yaki cikawa yace “okay kasha I will call Ogan ka
zance mai yabaka the rest of today da gobe kahuta, this work is draining you Aliyu banason shi,
anyway that will be another day talk, kasha maganin ka kwanta” ahankali yace “to Abba” Allah
kara sauki kaji gyadama Abba kai yayi tareda katse wayan, hannunshi yasa yajawo drawer

gefen gadon shi sanan yadauki paracetamol ya ballo guda biyu yana kallon maganin a
hannunshi kaman yay amai, yadade yana kallon maganin sanan yasa hannu yadauki goran
ruwan dake kan side drawer yabude kurba yayi sanan yajefa maganin da kyar ta hadiye sanan
yasa goran abaki saida yasha kusan duka ruwan sanan yaji maganin yatafi ahankali ya ijiye
goran kafin yakoma ya kwanta ya lumshe idanunshi bai wani dade ahakaba bacci ya kwasChe
shi.





1️⃣8️⃣


Free page
Wuraren 3 na rana yafarka, ahankali yake bude idanunshi yanabin dakin da kallo jin anrike
hannunshi yasa yajuyo da kanshi ahankali wata yar budurwa ce da zatakai 22yrs zaune gefen
gadon dake bala’in kama dashi kana ganinta kasan kanwanshi ce takama hannunshi gam tarike
tanadan gyangyadi, tana sanye da doguwan rigan atampa, Meena kenan he’s sure Gwaggo ce
tagayamata baida lafiya saisa tataho daga dawowanta daga school, dan murmushi yayi sanan
ya fizge hannunshi da karfi afirgice tabude idanunta takalleshi tana kara ware idanu tace “Ya
Hydar katashi sannu yajiki” hararanta yayi yace “meya kawoki dakina” cikeda damuwa tace
“yanzun nan muka dawo daga school muka tarar Gwaggo na kuka wai batada lafiya shine nazo
naga kana bacci, cha tayima na sata a keke nakawota wurinka nasan damunka kawai zatayi
saisa naki” dan jim yayi yace “jeki cemata tadena kuka I am fine” murmushi tayi sosai tana
kallonshi tana kokarin tashi dagakan gadon tace “Ya Hydar kanason Gwaggo amman kullum
fada kukeyi baka nuna mata kana sonta maisa” hanyar bathroom dinshi yawuce yace “kafin
nafito kibarmin daki inba hakaba jikinki zai gayamiki” tashi tayi ranta namata dadi ganinshi
lafiyanshi kalau tace “Ya Hydar zaka kaimu Jabi lake mall din? Kagama sai Gwaggo takara
yarda lafiyanka kalau ko” “go and get ready” yafadi murya chan kasa duk ya gaji yakosa tabar
dakin dansai sashi surutu take, shigewa bathroom din yayi abinshi yamaida kofan yarufe, tashi
tayi cikedajin dadi tai hanyar fita, sai yanzu tama lurada riganshi akasa dakin tsugunnawa tayi
tadauka sanan tamakalamai a hanger tabude wardrobe dinshi tasaka tawuce tafice danta
gayamusu su shirya.



Yadade abayin sanan yafito wani simple jallabiya yasaka yay salla sanan yatashi ahankali har
yanzu kanshi namai ciwo sosai daurewa kawai yake, shiryawa yayi cikin wani milk yadi mai
bala’in taushi danshi baya iyasaka kaya masu karfi, feffesa turare yayi sanan yadauki wayanshi
yana dubawa ganin baida miss calls yasa yafito yana tafiya one one, tundaga gaban kofan
dakin Gwaggo Meena ke kallonshi ganin yay wani kalan kyau tana murmushi ohh God duk
duniyan nan batada wanda takeso kaman Yayanta Hydar, hararanta yayi alamun kallon fa wuce

kigayamusu su shirya hakan yasa tawuce tashiga dakin Gwaggo tana kallon Gwaggo dataci
gayu itama tana zaune kan tabarman data shimfida akan lafiyayyen carpet din dake falon,
girgizakai kawai yayi baitaba ganin rigimammiyan tsohuwa irin Gwaggo ba, gatada carpet
amman tsabagen kauyanci saita shimfida tabarma akai, idanko yawone ko jikokin nata wani
zubin da gangan sukekin gayamata zasu fita dan tsohuwarnan Allah ya zubamata son zuwa
yawo kaman taci kafan kare.
Wasu yammata guda biyu ne zaune agefenta suma kyawawa dasu Amal dakuma Khadija duk
sunci gayu kansu daya, zama yayi abinshi Gwaggo tabishi dakallo bata kulashi ba shima bai
kalleta ba yakalli su Amal dake kallonshi suna gaidashi yace “kawomin abinci” tashi Amal tayi
dasauri zata fita yace “ina zaki”? Ahankali tace “falon Mami zani nadebo maka” girgiza mata kai
yayi yakalli fuskan Gwaggo yace “bani na Gwaggo” daure fuska Gwaggo tayi takalli Amal tace
“jeki uwardaka na abincinshi na cikin kula sabida ku na boye kafin ku cinye mai yara saikace
mayu barinma wanchan mai idanun kutaren” tanuna Meena tabe baki Meena tayi daga ita har
Khadija, Amal tawuce tadauko mai takawo, kafinma Gwaggo tai magana Khadija ta tashi
tadauko mai ruwa da drink daga fridge na Gwaggo ta kawomai bude abincin yayi dambu ne
lafiyayye yanasan dambu hakan yasa yaci ba laifi Gwaggo tana zaune tana kallonshi ganin
yadanji sauki yasa hankalinta ya kwanta sosai saida yagama ci sanan suka kwashe kayan sukai
kitchen dashi shikuma yafice suka biyoshi abaya suka fito Gwaggo natafiya ahankali dan
kafafun sun dawo a lallaba bata iya tafiya sosai saisa ko’ina za’aje da ita da keken guragun ta
tareda ita.


Mami suka gani a tsakar gida kan wani hadadden chair da table agabanta tadaura kafanta kan
table din Yar aikinta na gyaramata nails na kafa tana danna wayanta tana tauna cingum tana
murmushi, jin sahun tafiya yasa tadago kanta binsu tayida kallo tace “Hydar daga kannenka sai
Kakar ku kakeso nibaka sona saisa ba’a taba fita dani ba” tai maganan tana kallon Aliyu
dayamayi gaba abinshi kaman badashi akeba, kaman jira Gwaggo take taballamata harara tace
“akanme zai soki ke kika haifeshi jimini ikon Allah” dan dariya Mami tayi tai kara da cingum dinta
tace “Hajiya Gwaggo maida wukan a dawo lpy” “Mami mun tafi” yaran suka mata sallama,
“saikun dawo” Mami ta amsa yaranta tana murmushi tabisu da kallo tana hararan bayan
Gwaggo, saida sukai nisa sanan ahankali tace “Allah yakasheki mayyar tsohuwa kawai na huta,
mata takai kusan shekaru dari amman taki mutuwa” tana zaune tana kallonsu yaja mota suka
wuce sukabar gidan.



On a normal speed yake tuki yau danji yayi kanshi yasoma ciwo sosai amman yadaure dan
baiso Gwaggo tagane ballema tadamu, ahaka harsukakai jabi lake mall din wuraren 5:30.
Parking yayi wurin parking sanan suka fiffito, ganin yazauna aciki yasa Gwaggo tace “muje
mana” yatsine fuska yayi yafito yabude boot yaciro kekenta yana sata akai yace “zan jiraku
anan akwai wayoyin office dazanyi” yay maganan yana bama Meena ATM card dinshi yace
“idan kuka kararmin dakudi Abba zansa yabiyani da monthly allowance dinku” dariya sukayi
sanan Meena ta tura Gwaggo suka wuce tace “bye Ya Hydar” shiga mota yayi yazauna tareda

kwantar da kujeran yana kara karfin Ac sanan ya kwanta kanshi najuyawa ya tsani rashin lafiya
saisa baimaso ya kwanta ma wanan, ajiyan zuciya ya sauke ahankali yanaji zuciyanshi natashi
cikinshi najuyawa kaman zaiyi amai, jin amai yazomai dawani irin sauri ya yunkuro yabude kofa
yafito sai amai, kwaro amai yashigayi anan wajen motanshi sosai idanunshi sukai ja…..

Ahankali ita kadai take tafiya a parking lot din wayanta na kunnenta tana sauraron kwatancen
da Glory kemata na inda venue su yake acikin wajen, bakaramin kyau tayiba tana sanye dawani
english gown daya kaimata har kasa red yabi jikinta sosai ya bala’in fito da shape nata dudda
bawani kamata yayi ba amman sabida kalan yadin yasa yanayin jikinta yafito, fuskanta yay wani
kalan kyau yana glowing dudda bata shafa hoda ba dan ita hoda nasata kuraje a fuska saisa
tama daina sawa but ta gyara eyebrows dinta sanan tasa kwalli dayawani irin haska fararen
idanunta suka fito wallll, sai pink lipstick data kara kan pink lips dinta dayasa lips dinta yay wani
kalan crazy baby pink daya kara fito da fuskanta sosai, ta gyara gashinta daya gama hargitsewa
tai styling frontal hair din da gel dudda dama gashinta a kwance yake but karawa da gel datayi
yasa tai kyau fuskanta yafito sosai takawo wasu simple pearls earring silver tasaka, tayana light
peach karamin veil akanta dayadan zame kadan kasa sabida iskan da akeyi uwa za’ai ruwan
sama gashi bahadari just that garin is looking damn cozy, tasaka heel dayama kafanta kyau
silver dayafito da fine fine sexy toe nails dinta, tana tafiya ahankali tarataya wani karamin
handbag na LV a shoulder ta sai goran bottle water na Eva data rike tasha kadan aciki dan she
was thirty ahanya ma tasaya yanzun nan dazasuso.

Kaman daga sama taji kakarin amai na mutum chak ta tsaya at the same time taji kirjinta yawani
buga dum! Tsayawa tayi chak sanan ahankali tace “ok I am coming now nagane wurin” katse
wayan tayi sanan tajuyo tana kalle kallen inda take ganin bataga kowaba sai shiru dataji yasa
tacigaba da tafiya abinta, karajin kakarin amai datayi yasa tasake tsayawa chak ita kanta she
don’t even know why take tsayawa amman kaman something is pulling her, komawa baya
tashigayi ahankali tana waige waige kafin chan tahango wani Babban mutum dan that doesn’t
look like a small boy tsugunne in between wasu manyan jeeps guda biyu yabata baya yana
amai, tsigan jikinta taji yawani tashi, tun tana Yar karaman Yarinya ta tsani taga mutum naciwo,
part of the reason why kowa is her friend a school kenan inhar Khairy tasan u are sick to far she
die there Khairy is damn caring idan mutum naciwo saitamafi mai ciwon damuwa.


Takai almost 20second tsaye tana kallonshi yanda yake amai tsigan jikintai natashi tun yana
amai abu na fitowa har kawai amman yake babu abinda kefitowa, ahankali tadaga kafanta zata
wuce ta tafi samin kanta tayi dasake juyowa takalli bayanshi sanan takalli bottle water
hannunshi kafin ahankali tana tafiya gently tawuce lungun motoci adaidai bayanshi dab dashi ta
tsaya tana kallonshi bakinta nadan rawa dan tsoroma takeji mutum na amai tazo meruwanta
amman still tadaure ahankali tace “Sir do you want some help nakira maka security”? Batare
daya kalleta ba koyajuyo ba ya girgiza mata kai alamun no, jitayi zuciyanta yamata wani nauyi
kaman tai kuka tasake dukowa kanshi sosai anatse tace “but u are very very sick, do you want
some water, I have water, here gashi” tai maganan da sauri tana budemai goran ruwan tana

mikamai ta gaban fuskanshi, goran ruwan yabida kallo, murya chan ciki dabaya fitowa sosai
yace “thanks” goran tabida kallo ganin bai karba ba yasa ahankali tace “ka karba ka wanke
fuskan ka u will feel better, haka Mama kemin idan banda lafiya nai amai” jiyayi kanshi nawani
irin ciwo, azuciye yawani juyo da jajayen idanunshi dake cikeda zazzabi yawani taso kaman
zaki zai cinyeta baya tayi atsorace ruwan hannunta yafadi heel din kafanta ya turgude dawani
dutse hakan yasa kafanta ya turgude tai baya zata fadi atsorace hannu daya yasa ya chapko
hannunta dasauri yana kallon fuskanta da jajayen idanunshi kaman yanda itama a bala’in firgice
take kallon fuskanshi kirjinta nabugawa fast fast lips dintaI narawa sosai ganin police man
dinaCn ne.




1️⃣9️⃣



Cikinsu duka babu wanda ya iya wani motsi yana rikeda hannunta yana kallon fuskanta kaman
yanda take kallon nashi, ganin iska nawani irin kadawa sosai gyalen ta gabaki daya yay baya
iska na neman fizgeshi yay sama dashi yasa yay wani irin pulling dinta ta taso saura kiris tafada
kirjinshi da kyar ta iya maintaining posture dinta gabanta nafaduwa sosai tasauke idanunta
kasa, tundaga yatsunta datake wasa dasu tana yakushin riganta dasu yake kallo har zuwa
fuskanta da lips dinta dake rawa sosai zuwa gashinta dakeda bala’in kyau datai parking tai
donut da jelan gashin dayay yawa kana gani kasan tanada suma sosai gyalen na wuyanta,
ganin yanda ake iska sosai ta sandare awurin not her self yasa murya chan ciki yace “cover ur
hair” gyadamai kai tayi ahankali batare data kalleshi ba takai hannunta takamo gyalen daga
wuyanta zata yana akanta kwace gyalen iska yayi da karfi saikan fuskan Hydar dasauri tadago
kanta, ahankali ya lumshe idanunshi jin wani sassanyar kamshin da gyalenta ke fitarwa da
atake yaji ya kwantarmai da tashi da zuciyanshi keyi duk wani amai dayakeji yakoma, gently
yakai hannunshi yadaura akan fuskan nashi yadauki gyalen sanan ahankali yamika mata, kallon
fuskanshi tayi kafin ahankali takalli hannunshi dake dauke da gyalenta dayake mikamata sanan
tasa hannunta ahankali ta karba daidai wani kalan mugun ruwa sama ya sauko da karfinshi
dayama firgitata dasauri takalli sama sanan takalleshi kafin tajuya da sauri zata wuce.
“Ummulkhair!” Taji yakirata amugun natse dayasa taji gabanta yawani kalan fadi, tsayawa tayi
chak ruwan nadukanta sanan gently tajuyo takalleshi gani tayi yabude mata bayan jeep dinsu
shima yana tsaye ruwan na dukanshi, batasan mesa ba but kasa mai musu tayi ahankali ta tako
tazo har gabanshi sanan tashiga ciki ta zauna, bayan shima taga yashigo dasauri ta matsa
chan gefe yamaida kofan motan yarufe, daganan inda yake yadan mika hannu ya kunna motan
sanan ya kunna AC motan yadauki wani bottle water yadawo yazauna yadan bude kofan motan
kadan ya kuskure bakinshi kafin ahankali yamaido kofan yarufe sanan ya ijiye goran ruwan
akasa ya kwantar da kanshi yana sauke ijiyan zuciya ahankali dukansu suna sauraron yanda
ake ruwa da mugun karfi harda kankara ma.

Sunkai almost good 6min a motan babu wanda yacema wani wani abu kanta nakasa tana
fidgeting yatsunta, shikuma yana zaune gefenta kanshi naciwo amman kallonta yake kaman an
ijiyemai TV, ganin yanda ta takure tanajin sanyi sosai sabida ruwan dayadan daketa kadan
sanan ga sanyin AC motan daya kunna yasa ahankali yadan yunkuro hannunshi yamika ya
kashe AC sanan yadauki jacket dinshi na kayan yan sanda that is always acikin motan sanan
ahankali yawarware shi matsowa yayi kusada ita yana kallon fuskanta bala’in firgitata tayi jin
mutum kusada ita sosai dayasa takalleshi dasauri kallonta shima yake ko kyafta idanu bayayi
ahankali yadaura mata jacket din kan kafadanta yarufamata shi da kyau yana kallonta kaman
yanda take kallonshi tana nishi da sauri da sauri dayakejin hucinshi akan fuskanshi sanan
yadan matsa baya zai koma wurin dayake da zama kaman daga sama ahankali murya chan
kasa fa inda ace akwai mutum na uku amotan nan bazai tabajin metace ba tace “u are sick”
kallon kwayan idanunta yayi kaman baigane metace ba, gyadamai kai tayi idanunta sun cika da
kwalla sosai ahankali tace “wlh bakada lafiya, ur body is hot, let’s go to the hospital please” tana
karasa maganan hawaye ya gangaro mata daga idanu sharrrr, hawayen yabi da kallo kaman
wanda baitaba ganin mace tai kuka ba, murya chan kasa batare daya koma ba he’s still very
much close to her ahankali yace “you don’t want me to be sick” gyadamai kai tayi ahankali wasu
sababbin hawayen nakara taruwa a idanunta, murya chan chan ciki yana kallon kwayan idanun
nata dasukenan farare fat kaman farin gajimare yace “why”? Girgizamai kai tayi saikuma
ahankali tace “I don’t know, seeing u sick is making my heart to hurt” dan lunshe idanu kadan
yayi sanan yabude su yadaura akan nata, lips dinshi sukai motsi kaman whistling yana kallon
yanda take kuka mara sauti yace “stop crying” gyadamai kai tayi ahankali tana kokarin tsayar da
hawayen, hannunshi yasa yaciro handky daga aljihunshi yamikama mata yace “here” karba tayi
takai kan fuskanta tana goge hawayen saida yaga tagoge tass sanan yakoma gefenta yazauna
da kyau yace “mekikazo yi anan?” ahankali tace “today is Glory’s birthday my friend she’s
celebrating it anan” dan juyowa yayi yakalleta kaman mai nazarin wani abu yace “how old are
you” kallonshi itama tayi kafin tasauke kanta ahankali tace “20” kaman daga sama taji yace
“small Gurl” dawani irin sauri takalleshi tabe baki taga yayi batasan mesa ba abin saiya bala’in
bata dariya she don’t even know why, dan murmushi kadan tayi sanan tahadiye shi kallonta yayi
ganin yanda dimples dinta keta lotsewa alamun murmushi take amman tana hadiyeshi, kaman
daga sama taji yasake jefo mata tambayata anatse. “Are you in any relationship”? Dasauri
takalleshi, kallonta shima yayi fuskanshi looking he’s serious da tambayan, murya chan kasa
yace “kinada any man dakikeso…..or yake sonki”? Yay maganan muryanshi na breaking cus
shi kanshi baisan mesa yakema tambayanta this kind of wired question ba, dauke kanta tayi,
sanan ahankali ta girgiza mai kai alamun no, dan murmushi kadan yayi yanajin duk wani ciwon
kan dayakeji yana tafiya, jakanta dake in between them yasa hannu yadauka yabude wayanta
yaciro Dasauri takalleshi numbershi yasaka sanan yakira kanshi, danne danne taga yanayi
awayanta kafin yamaida ya ijiye cikin jakan, ganin ruwa na tsagaitawa yasa tadan kalleshi
ahankali tace “zantafi” yana kallonta right in the eye yace “where is ur driver? U should head
home” gyadamai kai tayi sanan ahankali tace “yanata chan bangaren” inda take nunamai da
hannu yakalla, ahankali yace “ok” bude kofa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login