Showing 84001 words to 87000 words out of 108975 words
Chapter 29 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf
zoki kaimai furanshi flat dinshi kidawo” kallon
Gwaggo tayi dasauri hakanan taji gabanta nafaduwa kwaryan furan Gwaggo tabata data rufe
ahankali takarba tana kallon Gwaggo, Gwaggo tace “wuce ki kaimai tunda yadawo baici komi
ba yanzu ma da kyar nasamu yace zai sha furan, tafi kafin yay fushi” Gyadamata kai tasake yi
sanan ahankali tajuya jikinta rawa yake sosai tafice daga dakin tai flat din Ya Aliyun kirjinta na
bugawa more the more she’s getting closer to flat din, tsayawa tayi agaban kofan takasa motsi
ahankali tadaga hannunta knocking kofar tayi shiru babu wanda ya amsa babu wanda yabude
mata takai kusan 3min ahaka sanan kaman wacce tazo sata tasa hannunta tabude kofan
ahankali tana kallon falon ganin bataga kowa ciki ba yasa ahankali tashiga cikin falon dakenan
sanyin Ac mix da kamshin turarenshi, ahankali takai kwaryan furan kan centre table na dakin
tsugunnawa tayi ta ijiye sanan tamike tsaye dasauri tajuya zatai kofa tafice kaman daga sama
taji muryan Ya Aliyu yakirata. “You!” Chak ta tsaya batare daya juyoba gabanta nafaduwa sosai,
cikin wata kalan murya da she will define it more of hatred voice yace “zokidau abinda kika ijiye
and take it out” gyadamai kai tayi ahankali sanan tajuyo batare datama iya dagakai takalleshi
balle tamasan daga ina yakamata maganan ba sanan tazo ahankali ta taugunna tadauki furan
sanan tamike tsaye. “Next time idan tanason naci kome tamin tabama wani yakawomin not you”
wani irin sanyi jikinta yayi dasauri tadaga idanunta dasuka wani cikeda hawaye ganinshi tayi
yana tafiya akan stairs zai koma sama bakinta harwani rawa rawa yake tace “Ya…..Ali….yu”
chak ya tsaya batare daya juyo yakalleta ba, ahankali takai dayan hannunta dat is very tashare
hawayen dasuka zubomata sanan gently tace “Ya Aliyu I am sorry, dan Allah kayafemin”
6️⃣3️⃣
Wucewa sama taga yayi abinshi batare daya juyo yakalleta ba, tadade tsaye awajen sanan
ahankali tajuya tafice daga dakin rikeda kwaryan furan jitayi babu abinda kemata dadi, dakin
Gwaggo tashiga ganinta da kwaryan furan yasa Gwaggo tace “ya shanye”? Girgixama Gwaggo
kai tayi tace “yace bazai sha ba” cikeda masifa Gwaggo tace “shiya sani ijiye kije kihuta abinki
kinji” ijiyewa tayi sanan tawuce dakinta tana shiga tafada kan gado kwanciya tayi dasauri
tafashe da kuka sosai murya chan kasa tace “he hates me, he hates me” tama rasa mezatayi
wayanta da Gwaggo ta ijiye mata akan gado ta dauka sanan tai dialing number Batool tana kira
tadauka tace “maiya sameki dazu naji kinyi ihu haka faduwa kikayi” kasa magana tayi kawai
tafashe da kuka cikin kuka sosai tace “Batool Ya Aliyu yadawo ya tsaneni sosai, Batool I don’t
even know what to do dan Allah help me, kinji” yanda taji tana kuka yasa Batool tace “batun
yauba bayan kin bani labari what u told him nagayamiki kinyi kuskure Khairy that’s not how to
make him rabu dake, but that one now is bygone, yariga yafaru Khairy rana daya so baya
komawa yazama ki, bansan Aliyun kiba kene kika sanshi, kinsha bani labarin fushin shi da
Kishin shi, Aliyu na sonki har gobe har jibi so ma mai karfi kuwa, you should just be diplomatic
about it, kinunamai kin waye u are a graduate, cikin sauki kija ra’ayinshi make him come for you
batare dayasan he’s even coming for you ba, you know his weak point, karki bada mata please,
zan turamiki number M shakur kibiya kudi ki shiga group din matan aurenta kiga yanda ake
karkato da hankalin muji mai taurin kai stop crying kinji kiyi wanka pray kije ki nemi abinda
zakici” gyadama Batool kai tayi ahankali murya chan kasa tace “thank you” katse wayan Batool
tayi hakan yasa ta ijiye wayan share hawayenta tayi tass sanan tasauka daga kan gadon,
ahankali tawuce bayi bayan tacire kaya tana kallon kalaban da akamata dasukai bala’in kyau
kaman anmata kafin attachment nan ko gashinta ne, hannunta tanunama madubi ta kalla shima
yayi kyau sosai sanan tawuce tai wanka tadauro alwala tafito daure da towel akirji tabude
wardrobe wani rigan bacci pink tasaka daya saukan mata zuwa guiwanta, rigan bacci yazo
dawani open cap dinshi hakan yasa ta ijiye cap don kan gado tahau kan dadduma tai sallan
magrib, tana idarwa wayanta tadauka takira Ya Maheer sunata hira sai wajen isha’i sanan sukai
sallama ta tashi tai sallan isha’i, jin cikinta na kuka dan saida yanzu ta tuna tun wainan safe
bata sakecin wani abu ba yasa ta tashi hulan kayan baccin tadauka tasaka ipen cap ne hakan
yasa duka gashinta yazubo gadon bayanta, tai kaman wata Cinderella, silipas dinta na gida
tazura akafa sanan tabude kofa tafito ko kadan batasan Aliyu na falon ba saida tafito falon, da
kallonshi kadan tayi tadauke kanta dasauri sai yanzu nema taga fuskanshi woww! Wlh kaga Ya
Aliyu zaka dauka balarabe ne gashin gemunshi da sajenshi sundan kara yawa kadan daya
haskaka fuskanshi, yana kwance kan dogon kujera waya a kunnenshi yana magana ahankali,
kallo daya tamai tadauke kai dasauri Gwaggo dake binta da kallo tace “indomie ko Khairiya”?
dan murmushi tayi akunyace dayar karaman muryanta tace “Gwaggo Kwai zan soya” tai
maganan zata shiga ciki dan kunya takeji Ya Aliyu yaganta ahaka daga ita sai Yar rigan baccin
da pant da tasaka aciki ko bra bata sakaba, ganin zata komaciki yasa Gwaggo tace “ina kuma
zaki yoo ba kitchen zakiba tundake bakicin abincin da normal mutane keci” ahankali tace
“Gwaggo hijabi zan dauko” baki Gwaggo tasaki tace “yau kuma nikike sama hijabin koko mijin
naki Hydar, wuce kitchen kije kinemi abinci kisama cikin ki kafin ciwon yunwa yakamaki”
gyadama Gwaggo kai tayi sanan ahankali tafito tawuce feeling so uncomfortable tana tafiya
kafafunta na harhardewa, daga inda yake kwance dudda waya yake but all abubuwan da
Gwaggo kefadi yanaji, kasa hana kanshi yayi yakalleta dan satan kallonta yayi sanan yamaida
kanshi kan wayan dan bayason yana kallonta motsamai da soyayyanta yake aranshi, juyowa
Gwaggo tayi tana kallonshi cikeda korafi tace “ni babanka yamazo yay maganan bikinku akaita
chan gidanka, yarinya batacin abinci salon wani abu yasameta ace nine bana bata abinci Iyye ni
wlh banajin dadin wanan lamarin ko kadan, tun safe fa waina biyu kawai taci bata karacin wani
abu ba” kofan da aka bude yasa tajuyo ganin Meena ne yasa ta watsa mata harara tace
“munafuka dayake yayanki yadawo dole na ganki a bangarena to fita” dariya Meena tayi tashigo
wata kyakkyawan budurwa dake kama da Mami biyeda ita tace “Hajo tazo hutu gidanmu shine
fa nakawota ta gaidaki, Mami tahanamu dafa indomie a kitchen dinta shine mukazo mudafa
anan” tai maganan Meena na zama kusada Ya Aliyu da gama wayanshi kenan yana kallon
Meena, Hajo datadan saci kallon Aliyu tashigo tana gaida Gwaggo da Ya Aliyu dabai amsata
bama sai tambayan Meena su Amal dayake tacemai sunyi bacci sanan ta tashi takalli Meena
tace “zomuje mudafa” wucewa kitchen din sukayi Gwaggo na ihu karsu bata mata kitchen ganin
Khairy a kitchen tana soya kokarin soya egg guda daya tahada tea a mug tana juyawa da cokali
yasa Meena tajuya cikedajin haushi tace “zomuje” dasauri Hajo takalli Khairy da itama kallonsu
taje batare data kulasu ba tace “akan mene muda kitchen din gidanmu zamu tafi” dan tana
ganin Khairy tagane matan Ya Aliyu ce dantaga video bikin da akayi a gidan nan, wucewa
Meena tayi tafice tace “to nidai ina falo kika dafa saiki kawo mana muci” tai tafiyanta itakuma
Hajo tashigo kitchen din tana daukan tukunya daya dan tara ruwa tana habaici, “adai gama
yawo da kaya babu breziya bazamu so mutum ba, dazu inaji rokonshi ake yama zauna da ita
yanaki aikin banza” tafashe dawani makirin dariya, dudda maganan ya sosama Ummulkhairy rai
batace komiba besides bamatasan waye yarinyar ba, juya kwanta tayi sanan tawuce tadauko
plate tazo ta kwashe itakuma Hajo tadaura ruwa agas din tanabin Ummulkhairy kallo da gefen
ido ganin yanda yarinyar keda shape dakuma diri ga kirji kaman zasu fasa riga atsaye fam dasu
hada komi Ummulkhairy tayi a tray tazo zata wuce da gangan Hajo tazo dabaya dabaya kaman
mai neman abu ta bangaje Ummulkhairy da saura kadan tafadi tai maza ta dafa fridge dinsu
amman gabaki dayan tray da kwan ta dakuma shayinta saida yazube akasa da tray abin suka
hadu sukai wani bala’in kara dayasa Gwaggo tai ihu daga falo tace “meya faru wayamin bari a
kitchen!” Takalli Aliyu tace “dubomin kitchen dina dan Allah”
Wani irin dago kai Khairy tayi zuciyanta na tafarfasa sabida bacin rai ta kalli Hajo, wani irin
makirin murmushi Hajo tasakin mata tace “oops my bad” ji Ummulkhairy tayi tazo wuya dawani
sauri ta yunkuro zata dauramata mari akunci. “Ummulkhair!” Taji muryan Aliyu daga bakin
kitchen din yakirata, juyowa tayi takalleshi da idanunta dasukai ja sosai, kafinma yay magana
ganinshi yasa Hajo tai kwabkwab da fuska kaman zatai kuka tace “Ya Aliyu sabida nazo na
kunna gas kusada ita taketa zagina shine garin bangajeni tazubar da abinda datafa shine kuma
zata maran, what is wrong with her” Dawani irin sauri Ummulkhairy tajuya tai kanta tace
“nikikema karya”? Takai hannunta zata chakumeta cikin fushi Aliyu yashigo kitchen din Khairy
ya kalla yadaka mata tsawa yace “ke wace irin mara tarbiya ce, why do you look for trouble?
Get out of this kitchen, out!” Dawani irin sauri takalleshi jin yanda yadaka mata tsawa, daure
fuska tamau yayi yana kallonta, jitayi kuka na zuwan mata amman ta daure wlh ba zatayi ba
agaban yarinyar nan ba kuma wlh idan bataci uban uarinyar nan agidan nan ba ba sunanta
Ummulkhairy ba, ahankali tajuya zata fice, fashewa da kuka Hajo tayi tace “Ya Aliyu batacemin
sorry ba” batare daya kalleta ba yace “come back here and say sorry” chak Ummulkhairy ta
tsaya bura’uba tsanan haryakai haka juyowa tayi da kanta ta kalleshi ido na cikin ido batare
data kalli Hajjo ba, ahankali tace “sorry” sanan tajuya dasauri tafice Gwaggo dake zaune ganin
Khairy tafito dagudu yasa tace “menene me aka miki?” tama kasa amsa Gwaggo dakinta tayi da
gudu tamaida kofa tarufe tafada gado tana kuka.
Ahankali yasauke ijiyan zuciya yabi tea ta da kwan data soya da duk suka bare a kitchen din da
kallo, yasan cewa he hates her bayamason yanasa idanunshi akanta dan the more he’s looking
at her the more yana tuna abinda tamai amman jiyayi bazai iya yabari ta kwana batare dataci
abinci ba.
“Ya Aliyu nadafa indomie dakai”? Kaman daga sama muryan Hajo yadaki kunenshi juyowa yayi
yazuba mata mugayen eye dinshi dayasa taji zuciyanta yabada ras! Cikin kakkausan murya
strictly yace “this should be the first and last time dazaki shiga harkan matata, off this gas get a
mop and clean this mess kibar flat din nan” gyadamai kai tayi ahankali sanan yawuce yafita
daga kitchen din yafito falo daidai Gwaggo nafitowa daga ciki tace “mekuka ma Khairiya take
kuka”? Dauke kai yayi yana kwanciya yace “bansani ba” daidai Hajo nafitowa daga kitchen din
bayan tagama abubuwan dayasata tayi ganin babu Meena ma afalon yasa tasan tawuce side
din Mami, cikeda masifa Gwaggo tace “dan ubanki kika kara dawomin daki saina maidake
gurguwa fita” fita tawuce tayi Gwaggo ta ballama Aliyu harara tace “kaima wuce kafita bacci
zanyi” akufule yace “saiki zo kifitar dani” tsaki Gwaggo tamai ta tashi tashiga ciki tace “kaiyita
zama karube anan mai bakin hali” tawuce dakinta tashige ta kwanta kan gadonta ranta abace
akanbar shikadai afalon.
6️⃣4️⃣
Shi baimasan mesa yama damu dabataci abinci ba taje ta kwanta, dan gajeren tsaki yaja sanan
yatashi tsaye yawuce corridor yashiga yana kallon dakin Gwaggo da wuta kenan kunne, hannu
yasa yadan daga labule ganin Gwaggo yayi kan gadon kauyenta dan haka suke kiran gadonta
babu yanda basuyi da itaba Dad ya chanza mata gadon nan ba amman taki tamakalema gadon
kaman mayya tana kwance share share tana bacci tabude baki tana minshari nada kara sosai
hararanta Aliyu yayi yasaki labulen ahankali yace “fitinanniyan tsohuwa” sanan yakalli kofan
dakin da Khairy keci dakenan akulle dan jim yayi yana kallon dakin kaman wanda aka ingiza
yawuce gaban dakin ya tsaya yay shiru yana kallon kofan kafin ahankali kaman barawo yasa
hannu yabude kofan ahankali wani kalan cool kamshinta ne mai bala’in dadi yadaki hancinshi
dasaida yasa yasauke ijiyan zuciya ya lumshe idanu tareda budewa sanan ahankali yasa kafan
damanshi sanan yashiga dakin dakenan da duhu yasa hannunshi ahankali yakunna wutan
dakin yanabin ko’ina na dakin da kallo dayake nan tsaf tsaf very clean a tidy kafin ahankali
yasauke idanunshi kanta, tundaga kan kafafunta yake kallonta sai yanzu yakema kallon kafan
da kyau da jan lallen yamai kyau kaman yaje yashafa, dogayen kafafunta very fresh yabida
kallo harzuwa kan cinyanta kafin idanunshi yasauka kan cikinta dayay flat pas kaman bata
tabacin abinci ba gently yasauke idanunshi kan boobs dinta he knows yanason Ummulkhairy
but baitaba tsayawa yamata kallon kurilla ba sai yau sabida yau yasan halas yake kallo, baitaba
sanin she’s this booby ba sai yau wani kalan ijiyan zuciya yasauke bashiri sanan yakalli
fuskanta she’s sleeping peacefully da dan ragowan hawaye a idanunta kitson kalaban datayi
duk sun zubo gaban fuskanta kaman yadauketa yagudu yakeji tafin hannunta yakalla dayaga
lalle sunma hannunta kyau wayanta dake side drawer dayay vibrating yay wajen yana tafiya
without making sound screen din wayan yakalla messege yagani daga Batool.
“Kinsamu kinyi apologyzing din” hannunshi yasa yadauki wayan ahankali sanan yabude yana
karanta all messages datakema Batool din tun bayan aure, daga tace takasa daina tunaninshi
batasan halin dayake ciki ba no body is saying anything to her saikuma messege datama Batool
nacewa Gwaggo da Dad kadai kesonta, Meena hate her waita yaudari Yayanta, Mami kuma
doesn’t even look at her zare idanunshi yayi daga wayan yakalli fuskanta sonta har tsakiyan
bargon kashinshi yakeji but at the same time yakasa dainajin haushi ta da tsananta on
abubuwan data fadimai kan Zayn is just like abu biyu na dambe azuciyanshi SO da TSANA,
saida yagama bincika wayan nata tass sanan ya ijiye yakalleta.
“Ke!” Yadaka mata tsawa daga inda yake tsaye akanta ko kadan batamayi motsi ba, dan
gajeren tsaki yaja sanan yakai hannunshi ya bubbuga filonta tareda kiran sunanta da karfi.
“Ummulkhair” wani irin firgita tayi tawani taso saura kadan ta tumbulo daga gadon yatareta da
hannunshi dawani irin sauri takalleshi idanunta sundanyi ja na nuna alamun bacci acikinsu,
hannunshi yadan kalla yanda ta rirrikeshi kaman zata shige jikinshi ganin tafarka daga baccin
tass yasa yadaure fuska yace “cikani” ahankali tazare hannayen ta da jikinta daga nashi tana
komawa baya sanan taja bargo tana kokarin rufe jikinta zuwa kirjinta, dauke kai yayi batare
daya kalleta ba yace “go and find something a eat, nobody sleeps with hunger agidan nan stand
up” wani abu taji yazo mata wuya hakan yasa takalleshi ganin ko kallonta bayayi yama dauke
fuska ne yasa ahankali tasaki bargon ta tashi daga kan gadon wardrobe tabude tadauko wani
doguwan rigan boubou sanan tashiga bathroom dagudu jin tabude kofan bathroom yasa yajuyo
yakalli kofan bathroom din, bude kofan tayi ahankali tafito kampala boubou yamata wani kyau
ajiki tama manta babu Dan kwali akanta ta gefenshi tabi tabude kofan dakin tafice yajuya tail
yana kallonta kaman baitaba ganinta ba yadade tsaye awajen sanan yawuce yafita daga dakin
yadawo falo a dinning yaganta zaune tazuba wani dan karamin rice tasa spoon tana kallo
batare datama tababa.
Dan jim yayi sanan yataho batare dayace mata komi ba yabude flask na rice don dayake nan
da zafinshi yadebo yakara mata akai abincin takalla sai kawai tashiga raira kuka ahankali,
wucewa da sauri yayi yawuce falo yay kwanciyanshi akan kujera tadade tana rera kukan sanan
tagoge fuskanta tadauki spoon tashiga cin abincin tana turo baki baisan ya akayi ba samin
kanshi yayi da ciro wayanshi daga aljihu ya danna video yana mata tanacin abinci tana turo baki
tana goge hawaye da bayan hannu kamna irin kananun yaran nan da aka tursasa suci abinci
yana wajen yana mata video har saida ta cinye sanan tazuba ruwa a cup tasha batare daya
kalleshi ba ta tashi daga dinning din fuuuu tai ciki samin kanshi yayi da dan murmushi sanan ya
tashi daga kan kujeran yay wajen dinning din yana kallon plate din da cokalin dake plate din
data bari awajen samin kanshi yayi da bude warmer yadebo rice shima yazuba plate din sanan
yadauki spoon dinta yadebi rice din yakai bakinshi yayi dan murmushi daidai wayanshi na
vibrating kafin ma yakalla yasan dad ne hakan yasa yatashi yadauki plate na abincin yafita daga
daga flat din Gwaggo yanaci zuwa flat din su Mami Dad ne kadai zaune a falo glass a idanunshi
yana wasu yan ruCbuce rubuce.
6️⃣5️⃣
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.
wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp
This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp
number na 07012181461
Thank u❤️
Ganin Aliyu yasa ya ijiye komi yature yana kallon plate na abincin hannunshi yace “sai yanzu
kake dinner Aliyu” gyadamai kai yayi yana zama kusada Baban nashi ahankali, yace “Dad ina
yini” Dad na kallonshi yace “how are you”? Abincin ya ijiye ahankali sanan yace “am fine Dad”
shiru Baban yayi yana kallonshi sanan anatse yace “Aliyu kadawo don’t you think yakamata
kamin magana” dan shiru yayi yasan mai Dad kefadi kafin ahankali ya yatsine fuska murya
chan kasa yace “Dad I told you I don’t like her again” shiru Baban yayi yana kallonshi kana
ganin yanda yake magana kasan karya yakema kanshi abinma saida yasa Dad yadan murmusa
yace “duk fushin nan dakakeyi naka na banza ne, ranan dakadan bude idanunka dana sanar da
kai na aura maka Ummulkhairy daga ranan kafara jin sauki, koda kaga nadawo na barka
dakacemin ba yanzu zaka dawo ba I just leave you ne dan nasan you need time to clear your
head dan haka Aliyu bikinku nan da 3weeks” dan zaro idanu yayi yana kallon Dad, mugun kallo