Showing 36001 words to 39000 words out of 108975 words

Chapter 13 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf

M Shakur   

09 Oct 2025

2846

addu’a tasan tabar ya tagari aduniyan nan muje
mukaita makwancinta, your mum is tired she need rest, go and pray for your mum” ahankali
Khairy tasake matsawa kusada Mama she can’t believe Mama ne nan kasa addu’an tayi sai
kuka ahankali tace “Mama dan Allah dagaske wai kin rasu?”, zuwa yayyinta sukayi kawai
rungumeta ahankali Manaf yace “Mama tarasu Khairy pray for her” Ahankali tace “Mama Allah

yajikanki Allah ya gafarta miki, Mama why did u leave me, shikenan bazan kara ganin ki ba,
Mama maisa baki bari na rokeki kiyafemin ba, kullum ina cikin batamiki rai inta rashin ji, Mama
Tayaya zan cigaba da rayuwa baki aciki Mama Innalillahi wa Innailaihi raji’un” tashi Baba yayi
ahankali hakama Baffa dasu Ya Hassan da Hafiz dakuma Zayn zasu dauki Mama dan kaita
waje salla, wani Zabura tayi zata tashi dasauri Manaf yariketa, Mom yabama ita tana wani kalan
nishi hannu Mom tasa takarbi inhaler ta tace “Khairy Khairy” kaman zata haukace haka takeji da
kyar ta iya kallon Mom tace “Mom na shiga uku, Mom Mama tarasu Innalillahi wa innailaihi
raji’un, Mom wlh wlh ko….” kawai maganan yakakare takara suma, ruwa Mom tashafa mata a
fuska tanamata addu’a, tafarfado ta sume tai having Asma attack haka tadingayi ahaka har
akama Mama salla aka tafi da ita, Khairy bamatasan inda kanta yakeba tana jikin Mom, jikinta
yay wani mahaukacin zafi dayasa Mom takalli Ammi dake zaune tanajan charbi tace “Hajiya kira
Alhaji Dr yazo jikinta yay zafi dayawa, kuma suman nan datakeyi yay yawa” dan jim Ammi tayi
sanan tadauki wayanta takira Baffa ta sanar dashi.


Bayan magrib Baba yashigo gidan tareda Baffa gaisawa yayi da matan dake falo dakemai
gaisuwa sanan suka taho sama tundaga stairs yake kallon Khairy dake kwance akasa gatanan
gatanan ne kawai baa cewa komi, tsugunnawa Baba yayi agabanta ahankali yadagota sharaf ta
taso Mom yakalla yace “tayi salla kuwa”? Girgizamai kai Mom tayi, Baba zaiyi magana kawai
tasaki wani sabon kuka mai bala’in tabarai dayasa kowa na dakin yazuba mata idanu tana taba
zuciyanta kaman ta mutu takeji, kaman tai hauka takeji, kaman tadawo da hannun agogo baya
takeji tama Mama duk abinda takeso batare datasa Mama fushi ba, duk su Baba magana suke
mata amman harga Allah bata gane komi kunenta ma yadode, duk suna zaune ahaka tai kuka
ta sume tadawo Dr yashigo gidan, allura kawai yamata aka samu tai bacci, Baba zai dagata Dr
yace “ku kawo bargo kurufa mata, let her sleep anan” Baffa da kanshi yashiga dakinta pink
bargonta da filonta yadauko yakawo Baba yakarba yasamata akarkashin kai sanan yarufa mata
bargon yana kallonta yana kafin yasa hannunshi yacire rolling gyalen dake kanta ya ijiye gyalen
agefe long kalaban ta suka bayyana duk akai shiru.


Hayowa saman sukayi duka yaran Hafiz na rike da jakanta daya dauko daga motanshi Dan
dazu amotar tabari dakinta yabude ya shiga ya ijiye sanan yafito yasamu gefe daya yazauna
afalon, suma su Hassan da Manaf suka zazzauna, ahankali Zayn ke hayowa stairs din da duk
yay wani irin tsayawama waje yayi yin wata waya saisa bai shigo tareda kannen nashi
ba,hayowa yayi kallo daya yama Khairy dake bacci akasa da aka lullube da pink bargo yadauke
kai sanan yawuce gefen Ammin shi yazauna akasa tareda daura kanshi kan cinyanta hakan
yasa tadaura hannunta ahankali tana shafa kanshi, kallon yaran Baffa yayi yace “kutashi kutafi
gida mu muna nan” cikinsu duka babu wanda yay motsi, ahankali Ammi dake shafa kan Zayn
tace “Son tashi katafi gida kahuta yau ka dawo daga tafiya” girgiza mata kai yayi ahankali yace
“I don’t wanna go Ammi” kallon Hafiz Baba yayi yace “wuce katafi gidan ka Hafiz” girgiza kai
yayi shima yace “Baba ai basu kadai bane kanwarta damai mata wanka duk suna nan” addu’a
Baffa yayi dukansu sanan aka shafa, aka zauna turus duk wanda yaga su Baba da yaranshi
saiya tausaya musu abinda kuma yahana yaran Baffa tafiya kenan Dan idan suka tafi gidan zai

musu wani iri kai mutuwa batada dadi! Baba da Baffa sauka falon kasa sukayi sukuma yaran
duk suna wajen kusan ahaka bacci ya kwashe kowa daga Ammi da Mom da duk suke kan
kujera zuwa su Manaf dake bacci rabi rabi falon yarage only Zayn ne baiyi bacci ba dayake
tattaba wayanshi maganan da Baffa da Baba keyi akasa yanaji.

Motsin da Khairy tayi cikin bacci yasa yajanye kanshi daga waya yazuba mata idanunshi kusan
sai yanzu nema yake mata a very good kallo tunda yazo, hawaye yaga suna gangarowa daga
gefen idanunta pink lips dinta na motsi sosai cikin bacci ta kankame pink bargon da aka
lullubeta dashi tana maganganu da kana gani kasan mafarki take. “Mama Mama wai kin mutu?
Ai baki mutu ba ko, bansan menama su Baffa dasukemin karya ba, Mama zansha madara, in
dauka, Mama Mama Maaaaa….” Wani dogon ijiyan zuciya tasauke na kuka kalabanta daya na
saukowa kan fuskanta, dauke kai yayi daga kallonta shi dabama danta ba mutuwan yajishi balle
yaran data haifa, he can’t even imagine loosing Ammi God no please, Allah ya sassauta musu
koma mesukeji a zukatan su.


Wuraren 4 daidai tabude idanunta daga kwance datake tana kallon saman dakin da kallo, the
first thing daya fado brain nata is mutuwan Mama, ajiyan zuciya tasauke tana assuring kanta
cewa mafarki ne tayi, juyoda kanta tayi tabi kowa na dakin da kallo, Hafiz nakan kujera yatakure
yana bacci, Ya Manaf na zaune shima kan kujera yana bacci, Ya Mu’az ma haka Maheer ne
kadai akasa yana bacci, sai Zayn da kanshi kekan kafan Ammi yana bacci shima kaman wani
auta, Mom dake saitin inda take akan kujera tana bacci itama ta kalla ajiyan zuciya ta sauke
zuciyanta na tsinkewa but she’s still in disbelief, bargon jikinta ya yaye ahankali sanan tamike
tsaye da kyar cikinta namata wani irin ciwo na yunwa dan jiya all through babu abinda tasa
abaka, tadade tsaye tana rikeda cikinta kafin ahankali tafara tafiya jelan kalaban kanta na lilo
abayanta tai hanyar dakin Mama, ahankali tasa hannunta tabude kofan kaman a kunnen Zayn
danshi baida nauyin bacci hakanan any movement kodan kara daza’ayi yana tashinshi da sauri
yajuyo da kanshi yakalli kofan tana tsaye bakin kofa tarike handle na kofan da hannu tana
kallon cikin dakin gashinta na lilo.


Ko’ina na dakin takebi da kallo idanunta namata gizo daga taga Mama tafito daga bayi tana
mata murmushi saita ganta kan dadduma tana mata murmushi, saita ganta kan kujera tana
zaune rikeda littafin zikirin ta saikuma chan taganta kan gado kwance tana mata murmushi,
hannayenta duka biyun tadaga takai kan idanunta ta murza idanun da kyau sanan taciresu
tasake kallon dakin amman babu kowa ciki dawani irin sauri ta shiga dakin tai bayi budewa tayi
dasauri tace “Mama kina ina” ganin babu kowa abayin yasa tadawo dakin tana juye juye kalle
kalle bakinta na rawa tace “Mama kina ina”? Gadon tayi ta yaye bargon kan gadon, jini jini
datagani a zanin gadon wanda na aman jinin da Mama tadingayi ne yasa taji kafafunta sun kara
sanyi kawai tayi kneeling awajen takifa kanta akan gado sai kuka kaman ta kwakulo zuciyanta
tayar takeji kukanta sa duk wani wanda zaiji tanayi kuka yake, kowa na falon tunda tafara kiran
Mama suka farka amman babu wanda ya iya shigowa yacemata wani abu abar Khairy tai kuka

dan ita akama Wanan mutuwan.

Da kyar Manaf ya iya tashi yashigo dakin gaban gadon yazo kusada ita yadaura hannunshi
akan bayanta murya chan kasa yace “Khairy stop crying and pray for Mama, kinga tun jiya baki
magrib ba balle isha’i, muje dakinki kicire rigan nan shower kiyi salla and pray for Mama, Mama
tariga tarasu……” wani kalan ihu tayi da saida gidan gabadaya ya amsa. “Mama bata rasu ba,
Mama batada lafiya babu wanda yafadamin, mena muku? Ni yarinya ce dazaa boyemin uwata
batada lafiya, nama Mama laifi dayawa bansami dama na roketa gafara ba, nabar Mama agida
natafi school nadawo kucemin Mama tarasu, babu wanda yagayamin Mama batada lpy saidai
kugayamin tarasu, Mama b…….a…” maganan yasoma gagaranta sabida mugun attack na
Asma daya taso daukanta chak Manaf yayi yafito da ita daga dakin yana karban inhaler da
Maheer kebashi, Mom tace “please ku kulle dakin nan tadena zuwa ciki” kwantar da ita kan
gadonta yayi yasa mata inhaler cus nishi take kaman zata mutu da kyar ta shaka, Mom tashigo
dakin takalli Manaf dake kanta tace “tafi Manaf” fita yawuce yayi daga dakin.




2️⃣7️⃣

Free page

Da taimakon Mom tai wanka ta chanza mata kaya zuwa wani simple atampa doguwan Riga
sanan tasata tai salla itadai tasan tai salla amman bamatasan metakeyi cikin sallan ba kotana
karatu dakyau kobatayi jikinta yay munannan zafi, kwanciya tayi kan dadduman Mom tazo
dagata tayi tacire mata hijabi tace “kwanciya akasan ya isa haka nan kar sanyi ya shigeki zoki
kwanta akan gado” Mom ta kwantar da ita kan gado ta kwanta lamo kan gado hawaye nabin
idanunta suna sauka kan katifan, hannu Mom takai tana sharemata hawayen ahankali tace
“Khairy nasan mekikeji aranki yanzu haka amman kisani kome yan uwanki sukayi da mahaifinki
sabida mamanki sukai hakan, shi mara lafiya ana so ana cikamai wishes nashi, barinma mara
lafiya kaman na mamanki, Mamanki ita ta haifeku duka idan she choose ke kadai zata
boyemawa rashin lafiyanta believe me tanada reason nata maybe taga Kece mai weak zuciya u
can not take it, and believe me yanzu idan nagayamiki Wanan abin dakike yi yanzu is not what
she wants Khairy, be strong dan yanzu Kece maman su yayyinki, kinyi tunani what Baban ki is
going through yanzu haka, matarshi dasuka tsufa tare bata kuma dawanne zaiji dake koko da
rasuwan da akamai? Khairy ki kwantar da hankalinki kinji, bari na sauka kasa na hadomiki ko
shayi ne kisha” Mom tashafa kanta kafin ta tashi daga kan gadon tawuce tafita daga dakin su
Manaf zasu shiga tahanasu.


Ranan haka aka wuni Khairy gatanan gatanan ne, takasa cin komi kotaci amai straight,
rasuwan Maman ta yabi gari bama asan ya kawayenta sukaji ba before you know it kawayenta
suka cika gidan harda Besty duka dakinta aka kawosu kallonsu kawai take kaman ta haukace,

babu wanda take amsa gaisuwan shi, duk wanda yazo gaisuwan bazaiyi kuka ba amman
dazaran kaga Khairy saikai kuka kawayenta sunyi kuka sunyi kuka harsun gaji, Besty tunda
tazo take rungume da Khairy da jikinta kaman wuta tana kuka da kyar ta iya tauna kosai guda
da Besty tabata abaki ahaka dare nayi suka tafi.



Hakanan yaji ya bala’in damu cus yakira Khairy yanaganin miss calls din daya sunkai 20 maybe
but all ba amsa same with text messages nashi ba reply, he don’t know why but kasa jurewa
yayi tashi yayi daga office din nashi yadauki car keys dinshi yafito wajen police station din,
motarshi yashiga yajata yafice daga police station din, he don’t even know why he’s driving to
layinsu Khairy but yasan zuciyanshi keeps pulling him to go there dudda bawai shiga gidansu
zaiyiba, ahaka har yazo layin, kofar gidansu yagani tsaitsaye da maza sanan gashi an bude
gate an saka canopy a compound din ga tabarmai maza sun zazzauna, hakanan yaji kirjinshi
yabuga dum! Waje yasamo yay parking motarshi yadade zaune sanan ahankali yafito ya tsaya
jikin motanshi yana kallon jama’a dake shiga da fita gidan yakasa zuwa, yana tsaye awajen Ya
Mu’az yafito tareda wasu friends nashi dasuka zomai gaisuwa, shiga motansu sukayi suka
wuce daidai zai juya yakoma ciki idanunshi suka sauka kan Aliyu dake tsaye jikin motanshi yay
folding hannunshi yana kallonshi tunani yafara inda yasanshi kafin daga baya kanshi yagayamai
police man din ranan nan takowa yayi zuwa inda Aliyu yake tsaye yamikamai hannu dasauri
Aliyu yabashi hannu yace “meke faruwane wucewa zanyi naga mutane gate abude shine nai
parking, what happen?” Aliyu yasake tambayan Ya Mu’az heart nashi nabugawa, ahankali Ya
Mu’az yace “Maman mu ce ta rasu, muje nakaika ciki kaman Baba gaisuwa” Ya Mu’az yay
maganan yana gaba binshi abaya Aliyu yayi har zuwa cikin gidan har inda Baba yake kan
tabarma tareda Baffa dawasu abokanen arziki Mu’az yakai Hydar, Baba nada gane mutane
kallo daya yana Hydar yace “Aliyu” hannu yamikama Baba anatse yace “Baba yahakuri, Allah
yajikanta Allah yamata rahama” ahankali Baba yace “Ameen Ameen Allah yayimaka Albarka”
sanan yakalli Baffa yace “Wanan ne officer dana gayamaka ranan da Khairy tai shirmen nan
yadawo da ita gida” dasauri Baffa yace “Allah sarki, yaro mai hankali angode Malam Aliyu, gashi
Ummulkhair ba lafiya da an kirata kamata gaisuwa nasan zataji dadin hakan” gyadama Baffa kai
yayi yakasa magana kirjinshi na bugawa dum dum, kafin da kyar ya iya tashi yamika musu
hannu yace “bari nakoma wajen aiki” addu’a su Baffa sukamai sosai sanan yajuyo Ya Mu’az
biyeda shi har waje zuwa wajen motanshi sanan Ya Mu’az yace “mungode Allah bada lada”
murmushi yamai tareda gyadakai har Ya Mu’az yajuya zai wuce yaji yakasa hakura ahankali
yace “Ya Ummulkhair take”? Juyowa Ya Mu’az yayi yakalleshi cikeda damuwa yace “not good at
all” yay shiru yana kallon Hydar din dayaga ya tsaya yaki tafiya yana kallonshi kaman yana jiran
yace wani abu ahankali Ya Mu’az yace “Mama had cancer all this while Khairy bata sani ba cus
Mama tahana afadi mata, as it is now kaga yau uku this is the third day da abinci bai shiga
bakin Khairy ba, she’s not handling the whole thing very well, she’s not doing okay, kuka suma
asma attack duka yahadu mata kaman zatai hauka takeji, kasan she’s very very close to Mama,
naji Baffan mu yana cewa yau zasu wuce da ita gidansu Dan gidan nan is not helping her at”.
Gyadamai kai Aliyu yayi idanunshi sunyi ja yakasa magana juyawa Ya Mu’az yayi yCawuce ciki.

2️⃣8️⃣


Free page
Shiga motan Aliyu yayi dasauri sanan yatada motan wani irin jan motan yayi da bala’in gudu
yayi tafiya mai bala’in tsayi sanan ya gangara gefen hanya ya kashe motan kafin yawani irin
daki siterin motan yace “noooooo” he just wish zai iya shiga cikin gidan yaganta, wayanshi
yaciro dasauri idanunshi sunyi ja baimasan mezaiyi ba text yashiga turamata. “Rashin uwa is not something I wish for even my enemy, but muna plan dinmu ne Allah is the
master of all planners. Ummulkhair nasan mekikeji, I know abinda zuciyanki kije because I was
once there, just know this wherever Mama is she’s resting, tana cikin jannatul Firdaus, I want
you to calm down, pray for Mama, cry but just little sabida nasan it hurts alot, babu wanda zai
gane how it hurts sai ke, so cry little and pray lot, be strong for me Khairy, and kisani cewa I am
here for you koda bana wajen presently but my love and my heart is there with you, I love you to
the moon and back Ummulkhair, Allah ya yassaremiki wanan nauyin dakikeji aranki”
Turamata text din yayi yadade ahaka sanan yafuzar da iskan yatada motanshi yawuce.


Bayan sallan magrib Mom da kanta tashigo dakin, Khairy na kwance kan gado tadagota tana
kallonta tawani irin rame tace “muje gidan mu, bayan kwana biyu saiki dawo nan bari nakawo
miki hijabin ki” bin Mom kawai take da idanu tadauko mata hijabin tazo har gaban gadon tasake
dagota danta kara kwanciya tasaka mata hijabin dagota tayi tasauko kasa baya tayi kaman zata
fadi dasauri Mom tariketa tana kallon fuskanta idanun idanunta sukai suntum har lokacin jikinta
da zafi ahankali tace “kiyakuri Khairy, kiyakuri” fita da ita Mom tayi tana binta luuu kaman wacce
tasoma zarewa duk su Baba da kowa na tsakar gida wajajen mota Mom tafito da ita binta da
kallo sukayi, dafa Baba Baffa yayi dayaga yana kallonta cikeda tausayi yace “don’t worry she
will be fine” karasowa wajen Mom tayi tasata acikin mota bata musu duk yanda akai da ita,
kowa shishiga mota yayi Baffa yana su Baba sallama sanan suka tafi da ita.


Suna kaiwa gidan parking suka yi, Zayn yafara saukowa daga motan Ammi side dinshi yawuce
dan yagaji he needs rest, Mom kuma tafito da Khairy dahar lokacin take yanda take, Ahankali
Baffa dake kallonsu yace “kitafi da ita side dinki tunda akwai Batool” gyadamai kai Mom tayi
tawuce da ita itakuma Ammi tadaure fuska tawuce abinta Baffa yabi bayanta yana amsa wayan
daya shigo phone nashi.


Kafin suma iso Batool tabude musu kofa tana kallon Khairy dan ita all this while bataje gidan
rasuwan ba tana gida tana kulada kannensu, zata fashe da kuka ganin Khairy Mom ta

ballamata harara hakan yasa tahadiye kukan taya Mom riketa sukayi sukai sama da ita zuwa
dakinsu zaunar da ita kan gado sukayi kwanciya tayi sharaf Batool zatai magana Mom tace “ki
barta jekimin tea yanzu zanzo nabata tasha yauma bataci komiba” Gyadamata kai Batool tayi
tafito daga dakin tsayawa tayi nan bakin kofa tana kuka ahankali, bude kofa Mom tayi tafito
ganinta yasa Mom taidan jim sanan tace “kinsan wahalan da akasha kafin Khairy tadaina kuka?
Tana ganinki kina kuka yanzu zata fara” Mom tai maganan tana janta daga wajen kofa sukai
stairs, cikeda da bala’in tausayi Batool tace “Mom kaman na Khairy mai surutu ba Mom kaman
tazare Innalillahi, duniyan nan babu komi cikinta Mom, look at Khairy damuka sunan Ya Hafiz da
ita muna wasa muna rawa, Mom I can’t stand seeing her this way” ahankali Mom tace “then u
should support her as ur sister, show her love abinda take bukata kenan yanzu, sanan mudena
nuna mata muna tausayinta, kijata ajiki u will help her tadawo daidai” gyadama Mom kai tayi,
Mom tace “good yanzu jekiyo mata tea kizo kibata tasha, lemme go and shower” wucewa tayi
zuwa kitchen da sauri.

Tea Batool tahado mata tadaura cup din a tray tadawo dakin nasu tana kwance sharaf agadon
yanda suka barta, ijiye tea tayi tahayo gadon tadagota ta tashi zaune ahankalli murya chan
kasa tace “Khairy zoki sha tea bakici komi ba” tsare Batool tayi da idanu da dazaran kaga
yanda take kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login