Showing 81001 words to 84000 words out of 108975 words

Chapter 28 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf

M Shakur   

09 Oct 2025

2808

dukansu haka suka gaji Wanan bakin halin
daga wajen ubansu, zauna kiga” zama ahankali Khairy tayi kan kujeran Gwaggo itama ta gyara
zama da kyau sanan takarasa kada furan tamika mata tace “ungo sha kena dama mawa”
ahankali tasa hannayenta biyu takarba tana murmushi sanan takai bakinta takurba furan kadan
dadi sosai tadade bataci abinci hakaba tass tashanye furan Gwaggo nawani irin murmushi
sanan takarbi kwaryan tace “kawo nan kiga banson kiyi komi, ko sauro banson ya cijeki zan
taya Aliyu kula dake harsu dawo daga kasan waje” kallon Gwaggo Khairy tayi dan batagane
metake nufiba hakan yasa Gwaggo tace “yauda sassafe aka tafi dashi kasan waje sabida
zuciyanshi ba lafiya Baban shi yakaishi wajen wani abokinshi likitan zuciya kidinga ma mijinki
addu’a kinji In sha Allah zaiji sauki” gyadama Gwaggo kai tayi ahankali tana kokarin rike
hawayenta dan duk itane dalilin Wanan rashin lafiyan nashi.

Yan aikin Mami ne suka shigo da manya manyan kulolin abinci zasu ijiye a falo tace “tafin musu
dashi chan dakin Amarya” wucewa cikin sukai sa abincin, ahankali Gwaggo tace “tashi kije kiyi
Kari ki kwanta ki huta anjima kawayena zasuzo su ganinki kinji” gyadama Gwaggo kai tayi

sanan ahankali tace “nagode Gwaggo” wani irin washe baki Gwaggo tayi tace “ohh Allah yabani
mai mini godiya, gantalallun yaran gidan nan kome zan musu babu godi bare nagode, yimaza
jekiyi Kari ki kwanta kihuta Khairiya Allah yamiki albarka” wucewa ciki tayi tana dan murmushi.


Da rana kawayen Gwaggo tsofaffi su kusan goma sukazo gidan damai kidan kwarya, wasu
tsofaffin wakoki suka dingayi suna sa Khairy rawa sai dariya ake kafin daga baya su bata gift
nasu, buhun gishiri, goruba, aya dasauransu sai dariya ake sanan suka tafi wajajen 6.


Bayan sallan isha’i mota yazo zai tafi da Batool da Amal Khairy tai kuka kaman me hakanan
tana gani suka tafi babu yanda ta iya aka barta ita kadai agidansu Aliyu danma Gwaggo na
sonta kaman tahadiyeta da abin duniyan sun mata yawa.
*****

Shigowa yayi falon Ammin nashi ahankali yana sanye da jumper na faran shadda yayi kyau
saidai yadan rame da ita kanta Ammin tagani but she knows he will be fine, tashi Baffa yayi
babu yabo ba fallasa yakalli Ammi dabasa wani good times yanzu sosai saidai yamaida ita yace
“muje ko” gyadamai kai tayi tana murmushi sosai ta mike juyawa Zayn shima yayi sanan suka
fito Mmotan Baffa suka shiga Zayn najan motan Ammi na nuna hanya harsukakai gidan
Aminiyanta dasuke kira da Hajiya Kwangila.


Babban gidane sosai ga ma’aikata ta ko’ina suna parking a compound din wata mata wacce
kibanta kenan kaman na Ammi bakinta hakoran makka guda hudu na gold sama biyu hakiran
kasa biyu tafito cikin shiga na alfarma tareda mai gidanta wanda yakenan business mogul
Chanchangii kenan, karasowa sukayi matan tawani rungume Ammi tace “barka da zuwa
aminiyata, ina yini Alhaji” tai magana tana gaida Baffa dake gaisawa da mai gidan cikin mutunci
sanan takalli Zayn da kanshi ke kasa ahankali yace “ina yini” cikeda fara’a tace “surukina Zayn
Oya dan Allah kushigo kun tsaya anan” tai maganan tana kama hannun Ammi sukai ciki
shikuma Zayn yagaida Baban daya rungume shi cikin ao sanan akai cikin gida, wani lafiyayyen
falo suka shiga aka zazzauna yan aiki suka shiga kawo kayan kwalama shaaaaa kafin sugama
suwuce.
Cikeda natsuwa Baffa yay gyaran murya yace “Alhaji to ga d’ana nan Zayn, da izininka inaso
idan ka aminta dashi kabashi permission na neman yarka, idan sunga juna sun aminta da juna
sai mufara maganan aure ko” wani kallon juna da Ammi da Hajiya sukayi sanan suka kama
hannun juna suna murmushi, Alhaji yace “Alhamdulillah Alhamdulillah, naji dadin hakan kuma
ina fata Allah yatabbatar mana da alkhairi kira Aisha wife” tashi Hajiya tayi tai sama sanan Alhaji
yace “sunan Y’ata Aisha, a UK tai karatu tayi Mass com, Aisha nada kirki dakuma hankali da
girmama na gaba da ita” ahankali Baffa yace “Masha Allah”
Wani hadadden daki Hajiya tashiga ganin wata yarinya zauna gaban madubi tasaka hadaddun
kaya tajuya ma kofan baya yasa tace “wai dan gidanku Aysha bazaki sauri ba maisa bakijin
magana ne namiki alkawari zakiso Zayn” hawayen idanunta tashare ahankali tace “Momy ni

Zayn din danakeso daban dan Allah ki karamin 1month na nemeshi yana nan Abuja kinji”
fizgota Mom tayi tadagata ciked masifa tace “wlh zan kwada miki mari nizaki maida karaman
mutum ga yaro chan da iyayenshi afalo da babbanko kinki fitowa dau gyalenki jor” ahankali
tadauki gyale zata yafa karba Mamanta tayi tayafa mata tana murmushi tace “kinga yanda kikai
kyau kuwa wuce muje” yakama hannunta saukowa falon sukayi, tunda suka fara saukowa Zayn
ke kallonta idanunshi kur akanta jiyayi zuciyanshi na bugawa fat fat fat ahaka har suka karasa
saukowa kasa kanta nakasa tace “ina yini Abba, Mom ina wuni” daga Baffa har Ammi murmushi
sukayi ganin yarinya mai natsuwa gata kyakkyawa gatanan fara kaman Zayn din, murmushi
Ammi tayi sosai tace “Zayn tashi kuje garden ku zanta mu muna nan muna namu na manya”
dasauri Hajiya tace “kai shi Garden Aisha” tashi tayi ahankali kanta akasa hakama Zayn shiya
fara gaba suka fita tana biyedashi kanshi akasa har zuwa garden suna shiga garden yawani irin
fizgota da mugun karfi baki tabude zatai ihu yadaura hannunshi kan bakinta yana mannata da
bango yana wani irin huci ware idanu tayi gabanta na mugun faduwa ganin Zayn Zayn data
dade tana nema, hannunshi yazare daga bakinta yanunata da yatsa yace “how dare you Ayshu”
wani irin murmushi tayi tanaji kaman zuciyanta zai fito sabida murna tace “Zayn” da yatsa
yanuna ta yace “listen to me kome zaki fadama iyayenki kifada musu baki sona karki sake kibari
ahada Auren nan dan bazaki taba jin dadin aure na, i can’t marry a girl datasan namiji awaje”
wasu hawaye masu zafine suka zubomata murya chan kasa tace “Bantaba son wani namiji
kaman ka ba Zayn” yana kallonta in the eyes yace “amman kuma kika bama wani chan virginity
naki” jitayi zuciyanta yamata zafi, ahankali tace “I regretted everything, I had sex once u were
the second sex danayi in my life dan Allah that shouldn’t be a barrier to aurenka Ya Zayn idan
bansameka amatsayin miji ba I can die” dauke kai Zayn yayi yawuce kawai yaje yazauna
rayuwan shi babu abinda kemai dadi but he just feel Allah ne ke kamashi, he has been a bad
boy, yaci mata daban daban turawa yasha shisha gashinan yanzu the only woman daya taba
samu bai sameta ba, look at yarinyar da Allah yahadashi da ita his life is ruin.


6️⃣1️⃣
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp
number na 07012181461
Thank u❤️





Yau one month kenan da bikinta, Baba, Anty Mariya dasu Ya Manaf babu wanda baya kiranta

yaji yaya take hakan namata dadi.
Ko kadan babu wani wanda yake kuntata mata agidan kawai dai she feels agidan Gwaggo
kadai ke sonta da Dad sauran harda Mami duk basa sonta barinma Meena, ko Meena natare
da Gwaggo dazaran tazo wajen zata tashi fuuu tafice, hakama su Amal da Khadija, Mami kam
ko kallo bata isheta ba gashi batada hanyan waya da Ya Aliyu taga yayake, tana zaune da
Gwaggo dabata barin ko tsinke ta taba kullum cikamata ciki da abinci da magani, bata wani
iyacin abinci ko Gwaggo ta lurada hakan fura indomie sune tafici indomie shine kadai aikin da
Gwaggo tabari tanayi shima sabida taga tana sone.


Yau ma kaman kullum tana zaune adakinta taji Gwaggo ta kwala mata kira, da sauri ta sauka
daga kan gadonta tana sanye dawani simple dogon Riga na atampa kai kyau, dan kwali
tadauka tadaura sanan ahankali tafito daga dakin nata tabude kofa tazo falon ganin Dad yasa
wani irin kunya yakamata da sauri tajuya takoma daki Gwaggo tai dariya tace “kaganta nan
Abdul haka yarinyar nan keda kunya wlh naji dadi da Aliyu yasami yarinya mai natsuwa haka,
mayafi takoma tadauko fa” dan murmushi Dad yayi danshi kanshi ta burgeshi, bata wani jimaba
tafito da Babban mayafi sanan tazo har gaban Dad ta tsugunna zata gaidashi dasauri yace
“Ummulkhairy zauna zauna” ahankali tazauna sanan kanta na kasa tace “Abba ina kwana
andawo lpy” ahankali yana kallonta yace “lpy lau Ummulkhairy yaya kike hope babu wani
matsala ko” gyadamai kai tayi ahankali zuciyanta namata wani kalan dadi buri ta kawai taga
Aliyu, kaman Dad yashiga mind dinta anatse yace “Aliyu yaji sauki garau Alhamdulillah, amman
mun baroshi chan ya tsaya yin wasu abubuwa nan bada jimawa ba shima zai dawo” gyadama
Dad kai tayi ahankali tanajin hawaye na zuwan mata amman tadaure tahana kanta yi, dan
murmushi Dad yayi yace “Bayan aurenku nai tafiya batare dana baki gift dinki ba Ummulkhairy,
ungo” Dad yay maganan yana mikamata key mota, ahankali tadago kanta takalli Dad dake
mikamata key ahankali tasa hannunta takarba kafin tamai godiya Dad yace “mota nasiyamiki as
my gift, nasan baki iya tuki ba nai hiring direba dazai koya miki tuki cikin 3 weeks yatafi kidinga
jan motanki da kanki kullum zai dinga zuwa yana daukanki 3hrs daily kinji” wani irin murmushi
tayi har ranta taji dadi tace “Abba nagode Allah yakara budi” sanan ta taho wajen Gwaggo
anatse tace “Gwaggo Abba yabani mota” wani irin murmushi Gwaggo tayi tace “Iyye akashe
lafiya muje Muga motan” tashi tayi tana kama Gwaggo suka fice Dad yabita da kallo now he
sees why danshi ke sonta Ummulkhairy is extremely calm ga natsuwa hankali ga kunya wani
mad Benz Dad yabata sabo fil ko Leda baa cireba, fitowa Mami tayi kallo daya tama motan
takoma daki abinta, Gwaggo tace “Oya shiga kitafi kifara koya kai ka ko yamata mota ahankali
kajini ko” Gyadamata kai direban yayi sanan suka tafi, shi kanshi Direban saida yay mamakin
yanda tai catching up kome yake ko yamata fast.


Kullum direban ke zuwa before one week Ummulkhairy ta kware saidai yan abubuwan dabaza
arasa ba bayan 2weeks direban yafadama Dad ta iya, Dad dakanshi ya shiga motan nata tajasu
har zuwa inda zaai mata license, nan da nan aka mata komi sai murmushi take, sanan Dad
yakaita shopping just to make her happy dan harga Allah yanason Yariyan kuma kome yaranshi
keso yanaso dudda Aliyu na claiming baya sonta kawai jinshi yake u can’t fight love bari

yadawo, duk wani abu datakeso saida Dad yasaya mata saida yamma sanan ta tukosu suka
dawo gida parking tayi a compound din batare da Dad yafita daga motan ba yace
“Ummulkhairy” kallon Dad tayi ahankali tace “naam” ahankali Dad yace “I know kin damu this is
almost 2month dabikin ku bakiga Aliyu ba, Aliyu is fine he’s just going through a lot now, but I
assure you yakusan dawowa, all I want from shine ki kwantae da hankalinki idan wani abu
nadamunki always come to me, always come to me, sanan duk randa kikeji zuwa wani gu
saloon or wani abu ko bananan kifadama Gwaggo ko Mami kafin kitafi, ki kula da kanki kinji,
everything will be fine, Allah yamiki albarka” ahankali tace “Ameen Abba nagode” tashi kije zan
sa’a kawo miki kayanki ciki” gyadama ABBA kai tayi sanan tawuce ta tafi.


6️⃣2️⃣



Bayan 3 month!
Sosai Ummulkhairy tai kyau kyau da wayansu barinma some kawayenta cewa suke tanada ciki
nan ko basusan haryau batama saka angon nata a idanu ba, tayi kyau sosai fatarta tai fresh
yana wani walkiya, jikinta ne har yanzu bai dawo ba sabida rashin iyacin abinci, yanda Gwaggo
da Dad ke sonta abin har mamaki yake bata ita badadan tamasan yanda Baba ke sonta ba
dazata iya cewa Dad yamafi Baba sonta itadasu Mami dasu Meena haryau suna nan yanda
suke. Wuraren 10 tashiga bayi danyin wanka bayan tagama gyara dakinta dana Gwaggo dudda
Gwaggo tahanata amman ina taki tasaka turaren wuta, wanka tayi tafito tana kallon wani kofin
tsumi da zafinshi akan madubinta tasan aikin Gwaggo ne tun kafin bikinta har zuwa yau babu
ranan da baa bata magani dauka tayi tasha tana tabe fuska sanan ta shafa mai tadauko wani
pencil gown na atampa light blue da ash tasaka yama jikinta dam yafito da kyanta fitowa falo
tayi Gwaggo tace “wuce kiyi kari kafin kitafi saloon din amiki kitso, Baban ku yama ijiye miki
kudin saloon din kafin yafice asibiti yanakan gadona jekiyi kari tukunna masa ce da farfesu”
gyadama Gwaggo kai tayi sanan tawuce ahankali tadebo masa biyu kachal tazuba farfesun
tadawo kusada Gwaggo tazauna tagumi Gwaggo tayi tace “ohh ni bantaba ganin makiyar abinci
irin Khairiya ba” dan murmushi tayi tafara ci biyun ma sabida Gwaggo tasata agabane tacinye
tass sanan ta tashi takai kwanon cikin wankewa tayi takife sanan takoma daki, wani karamin
gyale ash tadauka da karamin hand bag da wayanta da car key dinta tafito, Gwaggo tabita da
kallo tace “yarinyar kirki kinga yanda kikai kyau kuwa” murmushi tayi Gwaggo tace “saima kinyi
kitso da lalle zakiga yanda zakiyi kyau yau jedauko kudin akan gadona” wucewa dakin Gwaggo
tayi tadauki kudin datagani kan gado yan 1k bamatasan iya yawansu ba tafito rikedasu
zatabama Gwaggo Gwaggo tace “inyi me dasu wuce kitafi sabida agama dawuri” gyadama
Gwaggo kai tayi tace “Gwaggo natafi insiyomiki goro idan zan dawo”? Dasauri Gwaggo ta
Gyadamata kai tace “eh adawo lpy ayi tuki ahankali” gyadama Gwaggo kai tayi sanan tawuce
tafita daga dakin, wajen motarta tahango Meena tsaye taci gayu kaman fita zatayi hango Khairy
nazuwa yasa tajuya baya ta tashi daga jikin motarta karasawa wajen Ummulkhairy tayi harzata
shiga motanta saikuma taji no bazata iyaba she needs to talk to this girl today, dawowa tayi
sanan tasha gabanta tana kallon fuskanta ahankali tace “Meena ina zaki I can drop u naga

direban ku bayanan, let’s go with my car” dauke kai Meena tayi tace “I don’t need anything na
wacce tayaudari Yayana taso takashe shi, I hope idan yadawo yarabu dake cus u don’t deserve
Ya Hydar wlh” ji Ummulkhairy tayi jikinta yay sanyi all this while dama tasha zargin fushin da
Meena keyi da ita kenan gashinan yau ta tabbatar, kasa motsi tayi ganin haka yasa Meena
kawai taja tsaki tawuce side din Gwaggo, Khairy takusan 3min ahaka sanan tawuce tabude
motarta tashiga sanan tadata aka budemata gate tafice, wani babban saloon taje aka wanke
mata kai akai drying kalaba tasa aka mata yan kanana sanan tasa amata red lalle dan batason
baki nan aka shiga mata wani lafiyayyen jan lalle atafin hannu da yatsu dakuma kafanta, bayan
angama around 3 tasa aka mata facials da lip therapy, wani irin kyau fuskanta yakarayi lips
dinta yay jajir wuraren 5 tagama komi tabiya kudi sanan tafito, tsayawa tayi agaban building din
tasaima Gwaggo goro sanan tadawo tashiga motanta ta tada motan taja tana kallon
hannayenta yanda sukai kyau kaman wata Amarya tana kallon fuskanta ta madubi kaman ba
itaba fuskanta yay kyau lips dinta kaman na new born baby tsabagen pink din dasukayi,
ahankali take driving abinta looking so adorable harta shigo anguwansu, tsayawa gaban gate
tayi tai horn daidai wayanta na ringing kallon wayan tayi ganin Batool ne yasa da sauri tadauki
wayan da hannu daya tasa akunne daidai ana bude mata gate batare dayama kalli cikin gidan
ba taja motan tana waya.





“Mara mutunci wai bazaki zo wajena ba” parking tayi awajen parking sanan takashe motan
tabude tafito ahankali waya na kunenta still tana sauraron labarin da Batool kebata awaya,
sanan tasa hannu tadauko jakanta da ledan goron Gwaggo kafin tadauki gyalenta dake kan sit
tarike a hannu shima sanan tamaida kofan tarufe tafara tafiya tana murmushi tace “are you
serious Batool, yanzu yaushe zasuzo asa ranan I am so happy for you Batool” tai maganan
tana kokarin saka hannunta tabude kofan dakin Gwaggo daidai anrigata bude dakin, Amal da
Khadija suka fito dagudu dan Gwaggo ce tabiyosu sata sukai mata ko kadan basusan da ita ba
suna bude kofan suna fitowa aguje suna bugeta wani irin ihu tayi daga jakanta wayanta dake
kunnenta da car keys din hannunta zubewa sukai akasa itama tai wani irin baya zata fadi dan
gabaki dayama tasadakar faduwa zatayi chak taji an tarota bayanta yafada kirjin mutum
hannunshi gabaki daya kan flat cikinta ta kankame idanunta gam sabida yanda ta bala’in tsorata
ahankali ta furta “Ya Aliyu” danshi kawai yafado mata arai yanda he always hold her idan zata
fadi, tsayawa chak Amal da Khadijan sukayi jikinsu narawa suna kallon Gwaggo datafito arude
tace “Innalillahi badai ihun Khairy naji ba zubarmin da diya kukayi” murya dakuma kamshin
turaren da bazata taba manta kalanshi ba da jikin datasaba jinshi ba yasa ahankali tashiga
bude idanunta tadaurasu kan Gwaggo dake gabanta tana kallonta, dasauri Gwaggo tace
“sannu Khairiya da Aliyu bai tareki ba dakinyi mummunan faduwa barayin banza kawai ku
kwashemata kayayyakinta” ahankali tagyara tsayuwanta jikinta narawa gabanta nafaduwa
sotake tajuya takalli Aliyun amman takasa tsoron yin hakan ma take tanajin beating heart dinshi
abayanta, gently taji yana zare hannunshi dagakan cikinta kafin yacire gabaki daya, gently taji
yaraba jikinshi da nata yajuya dasauri, dasauri Gwaggo tace “bazuwa kayi kasha furan ba

dakace nadama maka” kaman daga sama Ummulkhairy taji maganan Aliyu.
“Nafasa sha adakin ki, kiba yaran nan sukawomin” Dawani irin sauri Ummulkhairy tajuya tadan
saci kallonshi bayanshi kadai ta iya tagani dudda bataga fuskanshi ba gani tayi yakara wani irin
haske gashin kanshi yakara yawa kaman tunda yaje baiyi aski ba gashin yay baki sun nannade
looking so coily, hannunta dataji an kama yasa dasauri tajuyo Gwaggo ce tana rikeda
kayayyakin ta dasuka fadi akasa tace “wuce muje kukuma barayi duk wacce tashigomin daki
wlh saina chanza mata kamanni” dariya su Amal sukayi suka wuce flat din Mami abinsu.

Suna shiga daki Gwaggo tace “dazu kina tafiya Saloon mijinki na dawowa nai nai da shegun
yaran nan sukiramin wayanki nace ki dawo sukaki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login