Showing 45001 words to 48000 words out of 108975 words

Chapter 16 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf

M Shakur   

09 Oct 2025

2892

hakaba. Ahankali yace “why are you laughing I am being serious
Gwaggo can gossip” wani irin rushewa da dariya tayi ashagwabe tace “stoppp Ya Aliyu u are so
mean” dan murmushi yayi yace “are u supporting that old woman now”? Girgizamai kai tayi tana
taushe bakinta, murya chan kasa yace “do you wanna meat her some day”? Gyadamai kai tayi
ahankali tace “yes” anatse yace “ok u will meet her some day, zakiga abinda nake fadi, I have
sisters also but duk ba anan naija suke aure ba, so they hardly visit sai salla salla, then my little
sister Meenah, she’s your age mate kinaso kiganta?” Gyadamai kai tayi tace “eh” ahankali yace
“you will I promise, do u have any lectures tomorrow”? Girgizakai tayi tace “a’a gobe Mom tace
zanje saloon nai kitso” dan murmushi yayi yace “ayi mai kyau, idan kin tashi da asauba after
observing subhi makesure to read Qur’an and ur books afterwards okay” murya chan kasa tace
“okay” agogo ya kalla ganin 1 nadare yasa yace “u need to sleep okay” gyadamai kai tayi
ahankali tace “saida safe” murya chan kasa dan daso samune suyita magana yace “Allah bamu
alkhairi, I love you Ummulkhair!” Dip taji ya katse wayan, wayan tabi da kallo kafin tarungume
wayan kam kam ahaka bacci yay awon gaba da ita.



3️⃣3️⃣

This book is 1k pay into 3107021073 aisha Muhammad first bank
Chat me up directly by clicking on this link
wa.me/+2347012181461


Yau bayan sun tashi sunyi salla tama Mama addu’a sosai hana Batool dake kokarin komawa
bacci tayi taja hannunta suka shiga kitchen, lafiyayen Moi moi tayi dayaji kifi da kawai sanan tai
kosai dakuma kunun gyada koda Baffa yashigo gidan yaganta a kitchen suna girki itada Batool
baisan lokacin daya ciro waya yamata video batare datasani ba ya aikama Baba sanan
yazauna kusada Mama a falon suna hira sanan suka fito dakomi Baffa saida yazauna yaci

kosan da kunun dudda abincin shi is ready, suna zazzaune saiga su Manaf sunzo dubata as
usual once in a while zokaga dadi bajewa akayi akai lafiyayyen breakfast afalon Mom saida aka
gama tass sanan sukai clearing tazo itada Batool zasuje sama suyi bacci ganin Baffa
namagana dasu Ya Manaf, kiranta Baffa yayi hakan yasa tadawo, zama tayi akasa dan gyaran
murya Baffa yayi yace “Khairy kafin mahaifiyanki tarasu tanata fama da Baban ki ya kara aure
sabida ku amman fir yaki” yadanyi shiru sanan yace “dazata rasu agaban kowa yayyinki nan
duk suna wajen ta barmini wasiyya kan na aurar da Baban ki karna barshi baida mata” dan
ijiyan zuciya yasauke yace “dalilin dayasa nakira su Manaf kenan su biyo tanan kafin su tafi aiki,
inaso nagaya muku nasamoma mahaifiyar ku mata” yasake shiru yana kallonsu sanan yace
“bayan long bincike akanta, yar limamin masallacin Utako ne, ba yarinya bace ta taba aure da
yara biyu, amman mijinta yarasu, yaran na hannun Maman mijin, tayi karatu a FCE tana
koyarwa Awani primary school dashi take taimakon kanta haka, tanada natsuwa ga kirki
gakuma ilimin addini, na nemama Baba aurenta inaso nan da sati daya ayi Auren hope kun
yarda Ummulkhairy” Baffa yakirata ahankali, murmushi tayi ahankali tace “Allah sanya alheri”
cikeda jin dadi Baffa yace “Ameen tashi to kitafi” tashi tayi tawuce shikuma Baffa yacigaba da
magana dasu Manaf.



Zasu koma bacci Mom tashigo tace su shirya suje saloon, shiryawa sukayi driver ya kaisu
saloon tsife kan akayi aka wanke ana gyaran kafansu, kitso akamata mai kyau shiku daya fito
da fuskanta, aka mata pedicure da manicure sanan suka biya kudi suka dawo gida, ganin
yanda taketa duba wayanta yasa Batool tace “wa kike jira ne awayan nan” hararanta tayi batace
komiba saikuma chan tace “Besty” hararanta Batool tayi tace “wlh karya kike” hararanta itama
Khairy tayi tace “serious bata dawo school ba yakamata kuma tashigo Wanan dazamu fara
exam next week” “laulayin ciki hala take” dasauri Khairy takalleta tace “ciki” Gyadamata kai
Batool tayi tace “haka kawata Zara tana aure yanda kikasan da cikin tai tuntube abakin kofa sai
ciki” dan murmushi tayi saikuma ta kalli flat cikinta tana picturing kanta da ciki, sosai Batool
kemata surutu har suka kawo gida, duba kitson da akamusu Mom tayi kitson yay kyau sosai
barinma na Khairy dan tanada wani irin gashi mai bala’in kyau, ga tsayi ga ciki gakuma santsi.
*****


Yau asabar tun ranan daya siyamata tsuntsu basu kara haduwa ba sabida yanason tai karatu
saidai waya da night, baicika kiranta during day time ba sabida aiki, most time text yake mata
just to check up on her, ko Allah yasan tanama Aliyu wani kalan so ne dan he’s super good to
her, he’s caring ya iyasa taji all damuwanta are gone, bata taba sanin she can’t put mutuwan
Mama behind her ba amman Aliyu helped her to, he’s just like her strength, yau sosai take
murna sabida zata ganshi, yace he’s taking her out yatura mata sunan french restaurant din
dazasu hadu.


Shiryawa tayi cikin wani dogon riga, silk ne milk color yadin is so lush rigan yazauna ajikinta

dazaka dauka wata black American model ne, zama tayi tadaura wani black cotton dan kwali tai
wani plain simple dauri tasaki jelan gyalen agefen shoulder nata, tadanja dan kwalin baya daya
bayyana gaban kitson kanta dayay kyau, kwantaccen gashin gaban goshinta tadau karamin
brush tai styling nasu da a bit gel daya bada wasu wavy corners subhanallah bakaramin kyau
tayi ba, kallon fuskanta tayi a madubi ganin wuyanta empty yasa tadauki wani simple two step
necklace dinta dakeda pendant na diamond tasaka awuyanta wuyanta yafara wani kyalli, sanan
tadauki kananun dan kunnensu tasaka, mikewa tsaye tayi tanabin kanta da kallo ganin yanda
kayan yabi jikinta yanda boobs dinta suka wanisa gaban rigan yay kyau yasa taji wani kalan
kunya, wardrobe dinta tayi tadauko wani simple dark army green a bit transparent veil normally
dark green goes with milk a whole lot yafashi tayi tagaban hakan yarufe kirjinta but still kana
hango kyallin diamond necklace dinta ta gyalen, komawa tayi tazauna kan kujera sanan tadauki
brush ta taje full black giranta sanan tadau man baki dake shining ta shafa kan lips dinta
dayawani haskaka pink lips din, ganin idanunta sunyi bala’in haske dayawa yasa yadauki
kwallin Batool ta zizara Omg, dan murmushi tayi dan ita kanta tama kanta kyau kaman taje
studio tai hoto, tashi tayi ahankali yau batajin saka hill hakan yasa tasaka slippers na Hermes
shima dark army green daya hadu yau complementing dressing nata gabaki daya, she look very
simple but yet super super elegant, wani cute little handbag tadauka na Charles and Keith beige
color dayasa tai kaman zata gasan kyau sanan tadauki turarukanta tafesa tanadan tunani
mezata gayama Mom tabude kofa tafito, afalo tasami Mom zaune Batool batanan taje gidan
kawarta amso note sabida fitanta da Aliyu yasa bata rakataba, ganinta yasa Mom tace “wanan
gayu haka sai ina Khairiry”? Dan murmushi tayi ahankali tace “Mom zani wajen Besty dubata
batada lpy” ahankali Mom tace “ayyah, laulayi Batool tagayamin dama, ki gaidamin da ita Allah
sarki yarinya, haka tadinga sintirin zuwa dubaki, ki gaishemin da ita please” gyadama Mom kai
tayi tawuce tafita Adamu na ganinta yatada mota shiga bayi tayi tazauna tagayamai inda zasu
suka wuce.



Wani hadadden eatry sukaje, saida Adamu yay parking sanan taciro wayanta daga jaka kafin tai
dialing number shi taga kiranshi ya shigo hakan yasa tadauka takai kunenta, murya chan kasa
taji yace “come out of the car” sanan ya katse wayan, ahankali tafito daga motan tama Adamu
bye yatada motan yawuce sanan tajuyo tana waige waige dan bata ganshi ba. “You look
breathtakingly beautiful Miss” taji muryanshi ta gefenta, dawani irin sauri tajuyo da kanta ta
kalleshi yana sanye dawani yadi mai laushi fari tass, yana wani irin kamshi mai dadi yasanya
black glasses a idanunshi yana kallonta hannunshi rikeda flowers masu kyau combination na
white and red yamika mata ahankali yace “flowers for Miss Khairy” fuskanshi takara kallo wani
irin murmushi tasaki daya bayyana white teeth nata tasa hannu takarbi flowers din sanan
ahankali takaisu saitin hancinta tai breathing in wani irin kamshi taji sunayi mai sanyaya rai kafin
ta fuzar tasake dago kanta takalleshi cikin wani classic voice tace “I love flowers thank you Ya
Aliyu, they’re beautiful” glasses na idanunshi yacire murmushi yamata yace “shall we”
gyadamai kai tayi sanan suka wuce ciki tana rikeda flowers dinta kaman wasu english couples,
akwai mutane amman badayawa ba table din daya musu reserving yakaita wajen sanan
yajamata kujera zama tayi ahankali tace “thank you” sanan ta ijiye flowers nata agabanta tana

kallonsu tana shafasu da hannunta, zama yayi kujeran dake facing nata yana kallonta baisan
maisa ba but yau kyan datamai daban ne kodan yakwana biyu bai ganta ba, abincin daya musu
placing order aka shiga kawomusu abinma mamaki yabata dan abincin sunyi yawa, this is a
brunch date wow! Murya chan kasa yace “do you like it” gyadamai kai tayi ahankali tace “thank
u” murmushi yasakeyi yace “zakici kosaina baki abaki” makemai kafada tayi akunyace sanan
tadauki cutlery tashiga cin lasgana dashi yafi shiga idanunta tsayawa yayi yana kallonta Khairy
nada wani irin natsuwa da inba kana tareda ita ba bazaka taba cewa tanadashi ba, she does
everything a natse calmly batada rawan jikin nan, kaman taji ajikinta ana kallonta hakan yasa
tadago kanta hada idanu sukai dashi akunyace ta sauke kanta tanajan gyalenta zata rufe
fuskanta dasauri yace “nooo Pickle sorry bazan kara kallonki ba look nazama makaho” kallonshi
tadanyi ganin yanda yay da idanu abin yabata dariya dan dariya tayi shima yayi sanan yafara
ciCn nashi .


3️⃣4️⃣



Saida sukaci suka koshi sanan suka ture ga uban abinshi sun rage akwai wayanda bama
sutaba ba ahankali yace “shall we?” Gyadamai kai tayi yatashi hakan yasa itama ta tashi suka
fito maiikatan eatry namai godiya suka wuce motanshi yabude mata shiga tayi sanan yamaida
kofan yarufe yadawo yazauna yatada motan suka bar wajen bini bini yake satan kallonshi ganin
sunzo wonderland yasa tawani ware idanunta aljihun motanshi yasa hannu yaciro mata 2 ticket
dinsu yamika mata Wanan Karan takasa boye excitement dinta tace “wowwwwww Ya Aliyu I am
so sosoooooo happy thank uuu” u welcome baby yay maganan yana shiga ciki parking yayi a
inda ake parking sanan yafito itama fitowa tayi she’s so happy datama kasa boyewa zagayowa
yayi ta inda take yace “are u happy” gyadamai kai tayi tana dan tsalle tace “yes thank uuu”
murmushi yamata yace “let’s go” ciki sukayi yariga yay recharging card nasu yace “me and u
competition yau zamuyi kin yarda”? Gyadamai kai tayi tace “and I will win cus I am a born
winner” murmushi yayi yace “let’s see then” da bumper cars suka fara suka shiga, both of them
were literally screaming suna bubbuge juna da motan shi kanshi Aliyu baitaba sanin he could do
this childish play ba sai yau, bugeshi tayi motanshi yakoma baya tahau ihu ta waigo tanamai
gwalo kwafa yayi sanan yatashi yafita itama fitowa tayi tana tsalle sosai kaman Yar yarinya tace
“I won yayy” hararanta yayi yay gaba dasauri tabishi sukaje next game dayakeso suyi shooting
target, indai target ne babu wanda yakaishi but da gangan yabarta shima taci wayyo
Ummulkhairy kaman zata zuba ruwa akasa tasha dan dadi, ice cream yasaya mata takarba
tanasha saida yajiraa ta shanye sanan suka shiga wajen 3D zasu buga car race, nan ma ita
taci, yanda takemai dariya ko shi kanshi baisan ta iya dariya hakaba she was really feeling
herself, ta iya game sosai sabida su Maheer dan sunayi a gida, all games na wajen nan saida
tayi har teddy bear saida taci katuwa tadauki abinta tana dariya, hararanta yayi yay gaba
dasauri tabishi tace “Ya Aliyu wait, fushi kake sorry but I told you I am a winner” juyowa yayi
yace “nine looser ko” hannu tadaura akan bakinta tana hadiye dariyan dake zuwa mata tace
“uhm’uhm” hararanta yayi yace “let’s go waje kiga wanda zamuyi I promise u will be the one to

loose” dasauri with confidence tace “eh muje” tabishi dasauri gaban rollercosta taga sunje koda
tana yarinya bata yarda tai abin nan ba sabida tsoro hakan yasa ta ware idanu, magana taga
Aliyu yayi da mutanen sanan yazo inda take tsaye yace “harkin fara tsoro ne” turamai baki tayi
tace “never” dan bakinta data turamai yakalla saikuma ahankali yace “mutafi to aga who will
lost, and yarinya kikamin kuka ko” dasauri tace “ni Bana kuka saikace wata baby” dariyanshi
yahadiye dan he already saw d fears a eyes nata, yace “let’s go” tana bite dashi suka shiga
wajen, ganin tsoro a fuskanta yasa bai bari ta shiga wajen one person ba, two sitter slot suka
shiga na mutane biyu, zama yayi sanan itama tashigo tazauna kusadashi ahankali sakamusu
abinda zai rike mutum yahanasu faduwa yayi sukadai akan makeken roller coaster dinan sanan
Aliyu yakalleta yace “kin shirya” gyadamai kai tayi gabanta na faduwa tim tim, juyowa Aliyu yayi
yakallesu yace “we ready” ajiyan zuciya tasauke hakan yasa yay dan dariya yaciro wayanshi
yana bude camera yace “I need evidence” turo baki tayi tana hararanshi sanan aka kunna abun,
rawa hannunta yafara tun kafin su fara moving, kawai jitayi sunyi sararin samaniyan Allah wani
kalan ihuuu tayi. “Wayyoooo Ya Aliyu banyi banyi nafasa, huuuuu wlh nafasa kayakuri” tai
maganan tana kankame idanunta jin kaman hanjin cikinta zai fito shiko dariya kaman zai mutu
yana musu video, jin suncigaba da sama abin nawani chillarasu kaman zai kaisu lahira yasa
kawai tawani kankameshi tana boye fuskanta akan kirjinshi. “Innalillahi, Ya Aliyu zanyi fitsari,
wlh u won, Dan Allah kayakuri kace subari wayyooo Allah na na shiga uku, Ya Aliyu zan
mutuuuu” alamu yamusu da hannu dasu kashe jin yanda heart nata ke beating, amman har
suka dawo kasa bata saniba ta kankameshi gam gam tana cewa zatai fitasari, yadade yana
zaune ahaka feeling her ajikinshi kafin ahankali yace “sokike kimin fitsarin ajiki cus we are down
already” dago kanta tayi daga jikinshi ahankali kaman matsoraciya kallon idanunshi take dake
cikeda dariya sanan takalli ko’ina ganin suna kasa, dan hararanta yayi yace “matsoraciya kawai
harda kuka” dan turo baki tayi sanan akunyace tasake takoma gefenta, ciremusu abin rike
mutum din yayi sanan yabude sit din yafita dagangan yashiga duba jikinshi yace “hope bakimin
fitsarin ajikina ba” rufe fuskanta tayi da hannu tace “ni banyi ba” sanan ta sauko tagefenshi tabi
da gudu tai restroom dan tagani wajen dasuke zuwa, shikuma yawuce dan sayomusu snacks
yana kallon video daya musu awayanshi.


Popcorn yasai musu, unsweetened yasaima kanshi dan baicin sugar shi ko kadan itakuma
yasaimata mai milk sanan yazauna yana jiranta.

Fitsari tayi sanan tafito tanadan murmushi ita kunya ma takeji, tana cikin tafiya taji an
kwalamata kira Ummulkhairy dasauri tajuyo, ganin class governor dinsu yasa tadan tsaya tana
murmushi shima yakaraso wajenta da sauri yana rikeda cotton candy guda biyu a hannunshi da
alama bashi kadai bane, ganinta yasa yace “wow kema kinzo shakatawa” murmushi tayi tace
“eh Governor ya aiki ya shirin exam” ahankali yace “Alhamdulilah” yana kallonta ganin yanda tai
kyau yadade yanason Khairy amman yakasa gayamata dan yake yayi yace “u look good
Khairy” murmushi tayi tace “thank you bari naje” tajuya zata wuce dasauri yabiyota gabanta
yasha sanan yamika mata one cotton candy dake hannunshi yace “atleast take this” girgizamai
kai tayi tace “no thank you Governor” dasauri yace “I insist Allah saikin amsa, nawane dana little
sister na dama, nakoma nakara sayowa, idan baki amsa ba zanta binki ne wlh” badan taso ba

bataso taga kaman wulakanci tamai wanan ma daya rantse saita amsa yasa gently tamika
hannu takarbi wanda yake bata sanan tace “thank u” tawuce da sauri binta dawani irin mayen
kallo yayi sanan yace “see you on Monday Khairy” ko tankashi batayiba dasauri take tafiya
kanta akasa dan tabata lokaci tabar Ya Aliyu chan, jitayi ajikinta ana kallonta, ahankali tadaga
kanta, Aliyu tagani tsaye rikeda pop corn guda biyu a hannu, fuskanshi kadai tagani ya tabbatar
mata da yaganta tareda class governor dinsu, jitayi kawai jikinta yahau rawa sakin cotton candy
don tayi akasa sanan ta taho da sauri kafin takaraso gabanshi gani tayi cikeda bacinrai yawani
irin jefar da pop corns din akasa yajuya fuuu kaman zaki yawuce dasauri tabishi tana kiranshi.
“Ya Aliyu Ya Aliyu” amman ko waigowa baiyiba har wajen dayay parking mota kafin ta isa wajen
dan one step dinshi shine like 3 or 4 step nata harya shiga mota wani irin jan motanshi yayi
Saura kiris yabuge wasu yarama ita kanta saida tai ihu Allah yakiyaye bai bugesu ba yafita
daga wajen da balCa’in gudu.



3️⃣5️⃣



Jiyayi kafafunta sun mata sanyi wani dan dakali tasamu tazauna bata taba sanin cewa Aliyu
nada fushi dakuma zuciya hakaba sai yau, sabida yaganta dawani saiya tafi yabarta anan, jiyayi
duk wani iri zuciyanta badadi kaman ba ita bane tagama dariya yanzun nan ba, ahankali tabude
jakanta taciro wayanta kiranshi tayi amman har kiran ya katse bai daukaba, hakan yasa takira
Adamu tafadamai inda take, baa dauki cikakken 20min ba saiga Adamu yazo mota tashiga suka
wuce gida.

Amota ma sake trying nashi tayi amman bai dauka ba, kaiwa gida sukayi hakan yasa tamaida
wayan jaka ta fito tashiga ciki, Mom tagani afalo tareda Batool Mom tace “yamai jikin” murmushi
tayi tace “yaji sauki Mom tace na gaidaku” “muna amsawa, jeki chanza kaya kiyi wanka ana ma
kiran salla saiki salla ki sauko kici abinci” gyadama Mom kai tayi tawuce, daki tashiga wanka
tayo tafito salla tayi sanan tazauna shiru jin Mom nakiranta yasa tafice taje abinci taci tadawo
daki wasa wasa har 12 bai kirata ba kasa hakura tayi she called him twice bai dagaba kuma bai
kirata ba da kyar bacci ya kwasheta ranan hakan yasa washe gari duktai wani kala data tashi
takasa tabuka komi koyasan da hakan ne message dinshi taga ya shigo wayanta. “Go and
study for exam naki u have

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login