Showing 78001 words to 81000 words out of 108975 words

Chapter 27 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf

M Shakur   

09 Oct 2025

2847

baka uBmarni kasaki Ummulkhairy ka auri
Aisha yarinyar kawata dana zaba maka”….
Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp
number na 07012181461
Thank u❤️




5️⃣8️⃣




Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp
number na 07012181461
Thank u❤️



Wani irin kallon mahaifiyar shi yake yana mamakin wanan wani irin tsana ne me Ummulkhairy
da mahaifiyarta sukama Ammi datakisu haka, cikin fushi sosai Ammi tace “nikake kallo kamaida
Yar iska ko bari kaga” filon kan gadonta tadaga tadauko wani sharp wuka tace “ai ita
Ummulkhairy wish din dead mahaifiyarta ake cikawa akanta nima bari na kashe kaina maybe

alokacin ne zakabi umarnina” kawai Ammi tadaga wukan da gaske zata chakama kanta dawani
irin sauri Zayn yazo hannunta da wukan kekai yakama chak yana kallonta saiga hawaye sun
zubo daga idanunshi sharrrrr murya chan kasa yace “Ammi basai kin dauki rayuwanki bane zan
miki biyayya ba” ijiyan zuciya yasauke kana ganinshi kasan abin namai ciwo sosai hawaye
yasake gangarowa daga idanunshi yana kallonta still. Ahankali yace “Ni Zayn nasaki
Ummulkhairy” da dayan hannunta dabai rikeba Ammi tanunamai uku, wasu uban hawaye ne
sukai gushing daga cikin idanunshi zuciyanshi namai ciwo ahankali yace “saki uku” sanan
yakarbe wukan hannun Ammi ahankali kafin yajuya zai fice cikeda zafi tace “ina zaka sami
paper ka rubuta kabama Mahaifinka nasan zaice nina saka amman na shiryamai kome zaimin
yayi, dolenshi dai yaje ya nema maka Aisha ka aura” bude kofanta yayi yafice yana goge
idanunshi yay side dinshi jiyayi yama tsani komi da komai bazaima iya kara 1 good minute anan
Nigeria ba, flat dinshi yawuce koda yashiga Mamu na bathroom hakan yasa yadauki paper da
buro yashiga rubutu yana share hawaye kafin ya linke yasa a envelope yadaura kan gadon
sanan yadauki wani bag pack yadauki su international passport dinshi da other necessary
abubuwa dayake bukata kafinma Mamu yafito yawuce kawai yafita yashiga mota straight to
airport.
Wanan kenan!!!



Wuraren 4 Baba da Baffa suka dawo gidan bikin dudda akwai mutane cikeda gidan sama
sukayi zuwa dakin Baba sanan suka tura Batool taje ta taho da Ummulkhairy.
Ummulkhairy na zaune adakinta abin duniya yamata yawa babu abinda kemata dadi aduniya,
tai wani irin zuru zuru Batool yashigo dakin tace “tashi muje su Baba nakiranki zaa fara miki
fadan Amarya” kallon Batool tayi tama kasa tashi ita kanta bazata iya explaining yanda takeji
yau dinan ba kaman tamutu kawai takeji, kamata Batool tayi tana gyara mata lullubi sanan suka
wuce zuwa falon Baba da ita suka bude kofa suka shiga, daga Anty Mariya sai Mom da Baba
da Baffa zaune suka shigo zama sukai akasa Baba na kallonta yanda tai kyau sanan yay
gyaran murya yace “Ummulkhairy nazo miki dawani sabon labari dudda nasan ba lallai bane
kiso kijishi ba” Baba yadanyi shiru kafin ahankali yace “dazu muna wajen daurin Auren yayyinki
babban amincin Zayn yakawo mana wata wasika daga Zayn” Baba yasakeyi shiru, ahankali
Baffa yace “Ummulkhairy d’ana Zayn ya aiko da wasika dake dauke da saki, yace yasakeki saki
uku!” Dawani irin sauri daga su Mom har Batool da ita kanta Khairy ke kallon Baffa, dan ijiyan
zuciya Baffa yasauke anatse yace “I don’t want to go into details Ummulkhairy, nasan Auren
Zayn burin mahaifiyar kine, amman wanann da tunkafin akai ko’ina Allah ya wargaza al’amarin
inaga akwai wata aya da Allah ke kokarin nunamana Ummulkhairy dan haka kiyakuri” wani irin
gyamboo taji zuciyanta namata tun dazu zuciyanta namata ba dadi amman na yanzu is like
times 1000, Aliyu kawai take tunanowa da wulakanci datamai, ta wulakanta wanda ke sonta
kaman zai haukace, tacimai mutunci, tamai gori da Zayn, tayi insulting pride na Ya Aliyu gashi
yanzu wanda yasa tamai haka yasaketa tunkafin akai ko’ina kaico! Wani kalan kuskure tayi
arayuwanta ne haka Ummulkhairy! Baffa ya katse mata tunani ta hanyar kiranta hakan yasa ta
kalli Baffa, anatse Baffa yace “Ummulkhairy mun daura miki aure da Aliyu ga sadakin ki nan!”
Wani irin zaro idanu tayi tanajin maganan kaman amafarki taga Baba yatashi ya ijiye mata wasu

bandir na kudi akan cinyanta, ahankali Baffa yace “saidai mijin naki Aliyu baida lafiya sosai har
yanzu yana gadon asibiti mahaifinshi yace ayanzu haka baimasan wanda ke kanshi ba, anjima
dukanmu nan bayan sallan magrib zamubar kome mukeyi muje mu duboshi, kekuma nan bada
jimawa ba dan mahaifinshi yariga yakiramu za’azo daukanki gidansu za’akaiki for now, idan
yazo yaji sauki In Allah ya yarda sai ayi duk bikin dazasuyi akaiki gidanki ki tare kinsan yanzu
babu wani shirye shiryen da akayi bikin yazo mutu bakatatan” Baffa yay shiru sanan Baba yace
“Ummulkhairy inaso idan kinje gidan mijinki kiyi koyi da halin mahaifiyarki, nasan Aliyu baida
mahaifiya tarasu, amman yanada Kaka da Matan Baba da kanne, nasanki da girmama mutane
inaso kibisu sau da kafa karnaje complain akanki sai yabo, ki kasance mai tsoron Allah da
biyayya ma mijinki dan yanzu aljannar ki na karkashin mijinki ne……..” Baba yashiga mata fada
mai ratsa jiki dayasa tafara kuka, har cikin ranta dataji ance an aura mata Aliyu jitayi kaman an
cire mata wani babban kaya azuciya amman kuma aliyu ya tsaneta, but ba matsala idan shine
battling dinta agidan mijinta she is ready zatai fighting for her love back she will win Ya Aliyu
back and taroki gafaranshi lokaci yayi yanzu dazata zama dat sensible and matured girl da
Mama koda yaushe kEhso tazama.


Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp
number na 07012181461
Thank u❤️



5️⃣9️⃣


Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp
number na 07012181461
Thank u❤️

Daga Baffa, Anty Mariya, Baba da Mom babu wanda bai mata fada da wa’azi cikinsu ba,
wajajen 6 Baba yace “wife kutafi da ita ta shirya motocin daukanta na hanya” gyadamai kai Anty
Mariya tayi sanan suka dagata ahankali tana kuka sosai daki aka kaita wanka akasa tayi sanan
aka bata ruwan turare tayi dashi sanan tafito shiryata sukayi cikin wani milk hadadden lafaya
mai bala’in kyau, 6:40 hadaddun motoci sunyi layi gaban gidansu kowane mota dan sanda ne
da full uniform keja dan duka boys sun Aliyu Dad yakira.
Tsaf aka shiryata bakaramin kyau tayiba aka lullubeta sanan aka fito da ita takasa daina kuka
she can’t believe shikenan dagayau tabar gidan iyayenta rungume Baba tayi gam gam ana
guda ana ayiriri sun dade ahaka shima Baba idanunshi sunyi ja sosai sanan yadagota yace “ya
isa haka kukan kar kanki yayi ciwo” ahankali yakama hannunta yasaukar da ita kasa ana binsu
suka fita tsakar gida har zuwa kofar gida da kanshi yabude kofar motan kafin ahankali yace “go
in peace Ummulkhairy, ubangiji Allah yama aurenki albarka, ina rokon Allah to bless your new
home yakuma haskaka rayuwan aurenki, go my daughter” yay maganan yana sata cikin motan
ta zauna ahankali tana kuka, shiga motocin su Mom sukayi da kawayenta da Batool sanan aka
tafi da ita.



Tsakanin gidansu Aliyu da nasu nada nisa sosai, dan sai wajajen 8 nadare sukakai, wowww
Batool dake gaban motan tafadi ganin Babban gidansu Aliyu, an bude gate wato kudi nada
kyau dudda su kansu basusan da bikin ba but they were able to pull something an zuba kujeru
hadadun agidan ga DJ an kawo, yan uwa sun cika gidan ko’ina hayaniya ga girke girke abinci
kala kala na yawo a tsakar gidan, kafin sufito daga mota Gwaggo da Mami dasukaci gayu na
gani afada sukazo taransu idan kaga Gwaggo zaka dauka an mata bushara da Aljanna ne, fito
da Khairy akayi daga mota kawai Gwaggo tafashe da kuka Dan she can’t believe Ummulkhairy
ce aka kawomata amatsayin Matar Aliyu danta, taruwa akai kan Gwaggo dake kuka cikin kuka
tace “ni kubani y’ata na rungume” murmushi su Mom sukayi sanan suka kawo mata
Ummulkhairy dakenan alullube tawani irin rungumeta tana mata ruwan saman addu’a a godiya
aka sanan tasaketa tace “kushigo” shigowa sukayi babban falon Mami aka fara kaita aka
zaunar da ita atsakiyan dakin ana waka ana rawa Mami na murmushi ana cemata saita saya
baki zata ganta, kudi Mami takawo da box na warwarayen zinare tadaura kan jikin Khairy ana
ihu ana guda sanan aka bude mata fuskan Khairy kallon fuskan Khairy da idanunta ke kasa tayi
sanan tamata addu’a kafin a dauketa akaita dakin Gwaggo, Gwaggo da dan kafafunta dababu
lafiya rawa tahauyi Haba zokaga dariya sanan takawo turaman zani guda ashirin tabama Khairy
da bandir na yan dubu dai dai guda uku, da zoben azurfa da warwaron azurfa da sarkan azurfa
masu kyau sosai aka dinga guda, tashi Mom da Anty Mariya sukayi sukai sallama da su Baffa
najiransu suzo aje aduba Aliyu, da Kyar Khairy tasakesu suka tafi sai kuka take sanan Kaka
takaita dakinta dan fir tace “ita awajenta Khairy zata zaune har zuwa aliyu yaji sauki tanada
dakuma daban daban dayawa a side nata, wani hadadden daki aka kai Khairy gadon ciki ma
sabone fill dan dazu da rana Dad yasa wani furniture company suka kawo aka chanza komi na
dakin aka fitarda nada zaunar da ita akai akan gado itada Batool da Amal kawarta sauran

mutane duk suka tafi.



Wuraren 10 su Baba sukakai asibitin Dad, Dad dakanshi yazo yadauke su akasa yace
“barkanku da zuwa” gaisawa sukayi suna sama Baba yace “yajikin nashi” ijiyan zuciya Dad
yasauke yace “Alhamdulillah muje” sukai sama har zuwa wajen wani daki, bude kofan Dad yayi
ahankali yashiga su Baba biyedashi Aliyu na kwance kan wani hadadden gado da kayan asibiti
idanunshi akulle he’s attach to wani machine, salati su Baba sukayi, Baffa yace “what’s the plan
yanzu” dan ijiyan zuciya Dad yasauke yace “wanan machine din shine taimakama heart dinshi
to beat, beating na heart nashi is very slow, so yanzu dai gobe zamu fitardashi zuwa Oman
akwai wani heart Dr achan he’s my very close friend tare mukai karatu a Ukraine yace
nakawoshi Aliyu will be fine” dukansu ajiyan zuciya suka sauke Baba yace “In sha Allah zaiji
sauki, please if u need anything we are here for you yanzu munzama family” murmushi Dad
yamusu cikedajin dadin maganan su yace “Allah yabar zumunci nagode sosai” motsi da Aliyu
yayi yasa dukansu suka kalleshi dasauri Baban yay wajen gado yana kama hannunshi yace
“Aliyu, Hydar I am here can you hear me”? Wani irin bude idanunshi Aliyu yayi kadan da kana
gani kasan baya cikin hayyacinshi sanan murya chan kasa yace “Um….mulk….hair” kafin
yakara lumshe idanu kaman bashi ne yay motsi ba, sakinshi Dad yayi yadanyi murmushi yajuyo
yakalli su Baba da jikinsu yay sanyi sosai yace “tun shekaran jiya haka yake saidai yadan bude
idanu kadan yakira sunan Ummulkhairy yakoma” dan murmushi Dad yasakeyi sanan yakalli
Aliyun yace “one thing I am sure of shine d’ana na bala’in son Ummulkhairy so thank you Alhaji
dakuka auramai Ummulkhairy bazan taba mantawa da wanan kyautatawan dakukamin da d’ana
ba” yay maganan yana juyowa yakalli su Baba daduk sukejin badadi suna addu’a Allah yabashi
lpy, sun dade a asibitin sai wajajen 12 na dare sanan suka tafi, Baba da Baffa sun dade suna
magana sanan kowa yawuce gidanshi.


Saida sukakai gida sanan Mom takalli Baffa kafin tafita daga cikin motan ahankali tace “one
thing danasani cewa inaso gamedakai shine rashin yanke hukunci acikin fushi, nasan ba
hurumina bane nan amman inaso na roki alfarma biyu daga wajenka” tai dan shiru tace “nafarko
shine inaso kamaida Ammi and inaso kai kokari and look at her situation and understand her,
batasan da Auren nan ba itace mahaifiyar Zayn, taci buri kan danta is understandable idan taki
yarda da Auren nan kowa da kalan zuciyanshi, kuma yanda Zayn bai auri yarinyar nan ba
barabonshi bace wlh inda rabonshi ne daba Ammi ba ko duk aduniyan nan ne basu isa suraba
Auren nan ba, sai alfarma tabiyu shine ko’ina Zayn yaje ka kirashi danka ne, nasan yanachan
cikeda damuwa yasa kazama karamin mutum da sauransu kanunamai bahaka bane yadawo
gida, Auren Ummulkhairy ko rashin aurenta won’t change kai mahaifinshi ne yazo idan yanason
wacce Ammi keso ya aura wato Aisha kaje ka nemamai Auren idan bayaso yakawo kowa
yakeso ya aura, rayuwa batada tabbas kowa datashi kaddaran just look at Aliyu yanzu
yanachan kwance rai hannun Allah yay giving up but Allah yaga zuciyanshi cikin sauki yabashi
Ummulkhairy, komi yafaru nada dalili sometimes abinda mu iyaye kesoma yaranmu is not the
best or Khair for them, I know u are hurt amman kayakuri and forget everything let this family

continue to be in peace kaji”? Gyadamata kai Baffa yayi ahankali bude kofa tayi zata fita dasauri
yakamo hannunta hakan yasa tajuyo takalleshi, ahankali yace “I am so lucky to marry a wife like
you, Allah yamiki albarka” murmushi tayi tace “Ameen” sanan tawuce ta tafi shikuma yadan
dade zaune a motan sanan yaciro wayanshi yakira number Zayn ringing yake yana gab da
tsinkewa yadauka.

Ahankali Zayn yace “Abba kayafemin I am so sorry” murya chan kasa Baffa yace “shiiiiiii Zayn i
understand you Allah yasa hakanne mafi alkhairi, kana ina”? Murya chan kasa tace “ina wani
hotel ban sami flight ba yau saida safe” anatse Baffa yace “dare yayi yanzu dan haka forget
about tafiyan nan gobe dasafe kadawo gida kajini, I am not angry with you one bit hakama
Baffan ka shima he’s not, so kadawo gida kadauki komi amatsayin kaddara inda Ummulkhairy
matarka ce da Ammi n ka bata isa taraba Auren nan ba, so it’s okay, kadawo gida inaso kafito
dawata yarinyar ka aura idan wacce mahaifiyarka keso ne to idan ma ba ita bane duk daya kaji”
gyadamai kai yayi ahankali yace “thank you Abba” murya chan kasa Abba yace “don’t cry again
good night son” ya katse wayan.



6️⃣0️⃣


Wanan Littafin na kudi ne karki karanta batare dakin biyaba kika karanta min littafi ban yafeba.

wa.me/+2347012181461
To chat me up on watsapp

This novel is 1k
Pay 1k into 3107021073 aisha Muhammad saiki turomin evidence of payment ta watsapp
number na 07012181461
Thank u❤️

Jirgin karfe 6 nasafe Dad da abokinshi sukabi aka wuce da Aliyu Oman.
****

Dukansu adakin sun makara sabida yanda akai bacci late jiyada daddare, Ummulkhairy tafara
bude idanunta wuraren 8 nasafe, saman dakin tabida kallo komi nadawo mata sabo she can’t
believe ita Amarya ce and tana gidan iyayen mijinta Aliyu anan ta kwana, tashi zaune tayi
ahankali tana kallon Batool da Amal dake shargan bacci sanan ahankali tamike tsaye tawuce
bayi, shiga tayi ta maida kofan tarufe sanan tabude tap wanke fuskanta tayi takalli madubi tai
wani irin fresh fatarta tayi da sulbi sulbi yakeyi tsabagen dirzan gyaran jikin da aka mata tarame
babu abinda yarage ajikinta banda boobs da hips, ijiyan zuciya tasauke ahankali sanan tadauki
brush sabo dake dakin tadauro alwala tafito daga bayin ganin Batool zaune yasa tashimfida
dadduman dake dakin tadauki hijabi tasaka tai salla.

Koda ta idar zama tayi tai shiru tana tunani, Aliyu kawai zuciyanta keso yagani tabashi hakuri,
tsayawa akanta Batool data fito daga bayi tayi tace “tashi kije kiyi wanka ki shirya” gyadama
Batool kai tayi sanan tamike tsaye ahankali tana kallon Amal dake bacci still sanin bata salla
yasa tawuce bayi batare data tadata ba.

Wanka tayi tafito daure da towel set na akwatin da Baba yamata Batool tashigo da daya shigo
daga cikinsui sanan ta ciro mata wani lafiyayyen lace ja, shiryawa tayi da taimakon Batool duk
wanda yaganta saiya kara kallonta, mayafi Batool takawo mata tayafa mata aka sanan ta
feffesa mata turare tace “fita kije ki gaida Gwaggo tana falo” Gyadamata kai Ummulkhairy tayi
sanan tabude kofa ahankali tafice tanabin corridor dake kamshin turaren wuta sanan tadaga
labule tafito falon, Gwaggo na zaune afalon kan daya daga cikin jerin kujerun dake falo 3sitter
tana burga wani lafiyayyen fura a kwarya, Meena na zaune kusada ita itama tasaka atampanta
mai kyau sosai, ganin Khairy yasa tawani irin ijiye wani empty kwaryan dake hannunta wanda
tarike tana jiran Gwaggo tagama ta tsammata tadauke kai, kaman ance Gwaggo ta waigo
sabida kamshin turaren da jikin Khairy keyi ganin Khairy gaban corridor kanta akasa kana
ganinta kasan kunya takeji yasa tawani washe baki tana kallonta tace “jama’a kuzo ku kalli
Matar jikana Ali Gadanga kusar yaki” dan gajeren tsaki Meena taja mara kara tana kara dauke
kai kaman taga kashi, ahankali Khairy takaraso gabanta sanan ta tsugunna har kasa akunyace
tace “Gwaggo ina kwana” dungure kan Meena Gwaggo tayi tsabagen dadi tace “dan gidanku
kalli yanda ake gaida manya ba irinku ba da kullum kedamuna da kud moni daga tsaye kuna
shanyemin jini masu bakin hali, tashi tashi kinji diyata Allah ya lullubeki da albarka, zauna
kenake dama ma fura zo zauna nan kusadani ke Meena matsa mata” gyara zama Gwaggo
tana kara matsa mata girgiza matakai Khairy tayi akunyace tana kokarin zama akasa dasauri
Gwaggo tace “kul karki zauna akasa, sokike sanyi ya shigeki kina amarya, zauna nan kan
kujera kusadani kiga, matsa mata Meena” tai maganan tana tunkude Meena wani mugun kallo
Meena tama Gwaggo kaman ta maketa sanan ta tashi fuuuu tafice daga dakin Gwaggo tabita
da harara tace “kinga bakin hali yan gidan nan ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login