Showing 18001 words to 21000 words out of 108975 words

Chapter 7 - ALKAWARIN ZUCIYA BOOK COMPLETE HAUSA NOVEL M SHAKUR .pdf

M Shakur   

09 Oct 2025

2841

da zafin ciwo, dan haka Alhaji I am giving you Wanan chance din cry as
much as u want now, after yanzu baka kara kuka ko nuna rashin kwazo sabida yaranka” kaman
jira Baba yake ahankali hawaye suka shiga kwararowa daga idanunshi, tissue Dr yadauka
yabashi karba yayi dasauri yakai kan idanunshi yana sharewa cikin wata kalan murya dake
sosarai yace “I don’t want Maryam to leave me, naso mu tsufa tare sanan mu mutu tare, why
are you doing this to me now Eh Maryama diyar albarka” saukan da kanshi las Dr yayi yana
sauraron Baba yakai kusan minti 15 ahaka sanan ya share fuskanshi tass da tissue Dr

yanunamai bathroom yashiga ya wanko fuskanshi yafito yama Dr sallama yafice zuwa dakin
Mama ganin su Manaf tareda ita tana bacci ana mata Karin wani abu kaman yellow madara
yasa yafito, zama yayi a kujeran gaban dakin sanan yaciro wayanshi number dayay saving da
Amini yay dialing, ringing daya aka daga cikeda barkwanci irin na manya yace “badai
kahanamin yarinya zuwa makaranta ba” dan murmushi kadan yayi sanan yace “jikin Maryam
yatashi muna asibiti Baffa” anatse daga dayan bangaren akace “Subhanallahi, turn d car Bala
muje asibiti” kawai aka katse wayan.


Yana zaune awajen ko cikakken 10min ba’a dauka ba, wani Babban mutum da akalla shida
Baba zasuyi sa’onni ya shigo cikin asibitin yana gyara Babban riganshi, farine mutumin sol
yanada kiba dan yamafi Baba, shida wani dan saurayi dabazai wuce sa’an su Manaf ba dayay
kama dashi dukansu fuskokinsu yanuna damuwa sosai, yana karasowa dafa kafadan Baba yayi
yace “be strong my friend, Allah yabama Maryama lafiya, Allah yatashi kafadunta, Allah yasa
kaffarane” tashi Baba yayi yanadan murmushi sanan yakalli yaron dake gaidashi yace “su
Baban Baby girl Hafiz, Allah ya raya” ahankali yace “Ameen Baffa” sanan suka shiga ciki, har
lokacin bacci take, da idanu Baffa yama Baba alamu su fito, suna fitowa yace “bazamu fitada ita
wajeba ko har yanzu tanakan bakanta”.



I will talk to her idan ta farka, ahankali Baba yace “Allah yasa ta yarda” kara komawa sukayi
wajen Dr ko akwai wani solution amman babu, dudda haka Baffa saida yakira some of the best
Doctors dayasani a Abuja but is still same thing hakanan suka hakura.

Wajajen 3:00 na rana tafarka, dakin tabi da kallo kafin ahankali tafara yunkurin tashi dasauri
Manaf da Mu’az suka dagota, ahankali Mu’az yace “kinajin yunwa Mama mezakici” dakin
asibitin tabi da kallo kafin ahankali tasauke ijiyan zuciya tadanyi murmushi ganin duk sun damu
tace “ya akayi bakuje aiki ba yau, laaaa is that Hafiz” tai maganan tana kallon Hafiz dake zaune
kan kujeran gaban gadon yana kallonta cikeda tausayi, cikeda murna tace “zonan zoka
nunamin hoton jikata nagani” dan murmushi yayi yataso yazo, wayanshi yaciro yafito da picture
cute baby girl dinshi yabata karba tayi tace “Masha Allah tubarkallah, Allah ya rayamana kaga
yarinya kaman Babanta Yan biyu” tai maganan tana nunamusu hoton kafin idanunta ya sauka
kan time din wayan ganin karfe uku har da minti goma yasa dasauri tamikamai wayan takalli
Mu’az tace “kiramin Dr yasallameni inkoma gida, Khairi takusan dawowa daga school” tana
maganan saiga Baba da Baffa da Dr sun shigo tare, Baffa na ganinta yace “ya jiki Maryam”
murmushi tayi tace “Alhamdulillah Baffa, ya ji kalle inasu Hajiya Asiya” kafinma taji amsanshi
tace “Dr zokai discharging dina natafi gida” ahankali Dr yakaraso wajen yace “Hajiya kibari mu
dubaki na kwanaki tukunna saimu sallameki” kallon Baba tayi sanan takalli Dr rai Adan bace
tace “sallameni yarana banaso su dawo Bana gida Dan Allah” kallon Baba tayi sanan ahankali
tace “daman Wanan ne shirinka idan ka kawomi asibitin arikeni” dasauri Baffa yazo wajen
anatse yace “Maryam kalleni nan” ahankali tajanye idanunta dagakan Baba dake kallonta kuri
takalli Baffa, anatse Baffa yace “Maryam kiyakuri ki zauna likitocin nan su cigaba da baki

gudunmawa, zamanki agida zai karasa ciwon yazama worst ne, dan Allah maryam inhar kinajin
magana ta” lumshe idanunta tayi sanan tabudesu ahankali tace “Baffa tun ina yarinya kasanni
ban taba cemaka no ba, kome kacemin inayi dan haka yau Baffa dukanku anan zan rokeku
alfarma, dagayau dan girman Allah kome zai sameni karku sake dawodani asibiti, Baffa nasan
kalan chutan danake dashi, nasan metake nufi, da inzauna anan allurai da maganinsu yakarasa
cinyeni gwara in koma dakina, I want to die adakina tareda yarana dakowa, I hate hospital and
zaman asibiti shizaifi kasheni dawuri sama da komi, please Baffa dan Allah, idan baka yarda ba
naji zan zauna, amman rokonka nake please Baffa” kowa na dakin saida jikinshi yay sanyi har
Baffa, ahankali Manaf yakalli Baffa yace “Baffa please grant Mama wish, let’s just take her back
home ko Hafiz” gyadamai kai Hafiz yayi da idanunshi sukai jajir, hakama Mu’az, ganin Baffa da
Baba sunyi shiru dan su sunfiso tazauna a asibiti tasami lafiya yasa ahankali Dr yace “Alhaji
kubarta takoma gida, idan anything come up ku kirani ni zandinga zuwa nadauki Wanan nauyin”
ahankali Baffa yakalli Baba dakokadan baisoba, kallon kayakuri takoma gidan, hakan yasa
ahankali Baba yace “shikenan” murmushi Mama tayi sosai nan da nan aka zaremata drop din
sanan Dr yarubuta mata magunguna suka saya sanan suka dawo gida gabIaki dayansu.



ALKAWARIN ZUCIYA


✍M SHAKUR



1️⃣4️⃣

Free page
Wuraren 8:50Am sukakai school. Adamu na parking wajen parking tafito da saurinta bama ta
tsaya mai sai anjima ba tashiga sauri cus 9 dot mutumin nan ke shiga aji gashi baya wasa da
attendance, tana cikin tafiya zuwa class saiga wasu yammata su hudu sun taho tunda suka
ganta sukahau ihun murnan ganinta Khairy nada wani irin farin jini naban mamaki wajen mata,
tareta sukayi. “Khairy how far”? Murmushi tayi dake karamata bala’in kyau tace “lpy lau wlh,
yanaga zaku waje daban ba class garemu ba yanzu” yatsine fuska sukayi, daya daga cikinsu
tace “wlh dabaki wani wahalar da kanki ba wajen class din Mr Okeme ba ba’a taba ganewa ba,
ke saurayinki Ahmad celebrity yazo nemanki fa” hararanta Khairy tayi tace “Malama niba
saurayina bane kidena hadani dashi, na wuce class nidai” tai gaba abinta ranta abace, daya
daga cikinsu ne ta daga murya tace “idan yakadoki meet us a garden chan mukayi” daga murya
itama tayi tace “that’s not gonna happen Ladies” tana tafiya wasu another set na yammata na
tareta bamata tsaya sauraransu ba tace “I will see u later ladies inada class now” tahau tafiya
gudu gudu sauri sauri, duk inda tabi ana kwalamata kira Khairy Khairy waving mutane kawai
take tawuce benen dazai kaita ajinsu tana kaiwa yana shiga tana tsaye yana kallonta yaja
kofanshi yarufe, ahankali ta yatsine fuska murya chan ciki tace “this wicked man cannot make

heaven” sanan tajuya tana kallon kasa daganan bene yanda student kowa na takanshi sanan ta
fuzar da iska ita dai ko itace allazi boko bazata taba tsayuwa jikin window har agama 2hrs class
ba, tashi tayi abinta tafara tafiya tawuce tana sauka daga staircase abinta tanadan turo baki ita
kadai tana kunkunai. Sabida yanda ranta yake abace taji bamatason tabi normal hanya friends nata suyita tareta da
magana hakan yasa tabi ta parking space dan taje garden daga wajen, ahankali take tafiya ita
kadai a parking space din tana cikin tafiya a parking space din taji an kwala mata kira. “Khairy”
dan tsayawa tayi jim batare data juyoba jin muryan namiji ne ke kiranta, tunani tafara acikin
kanta muryan waye wanan sai chan taja wani kalan annoying tsaki tacigaba da tafiya abinta
gani kawai tayi ansha gabanta wasu maza guda biyu sunshamata gaba suna sanye da kananun
kaya sun bubbude hannuwa irin suna tareta dinan, wani kalan daure fuska tayi babu ko alamun
wasa akai tace “me haka” dan dariya sukayi daya daga cikinsu yace “listen to Ahmed mana
Khairy yasan bazaki tsayaba saisa yace mutareki” yay maganan suna nuna mata bayanta,
juyawa tayi cikeda masifa wani black skin guy ne da dududu bazai wuce mate nata ba in age
maybe 20 ko 22yrs haka yake, yana sanye cikin rugget kayan yan iska dinan, crazy baggy
jeans da wata babbar baggy riga yayi dying gemunshi zuwa blond color kana ganinshi kaga irin
yan iskan yaran nan gashinan very popular aciki school nasu, wani kalan mugun kallo tamai da
manya manyan idanunta tace “kai da boys dinka Ahmad should get out of my way” wani kalan
murmushi yamata tareda daura hannunshi akan kirjinshi yana shafawa yace “auuch! I love it
when you look at me like that Khairy with those ur big big lulu white eyes, Baby my heart only
beat for you” spitting miyau tayi agefenta sanan tajuyo takalleshi tace “you disgust me Ahmad,
nagayamaka time without numbers stop wasting ur time on me, you are not my type of guy, idan
maza irinkane suka cika duniyan nan I rather die banyi aure ba dana aureka, I don’t like you an
taba soyayya dole ne” dan takowa sahu daya yayi zuwa gabanta, tsayawa chak tayi tareda
kama waist dinta kirjinta na bugawa fat fat, wani mayen kallo yabita dashi barima kirjinta dayaga
yacikamai idanu tunba yauba tunda ya lurada yanda Khairy keda boobs yaji yakara haukacewa
akanta, dan hucin zafi Ahmad yayi yana kallonta still sanan yanuna kanshi yana bude
kafafunshi da tsabagen effizy sun koma kaman boleg yace “look at me kinsan how many babes
anan School namu ke kiyamun laili because of me eh? Look at me Khairy, I have money, I was
born in wealth, banda haka I am a hip hop rapper number 1 a arewa, yaro mai zamani, har rap
nayi da sunanki natura miki a watsapp u don’t even open my chat balle kiji how much I love you,
Khairy tell me mezan miki dazaki soni eh, kinga we are the only ones here, just tell me babu
kowa don’t be shy Khairy, baki sona don’t u wish to be mine, don’t u wanna make matan
makarantan nan jealous ace Kece tawa, I want you to be my Choima while I become your
Davido, lemme make you famous, lemme make u a star gurl, what will I do to make you mine
baby na? Don’t u want all of this” all maganganun dayake mata jitake kaman tai amai bala’in
kyaman Ahmad take bawai he’s dirty bane, kawai dai yanayinshi yanda yake dressing yana
shiga kaman wani su wizkid yayi coloring gemunshi da halinshi na waka ita kawai he’s not her
spec, yana mata magana yana wani wawware fingers kaman yana rapping yana kama tsakiyan
baggy wandonshi, ko kiranshi amatsayin boyfriend nata ma bataso ta tsani taji anyi, bakin ciki
da haushin shi yamasa tama kasamai reply kawai tajuya ta gefenshi zata wuce dan sometimes
idan abu is really annoying agareki rasama abinda zakace kake, kawai ji tayi yariko hannunta
“don’t go baby wait” wani irin juyowa tayi batai wata wata ba kawai ta daukeshi da mari jikake

tass! Wani irin ihu abokanenshi sukayi suna waige waige ko there’s anyone there dayaga Marin
datama Ahmad dan zai zama abin kunya ance wata tamari hiphop rapper. “Ke celebrity kika
mara” fizge hannunta tayi tana kallon yanda yadaura hannunshi kan kuncinshi yana wani irin
kallonta da idanunshi dasukai jajir dan marin ya shigeshi, rawa jikinta yafara da sauri tajuya
Ahmad daya bala’in zuciya yace “ku bita” jin haka yasa ta kwasa da bala’in gudu acikin parking
space din dababu kowa tana kalle kalle, kaman ance takalli right side dinta, hango wani dogon
mutum tayi yabata baya Awani lane na motoci yana tsaye jikin wata suv waya a kunenshi da
alamu waya yake, wani irin kwana tayi tana gudu tai lane din dayake batai wata wataba tana
kaiwa daidai inda yake batai wata wataba tawani zaga ta gabanshi ta shige kirjinshi at once
tana boye fuskanta akirjinshi jikinta ko’ina narawa sosai sabida tsoro yanda maza har biyu
komatace uku suka biyota, cikin Yar siririyan muryanta that is trembling sosai tace “please save
me…..plss…….I’m sca…….” tana maganan tana nishi da sauri da sauri dayake jinshi harcikin
fatan kirjinshi don fuskanta gabaki daya na wajen ne, daidai lokacin daga boys din Ahmad din
har Ahmad din dukansu sunzo wajen sun tsaya agabansu suna maida ijiyan zuciya sabida
gudun dasukayi, One by one mutumin ke binsu da kallo batare daya furta ko a word ba har
lokacin wayan nakan kunneshi bai cireba, faduwa gaban Ahmad yayi ganin fuskan mutumin
dake kallonsu, ahankali yajuya sadaf sadaf daso samune ko takalmin shi da kasan wajen karma
suyi motsin nuna alamun yana moving sanan ya yafito abokananshi da hannu yace “let’s go
guys” dasauri sukace “marinka fa tayi Boss” da saurinshi kaman ana hankadashi yawuce yace
“shikenan nidai natafi ku ku tsaya” ganin yanda yake tafiya da saurin bala’i tun bayan yaga
fuskan mutumin yasa suma sukasha jinin jikinsu suka juyada sauri suka wuce.

“Eh Gwaggo ina jinki sorry ba shareki nayiba, Abban nake jira nariga nakawo shi…” ahankali
tashiga dagoda kanta kaman wata mara gaskiya cikeda kunya jin mutum na wayanshi ta
tsokano fada tazo tafada jikin shi, kanta akasa ahankali sadaf sadaf tashiga fitowa tana
matsawa baya kafin gently kanta nakasa batare data kalleshi ba tace “thank you” sanan
ahankali tajuya tashiga tafiya har lokacin gabanta nafaduwa sosai. “You!” Taji kaman daga sama
mutumin yakirata chak ta tsaya batare data juyoba, “turn around” taji muryanshi anatse yet with
authority batasan mesaba amman kasa ketare abinda yace tayi tayi hakan yasa gently tajuyo
sanan ahankali tadaga fuskanta takalleshi, wani dogon saurayi ne fari sol dashi kaman balarabe
yana sanye da jumper na farar shadda bugaggiya kanshi babu hula gashinshi akwance baki
sidik sai kyalli yake hannunshi rikeda iPhone 13 yazubamata idanu dababu alamun wasa daidai
da digi acikinsu, hakanan jitayi takasa jure kallon mutumin dataga kaman ta sanshi amman ta
manta a ina ta sanshi ta sauke kanta kasa, anatse yace “the next time I will see you making
trouble I will arrest you!” dasauri tadago kanta ta kalleshi saida yafidi kalman arrest sanan police
din ranan yafado mata arai, dauke kai yayi daga kallonta sanan yabude kofar motan daya tsaya
jikinta ya shiga ciki tareda rufe marfin motan da sauri dayadan firgitata sanan ahankali tajuya
tacigaba da tafiya ahankali.



Samin kanshi yayi da binta da kallo ta madubin motan, yanda take tafiya ahankali har lokacin
bata dawo daidai ba, sanan ahankali yadauke kanshi daga kallonta jin wayanshi na ringing

again screen din yakalla ganin Grandma yasa yabude motan yafito yace “this woman will not
allow me leave in peace”.

Garden din takarasa tun daga nesa kawayenta dasuka hangota suka kwalamata kira hakan
yasa takarasa zuwa inda suke zama tayi sanan tadauki bottle na ruwan dake gaban Farida
tabude takai bakinta ta kwalkwale duk kallo suka bita dashi, saida ta shanye goran ruwan tass
sanan ta ijiye tana sauke ijiyan zuciya, Farida tace “daga ina kike haka duk kinyi zufa kaman kin
fito daga yaki” dan yatsine fuska tayi kaman bazatai magana ba ganin yanda suke kallonta yasa
tace “Ahmad na mara shine yabiyoni and someone…..” tadanyi shiru kafin ahankali tace “wani
mutumi yataimakeni” atare dukansu all the 5 friends sukace “wani mutumi” shiru tayi sai chan
tace “oho nima ban sanshi ba” dukansu dariya sukahau yi dasauri takallesu tace “me” hada baki
sukayi sukace bakomi, sharesu tayi kawai cus she doesn’t even feel okay batasan mesa ba,
duk suna zaune wata kawarsu tashigo eatery dagudunta tana haki tace “kufito kugani yan
sanda sun shigo school dinan anzo ana kwashe su Ahmad da Gang dinsu” dasauri Farida tace
“ke haba let’s go video it musashi a internet” dukansu tashi sukayi itama ta tashi tabisu suka fice
daga cikin garden din, van suka gani na police gaban wani eatry dake kusada garden din
dasuke ciki, dasauri suka karasa gaban eatry din student sun cika wajen suna kallon Van din
police, suna tsaye wajen dayay cha da mutane sukaga an fito da Ahmad da akasamai handcuff
a hannu an sashi a van din sai abokanen shi na dazsu dasuka biyota guda biyu saikuma wasu
guda biyu daban yan sandan sun fito dasu ana sakasu a van din saiga police man dinan shima
yafito daga eatry har lokacin yana sanye da kayan dazu farin shadda waya a kunenshi still,
hada idanu sukayi batasan mesaba jitayi gabanta yafadi dasauri ta sauke kanta kasa tareda
juyawa ahankali tamabar wajen bata kara juyowa ba kawai tai hanyar class nasu, daidai lokacin
ana shirin fara wani lecture kujera tasamu atsakiyan ajin ta zauna sanan tabude jakanta taciro
note nata da pen aka fara lecture ko kadan takasa concentrating batasan mesa ba she just
keep seeing police man face din da what happen today, gabaki daya all through da day har
yamma ita kanta tasan yau ba school tazo ba takasa natsuwa tunanin shi da komi yacika mata
kai, wuraren 5 na Yamma Adamu direba yazo daukan ta shiga motan tayi ahankali tace “Adamu
please kafara kaini Coldstone nasayi ice cream nasha saimu wuce gida” cikeda girmamawa
yace “to Miss Khairy” daura kanta tayi akan kujeran tajuyar da kanta tana kallon hanya tareda
fuzar da ijiyan zuciya, she just hope tanashan ice cream dinan sanyin shi zaisa brain nata yay
sanyi tadena all tunane tunanin datakeyi tun safe.


Agaban wani Babban joint na coldstone Adamu yay parking hakan yasa tabude motan tafito ta
shiga ciki, daidai wani Babban Jeep na shigowa wajen parking yayi kusa da Benz da Adamu ke
ciki, bude gaban motan yayi yafito ahankali wanan karan yana sanye da kayan yan sanda Rolex
din dake daure a hannunshi yakalla shidda saura, sanan yazaga zuwa boot din jeep din yabude
keken guragu yaciro ya ijiye ya maida boot din yarufe sanan yadawo bangaren baya yabude
motan wata kyakkyawan tsohuwa ce fara sol kaman balarabiya zaune abayan tasaka Riga da
zani irin na tsofaffi anmai dinkin Bubu kafafunta da hannayenta sunsha lalli, hannunshi
yamikamata batare dayace mata uppan ba hararanshi tayi tana kama hannun nashi tamike
tsaye da kyar tana masifa tace “idan kaga dama kai gaba dani dagayau

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login